Showing 48001 words to 51000 words out of 99653 words

Chapter 17 - SANADIN ACCIDENT COMPLETE BY FASMA

FASMA   

05 Jul 2024

14076

kan tana son dan karamin bakin nan ..shiyasa ma yake biye mata ..
Maysam na ganin haka ta kauda fuskar ta gefe.
juyota yayi .yana kallonta
Ta kuwa rumtse idonta kam
Jin an tsaya yasa ya fasa dan yana da tabbacin sun iso wurin shopping din daya bada oder akawo su...
Maysam kam hamdala tayi ganin ya fasa dan ita tana ganin kazantar yin hakan....
Haka suka wuni yana kaita wuri2 a takaice de yau Maysam ta gama wa garin kallo ....se daf da magarib suka dawo inda suka tarar da labarin abunda ya samu waziri .......
.
Wato bayan futar su da kamar awa guda SARKI yane mi Waziri tate da sauran yan fada....
Shi kam lokacin ji yake ko an bugo kati ne ma..da sassarfa ya amsa kiran..
Fada tayi tsit kaf makaraban fadar sunan nan zaune jiran jin abunda me martaba zece dasu ....da farko se da yayi mu su nasiha tare da jan hankali..can de ya sanar musu cewa an fasa auren nan ...
Be gama rufe bakiba Waziri yayi cuwat tare da fadin to baka isa ba ....aure kamar an yi shi an gama..
Nan aka fara kallon2 ..
Sarkin hukunci har yayi wata irin wawura ya iso gaban wazir jiran umarni kawai yake..ya zartar
Fadawon gaba daya suka shiga bawa Sarki hakuri
Gyara murya sarki yayi fadar tayi tsit banda waziri daya ke fadace2 kamar wani sabon kamu...se wani fizge2 yake..
Da karfin tsiya aka zaunarshi amma bakin nan ya kasa rufuwa .....
Shiru akayi ana sauraron shi ..wai kun san mi fans?
Gaba daya sirri shi dana Madina ya shiga tonawa kaf duk abunda sukayi seda ya fada da irin makircin da sukayi ...kan kace mi fadar ta kacame da hayaniya..
Gyaran murya sarki ya karayi bacin rai karara a fuskar shi ya bada umarnin da aje a tsare waziri har se an yi bincike akanshi ...dan abun nashi ba sauki da alama ma ya fa haukace...
Lokacin da labari ya isa ga muheeba sumanta biyu da kyar ta dawo normal ...ga rashin cikar buri .ga waziri ya haukace abun ya game mata biyu ..mahaifiyar ta ma banda jimami babu abunda take..
To fa Abangaren Madina kam dadi kasheta ne kawai beyi ba dan ita jitake aikin bokan su ne yaci ....ranar kam bayinta ma sun san tana cike da murna ,,...tace kowa yaci tuwo dani to miya yasha harni ze ci amana ta kadan ma ya gani....
Sede tashin hankalinta guda ..shine yanda waziri yake fallasa asirinsu amma dayake ta jima tana makirci babu wanda ya zargeta ...dan tana nuna tana son Murad a gaban mutane so babu wanda zeyi tunanin ta aikata hakan... Gashi kuma an sheda cewa waziri ya samu tabuwar hankali da wannan take kwantarwa da kanta hankali..
Murad kam beyi mamaki ba dan dama yasan akwai wata a kasa ..Sede yayi addu'ar Allah ya qara kare su daga sharrin masu sherri.
Haka rayuwa tayi ta tafiya yau sati cur da faruwa wannan al'amari amman jikin waziri se gaba yake yi kai yaneu har da bugo ma ya fara ..
Bayan bincike me zurfi da sarki yasa akayi mushi a ka gano irin makircin da waziri da iyanlanshi sukai amma abun bakin ciki ba'a gano nasu Madina ba ...haka aka yanke wa su Maheeba hukunci barin garin itada su waziri bayan an yi musu horo me tsanani itada Mahaifiyar ta...
Haka suka fito daga masarautar da kullin kayan su Miheeba se waiwaye take tana ma masarautar kallon karshe..Mahaiyar Muheeba fadi take duk ke kika jawo muna da baki kwallafa rai ba da duk hakan bata faru ba ..dama boka yace kada mu bari asirin nan ya karye ka irin ta nan yanzu mahaifinki ya haukace..
