Showing 33001 words to 36000 words out of 99653 words
ya shige itama tana ganin haka ta shiga ...suna gani ya shiga mota suma suka fara haramar shiga sauran motocin amma se ya daga musu hannu ya na nufin baya bukata .......
Ba karamin mamaki dogaran sukayi ba amma babu yanda suka iya haka suka dawo..
Har sun shiga mota yace ke wai bakida nikaf da safa ne?
Girgiza mishi kai tayi......
Dan jim yayi sannan ya tada suka tafi ...
Shopping mall ya kaita kayan kam babu irin wanda bata dauko ba kama daga lesh ,,,atampa ....daganan suka nufi bangaren turare da man shafawa ...ganin be dauki komi ba yasa ta dauki wasu mayun turare tare da mayyukan su da sabulunsu har kala biyar duk na maza se kuma irin set din na mata shima kala ukku...
Bayan sun gama layin nikaf da safa ya nufa ..ya jibgo mata yana fadin ko a school ne to ki tattabatar kin saka safar nan ...ehe...
Ita de to ne nata bayan sun gama ya kaita wurin wasan yara ...
Yana daga gefe se wasannita take a ranshi yace wannan ba aure ba aka mun raino de aka ban .....
Kai ranar yakaita wurare daban2 ..se la'asr likis suka dawo ..bayan sunyi sallah direct dinnig suka nufa dan sun kwaso yunwa......
Set din turaren nan kala biyu ta doko ta bashi tace naga baka sai komi ba shi yasa na dokoma...
ba karamin mamaki yayiba nan ya amsa tare da fadin ashe. de bakida rowa ..
Dariya tayi tareda rufe fuskar ta..
Shima dan murmushin gefen baki yayi ...
Washe gari kuwa sha daya na safe ma acan tayi musu inda suka bar dogarai da kuyangi zasu shigo motocin su dawo dan su jirgi suka biyo ,,,dukda yasha kauyanci wurin Maysam..dan ita jirgin ma se ranar tayi mishi kallon gaba da gaba ...
murna wajen fulani ba'a ma zancan girke2 iri2 tasa aka yi musu ...sosai taji dadin yanda Murad ya rage hantarar Maysam a daya daga cikin dakunan fulani Maysam ta sauka yayinda Murad ke nashi bangaren ...
Da dare bayan sun futa ta fito da turaren ruka ta bawa Fulani set biyun na mata da buyu na maza tace wannan naki ne keda dady ne (Sarki) se kuma wannan ta fiddo wasu set din iri daya guda biyu tace wannan kuma daya na Abbana ne dayan na inna Murza...
Zo kaga Murna wajen Fulani kamar wacce batafi karfin kayan ba ..nan ta ringa saka mata albarka..dan gaskiya taji dadi kuma ta yaba da hankalinta..
Shima me martaba ba karamin nuna jin dadin shi yayi ba tare da saka mata albarka....
Lokacin da aka jewa da Malam Musa da wannan alheri har kukan murna da jin dadi yayi ya saka mata albarka yafi cikin kwando...sab'anin Murza da bakin ciki saura kiris ya kashe ta wunin ranar tayi shine tana tunanin yanda zatayi da Maysam tsaki tayishi yafi sau a kirga a ranta tace wannan yana nufin kenan tana can tanjin dadin rayuwarta ko....?can tace kai wly da sakema wai abawa me kaza kai ....
Madina sosai ta sawa lamuran waziri ido ta baza bayinta ko ina dan ganin mi waziri ke barkatawa dan yanzu yama dena shigowa part dinta .. Aranta tace kowa yaci tuwo dani to miya yasha...
.
Su Murad kuwa Tunda sukazo tare suke yawo duk inda yayi tana binshi dare ne kawai ke rabasu ba karamar shakuwa da juna sukayi.ba....har Mahmud yana tsokanarshi da cewa kode ya fada tarkon son Maysam ne...
Shikuwa se ya yatsine fuska yace ina abunso anan dan farin nata ko dan dogon hanci da karamin bakin ze jani...yaja tsuka ...yace yarinyar da ko kirgen dangi ma bata faraba ina abunso a jikinta .....
So daya ne nakeyiwa Sweetbaby na..wannan itama tanacin alfarma fulani ne yo banda wahalar raino ma ba abunda nake....
