Showing 69001 words to 72000 words out of 87802 words
ya nisa yace"wannan shine tarihin rayuwar Munari idan kaji zaka iya aurenta ka aureta amma ka sani kowa ya d'ebo da zafi ya sanyawa bakinsa".
Baba Labaran yayi shiru na mintuna kad'an can yaja nannauyar ajiyar zuciya yace"hmmm gaskiya naji dad'in yadda ka sanarmin halayyarta amma fa inason aurenta ahaka".
Safwan yayi saurin kallonsa afirgice cikin matuk'ar razana yace"shikenan tunda kaji ka gani zaka iya aurenta ubangiji ya sanya Alkhairi".
"Amin Safwan nagode sosai nizan koma gida".
"to ba komai Labaran".
Baba Labaran ya dawo gida ya cigaba da harakokin gabansa tareda share maganar da Safwan ya sanar masa ababin rayuwarsa, shirye shiryen aurensa ya cigaba dayi yana gyara d'akin dazai saka amarya itadai Latifa tana gefe tana kallon ikon ubangiji saboda tayi matuk'ar mamakin yadda ya chanza mata gaba d'aya, wato inda ace bata tab'a haihuwa arayuwarta ba da tozarci da k'ask'ancin sai yafi haka itadai tana k'ara godiya sosai ga ubangiji daya bata k'waya tak aduniya taga wasu da yawa suna neman haihuwa da kud'insu ahannu ruwa ajallo amma ubangiji bai basu, shiyasa take daurewa tana danne bak'in ciki da damuwar dake cunkushe azuciyarta saboda bata fatar ta tashi tabar 'yarta guda ahannun kishiya.
Baba Labaran ya tura magabatansa gidansu Munari nan take aka yanke musu sadaki suka biya sannan aka saka sati uku ranar aure, sunyi abin cikin matuk'ar mutunci da karamci sannan magabatansa suka d'ungumo suka dawo gida fuskarsu asake cikin murna sun sanarwa baba Labaran duk abinda ake ciki yayi musu godiya sosai cikin farin ciki da tsagwaron son haihuwa da yawa.
Bayan sati uku aka d'aura auren Munari da baba Labaran aranar assabar mutane suka shaida d'aurin aurensu, anyi aure lafiya mutane suka kama gabansu da dare aka d'auko amarya aka kawota gidan mijinta,adaren ranar baba Labaran da amaryarsa sun gwangwaji amarci fiyeda misali domin Munari ba baya wurin bak'ar jaraba da son haraka.
Washegari da safe suka fito manne da juna Latifa tana kishingid'e saman pillow zaune atabarma itada d'iyarta Fauzeeya suna karin kumallo,ganinsu yasa Latifa ta duk'ar da kanta k'asa domin kada idanunta suyi tozali da abinda zai mata barci cikin dare, har abakin garka Munari ta rakasa bayan ya fice Munari ta juyo ta komo cikin tsakiyar filin gidan gab da zata wuce kenan taja tsoki mtsssssss tace"walak'antattar banza yanzu kika fara shiga k'unci da uk'ubar rayuwa acikin gidan nan matuk'ar ina cikinsa! ".
Kalamanta sun soki k'ahon rayuwar Latifa amma babu yadda ta iya saboda sai bango ya tsage k'adangare ke samu wurin shiga, dayake bata iya fitina ba ta musk'uta tace"duk makirci da tuggun da zaki shiryamin ubangiji yana kallonki ".
Munari ta rike kwankwasonta cikin matuk'ar tashin hankali da son masifa ta wurga mata harara tace"auuu na zata kinada bokan dazai iya miki magani ne? Amma na fahimci baki abakin kowa wurin miji kin mayarda kanki jaka ballagazar mace".
"naji bana iyawa kinji tafiyarki d'akinki ".
"bazan tafi ba saina tsefeki daga bindi har wutsiya".
Latifa bata sake tanka mata suka cigaba da karin kumallonsu babu abinda zuciyarta keyi sai suya da tafasa, Munari tsaye tayi tanata balbalin masifa bakinta ko tsayawa hutawa ba yayi, saida taci taci sannan taja bakinta ta tsuke ta shige cikin d'akinta.
Tana shigewa bada dad'ewa ba saiga sallamar baba Labaran ya shigo faram faram tsakiyar filin gidan da leda rike ahannunsa Latifa tana zaune yazo ya wuce da aleda agabanta kazil baice mata ba ya shige cikin d'akin amarya Munari,Fauzeeya ce ta shagwab'e fuskarta cikin kurciya tace"Inna baba ya gifto ta gabanmu bai baki naki leda ba ko bai ganmu bane?".