Muheeba kam kukan ta na rashin aure nan ne takeyi aka ma bata kawo da rashin lfy waziri .....keken naped suka shiga ze kaisu aรฉroport su shiga jirgin zuwa ghana wajen dangi su...dan sun kwaso kudi..
Suna tsaka da tafiya ..abunka da mahaukaci ya faki idon su ya karkata musu sitiyarin ..naped dun ..jikake katsam..sun gamu da wata babbar motar .....
Kuyi manage da wannan ..
Fans nasan kuna min uzuri aman ku kara akan nada ....ina yinku irin more totaly din nan..
Fasma ce
[9/2, 10:16 AM] A A Dboy: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ ๐Ÿ“š๐Ÿ“š_*
[9/2, 10:41 AM] A A Dboy: ๐ŸŒน๐ŸŒน *SANADIN ACCIDENT* ๐Ÿ’ฅ๐Ÿš‘๐ŸŒน๐ŸŒน

๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ชStory&Written
by
*FASMA* ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

๐Ÿ…ฟ๏ธ 73__74
```Manzon Allah (SAW) yace'kumya tana daga cikin imani'
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
```
Jikake kwatsam sun gamu da wata babbar mota .......
Me babbar motar ya kuwa tsere ya barsu nan ...
Gaba dayan su a sume suke ...da kamar minti goma me a dedetan shi ya fara farfadowa cikin ikon Allah be ji wani ciwo sosai ba se dan gurje kafa dayayi ...Muheeba kam da wani irin taratsi ta farka ...ganin ta nan shaye a kasa komi ya dawo mata ...kuka ta shiga rerawa gashi tana son tashi amma ta kasa wani irin radadi takeji a kafarta da fuskar ta ...hannu ta kai ta shafa fuskar wani razannan ihu ta saka jin wani bala'in zafi ga kuma jini ya bata mata hannun..
Wannan ihun shi yayi sanadin farfadowar Mahaifiyar ta ........
Ita kam da alama bataji ciwo ba itama se karayar data samu a hannu ...rarafowa tayi kusa da Muheeba ..nan suka shiga rera kuka .....ganin duk glass ya yanyakewa Mufeedar fuska kuma da alama kuma ta samu karaya a kafar hagu.....me adedeta kam fada ya shiga yi musu sun san mahaukaci ne miyasa zasu shigar me a dedeta ..nan ya dinga bala'i kan se sun biyashi adedetar shi.dan baze dsuki asara ba....
Ganin abun bana karewa bane yasa suka bashi. kudi me yawa .dan sun kwaso kudi ..ba ko kunya ko tausayi ya karbe a bunshi ...da kyar ma ya dan ja adedetar ta bar titi ..yayi tafiyarshi...
Can Muheeba ta lura da waziri fa baya numpashi iya karfinta ta ce Abbaaaaa ..tana kokarin jan kafar ta isa...Maihaifiyar tata ta daure da sauri ta isa kusa da shi tana fadin waziri2 amma ina baya ko motsi .....daya ke sun kusa eareport din shiya sama babu gida je nan kusa ...baya ta koma cikin gari dan neman temako.....cikin sa'a ta gamu da wani me adedeta ...shima da farko ya so kin daukar su amma seyaji tausayin su ga kuma kudi me yawa da zasu bashi in de har ya kaisu cikin gari...
Da kyar ya iya saka waziri a motar ...suma suka lallaba suka shiga ...
dede wata clinik ya kaisu yana ajesu yayi tafiyar shi dan ma kada ace se yaje police station yayi reporte. ..
Dayake abun na masu kudine nan danan aka anshe su akayi emergency da su ...akayi musu dorin karaya da duk wanin abun da ya dace...tare dayi musu allurar bacci dan su sami hutu...
Lokacin da suka farfado daki daya aka kaisu..bayan doctor ya shigo ya kara dubasu har ze fice Muheeba tace ya jikin Abbana...
Seda ya share gumi tukon ya fara yi musu nasiha sanna ya sanar musu cewa waziri ya rigaye mu zuwa gidan gaskiya Allah yayi mishi cikawa se de kuyi mishi addu'a dan har an bunneshi ..
Wani irin ihu Muheeba ta saka se kawai ta sume nan..
Tashin hankali mahaifiyar ta shiga ga Mutuwar miji ga diya ta sume se kawai ta shiga rera kuka itama..