Mahmud ya sheke da dariya yace gaskiya nawan ka iya tsara mutum .fa.....da wani ne na tabbata ze kama zancen nan...amma yo ai ko irin kallon dakake binta dashi ko makaho ze gane bare aka zo ga zancen kishi .....
Murad yayi kicin2 da fuska yace a'aa ya ishe ka hakafa inayin haka ne dan kare martabar aure tunda de an rigaya an auramin ita babu yanda zanyi ne...
.
A bangaren Maheeba kuwa ba karamin tada hankalinta ba tayi dan ita se yanzu tasan Murad yanada mata duk da taga yarinya ce karama aman kyaunta ya tsora tata...
Nan fa ta dagawa mahaifinta Waziri hankali .....babu yanda ya iya haka yayi shiri zuwa ga Murad da zancen.......
Zaune yake shida Maysam datake kan cinyarshi se wasa take da sajen fuskarshi tana dariya yayinda shikuma yake daddana waya a lambu ga kayan marmari cike a gabansu ...
Ganin waziri yasa Maysam sauka ta zauna a kasa kusa dashi...jin ta sauka yasa ya do kai ya kalleta seyabi inda take kallon ..tsinkayo waziri yayi yana magana da dogaran dake kofar shigowa lambu...
Iso akayi wa waziri ...bayan ya kwashi gaisuwa se kuma yayi shiru ...Murad ma shiru yayi mishi dan yan Mulkin sun motsa ..
Can Waziri yace ranka shi dade inason yin magana dakai ...
Hannu ya daga alamun ya fadi yana saurarenshi ...
Kallon wurin da Maysam waziri yayi ..cuwat ta mike zata basu waje..Murad ya dawo da ita kan cinyarshi ....
Waziri a ranshi yace tirkashi wata zufa ta karyo mishi .....
Can yace dama zancen wajen y'ata ne....ina son ka aureta ....
Ba Murad ba hatta Maysam da sauri ta dago ta kalleshi ...Murad ma kallon nashi yayi yace....
Wash kuyi manage da wannan...
Bansan haka masoyan wannan book din keda yawa haka ba ...a gaskiya ina alfahari daku Rabbi ya bar kauna da zumuncin mussaman yan group din HAUSA YOUNG NOVEL na facebook ..ina jin dafin yanda kuke nuna kaunar ku ga book din nann...ban manta da kaiba Ahmed Gumel ...godiya me tarin yawa Alherin Allah ya kaimaka a duk inda kake......sauran groups ban manta dakuba kusan ina yinku irin dayawan nan
...
Fasma ce
Ahmed Gumel
55__56
```
Manzon Allah (SAW) ya ce''me zuwa gyadar da marar lafiya ,ya kama wata hanya daga hanyoyin aljanna har yaje ya dawo''
Muslim ne ya rawaito shi``` .
Ba Murad ba hatta Maysam da sauri ya kalleshi....Murad ma kallon nashi yayi se kuma ya kalli Maysam wacce tuni yanayin ta ya sauya......
Ido cikin ido ya kalli waziri yace ''non je n'en ai pas besoin''(a'a bana bukata) wannan bashi ne karo na farko ba dakazo min da zancen auren y'ar ka amma ina son wannan ya zama na karshe .....yace kanacin darajar tsufan kane da wani ne da nasa an hukuntashi. .ya cigaba da fadin idan dama wannan ce maganar dakazo muye to kana iya tafiya na sallame ka ....
Waziri ba karamin mamaki yayi ba haka jiki ba kwari ya tashe ya zazzage wandonshi ya fice a ranshi kuwa fadi yake taya hakan ta kasance bayan boka ya jaddada mun yuyuwar hakan....har ya bar lambu yana tunanin wannan al'amarin ....
Yana tafiya Murad ya kalli Maysam dake cinyar shi duk tayi wani kicin2 da fuska duk da karanci shekarun aman taji zafin furucin waziri....
Yace yade yar gidan Momy ke baki san fushi baya miki kyaune ba .yanda fa kika son kunun safe kirtup din nan to haka kike in kinyi fushi.........
Babu komai ta ce mishi tare da yin haramar tashi daga cinyar dan inhar ta tsaya to zata iya fashewa kukan da ita kanta bata san dalili ba...
Dawo da ita yayi ....yace ke bason iskanci to mi akayi miki ne daza kiyi tawani turowa mutane baki ya shantu....
