Showing 18001 words to 21000 words out of 87802 words
k'ofar d'akinta ta rufe tana isa tsakiyar parlourn ta samu cushion ta zauna tana danne danne cikin phone d'inta da Yaseer bai jima da siya mata ba, tayi nisa cikin danne dannenta saiga sallamar Yaseer ya shigo cikin parlourn ahanzarce ta amsa masa cikin k'auna da shauk'in so mik'ewa tsaye tayi ta iso wurinsa ta amshi briefcase d'insa tana jifarsa da kallon soyayya murmushi Yaseer ya sakar mata yana lumshe fararen idanunsa tareda shak'ar daddad'an k'amshin turarenta, cikin wani irin salo dake narkar da zuciyar masoyi Fauzeeya ta sassauta murya cikin tattausan lafazi tace"welcome back my dream".
Yaseer yayi murmushi yace"yauwa".
Atare sukayi masauki saman cushion yayinda Fauzeeya ta sake mik'ewa tsaye ta nufi wurin frizer tire ta ciko masa da kayayyakin motsa baki ta kawo ta dire agabansa ta zauna gab dashi suna jin numfashin juna, da kanta ta tsiyaya mishi ruwa cikin kofi ta mik'a masa cikin yanga tace"sha ruwa kaji sanyi masoyina"..
Yaseer ya amshi ruwan yasha yayi gyashi yace"Alhamdulillahi kamar ko kinsan ina jin k'ishirwa sosai".
Fauzeeya tayi fari da idanunta cikin kissa tace"haba yah Yaseer taya za'ayi zuciyoyinmu su zamo makusanta juna amma ace in kasa gano abinda kake buk'ata hmmm ka sani soyayyar da nakeyi maka tafi k'arfin wasa".
Yaseer yace"na fahimci haka tuntuni shiyasa na baki babban matsayi azuciyata".
Fauzeeya ta rausayar da kanta cikin shagwab'a ta k'ara matsowa kusa garesa kamar zata shige masa cikin jiki, k'afafunta suna gugan nasa kashe masa ido d'aya tayi tace"kardai in cikaka da surutu muje kaci abinci kayi wanka".
Yaseer ya kalleta cikin fara'a yace"to bari dai in fara yin wanka kafin inci abinci".
Ya tashi tsaye yayinda Fauzeeya ta dubi k'yak'k'yawar fuskarsa wadda ke k'ara narkar da zuciyarta cikin sonsa da begensa tace"ya naga zaka tafi ko inzo in tayaka wankan ne?".
"ki barsa kawai nagode idan mukayi aure zaki iya tayani kinji babyna".
"shikenan ba komai".Inji Fauzeeya.
Yaseer ya fice daga cikin parlourn direct room d'insa ya nufa ya cire tufafinsa ya d'aura towel a k'ugunsa ya fad'a cikin bathroom, ya jima yana wanke jikinsa sannan ya nufi daga cikin toilet d'in ya zauna saman gadon yana shafa lotions ajikinsa, jalabiya ya ciro daga cikin wardrobe ya zura ajikinsa silifas ya sanya a k'afafunsa ya jawo k'ofar d'akin ya dawo cikin parlourn.
Yana zama saman cushion Fauzeeya ta dubesa tace"to muje kaci abinci tunda ka gama wankan".
"OK muje d'in".Yana k'arasa maganarsa ya mik'e tsaye Fauzeeya tana gaba yana binta abaya itace tayi masa jagora har dinning table, suna isa taja masa kujera ya zauna itama taja kujerar ta zauna serving d'insa tayi ya fara cin abincin da spoon, Fauzeeya sai kallonsa takeyi ta wutsiyar idanunta tana murmushin farin ciki da murnar yadda ta samu shiga cikin zuciyarsa farat d'aya.
Yaseer kansa yana noce k'asa sai cin abincinsa yakeyi atsanake har ya k'oshi ya cika kofi da ruwan lemu yasha rabi ya ajiye sauran yace"babyna wannan girkin naki yayi dad'i sosai ya kamata in baki tukwici".
Fauzeeya tayi murmushin dake bayyanar da hak'ora tace"kayyy yaya ka daina fasamin kai wannan irin santi haka?".
"ba wani fasa kai sai gaskiya babyna".Sanya hannunsa yayi cikin aljihunsa ya zaro kud'i masu yawa ya mik'a mata Fauzeeya ta girgiza kanta tareda nok'e kafad'a tace"kabar kud'inka yaya basai ka biyani ba".