Can zuwa dare ta farka babu wata addu'a sema kiran Abbata datakeyi ..nan mahaifiyar ta shiga lallashin ta ....
Tana kuka take fadin duk nice sila da ban nuna ina soba da duk haka bata faru ba gashi yanzu SANADIN ACCIDENT na rasa Abbana wanda na fiso ...ga kafata ta karye ..kaico na ni Muheeba naga rayuwa .
Mahaifiyar ta shiga lallashin ya itama tana me tausaya wayar tata..
.
To fa a bangaren Madina da Murza ba karamar murna sukayi ba dan duk ji suke aikin bokansu ne yaci...Murza harda zuwa yi mishi godiya tare da kara mishi kudi daga Madina..se kuma suka fara shirye2 yanda za suyi asirin ya kama Murad..
A bangaren su kuwa rayuwar jin dadi suke ...yana kula da ita matuka wai saboda Fulani taji dadi yake yi a cewar zuciyarshi fa....
Tana cika sati ta fara shiryen2 komawa ecole ..wannan gamin ma seda ya rakata har Maradin .
Lokacin da zuyi bankwana shi ze dawo dan so yake washe gari shima yayi ficewar shi England....
Suna mota a aereport se shagwaba take mishi ..shi kuma se lallaba ta yake kan ta yarda suyi tafiyar su England ....
Da farko har ta amince amma jin wai in ta tafi baza ta cigaba da karatun ta yasa tace ta fasa zuwan ..wai rayuwar can da nan ba daya bace...itade jinshi kawai take...se turo dan karamin bakinta take ...dan tana son karatun ta..gashi a islamiyya ma sun yi nisa
Batayi aune ba taji Oga Murad ya shiga kissing dinta ....
Tureshi take amman kamar batayi .dan mayen electric shok din nan se ratsata yake..shima wannan karon dauriya kawai yakeyi .....tun tana jin dadin abun har yazo bakinta banda zafi babu abunda yake yi mata. .
Kokarin tura hannushi yake cikin rigarta(ni kuwa nace to mi ka aje ne a wurin kaida kace babu su
...)...
Rike hannun tayi tana girgiza mishi kai kukan ma ya kafe..
Amman shi kam se kara turashi yake ...
Ganin ana shirye2 fara kiran ma su tafiya yasa da kyar ta rabashi da jikin ta se haki take tace nide gaskiya2 ...se kuma tayi shiru..dan azahirin gaskiya bazatace ga abunda take jiba
Yana mede numpashi yace kede gaskiya mine?
Cike da yarinta da tsoro tace nide bana son wannan abun muryarta har sarkewa take
Kuri ya kafeta da ido yace miye din bakya so ...
Tace kawai se ayi ta durawa mutum miyau gashi bakin ma se zafi yake mun...
Jim yayi can ya kalleta yace bade ba kya so ba..
Ta gyada kai..
Yace shikenan bazan kara yi miki ba..
Cike da yarinta kuma ta fada kanshi tana Merci beaucoup yayana(thanks alot)..
Goshinta ya ma kiss sanna ya fita ...ya nufi wurin da ake kiran passengers...
Tana daga mishi hannu har jirginsu ya daga ...duk kuma se taji ba dadi
Driver ya dawo da ita school dinsu . suka hade da kawayenta nan suka shiga revision'(review)din karatun su dan shugaban makarantar yace inde har sukayi kokari suka kawo maki excellent to ze yi musu tsallaken Ss2 direct kawai suje Ss3 ..dan haka sun dauri niyar yin karatu na ban mamaki ..
Haka Murad ya dawo jiki ba kwari dan be ji dadin abunda Maysam tace mishi bs. .....
Tun nan aereport din ya ciri ticket zuwa England gobe...
Yana zuwa ya sanarwa da fulani f......fatan alheri tayi mishi
Zuws dare kuma Yana sanarwa da me martaba zancen tafiyar Madina ta shigo karaf se akkunan ta ...
Wata dariyar mugunta tayi ta koma bangarenta...
Jakadiyarta wacce tayarda da ita ta bawa magani a turara mishi..tace tayi maza ta tafi yanzu kan ya dawo daga wajen sarki
Cikin sa'a kuwa bata sha wuyar shiga bangaren Murad ba. ..nan ta turara tafice abunta..
