Showing 6001 words to 9000 words out of 99653 words

Chapter 3 - SANADIN ACCIDENT COMPLETE BY FASMA

FASMA   

05 Jul 2024

14080

A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[8/17, 1:17 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

🅿️ 11__12
```Manzon Allah (SAW) yace ''Idan mutum yayi kiran matarsa zuwa shinfid'arsa sai taki zuwa ya kwana yana fushi da ita to mala'iku zasuyi ta tsine mata har safiya ''
Buhari da Muslim ne suka rawaito shi
```
Wasu motoci ne sunfi goma na gani se gudu suke ....
Oda suke yi mata amma ina bata ma jinsu tana can tana tunanin ta ..
Irin gudun da suke yasa d'aya daga cikin motocin wanda take tunkararta tayi qoqarin kauce mata amma inaaa seda ta bugeta jikake kiiiiiiiiii...
Wani razananna ihu Maysam tayi segata a qasa ta fad'i a sume.....
Cikin hanzari mutanen motocin suka fito kowa se rabka salati yake...
Amma shi wanda yake cikin motar da'aka kad'eta be fitoba yade zaro qafarshi guda waje kuma da alamu baze fito ba...se direban ne ya fito da gudu...
Wata kyakyawar mata fara me kimani shekaru 45 zuwa 50 ta fito daga d'aya daga cikin motocin ta iso har inda ACCIDENT d'in ya faru.se innalillahi ....takeyi...ganin yarinyar ta suma yasa ta bada umarnin susata mota su kaita hospital.....Sa
rauniya MARIYAMA kenan wacce ake cewa Fulani matar sarkin garin Damagaram wato ZINDER mace me tausayi ,,rikon amana ..hakuri .da kuma gaskiya ...
mazan naga sun tunkari ta da niyar d'aukanta
Cike da b'acin rai Fulani ta daka musu tsawa tace bakwa ganin mace ce da kuke famar d'aukan ta ....da sauri naga sun rusuna suna bata hakuri ..
Se a lokacin na qare musu kallo kayan jikin su irin na dogarai sarauta ne ......
Wasu mata nagani su ukku masu kaya iri d'aya da alama kuyangu ne ...da sauri cike da zafin nama suka dauki Maysam suka sakata a mota suka fice daga garin ma gaba d'aya ba tare da sunyi abunda ya kawo su.....
Direct masarautar su suka fice da ita dayake sunada clinik anan cikin masarautar dan haka emergency na clinik din aka kaita ...nan da nan Doctarori kwararru na clinik d'in suka ansheta dan ceto rayuwarta .....
Sunfi awa biyu tukon suka fito suna goge zufa...abin mamaki fulani na nan zaune tana jiransu ...
Nan suka rusuna suna kwasar gaisuwa ...
..
Damuwa qarara kwance a fuskarta tace Doc da fatan de bata mutu ba?
Doc Mansur yace muje office de...
Nan tabi bayanshi tare da kuyangu mata suna take mata baya ..
Bayan su zauna Doc ya fidda lunette(gilashin).
Yace sede kuyi hakuri yarinyar ta samu karaya a qafarta ...
Innalillahi ......fulani tafurtawa..tace yanzu ta farfard'o ..
Eh ta farfard'o da kyar sakamakon irin razanar da tayi amma kada ku damu ''elle est hors de danger''yanzu mun mata karin ruwa tare da allurar bacci koda zata farka se zuwa nan da 8hours kenan gobe da safe incha Allah...
Nan tayi godiya ta fice cikin gida ...
Bisa doguwar kujera ta falon yake a kwance ya malla'ka ''écouteur''(earpice).a kunnenshi.ya rufe ido kamar me bacci...dogo ne .fari ba irin sosai d'in nan ba ..yana da sumar gashi tare da saje yanada faffad'an kirji ...gashi da dongon hanci ..bakinshi kuwa irin kiss me baby nanne lol ......Prince MURAD kenan
Besan da zuwanta ba se jin kiran sunan shi da tayi ..
Tashi yayi zaune yace na'am Momy .tareda fidda earpice d'in.
Fulani tace yanzu abunda kayi ka kyauta kenan ?
Kicin2da rai yayi..kallo daya yayi wa kuyangi eh kuwar har rigay2 futa suke dan sun gane ma'anar kalon
yace to ni mi nayi ne Momy?