Yaseer ya kalli cikin k'wayar idanunta yace"ba biyanki nayi ba my Fauzee k'yautatawa ce kinsan ita zuciya an halicceta dason mai k'yautata mata da k'in duk wani mai munana mata".
Fauzeeya ta marairaice fuskarta cikin tsananin tausayi da soyayyarsa wadda ta riga ta wanzu da kwaranya cikin jini da k'ofofin jikinta tace"nasan da haka amma da kabar kud'inka ka k'ara cikin lalurar gida ai".
Da wasa ya harareta yace"ce miki akayi banida kud'in da zanyi lalurar gidana ne? Idan baki amsa ba zamu iya samun sab'ani atsakaninmu".Yace rayuwarsa ab'ace.
Ganin rayuwarsa ta b'aci yasa Fauzeeya ta amshi kud'in ahannunsa cikin kunya da ladabi tace"nagode sosai ubangiji ya k'ara d'aukaka da bud'i na alkhairi".
"Amin amma ki daina yimin godiya my Fauzee addu'ar ma ta wadatar".
"to yaya kayi hak'uri bazan sake ba".
"karki damu bakiyimin wani laifi ba".
____________________
Safiya ce zaune cikin katafaren shagonsu itada Nazifa suna zantawa akan yadda zasu k'ara habbaka cigaban business d'insu, Anwar yana gefe yana lura da mutanen dake shigowa cikin shagon suna siyen kayayyaki.
Ledar tsire ce agabansu suna ci suna korawa da maltina alokacin ne Nazifa ta dubi fuskar Safiya tace"Safiya kinsan wani abu?".
"sai kin fad'a Aminiyata".
"hmmmmmm dana koma gidanmu jiya da dare in gaya miki da safe Abbana ya kira mahaifin Yaseer sukazo gidanmu aka shiryamu, sai gani gabansu suna jefomin tambayoyi akan abinda ya samu fad'a nayi tsuru tsuru alamun rashin gaskiya ya bayyana k'arara afuskata shiyasa akayi saurin gano banida gaskiya ".
Safiya ta bushe da dariyar k'eta tace"amma Nazifa ke k'aramar shed'aniya ce duk iskancinki ashe kinada tsoro kamar farar kura ".
"kina wata magana daban Safiya ai idan bama Abbuna yana gudun b'acin ran mahaifiyata ba da kashina ya bushe wallahi banida mai cetona ahannunsa ".
"ashe babanki ba baya ba wurin tsauri da kafewar zuciya".
"hmmm bari kedai Abbuna kaifi d'aya ne baya tab'a chanza maganarsa idan ya furta ".
"Nazifa kinada agabanki idan kika sake yin yaji fa saboda haka ki rufawa kanki asiri komai zakuyi kuyi atsakaninku kada ki sake yin yaji domin gujewa fitinar mahaifinki ".
Nazifa ta musk'uta cikin yanayin takaici tace"idan har bai sake marina ba bazanyi yaji ba amma ki sani muddin ya sake marina dole inyi yaji saboda niba jakar gidansu bace!".
"Allah ubangiji ya sawwak'a Nazifa".
"Amin k'awata".
**********************
*BAYAN KWANA BIYU*
Alhaji Taheer mahaifin Yaseer da kansa yaje gidan Alhaji Mu'azu mahaifin Nazifa ya sanar masa abinda ake ciki, Alhaji Mu'azu bai nuna damuwarsa ba duk dayake yasan d'iyarsa ce za'ayiwa kishiya farin cikinsa ya nuna afili, ya koma cikin gidansa ya shiryo suka fito abokansu biyu suka kira suka shiga cikin mota suka nufi hanyar unguwarsu Iya Kulu kwatancen da akayi musu sukabi har suka iso bakin k'ofar gidan Iya Kulu mai tsamiya.