Yana shigowa ya shaki kamshi .nan ya fara jin kanshi yana juya mishi tare da wani irin ciwo..sunan Allah ya shiga kiran ..se yaji abun ya lafa amma mi se yaji duk garin ma ya ishe shi ...gaba daya Allah2 yake gari ya waye ya tafiyarshi ...baccin kirki ma beyiba
Garin na wayewa dama jirgin 9h ne ze bi ..dan haka tun takwas ya shiga yayi wa Fulani da Sarki sallama ...ya fice cikin sauri..
Fulani kam wanna karon ma a jikinta taji kamar ta hanashi tafiya .amma se ta bishi da addu'ar Allah ya tsareshi ya kareshi da duk wani abun cutarwa daga mutum ko aljan..
Madina dadi kamar ta mutu ..se boka ta ke zumbudawa albarka...(hum .)....
Bayan sati da faruwar haka.. Da dare Sarki da matanshi suna hira dan kullum su se zuwa dare suke samun ganin shi. ..
Fulani tace dama akwsi wsta shawara dana keson badawa ....
Sarki yayi dan murmushi yace ai ke duk dhawarar da zaki bada me amfani ce dan haka kafin ma naji miye na amince ...
Fulani ma dariyar marar sauti tayi dan tana jin dadi irin confidence da sarki ke yi mata..
Madina wacce ta kullu jin furucin sarki tayi kwafa tare da yi tsaki kasa2 a ranta tace shiyasa a kullum tsanarta tske kara ruruwa a zuciyata. Se shegen iya kissa dan inta na wuri sarki mantawa ma yake da akwai wani a wujen ko a'a..shiyasa take mata lakabin makirar mace..dan gani SWEETBABY ma renonta ce kafin Accident shi ya sama Murad ya Makalkale mata ya kasa yakiceta daga rayuwarshi..(jifa wani sharri )
Sarki yace ina sauraronki
Fulani tace dama cewa nayi in baka zabi wanda zaka sa a matsayin wazirin ka mi ze hana a nada Malam Musa mahaifin Maysam ...
Sarki yace kamar kin shiga zuciyata kin gani nima haka nayi wannan tunanin ..
Fulani tace to ai dama ni cikin zuciyarka nake shi yasa na gani . tanayi tana wani sakin sharme...a tare suka saki ma juna murmushi..
Kutttttt wani malolon bakin ciki ya ziyarci zuciyar Madina ..ta daure de tayi gyaran murya dan ta hago wanni abun ..
Itama cike da irin tata kissar tace wannan shawara tayi ..ina goyon bayan hakann.......
Washe gari kam Madina ta sanarwa da Murza cewa sun kusa dawo wa nan dan haka sesu ci karansu ba babbaka..
3 jours(days)da yin maganar Sarki ya tura sakon san ganin Musa ...
Babu bata lokaci ya ansa kiran ..Murza kan se murna ake za'a kaura birni..
Bayan ya iso sarki yayi mishi bayanin kiranshi ...da farko ya so ya kiya amma se yaji baze iya cewa sarki a'a ba dan haka ya amince..ba karamar murna sarki yayi ba..
Kafin sati ya zagayo har sn nadashi sun kauro masarautar....
To fa Murza a masarauta kusa da Madina ..se yaya kenan..
Love you all irin more din nan

Story&Written
by
*FASMA*
*Alherin Allah ya kaiwa masoyan wannan book din a duk inda kuke ..hakika* *ina jin dadin comment din ku kuma yana bani kwarin guiwa ...daya wa naga sakon ninku..wasu* *suna cewa ina jan aji da rai ..to bahaka bane muma muna da uzuririka a gabanmu .....Allah* *ya bar kauna da zumunci ina yinku iri more totaly din nan*
*Pls masu juyamun littafi ku dena bana so . ...kun san kanku base na tona ku cikin jama'a ba so tun kafin abu yayi nisa ku fasa ....*
Dedicated to all my fans
75__76
```Manzon Allah (SAW) ya ce''babu d'a'a(biyayya)ga kowa cikin sab'on Allah''
Bukhari da Muslim suka rawaito shi.```
Murad kam fushi ya dauka da Maysam ..ga zuciyar shi na azalzalarshi kan ya kira ta amman yayi biris da ita seda yaji ta fara mishi zut2 din nan sanna ya kira office din ..lokacin sun gama lecture kenan ...