Dama me nema se kawai ta fashe mishi da kuka tare da tashi da gudu ta barshi nan ....
Shi abun ma mamaki ya bashi ....
Tashi shima yayi ya mara mata bayan.....
A palon fulani ya tarar da ita se kukan shagwaba take zubawa fulani kuma tayi2 ta fadi mata abunda ya sakata kuka amma taki fadi ,,,,se aikin rararshi take ....
Bata san da shigowarshi ba se jin gaida fulani .data ji..
Tsit kakeji tayi ,,,tayi saurin tashi tare da fadin Momy bari na shiga ciki
Tana shiga ba ko kunya Murad ya bita dakin ...
Abun ba karamin mamaki da birgewa ya bawa fulani ta bisu da addu'a kara samun zaman lafiya tare da kara hada kansu .tayi dan murmushi....
Shi kuma ya na shiga yaganta a kwance bisa gado tana kuka ciki2...bisa daya daga cikin kujerun dakin ya zauna yace ke taso kizo nan ...
Firgit ta tashi ta zauna tayi rau2 da ido ...
Yace ke wai bada ke nake ne ba ''viens ici''(zonan)
Jiki ba kwari ta taso tazo tana murza ido tace gani yaya...
Daga zaunan ya dauketa ya dorata bisa cinyarshi ya goge mata hawayen ....yace wai mi yasaki kuka..
Shiru tayi mishi ...
Can yace zaki sha chocolats ?
Ta girgiza kai alamun a'a
Yace to alewa fa?
Nan ma tace a'a
Ace cream fa?
Naman ta girgiza kai...
Yace to mikike so ?
Ta ce ba komi ....
Shikenan amman kukan nan ya isa haka kada ki jawa kanki ciwon kai...
Ta ce to......
Algyabar ya fidda mata yace to maza je kiyi wanka dan kiji dadi jikin ko kinaso na miki ne?
Kamar da wasa tace e'e...
Be tsaya bata lokaci ba ya fidda mata kayan suka shiga tolet din ya wanko ta tas ya dado ta a towel .....
Koda ya fito ya lura duk kayan jikin shi sun bace da ruwa komawa yayi tolet din kafin yace ki tabbatar kin saka kayanki kafin na fito .sanan ki tafi dakina ki dokomin kaya comlet guda......dan baze iya fita da kaya a jike haka ba ..kuma shi baze bari har su bushe a jikinshi ba....
yana fitowa ya ganta kwance bisa gado bacci ya kwashe ta Abunka da sauran kuka....
Allah yasoshi akwai irin rigar wankan nan a tolet din kuma tanada tsayi dan har ta fice mishi guiwa .......
Abun takaici yama rasa yama zeyi ...shima gadon ya hau ya kwanta kan kace mi bacci yayi awon gaba da shi...
Ta rigyashi tashi ya saka kayanta ta dau wayarshi ta fara game abunta dan ita tama manta da wani doko ishi kaya.....
Tana tsaka dayi kiran Mahmud ya shigo batayi wani dogon tunani ba ta dauka tayi sallama tare da fadin ina kwana yaya Mahmud....
Cike da jin dadi ya amsa nan ta dunga zuba zance
Hayaniyar ta tadashi daga baccin ...da sauri ya anshe wayar ya kara akunnen shi jin Mahmud se ya kashe wayar...ya zare bata ido yace waya baki izinin daukan wayata ne...
Ganin ya fara hayayyakoo mata yasa tayi kalar tausayi tace kayi hakuri bazan kara ba....
Bece komi ba ya fara dube2 ko ze hango kayann...can yace ke ina kayan ne....
Wani waro ido tayi tare da fara yarfe hannu tace kayi hakuri na manta ne ...
To kuma yanzu mikike jira ?
Da sauri ta mike tayi hanyar fita ...
Dakatar da ita yayi yace ke haka zaki fita .babu hijab..
Kallon jikinta tayi riga da jupe ne na atampa....
Da sauri ta dawo ta dauka ta fita tana gungunin shi wannan yaya cikin bangare dayan ma se mutun ya saka hijab...
Bata ankara ba taji yace ke uban miye kike cewane?naji kamar kince yaya....
Jikinta har bari yake baki na karkarwa tace cewa fa kawai nayi kai yayan nan nawa akwaishi da kirki2...