Latifa tayi nishi mai tattare da d'acin rai tace"bai lura damu bane ki bari anjima idan kikaje wurin Iya Kulu zata siya miki duk abinda kike buk'ata ".
Ta marairaice fuska tace"to Inna".
Shafa kanta tayi cikin k'auna ta deb'e mata majina tace"yauwa d'iyar albarka karki damu komai na duniya yanada iyaka kinji wata rana sai labari ".
Fauzeeya ta jijjiga kanta duk dayake bata fahimci inda maganar Innarta ta dosa ba tace"uhmmmm".
Aranar baba Labaran ya siyo k'unshin nama aleda suka cinye tass sukayi gyatsa ko kad'an basu ragawasu Latifa, sannan suka rungume junansu cikin so da tsantsar k'auna sunata yin abu guda.
Ahaka rayuwar Latifa ta kasance cikin gidan atakure cikin matuk'ar tsamgwama da bak'in ciki arayuwa, saboda babu irin walak'anci da tozarcin da baba Labaran baya mata rayuwar Fauzeeya ta taso ne cikin damuwa da fuskantar tsantsar *RASHIN SO* awurin mahaifinta, tun bata fahimci cewa mahaifinta baya k'aunar mahaifiyarta ba har tazo tasan komai dayake ko agaban idanunta cin mutuncin Latifa yakeyi tareda haddasa mata tashin hankali da fitinar rayuwa, gashi babu wanda zata tunkara da wannan maganar domin iyayenta sunsha yi mata nasiha da hak'uri arayuwa shiyasa take daurewa tana b'oye damuwarta ga mutane.
Wata rana Iya Kulu ta kawo musu ziyarar bazata ta cimma yadda baba Labaran yake tozarta rayuwar Latifa akan bare kamar d'ai da duniya bai santa ba, aranar yasha fad'a da nasiha tareda yi masa kashedi mai tsauri akan ya daina takurawa Latifa adalilin banzar matarsa haka dai baba Labaran yaba Iya Kulu hak'uri akan bazai k'ara ba tareda kalallameta da dad'in baki, anan ta yini rungume da Fauzeeya ajikinta dak'yar suka rabu da zata wuce ko kallon arzik'i bata samu awurin Munari ba, saima sak'on harara da take jifarta dashi Iya Kulu tana lura da ita saidai yi tayi da d'ai da duniya kamar Allah bai halacci Munari bata ,Iya Kulu tana saka k'afarta tabar gidan baba Labaran da Munari suka rufe Latifa da zagi suna aibanta iyayenta.
Saida suka gaji da ci mata mutunci sannan suka shisshige cikin d'akin Munari suka barta zaune cikeda matuk'ar tarin bak'in ciki, ganin sun shige d'aki yasa itama ta shiga cikin d'akinta ta saki rikitaccen kuka mai ban tausayi da nadamar auren Labaran zuciyarta sai wani irin k'una takeyi mata wani irin abu ne ya tokare mata a k'irji jijiyoyin kanta suka tashi rud'u rud'u, ta dad'e tana kuka babu mai lallashinta dole daga baya taba zuciyarta hakanan, amma ji takeyi kamar ta kashe aurenta ta huta da alak'ak'ai da uk'ubar rayuwa domin ta tabbatar idan abin ya cigaba da kasancewa haka za'a iya wayuwar gari ta zamo gawa.
Haka Latifa take rayuwa agidan da dad'i da babu dad'i ta kawo na mujiya ta saka musu, ab'angaren baba Labaran ganin Munari shiru bata samu ciki ba yasa ya d'auki damuwa da rashin kwanciyar hankali ya saka azuciyarsa.
Tun yana b'oyewa Munari haihuwa yakeso har yazo ya furta da bakinsa shifa so yake ta haihu, bata bari ya k'arasa maganarsa ba ta balbaleshi da fad'a cikin b'acin rai tace aiba ita zatayiwa kanta ciki ba shi yakeyi kuma ya kasa, baba Labaran yaji zafin yadda take sako masa maganganu masu zafi nan ya biye mata sukayi kacha kacha suka tashi baram baram tunda kowanensu bayada hak'uri wurin cin mutunci da tozarci.