Suna parker motarsu suka kira wani yaro yayi musu sallama da Iya Kulu yaron ya juya ya shiga cikin gidan bada jimawa ba saigashi ya fito yace musu ance su shiga cikin gidan, fitowa sukayi cikin natsuwa da kamala suka shiga cikin tsakiyar gidan da sallama, baba Labaran dake zaune ya amsa musu tareda yi musu barka da zuwa zazzaunawa sukayi saman tabarmin dake shimfid'e awaje ga kayan motsa baki nan jajjere an aje agabansu, gaggaisawa sukayi cikin mutunci da dattijantaka sannan suka koro bayanin dalilin dayasa suka zo baba Labaran yayi na'am da maganarsu nan da nan ya amince da buk'atarsu suka biya sadakin Fauzeeya nan take dubu hamsin, sannan aka saka bikin aure nan da watanni uku, daga baya su Alhaji suka d'an tab'a cin abubuwan da aka kawo musu sannan suka mimmik'e tsaye sukayi musu sallama baba Labaran yayi musu rakiya har wajen motar sannan ya juyo ya dawo cikin gidan, suna shigewa cikin motar Alhaji Taheer ya tadda motarsa suka nufi hanyar zuwa gida cikin farin ciki da murnar yadda iyayen Fauzeeya suka amshesu hannu bibbiyu cikin girmamawa da karamci............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 12*
Saida suka aje abokaninsu k'ofar gidajensu sannan Alhaji Taheer yakai Alhaji Mu'azu har gidansa tareda yi masa godiya mai tarin yawa, nuna masa yayi babu komai ai anriga an zama d'aya sukayi musabaha da juna Alhaji Taheer ya juyo ya dawo cikin gidansa ya gayawa hajiya Sadiya duk abinda ake ciki, hak'ik'a tayi matuk'ar farin cikin wannan maganar domin tasan d'anta zai kasance cikin kwanciyar hankali da farin ciki mara misaltuwa, agabanta Alhaji Taheer ya kira wayar Yaseer ya gaya masa duk abinda ake ciki tabbas Yaseer yayi matuk'ar murna da farin ciki fiyeda tunanin mai karatu saboda yana cikin matsanancin halin da yana buk'atar mace da kulawa na musamman arayuwarsa.
Sun jima suna tattaunawarsu awaya sannan daga k'arshe sukayi sallama da juna cikin murna da sanyin zuciya.
Tun daga lokacin da aka rana iyayen Yaseer suka fara shirye-shiryen auren d'ansu yayinda itama Iya Kulu tana can tana nata shirye-shirye domin ganin tayi gwargwadon abinda take iyayi, haka awurin ango Yaseer tuni yayi sayayyar abubuwa masu yawa kunsan abu ga mai kud'i babu wuyar yi, duk da Nazifa taga yana siyen kayayyaki tareda k'ara gyara gidansa hakan baisa tayi tunanin zai k'ara aure ba, koda yake agabanta ko magana basayi da juna amma idan ta fita zuwa shago yinin rannan soyayya zasuyi ta bugawa kamar su lashe junansu, dayake su Sameer yara ne ko agabansu suna firar soyayya amma basu iya gane komai saboda wayonsu baikai can ba.
********************
Fauzeeya ce na hango zaune tana mopping d'in parlour yayinda yau Nazifa bataje ko'ina ba saboda batajin dad'in jikinta, fitowa tayi daga cikin room d'inta cikin yanayin rashin lafiya ta dawo cikin parlourn ta zauna, Fauzeeya ko kallonta batayi ba bale tace mata ya jiki saboda tsananin kishinta da takeyi sannan kuma kwata kwata Nazifa batada mutunci batasan daraja da kimar d'an Adam ba, cigaba da mopping d'in takeyi harta k'arasa saiga Yaseer ya shigo cikin parlourn.
Yana shigowa idanunsa suka fad'a cikin na Fauzeeya murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa da martani yace"sannu da aiki Fauzeeya gaskiya kina fama da ayyuka da yawa ya kamata in samo miki mai taimakonki".
Cikin guguwar so tace"a'a nagode aiba wasu ayyuka bane masu wahala nakeyi ba ina iya yinsu gaba d'aya batare da mataimaki ba".
"kin tabbatar da zaki iyayi bamu takura miki ba?".
"na tabbatar yaya karka damu".
"to shikenan tunda kin fad'a da bakinki zaki iyayi ba damuwa".
"OK yayana".
Tun lokacin da suka fara maganganunsu Nazifa tayi shiru tana mamakin ikon Allah bak'in ciki da kishin mijinta ne ya bayyana k'arara afuskarta, zuciyarta sai tafasa da zogi takeyi mata cikin zafin rai batare dasun ankara da ita ba ta tashi tsaye tana kallon fuskar Fauzeeya ta k'araso wurinta batayi wata wata ba ta d'auketa da gigitattun maruka biyu masu rad'ad'i da zafi azuciya, asanadiyyar haka saida Fauzeeya ta gurfana k'asa ta fashe da kuka dafe da kuncinta!.
Yaseer yayi sauri d'ago idanunsa cikin b'acin rai da k'unar zuciya yace"mi tayi miki da zaki mareta Nazifa!? ".