Murmushi kawai yayi dan yajita sarai.......
Kayan ta kawo mishi se kuma ta tsaya ...
Ya kalleta yace ke fice mun a daki ko kina tsaye zan sa ne...
Turo dan karamin bakinta tayi tace to ni shine ka kalleni hakanan harda yi mun. Wanka ...to nima kawai ka saka ina nan ..kaga kenan mun joje ko...
Wani kallon bakida wayo yayi mata yace ke ni sa'an wasan kine?ina wasa da kene?
Dariya ta kyalkyale tace to shikenan ni na tafi ma....
Ta fice abunta tana fadin ma hadu ne the next time...
Shikam yanzu mamakin kanshi yake yanda yake sake mata ...baya ma iya mata fada sosai....zuciyarshi tace kawai de kanayi ne saboda farin cikin fulani ne....se kawai yayi na'am da hakan....
Yana gamawa direct inda yasan ze samu Mahmud yayi ....,ya koci sa'a yana nan..bayan sun dan gaigaisa irin ta abokai..se kawai Mahmud ya kwashe da dariya yace kai mutumen kana bada wuta fa....
Cike da rashin gano mafitar hakan yace kamar yafa?
Mahmud yace a'a ba komi naga yar raino ce harta fara taya bacci ya fadi cike da zolaya....
Wani dogon tsuka mtsssss yaja yace kaifa dan iskane .....towai ma idan ma hakane miye na sawa mutum ido ne?gwauro da kai amma ka iya sa ido...dan Allah a daure ayi aure ko sa ido ze ragu...
Kwashewa da dariya Mahmud yayi yace shikenan zance Maysam ta samo min yar reno kamarta kaga se mu gamu mu reno su ko.....
Ganin abun ya fara zama iya shege yasa Murad fadin idan zaka fadan dalilin kiranka to ka fadan odan kuma ba haka kaga tafiyata...
Gimtse dariyar shi Mahmud yayi yace shikenan ...nan suka firar su ...ganin haka yasa na fiyo ta marawa Waziri baya shima
.
A bangaren waziri kuwa kasa fadawa diyarshi abunda ya faru yayi ..se kawai yace ta shirya itada mahaifiyar ta su rakashi wani gu...
Basuyi wani musu ba suka shirya han suka kama hanya ...suna tsaka da tafiya ya gaya musu komi har Maheeba zata fara bambami waziri yace a'a tsaya ai yanzu haka wajen boka zamu daku kuji mike faruwa da kunnenku...
Ajiyar zuciya Maheeba tayi tace yauwa Sekayi Abbana....suka tafa itada uwarta.......
Suna isa basu wani ji tsoro ba duk da cikin daji ne ga datti ga komi....
Suna zuwa kafin ma su zauna Boka ya sheke da wata karuwar dariya .....bayan sun zauna se kuma yace na san mike tafe daku ba sekunyi bayani ba Dan mutanen mu sun sanar damu komi....hahahahha....
Ya cigaba da fadin ku kwantar da hankalin ku ...yaron ya zo muna da taurin kai seda muka sha jinin jarirai ukku amma. Shiru...shiya sa zamu biyo mishi ta bayan fage
Kude ku aje hankalinku gu daya ku saurara Sarki da kanshi ze yi maganar auren idan kana so kuma zama ka iya dan turzawa ka gani ....shi da kanshi zece se anyi aurennnn....
Maheeba tawani kwashi shoki daga nan zaunan tace se kayi Boka aikin ka yana kyau.waya ganni a garakal mulki...hhhhh..
Boka ya cigaba da fadin muna bukatar jarirai ukku daya fari,daya baki da kuma masara (yan japon,),,se kuma jinsi shanu suma haka ,,,rakumma kuma na saudia ...
Caraf Mahaifiyar Muheeba ta carafke da fadin wannan ai se ku yankan wuka zade mu bada kudi se a tura akawo ......
Gyada kai Boka yayi se kuma yace wani hanzari ba gudu ba ...
Dam gabansu ya bada...
Yace se kunyi taka tsan2 kada ku bari asirin nan akar yashi ....da kuwa kai da ke ya nuna waziri da matarshi yace idan ya karye komi ze iya samun ku dan haka ku kiyaye.......