Sunfi fiyeda sati biyu suna gaba da juna baba Labaran da kansa ya sauko ya bata hak'uri suka shirya kamar farkon aurensu, cikin haka ne ciwo ya kwantar da Latifa Iya Kulu ta dawo cikin gidan da zama tana jinyarta sai taji sauk'i sannan ciwo ya k'ara anzama har ya zamo sai an kwantar da ita an tayarda ita, ganin haka ne yasa hankalin Iya Kulu dana sauran danginta yayi k'ololuwar tashi fargaba da tsantsar tsoro ne ya wanzu azuk'atansu tururuwar gaidata sukeyi akowane safiya, 'itama Fauzeeyar hankalinta ya d'unguma zuciyarta ta tsinke gabanta ya har fatfatfat yakeyi mata tasha b'oye cikin wani d'aki tana rusar kukan bak'in ciki da tsantsar takaicin rashin lafiyar mahaifiyarta, cikin haka ne ubangiji ya amshi ran Latifa ta rasu wanda asanadiyyar haka duk wani masoyinta saida ya razana da kad'uwa adalilin mutuwarta tareda tausayawa rayuwarta d'iyarta Fauzeeya! Ina lillahi wa ina ilaihirraji'una!....... ....
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 41*
Itace kalmar dake fitowa daga cikin bakin mutane da Iya Kulu ta rikice sai zubar da kwallar zallar rad'ad'i da tsantsar zafin mutuwa takeyi, nan da nan akayiwa gawarta wanka aka kaita makwancinta na gaskiya gari duk ya karad'e da mutuwar Latifa mace mai kirki da zaman mutunci da kowa fuskarta sake take da kowa batada matsala arayuwarta, da Fauzeeya taji cewar mahaifiyarta Allah yayi mata rasuwa tayi suman daya kai uku saida aka kira likita ya dubata yayi mata allurar barci domin yadda take gunjin kuka tana wayyo wayyo idan ka ganta saita baka matuk'ar tausayi, Iya Kulu itace kawai mai iya lallashinta tana gaya mata kalamai masu sanyaya zuciya.
Bayan rasuwar Latifa da sati biyu Fauzeeya ta fara fuskanta azabobi da uk'uba iri iri daban daban daga wurin matar uba, dayake baba Labaran bai wani damu da ita ba ko yaga Inna Munari tana kashinta kamar jaka uffan baya cewa domin yana gudun b'acin ranta.
Nan da nan rayuwar Fauzeeya ta chanza yanayin kammaninta duk ya rikid'a ta koma tamkar wadda batada gata aduniya, domin tun tana k'ank'anuwarta Inna Munari ke sakata ayyukan da suka fi k'arfinta idan tayi ba daidai ba ta jibgeta son ranta babu mai shigowa cikin gidan ya bata hak'uri saboda kowace matar aure dake cikin unguwar tasan halinta, saidai kaga suna lek'owa ta katanga suna kallon cin zarafin da takeyi mata tareda walak'anta rayuwar Fauzeeya, wasu har zubar da kwallar zallar tausayinta sukeyi suna zagin Munari azuciyarsu wasu kuma idan ta fito waje har janta sukeyi su kaita gidansu su bata abinci taci saita k'oshi domin sunyi zaman mutunci da mahaifiyarta wasu har k'yautar kud'in cin abinci suke bata saboda duba d'aya zakayi mata ka gane tana cikin matsanancin hali da k'angin rayuwa.
Duk irin cin kashi da tozarcin da Inna Munari ke yiwa Fauzeeya Iya Kulu batada masaniya akai, sai ran nan da wata mak'wabciyar Munari taje gidan Iya Kulu take gaya mata duk ire iren walak'anci da tozarcin da Inna Munari takeyiwa jikanyarta tun anan Iya Kulu ta yamutse hankalinta ya d'unguma zuciyarta ta tsinke gabanta ya dinga bugawa da k'arfi, dak'yar ta bud'i baki tayi mata godiya sosai matar tana wucewa Iya Kulu ta jawo mayafinta ta yafa ta sanya takalminta idanunta har duhu duhu suke gani akan tsantsar fargaba da bak'in cikin abinda akace Inna Munari tana yiwa tilon jikanyarta ta fice daga cikin gidanta.
Tana isowa tsakiyar filin gidan ta hango Inna Munari tanata dukan Fauzeeya kamar ta samu jaka da gudu ta isa wurinsu ta jaye Fauzeeya agabanta ta mayarda ita abayanta, ganin haka ne yasa Inna Munari ta harzuk'a ta taso cikin hasala gadan gadan zata kaiwa Fauzee wawura da nufin ta chapkota, tana kawo hannunta Iya Kulu ta buge mata hannu ta d'auketa da mari biyu cikin matuk'ar b'acin rai ai kuwa nan da nan Inna Munari ta saki razananniyar kuwwa ta dafe kuncinta! Wani irin rikitaccen zafi da rad'ad'in ciwon mari ne ya ziyarci sassan jikinta da ruhinta!.