Da sallama ta amsa .. Tu nan yaji wani mayen sanyi yaji a zuciyarshi amma wani bangare yana tunatar dashi cewa yayi fa fushi da ita .. Dan haka
Amsa sallamar yayi a dakile kamar ba shine ke daukin kiran ba.
Cikin sanyi jiki ta gaishe shi tare da tambayar ya aiki. .
Da kakkausar murya yake amsa mata fada2..
Maysam ta sake cewa yaya mi akayi ne ?ko nayi maka wani laifine,?
Cike da kaguwa cikin fada yace au baki ma sani ba shikenan..yana fadar haka ya katse kiran..
Gaban Maysam ya bada dam ta fara tunani ...ji take kamar tayi kuka dan ita bata san lefin ta ba kuma gashi shi be fada mata ba...
Har ta juya zata fita ya sake kiran dan zuciyar shi ta hanashi sukuni tana ayyana mishi cewa Maysam na can na kuka ..shiyasa ya kasa resister ya sake kira..
Tana dagawa taji shine yayi sallama bata jira taji me ze ce ba ta saka mishi kuka....
Tirkashi nan ya dafe setin zuciyarshi yana fadin why nayi mata fada gashi yanzu na sakata kuka..beyi aune ba yaji kwalla ta cika mishi ido..da kyar ya daure ya rarrashe ta ...
Maysam tace shikenan amma yaushe zaka dawo nayi missing dinka fa....
Dan jim yayi dan shifa baya ma jin ze dawo kasar..
.
Yace ni kaina bansan ranar dawowata ba kai inaga ma bazan kara dawowa ba ...
Bata kawo komi ba dan ta zaci dan ya tsokane ta ne kawai dan lokacin daza suyi bankwana ya jaddada mata baze yi 3months ba ze dawo shi ya sama bata dau abun serious ba...
Zata sake jefo mishi wata tambayyar ya katseta da fadin kin ga se anjima inada aiyuka ...be jira mi zata ceba ya katse kiran dan kwata2 ma baya son ta mishi zancen.......haka ta koma aji jiki ban kwari dasu Maheeba suka tambayeta ganin mood din ta ya sauya aman se cewa tayi ai bata jin dadi ne...
Sarki kuwa ba karamin dadi yake jiba kasancewar Malam Musa wazirin shi ...
Lokacin da labari ya isa kunnen Maysam harda kukan dadi tayi tace gashi yanzu SANADIN ACCIDENT ta samu gatan da ba kowa ke sa'an samun shi ba..da tana cikin 'KUNCIN RAYUWA(littafi na na gaba in sha Allah).na azabar Murza aman yanzu...ta samu Mahaifiya wato Fulani ..ga karatun boko da islamiyya. Gashi kuma yanzu anyi wa Abbata Waziri.ita kam in bata godewa Allah da wannan ni'imomin ba dayayi mata to mi zatayi ...har Fulani ta kiraya ta shiga yi mata godiya har seda ran fulani ya soma baci tukon ta dena..
Haka rayuwa tayi ta tafiya inda zuwan Murza ya kara sa zuciyar Madina kara yin baki yanzu bata da wani buri na taga Murad ya mutu...sabon boka ma yace mata hakan bame yiyuwa bane amma taki hakura kullum da irin plan din datake shiryawa....
Murza kam ta zama tabarya me baki biyu ko nace me fuska biyu ma ..dan yanzu tana yawon shiga bangaren fulani tana nuna mata ta shiryu ta dena abunda take alhali tsegumi ne ke kawota dan ta kai wa Madina rahoto. ..duk abunda ta gani ko taji a bangaren fulani to seta gayawa Madina shi. Amma har yanzu ba'ayi katari taji Fulani ta kirayi Murad a gabanta shi yasa suke kara jin dadi .
Basu san duk safiya se Fulani ta kirashi a waya ba ...kuma kullum seta nemi ya dawo amma se ya fara kawo mata kabli da ba'adi ..kullum cikin yi mishi addu'a take .
Ita kam Madina zuwan nan Murza yayi mata dadi tana samun information akai2..
.
A banagaren su Muheeba kuwa bayan sun ji sauki amma fa fuskar ta bata dedetu ba duk tayi wani tabo2 babu kyan gani ...
Kullum cikin kuka take ganin haka yasa Mahaifiyarta ta cira musu ticket zuwa wajen danginta na Ghana ..(safe journey du Muheeba Allah ya raka taki gona )
A

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login