Dariya naga sunyi sukace hakan bazama ta faru ba...nan suka zube mishi makkudan kudi suka tafi cike da farin ciki.da ......
A hanyar su ta dawowa ...Muheeba tace Abba ai mun mance da wannan matar tashi me kama da aljanu ai da mun gama ta da boka itama...
Waziri yace ki kwantar da hankalin ki ki bar batun yarinya keda mulki ne ze kaiki mi gaminki da ita iya kacin ta de ki bata oder kuma dole tabi...
Ee fa hakane Abba ....nan sukayi ta hirarakin su har suka iso..
Fulani kuwa ganin Maysam tana son koyon girki yasa ta sakata a makarantar koyon girkin har na tsayon wata daya wanda zeyi dede karewarta dede fara Azumin Ramadan ..dan acewarta tana yiwa Maysam kwadayin ta samu ladan aure a wannan wata me albarka koda ko iya girkin ne da gyara gida zatayi.....
Kan kace mi tuni ta fara kwarewa dayake akwai ta brain....tun tana taya fulani dan ita take shiga cuisine din da kanta ta dafawa sarki abinci inde har ita takeda girki a cewarta mulki baze hanata samun wannan ladan ba.. kai akazo wani sa'in ma Maysam ita take musu girkin ....
Ana haka har watan azumin Ramadan ya kama.....
I love you all
Fasma
Ahmed Gumel
[9/2, 9:57 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ ππ_*
[9/2, 10:00 AM] A A Dboy: πΉπΉ *SANADIN ACCIDENT* π₯ππΉπΉ
π³πͺStory&Written
by
*FASMA* π³πͺ
π
ΏοΈ 57__58
```Manzon Allah (SAW) ya ce''ku kawata mazaunanku da yin salati gare ni ,lallai salatinku gareni haske ne a gare ku ranar Alkiyama''
Hakimu ya rawaito shi.```
Ana haka har watan azumin Ramadan ya kama....
Gaba daya Maysam ta koma bangaren Murad kwana kawai ke kawo ta bangaren fulani....
De temakon bayinta take yin komi ...shi har mamakinta yake dan kuwa yanzu ta koyi komi kama daga shimfidar gado komin girmanshi gyaran daki ,wanki tolet kam ko wata babbar se haka ...
Tare suke shan ruwa suyi buda bakin su tare bayan sallar trawi kuma ta dawo ta tayashi hira ..kai atakaice de sun dan shaku ,,dukda har yanzu sweetbabyn shi na nan makale a zuciyar shi hasalima yanzu ya na jan Maysam jikin shi ne dan tana tsananin kama da ita ko shagwabar ma gani yake iri dayace kai wani zubin mantawa ma yake cewa wai Maysam ce a gabanshi dan jinshi yake kamar yana tare da sweetbaby .......shiyasa ma duk wata mugunta hanttara ya dena mata har Mahmud yana tsokar nar shi dan kuwa kusan duk futar da zeyi tare suke yi da Maysam idan
Kuwa wajen abokanen shine to se ya barta a cikin mota ya kunna mata game ya bata ......
Azumi kam tun tana jin wuyar shi har ta saba yanzu dayake acan garinsu bawani yi take ba Murza bata ma barinta a cewar al'adar qauyen seka fara menstrue ko kuma anyi maka aure sanna zaka fara duk da de ita inde har Malan Musa na gari to kuwa ze tadda ita tayi......
A kwana a tashi ba wuya yau har azumi ya kai biyar ....bayan sallar la'asr Murad ya shigo gaida fulani bayan sun dan taba hira fulani ta kalleshi tace wai ya najika shiru har yanzu ne....
Ya dago kai yana kallonta da alamar tambayta kwance a fuskar sa yace wani abun ne akayi ....
tabe baki Fulani tayi tace kana nufin baka san akan mi nake zance ba?
Cike da shagwaba yace to ni ina zan sani ne ?
Shikenan to zancen kai sucre(sugar)ne gidan sirrin kanka ne a bisa al'adar garin nan idan azumi ya kama to duk wani saurayi ko magidanci zeyi kokari ya kai sucre gidan surikin shi ....
Gyada kai yayi yace shikenan zuwa gobe zan saka akai musu .....
Caraf fulani ta katse shi da fadin kai ya kamata ka kai da kanka dan hakan yana cikin al'adar kuma yana nuna ka mutunta