Huci tayi kamar kumurci cikin suyar zuciya da son fitina tace"na mareta Yaseer! Akan mi zata tsaya tana magana dakai agaban idona wato dama idan bana nan abinda kukeyi kenan to Allah ya tona asirinku babbak'un munafukan Allah! ".
Cikin b'acin rai Yaseer ya kalleta idanunsa har chanza colour sukayi jajir jijiyoyin kansa suka mik'e tsaye rud'u rud'u cikin tsantsar takaici da bak'in ciki yace mata"kinga Nazifa kiyimin shiru banason maganar banza! Da kike cewa ta dainayi min magana wannan ai zancen banza ne kulawa kike bani ko shagonki kike kulawa dashi?To bari kiji Fauzeeya ba baiwar gidanku bace saboda haka nayi miki kashe mai tsauri karki kuskura ki k'ara d'aga hannunki ki mareta idan ba haka ba zanyi miki abinda baki zato ko tsammani! ".
Nazifa ta rik'e k'ugunta cikin raini da walak'anci tace"akan wannan karuwar yarinyar zaka zo kana d'agamin murya to ko gobe ta sake yi maka magana saina mareta! Kuma baiwar gidanmu ce saboda mahaifiyata ta d'auko min ita daga matsiyacin gidansu ta kawomin ita domin ta dingayimin wasu ayyukan gida".
Yaseer yayi mata walak'antaccen kallo yace"mahaukaciyar banza ke atunaninki wannan abin da kikeyi kishi ne?To tsabar hauka ne irin naki kuma kinyi kad'an ki hana mana magana da juna baki isa ba".
"kaine baka isa ba Yaseer saboda ni nakeda iko da Fauzeeya a k'ark'ashina take idan ka nemi gayamin ba dad'i sai in koreta ta koma gidan ubanta Labaran, wanda bai aje komai sai tarin tsiya da talauci! ".
Yaseer ya wurga mata harara yace"tun yanzu kije ki koreta idan gidanki ne Nazifa ai kin riga kinyi *SAKACI* arayuwarki muddin akaina ne babu abinda zakiyi ki burgeni ko kiban sha'awa".
"aiba son nake in burgeka ba domin bakada wata daraja da kima awurina! ".
Hak'ik'a yaji matuk'ar zafin kalamanta har cikin jini da jijiyoyin jikinsa numfashi ya saukar mai tattare da bak'in ciki da k'angin rayuwa yace"tabbas kin nunamin bakida mutunci da sannu zaki gane kurenki Nazifa zaki gane yanayin rayuwa yana iya chanzawa akowane lokaci saboda haka kibi duniya asannu".
Nazifa ta tashi tsaye taja tsoki mtsssssss tayi masa kallon k'asa da sama ta tofar da miyau tace"bazan bi duniya asannu ba kuma ka sani daga kai har ita sainayi maganinku acikin gidan nan azzalumai kawai marasa tsoron Allah ".Tana kammala maganarta taja k'afafunta fuuuuu ahasale tayi cikin d'akinta cikin matuk'ar b'acin rai da tafasar zuciya.
Tana ficewa daga cikin parlourn Yaseer ya saukar da doguwar ajiyar zuciya cikin lallashi da tattausan lafazi ya kalli Fauzeeya yace"kiyi hak'uri my Fauzee duk nine naja miki wannan maruka alokacin dana shigo cikin parlourn ban lura da ita ba kinji".
Fauzeeya ta d'ago idanunta da sukayi jajir akan kuka murmushin dake b'oye damuwarta tayi tace cikin k'auna da soyayyar gaskiya "ka daina bani hak'uri yaya Yaseer wannan ba komai bane illa k'alubalen da muka fara fuskanta nida kai, ka sani duk abinda matarka zatayimin bazai tab'a girgizani ko ya razanani akan in rabuda kai ba soyayyar da nakeyi maka yafi gaban kwatance, saboda haka na baka amanar zuciyata ina fatar kaima *SOYAYYAR GASKIYA* kakeyi mini bazaka tab'a cin amanata ba".
Yaseer ya langwab'e kansa cikin k'aunarta yace"bakida wata damuwa matuk'ar muna tareda juna ki sani ruwa ko iska basu isa su rushe soyayyar dake tsakaninmu ba,nayi miki alk'awarin idan mukayi aure zan rik'eki amana da baki tsantsar kulawa da soyayyar gaskiya ".
"naji matuk'ar dad'in zancenka ubangiji yabarmu tare".