Iya Kulu taja hannunta suka shige cikin d'akin dayake mallakinta wato na mahaifiyarta marigayiya Latifa shine take rayuwa cikinsa, wurin tufafin Fauzeeya suka nufa Iya Kulu ta kwashe mata tufafi tsab ta saka cikin Ghana must go bayan ta gama saka mata kayayyakinta cikin jikka, taja hannun Fauzeeya suka fice daga cikin gidan da zasu tafi basu ga kowa tsakar gidan ba domin tuni Inna Munari ta fad'a cikin d'akinta domin tayi jinyar kuncinta.
Rayuwar Fauzeeya ta koma gidan kakarta Iya Kulu wadda take ji da ita da matuk'ar sonta domin duk abinda takeso shi Iya ke siyo mata ko taba ta kud'i ta siyo da kanta ta dafa jagwalgwalonta, tun Fauzeeya bata iya sarrafa abinci ba har tazo ta k'ware babanta bai biyo bayanta ba ya tambayi ba'asin abinda yake faruwa sai bayan tayi wata guda agidan kakarta, aranar da yazo ya gamuda tsananin b'acin ran Iya Kulu saboda fad'a ta dingayi masa tayi masa wankin babban bargo domin taji matuk'ar ciwon yadda ya maida kansa lusarin namiji mace tana juyashi kamar waina atanda, dayaga Iya Kulu ta hasala sosai ya dinga bata hak'uri hmmmm in tak'aice muku saida baba Labaran ya sance jikinsa ahankali sad'af sad'af sad'af yabar gidan batare da sanin mahaifiyarsa ba saboda shi bayason fad'a da hayaniya arayuwarsa.
Haka dai Iya Kulu ta cigaba da kulawa da jikanyarta cikeda matuk'ar so da tarairaya har Fauzeeya ta shekara goma, cikin haka ne hajiya Ramlat tazo wurin mak'wabciyar Iya Kulu mai suna Badariya dayake dama sunsan juna, suka cigaba da firarsu cikin matuk'ar farin ciki da shak'uwa anan ne hajiya Ramlat ta nunawa Inna Badariya yarinya takeso wadda zata dinga yiwa 'yarta Nazifa saboda jiya satinta biyu dayin aure kuma bata saba da wahalar ayyukan gida da girke girke ba, Inna Badariya tayi shiru can tace ita batada k'aramar yarinya yaranta mata duk sunyi aure amma mak'wabciyarta Iya Kulu tanada jikanya, hajiya Ramlat ta nuna mata ta kaita gidan suje su nemi alfarma awurin Iya batayi mata wata gardama ta tashi tsaye tana gaba hajiya Ramlat tana biye abayanta har suka iso cikin tsakiyar gidan da sallama abakinsu, Iya Kulu ta amsa musu cikin sakin fuska tareda d'auko tabarma ta shimfid'a musu suka zazzauna akai ruwan randa masu sanyi ta dire agabansu ta zauna, saida sukayi gaishe gaishe atsakaninsu sannan Inna Badariya ta koro mata bayanin abinda ya kawosu Iya Kulu tayi shiru tana tunanin bukatarsu can dai ta nisa tace"gaskiya bazan iya bada jikanyata k'waya d'aya rik'o ba saboda ina gudun abinda zaije ya dawo ".
Inna Badariya ta gyad'a kanta tace"karkice haka Kulu aiba rik'on sakainar kashi za'ayi mata ba har makaranta za'a sakata ta samu ilimi ta waye kinga kuwa bayarda Fauzeeya riko yanada matuk'ar amfani awurinki da ita".
"bazan iya nisa da ita ba ita kawai nake gani inji sanyi araina saboda kinsan mahaifiyarta ta rasu! ".Iya Kulu ta fad'a cikin sanyin jiki tareda sanya gefen zanenta tana share kwallar data zubo mata afuskarta.
"Ayyah ubangiji Allah ya jik'anta mutuwa ba dad'i sai hak'uri da juriya".Inji hajiya Ramlat kamar mutuniyar arzik'i.
Inna Badariya tace"wannan ba matsala bane hajiya zatayiwa 'yarta magana akan ta kula da ita sosai ".