Au baka ma san mikayi ba ..?..jinake motarkace kuma kana ciki kuka kad'e yar mutane amma ko ka leqo ..idan fa da ta mutu ..kuma a haka kace kai docteur ne ....
Haba Momy jiya2 nanfa na dawo amma har kin fara gajiya dani ...kuma kun sani ba tun yau bana son zuwa hanyar qauyikan nan ..dan kullum inde nabi hanyar to se munyi ACCIDENT imma da mutum ko da dabba..amma kuka matsa keda me martaba da sena je
Kuma fa kada ku manta a wannan hanyar ce mukayi ACCIDENT din da yayi sanadiyar rasa qanwata ,,jinina ..rabin raina ''ma raison de vivre''sega hawaye sharshar yana futa daga idonshi ..
Fulani Tausayin d'anta ya ka mata ...ta dora kanshi bisa cinyarta tana goge mishi hawayen tace ya za'ayi na manta da tragic ACCIDENT d'innan wanda a SANADIN ACCIDENT d'in ne na rasa y'ata ....ga ciwon zuciya da Qanwata ta kamu dashi ...dama abubuwa da dama..sede muce Allah ya kai haske kabarinta.....ameen cewar Murad
Tashi zaune ya kumayi yace amma ni Momy a kullum zuciya na na bani bata mutuba ....a kullum ina ji ajikina kamar tana raye a wani gurin ..shiyasa bazan tab'a yin aure ba ...
Fulani tace haba wai bana hanaka fad'in kalman nan ba .......tun lokacin da abun ya faru kake fad'in haka..kuma kasan hakan baze ta tab'a yuyuwa ba..dan kuwa ko satin da ya huce seda me martaba yayi zancen aurenka tundade ka gama karuntun ka kuma har kana aiki...
Haba Momy nifa bazan tab'a yiwa Angel kishiya ba ..ita kad'e ce a duniya kuma haka ma a aljanna..
Momy tace kajiye mun yaro da shirmen banza ..to ina Angel d'in take ne?..itada bata ma doron kasa amma har kana wani baza kamata kishiya ba.....to tun wuri ma ka fidda wannan daga kwakwaluwar ka...
Bece komi ba ya tashi ze fita a palon yana fad'in bari na tafi mosque...
Girgiza kai kawai tayi ta shige rooms dinta...
Washe gari Maysam bata farfad'o ba se wajejen sha biyu na rana ..da Fulani tayi arba wanda.shigo warta kenan itada jakadiya ....
Da sauri tayi yunqurin tashi amma seta ji wani zafin bala'i a qafarta se a lokacin ta tuna abunda ya faru ....
Nan ta fara kuka qasa2.....jakadiya ta futa kiran docteur..... Fulani kuwa matsowa tayi kusa da ita tace sannu ya jikin..?
Da kyar ta'ya furta da sauki..
Ita Fulani a tunanin ta kukan zafin da qafarta take ...ita kuwa anata b'angaren kukan had'uwar ta da Murza take..abunda ya fara fad'o mata a rai shine ko ina shanun data fito kiwo suke......
Fulani ta katse mata tunani da fad'i kiyi hakuri kiyi shiru kinji tsautsayine inya wuni baya kwana ......tace ya sunanki ne?
MAYSAM kawai a takaice ta fad'a..
Fulani ta sake maimaita sunan tana shirin kara wata maganar ...
sega Doc ya shigo nan kwashi gaisuwa wurin fulani ..sannan yayi yan gwaje2 shi yace alhadulillah komi normal se karyar qafar kawai ...amma a bata abinci taci yana fad'ar haka ya fita a d'akin ...
Maysam tace karaya kuma na shiga ukku ni se kawai ta fara kuka.....
Ta kalli Fulani tace dan Allah baku ga shanun dana 'e kiwonsu ba...?
A'a fulani tace ..amma bari zan tura a gani ..yama sunan qauyen ku da a sanar da iyayenki kada suyi ta nemanki ....
Nan ta fad'i sunan tare da suna Malam Musa amma addu'a ce fal ranta Allah yasa a samun shanun....(baiwar Allah a memakon kiyi add'ar samun saukin ki amma ke ta shanu Murza kike...
..)
Fulani tace a memakon kiyi ta lafiyar amman ki ta shanu kike
Maysam tace shanun Murza ne..
Wacece kuma Murza?
Innata ce cewar Maysam
Bata qara cewa komi ba daga haka
Bayan kwana biyu tana jiyya nanfa hankalinta ya koma gida Alla2 take a meda'ita gida ..