"Amin my Fauzee tafi d'akinki ki kwanta ki huta nasan matakin dazan d'auka akanta! ".
Fauzeeya ta b'ata fuskarta cikin sagarci tace"dan Allah yah Yaseer ka k'yaleta karkayi mata komai matuk'ar akaina ne ".
"ba komai na hak'ura kinji".
"nagode da kayimin wannan alfarmar ".Tana ida maganarta taja k'afafunta ta nufi cikin room d'inta ta kwanta saman gado hawaye masu zafi sai sintiri sukeyi saman fuskarta cikin tsananin damuwa da tausayin kanta.
Zaune Yaseer yayi saman cushion zuciyarsa cunkushe da bak'in ciki da tsantsar damuwa domin abinda Nazifa tayi masa yayi matuk'ar sanya b'acin rai da takaici azuciyarsa kallo d'aya zakayi masa ka gano yana cikin matsananciyar damuwa.
____________________
Da safe misalin k'arfe takwas daidai Yaseer yayi breakfast ya fice daga cikin gidan ya nufi office d'insa yayinda Nazifa har tayi wanka ta shirya cikin shaddarta doguwar riga taji aiki, ta kawo handbag da mayafinta ta rataya a kafad'arta fitowa tayi daga cikin room d'inta ta dawo cikin parlourn ta zauna.
Tana zaune tana karkad'a k'afafunta cikin gadara da tinkaho ta k'walawa Fauzeeya tace da k'arfi "Fauzeeya! Fauzeeya!! Fauzeeya!!! ".Har sau uku tana kiran sunanta.
Fauzeeya tana zaune cikin room d'inta taji ana k'wala mata kira da sauri ta mik'e zumbur tsaye afirgice ta fito daga cikin d'akin ta iso gaban Nazifa ta gurfana tace"gani Aunty ".
Wani irin matsiyacin kallo ta jefeta dashi cikin isa da kashedi tace mata "keee dan kutumar ubanki yanzu kikaji na kiraki ko? Ki saurareni da k'yau daga yau kada ki in k'ara ganin ko kallon fuskar mijina kinyi bale har kiyi masa magana idan ba haka ba akan mijina zan iya kasheki kibar duniya! ".
Afirgice Fauzeeya ta d'ago fuskarta domin ta gasgata abinda Nazifa ta fad'a cikin k'wayar idanunta ta hango rashin mutunci da kishin mijinta kwance kallo d'aya tayi mata ta tabbatar zata iya aikata abinda ta fad'a, jikinta amace saboda ta gama tsorata da lamarin Nazifa tace "kiyi hak'uri bazan k'ara ba".
Nazifa tayi k'yafci cikin masifa tace"kima sake kiga mummunan hukuncin dazai biyo baya saboda haka ki kiyayeni tun kafin ki riski kanki cikin kabari idan kunne yaji gangar jiki ta tsira! ".
Fauzeeya ta jijjiga kanta alamar gamsuwa da maganarta tace"to Aunty".
"ba wani to Aunty kinji dai abinda na gaya miki idan ba kina shed'aniya ba taya za'ayi ki dinga shisshigewa mijina salon wannan manyan boob's d'inki da hives suja ra'ayinsa ya aureki, wato adole ke gaki kin balaga kinsan dad'in maza ko to abi wasu mazan badai mijina ba! ".Tana kammala maganarta taja k'afafunta ta nufi hanyar fita daga cikin parlourn direct wurin parking lot ta nufa.
Fauzeeya tana gurfane ta saki rikitaccen kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro taji kukan motar Nazifa ta fice daga cikin gidan gaba d'aya, kuka takeyi tana shassheka kamar zata shid'e wani irin d'aci da k'unci ne ya tokare mata a mak'oshinta ji takeyi gwamma mutuwa da wannan k'azafin da Nazifa tayi mata, saida taci kukanta ta k'oshi sannan ta lallashi zuciyarta ta mik'e tsaye ta nufi cikin kitchen domin ta girka abincin rana.
Tuwon shinkafa da miyar alayyahu ta dafa miyar taji naman kaza k'amshin girkinta duk ya gauraye cikin gidan gaba d'aya, tana kammala girkin ta juye abincin cikin babbar kula miyar kuma cikin k'aramar kula kwashe kulolin tayi ta jajjera saman dinning table ta dawo kitchen ta had'a musu coconut drink takai saman dinning table ta aje sannan ta juya ta fad'a cikinroom d'inta domin tayi wanka...........
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special