Hajiya Ramlat ta dubi fuskar Iya Kulu tace"ki kwantar da hankalinki da yardar Allah zamu riketa amana hannu bibbiyu nayi miki alk'awarin ba za'a tab'a samun wata matsala ba".
Inna Badariya ta girgiza kanta tace"ki yarda da kalaman hajiya babu abinda zai samu jikanyarki insha Allahu sai alkharin Allah".
Haka dai suka cigaba da kalallameta da dad'in baki suna rok'onta akan ta amince da buk'atar hajiya Ramlat, dakyar da sudin goshi suka kawo kanta ta amince da yardar akan Fauzeeya zata koma gidan Nazifa, aranar ne aka shiryawa Fauzee kayanta wuri d'aya hajiya Ramlat ta sake dawowa zata wuce da ita aranar Iya Kulu da Fauzeeya sunsha kukan rabuwa da juna domin har k'ank'amewa ajikin juna sukayi dak'yar Inna Badariya ta b'an'bareta ajikin Iya Kulu suna kuwwa tana komai aka rabasu hajiya Ramlat ta wuce da ita gidanta daga baya ta kira Nazifa awaya tazo ta d'auketa ta koma gidan Yaseer.
_Wannan shine dalilin komawar Fauzeeya gidan Nazifa amatsayin 'yar aiki, yanzu gashi asanadiyyar son zuciya da *SAKACI* irin na Nazifa yasa ta samu damar sace zuciyar mijinta, ta tashi daga matsayin 'yar aiki ta koma matar gida mafi soyuwa zuciyar Yaseer Taheer._ 😂 😂
*SILAR AURENSU*
Alhaji Taheer Muhammad da Alhaji Mu'azu Yahaya asalinsu 'yan jahar Jigawa ne suna zaune cikin garin birnin kudu ne suda iyayensu, abotarsu ta samo asali ne tun daga iyayensu har abin ya zamo musu zumunci mai k'arfi atsakaninsu yaransu suka tashi kansu ahad'e duk abinda zasuyi tare sukeyi, ganin shak'uwa mai k'arfi ta wanzu atsakaninsu yasa komai tare akeyi musu hatta aschool basu tab'a rabuwa da juna ba daidai da rana d'aya, sun taso cikin tarbiya da wadata har suka kammala karatunsu suka shiga harakar yin business.
Cikin ikon Allah dukiyarsu ta habb'aka sai hauhawa takeyi arana d'aya suka samu matan aure sukayi aurensu, sunan matar Taheer Sadiya yayinda sunan matar Mu'azu Ramlat bayan amare sun tare ajibga jibgan katafaren gidan mazajensu na wani lokaci nan da nan Sadiya ta samu ciki ta haifi sankacecen d'anta jawur dashi yaci suna Yaseer alokacin Ramlat bata samu ciki ba, basu wani damu ba itada mijinta saboda tasan komai na Allah kuma lokaci yana zuwa.
Safiya da mijinta Taheer suka cigaba da rainon d'ansu cikin matuk'ar kulawa da tsantsar soyayyar gaskiya haka Yaseer ya tashi da farin jini da soyayyar iyayensa, alokacin kuma shiru hajiya Ramlat ko batan wata bata tab'a yi ba ganin shekaru suna tafiya mutuwa tana k'ara kusantomu kwanakinmu aduniya suna ragewa yasa hajiya Ramlat ta d'auki tsantsar damuwa da bak'in cikin rashin haihuwa ta sanya azuciyarta nan take ta rame akwanakin nan adalilin rashin haihuwa mijinta Alhaji Mu'azu shike lallashinta yana bata maganganu masu dad'i akan ta rage yawan saka damuwa da bak'in ciki azuciyarta, dak'yar yake samu ta sauko ta cigaba da harakokin gabanta tamkar batada wata damuwa azuciyarta.
Rayuwar gidan ta cigaba da gudana zuciyar hajiya Ramlat cunkushe da tsantsar damuwa da bak'in ciki cikin ikon Allah Ramlat bata samu ciki ba saida Yaseer ya shekara bakwai aduniya, shima mahaifiyarsa tun daga kansa bata sake haihuwa ba yanada shekara takwas aduniya Ramlat ta haifi santaleliyar d'iyarta k'yak'k'yawa aranar biki jaririya taci suna Nazifa, hmmmmmm fad'ar irin tsagwaron farin ciki da murnar dasu hajiya Ramlat sukayi adalilin haihuwarta fad'i ma b'arnar baki ne.............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