Bayan docteur ya duba ta tace itafa qauyensu takeso a mayar da'ita .
Yace ai ko a barki ki koma senan da one week ..nan fa ta shiga kukan ita dole a kaita gidan
Suna haka sega Fulani da kuyangunta sun shigo tare da kulolin abinci...
Fulani tace ya akayi ne take kuka ...nan docteur ya labarta mata ..tace jeka abunka zanji da ita ..nan ya fita kuyangu ma sukayi waje ...
Fulani tace kiyi hakuri nan da satin nida kaina zan sa akaiki qauyen ku ..kuma na tura an sanar da innarki . cewa ACCIDENT kikayi kinanan
Wani kukan ta saki jin Murzace aka sanarwa ba Abbata ba ..tace nide dan Allah ku barni ta tafi dan walahi inna Murza dukana zatayi..
Fulani takalleta da kyau tace duka kuma bayan an sanar da ita bakida lafiya..
Se alokacin ta tuna subul da baka datayi ..
Fulani ta share mata hawayen dake zuba a idonta tace ko zaki iya bani labarin ki ....dan da alamu kina da damuwa gaki kuma yarinyar karama dake ...
Ganin irin kirki da kulawar da fulani ke mata yasa Maysam bata labarin rayuwarta amma ta b'oye mata ita yar tsintuwace...
Bakaramin tausaya wa fulani tayi mata ba har seda tayi kwalla bata sani ba ... Lalashinta tayi sosai harta saki ...ta bata abinci taci
.Maysam a ranta tace kamar ba matar sarki ba ko kad'an bata da girman kai...
Fulani tasa akayi mata gwanji HIV aka ga batada komi .....nan ta qara tabbatar da irin makirci na Murza
Bayan sati kuwa.ta murmure tayi kyau har wani shining take ...sosai fulani ke bata kulawa gashi har sun dan shaku da buna dan kuwa tana zowa dubata a kullum...
A b'angaren Murad kuwa ya koma England dan can yake aiki kuma a leqe bezo yaga yarinyar dasuka kad'e ..
Fulani tayi fad'a har ta gaji ta kyaleshi
A qauyen kuwa bayan kwana hud'u dayin Accident d'in Malan Musa ya dawo ya tarar da abun bakinciki dan kuwa.Murza ce mishi tayi Maysam ta gudu itada wani saurayin abokin karuwancinta ..kuma duka qauyen abunda.suke cewa kenan...alhalin Fulani ta turo dogarai an sanar da Murza da accident ne har aka bukaci ta biyo su amman taqi amman dan iya makirci ta shirya wannan qaryar..
Sosai hakalin Malan Musa ya tashi shide yasan qarya akeyiwa Maysam tsoranshi daya tana ina yanzu?
Nan ya fara kewayen qauyika na kusa dasu amma ko mekama da ita be gani ba yau har tsawon sati kenan..
Maysam kuwa sauki ya fara samuwa nan tace itafa a meda ita gida
..fulani batayi gaddama ba nan aka sallameta tare da alkawali za' a ringa zuwa diba ta har ta warke ..jakadiya da kuyangu biyu aka bata yan rakiya tare da d'umbun alheri harda keken guragu aka bata..
Kafin su fice aka kaita wurin me martaba sarkin Damagaram Alh MUSTAPHA sari me gaskiya dantako da adalci..ta kwashi gaisuwa sanan suka kama hanya wanda harda kukan rabuwa da fulani tayi ..ita ma a b'angaren ta fulanin bata so rabuwa da'ita ba...
Muje zuwa...
Fasma ce
Ahmed Gumel
[8/17, 1:17 PM] A A Dboy: POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ 📚📚
[8/17, 1:24 PM] A A Dboy: 🌹🌹 *SANADIN ACCIDENT* 💥🚑🌹🌹

🇳🇪Story&Written
by
*FASMA* 🇳🇪

🅿️ 13__14
*Sakon gaisuwa ta musamman zuwa ga y'an kungiyar mu Star writer's Ass hakika ina me farin cinkin kasan cewa cikin wannan kungiya* *Allah ya qara had'a kamu* ...
*Alherin Allah ya kaimu ku a duk inda kuke* :
*Queen baby* ( *in-law d'ina* )
*Momyn Mufeeda* ..
*Ummu*
*Hadjara Arfat .. ina sokon sosai* . _Allah ya bar zumunci_
Dedicated to All my Fans
13__14
```Manzon Allah (SAW) yace''Duk wanda baya tausayin mutane to shima Allah ba zaiyi masa Rahama ba''
Bukhari da Muslim suka rawaito shi``` .
Tafiyar awa biyu ta kaisu kauyen .
Maysam tunda suka tunkari unguwar su kirjinta yake ta fat2 tsoranta daya kar ace Malan Musa bayanan..
A kekenta na guragu kuyangun suka turota har tsakar gidan ...idan sukayi ta kwad'a sallama sega Musa ya fito daga bayi da buta a hunnu wanda besan lokacin data fad'i daga hunnunshi sakamakon tozali da yayi da Maysam ..
Da sauri harda d'an gudun shi ya qaraso wanjenta ya rumgumeta yan shafa kanta yana fadin yar Abba kece?ina kika shiga tsawon lokacin nan ?kisan kuwa irin wahalar neman naki danayi?
Itama qanqameshi tana kuka me game da dariya ..sun jima a haka sai da jakadiya tayi gyaran murya tukon ya san ashe da mutane a wajen.
Sakinta yayi yana kallon su yace ku kwa daga ina bayin Allah ...
Maysam tayi saurin cewa Abba ka bari ku gaisa mana ....
Taburma ya dauko ya shinfid'a musu ...ya kawo musu ruwan sha .suka gaigaisa ....
Jakadiya ce ta labarta mishi komi game da ACCIDENT d'in
Sosai ya tausayawa yar tashi har da kwalla ashe tana can tana jiyya Murza da yan qauyen sharri ne kawai suka kulla mata daman ya san haka kawai Maysam baza ta bar gida ba ...
Da zasu tafi Malam ya musu sha tara ta arziki duk da yasan sun fi qarfin abunda ya basu....
Murza na d'aka tana jin duk abunda suke fad'i a ranta tace ai walahi baza ki tab'a warkewa daga karayar nan ba ...gurguwa ma zan meda ke shegiya mayya ina jin dadi na rabu da ke ashe kika ce ina nan dawowa...tayi tsuka yafi a kirga ...(jifa se kace gurgunta mutum din a hanunta yake
.)
Wunin ranar har dare Maysam na bawa Musa labari irin kirkin da kulawar da Fulani ta bata ..shima ya labarta mata irin yawon neman daya yi mata...
Haka rayuwa tayi ta tafiya yau har tsawon wata guda idan Maysam yanzu sauki ya fara samuwa sosai ta murmure abunta har wata qiba tayi tana jin dadi rayuwarta dan kuwa Musa yanzu baya zuwa ko'ina yana zaune yana jiyyar y'ar shi har ta warke ...
Lokacin kuwa Murza had'e zuciya ne kawai batayi ba dan haushi taso yayi tafiyar kasuwancin shi dan ta samu damar idasa qafar Maysam.. ga aikin gida ita kad'e keyi Maysam na zaune sede a dafa a bata taci....
Zowan su jakadiya ma ukku dan duba lafiyar Maysam d'in....
.
Zaune yake a gaban me Martaba ya sadda kai kasa se bada hakuri yake
Fulani na gefen me martaba gefen d'ayan kuwa wata matace wacce za suyi sa'anai da Fulanin kyakyawa ce itama hjy MADINA kenan matar sarki ta biyu kishiya ga uwar gida hjy Maryama (mahaifiyar Murad) amma se wani yatsina fuska take kamar wanda taga kashi a wurin ..qasa2 kuma inta faki idon sarki seta zabgawa Murad harara..
Fulani na ganin duk abunda take yi batade ce komi ba dan idan sabo ta saba da hakan...
Sarki kuwa se fad'a yake yiwa Murad yace to walahi bari kaji na baka sati biyu ka fito da mata in kuwa bahaka ba zan aura maka wacce naga dama ..
Shide Murad hakuri kawai yake badawa..
Caraf Madina tace a d'an qara mishi lokaci de d'an nawane se da lallab'a cike da kissa tayi maganar ...
Murad beyi wani mamaki ba dan kuwa ta kware wajen makirci a gaban sarki zata nuna tafi kowa sonshi ...
Sarki yayi murmushi yace ai d'an naki ne bayaji yaune ake mishi magana d'aya ...
Ta qara cewa ayide mishi hakuri wannan gamun ze kawo ...
Kasa cewa komi yayi dan takaici ...
Bayan sun dawo bangaren Fulani nan ya dinga yiwa fulani kuka kamar qaramin yaro shifa bayason aure kuma bazeyi aure ba ...itade fulani lallashi take tare da yi mishi nasiha ranar a nan b'angaren ya kwana ...a zuwan washe gari ze koma wajen aikin shi..
.
Maysam kuwa sauki ya samu har tana d'an taka qafar ...
Ganin haka Musa yace zeyi tafiya amma a ranar ze dawo ..Maysam bataso ba amma ba yanda ta iya ..haka yayi sabko ya tafi..
Ranar Murza har zubda ruwa a qasa tayi tasha ...ko awa guda da futa beyiba Murza kwallawa Maysam kiran wanda seda gabanta ya bada ras tasan kiran Murza babu alheri cikinsa ..haka ta turo keken ta fito tace gani inna. ...
Wata dariyar mugunta tayi tace yau daga ni seke agidan nan(nace se kuma Allah ba) kiyi abunda na saki ki tsira ..bakiyishi dedeba jikin ki ya fanshe ki ...
Itade kallonta take batace komi ba..
Murza tace kaf aikin gidan nan yau kece me yinshi daga sharar garken shanu zuwa ta tsakar gida ..wanke2 girki .wanki d'oko ruwa a rafi....
Batace komi ba hakanan ta lallab'a tayi shara da wanke2 ...tana cikin jan ruwan wanki gugan ya kubce ya fad'a rijiyar ...
Wani uban dundun tayi mata wanda seda gantsare ta saki kukan wahala ..
Murza tace to kuwa tunda kika bari gugan ya fad'a seki fice rijiyar cikin gari ki d'auko ruwan..
Ta d'auko tulun kenan bisa tsautsayi shima ya kubce ya fad'i a bunka da laka daidaya tayi anan.....daman me karaya inashi ina iya dauko ruwa inba muguntaba ...
Murza bata tsaya b'ata lokaci ba ta fara jibgar ta daman da gangan tasata ..iya qarfinta take dukanta har Maysam ta fad'o daga keken aman wannan be sa Murza ta dena kishinta ba..
Cike da mugunta tasa qafa ta take qafar me karayar tana wani mummurza qafar har wani cije leb'e take irin na inkana yiwa wani mugunta ..
Wani quwa Maysam tayi se kawai tayi suman wahala ...tajata rana ta yar anan..(Allah sarki Maysam .)
Kan kace mi qafar har ta fara kumbura ...
A dede wannan lokacin sega su jakadiya suna rafka sallama a gidan jin shiru yasa suka leko daga zauren gidan ..ganin Maysam a yashe tsakar rana ga kuma babu alamun rai a tare da ita da gudu suka qaraso cikin gidan suna salati ganin irin kumburin da qafar tayi yasa suka d'auketa dan kaita likita..
Eh kuwa sega Murza nan ta fito nanfa tace babu wanda ya'isa yatafi mata da y'a ta fara musu borin hauka tare da zage2 hakan ya tunzura jakadiya ta kwallawa sarkin hukunci kira dayake tare suka zo ...
Murza na gani shirgegen qato fuskar nan murtuk ai da gudu ta shige daki ta kulle tana ihu b'arayi zasu sace Maysam wai anufinta ko makota zasuji ...
A guje suke tafiya tun a hanya jakadiya ta sanarwa Fulani abunda ya faru nan fulani ta dinga kiran doctarori kan kace mi duk wani kwararen docteur na garin me d'orin karaya ya zo clinik jiran iso warsu kawai ake...
Har suka iso Maysam bata farfad'o ba an shafa mata ruwa yafi a kilga aman shiru ....
Suna isowa aka kaita emergency nanfa doctarori suka dukufa neman ceto rayuwarta....
Seda suka shafe awanni tukon suka fito fulani na nan tana jiran fitowarsu kamar wancen lokacin....
Bayan sun kwashi gaisuwa d'aya daga cikin doctarorin yace alhadulillah munyi nasara aman a gaskiya yarinyar nan ta wahala dayawa kuma karayar ta dawo sabuwa har ma tafi ta farkon dan haka tana bukatar hutu a 100% ...yanzu haka mun mata allurar bacci ...da zasu tafi akayi musu biya me tsoka ..
.
Malan Musa kuwa be dawo gida ba se can cikin dare dan haka besan abunda ke faruwa ba .se washe gari yaga bega wulgin Maysam ba har goma tayi ya kasa hakuri yace waini Murza ina Maysam ta shigane ...
Kamar jira take ta saki kukan munafunci tace ai Maysam jiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login