Showing 33001 words to 36000 words out of 87802 words
amma ko juyowa baiyi ba ya kalleta bale tasa ran zaiyi mata magana yadda ya nuna mata halin ko inkula taji matuk'ar zafi har cikin ranta, jijiyoyin kanta sun bayyana akan b'acin rai can ta nisa tace"daddyn Sameer ya naga kana sanyawa Fauzeeya tufafinta cikin akwati ko bazata dawo bane!?".
Sai alokacin ya d'ago idanunsa ya dubeta yace"itace tace in kai mata tufafinta gidan kakarta itada dawowa sai anyi aurenmu! ".
Rasssss fad'uwar gaba ya ziyarceta tsantsar kishi da tsagwaron k'iyayyar Fauzeeya ne ya bayyana k'arara cikin k'wayar idanunta wani irin d'aci da zogi zuciyarta keyi, saboda ta tabbatar idan har Yaseer ya auri Fauzeeya zai iya walak'antata ya tozarta da rayuwarta ,batace masa k'ala ba har saida ya kammala sanya tufafin cikin akwati sannan yaja akwatin ya nufi parking lot da ita.
Yana fitowa itama ta fito tabi bayansa har parking lot agabanta ya sanya akwatin abayan boot d'in motarsa, yana sakawa ya kulle bayan boot d'in ya juyo ya kalleta yace"lafiya kika biyoni parking lot?".
Nazifa ta marairaice fuskarta kamar zatayi kuka kishin mijinta ne ya bayyana k'arara afuskarta tace"ina zakaje ka barni yanzun nan? ".
Yaseer tsaye yayi sororo kamar wawa yana kallonta can yace"kamar ya ina zan tafi inbarki bayan na gaya miki gidan kakar Fauzeeya zanje in kai mata tufafinta ".
Data rasa abinda zatace sai tace"naga wai zuwanka gidan yayi safiya da yawa ".
"keeee banason shirme maza ki koma cikin gida banason munafurci! ".
"haba daddyn Sameer ka fahimceni......... ".Katsa mata tsawar da yayi ne yasa ta razana ta nufi cikin parlourn da saurinta har tuntub'e ta tashi yi akan ta rikice da gigicewa!. Yaseer ya bud'e gaban mazaunin driver ya zauna tareda danna horn maigadi ya wangale masa get yya fice daga cikin gidan ya nufi hanyar unguwarsu Iya Kulu............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 20*
Yaseer yana fita daga cikin gidansa ya saita motarsa saman kwalta tuki yakeyi cikin natsuwa da k'warewa har ya iso bakin k'ofar gidan, bud'e k'ofar motarsa yayi ya kira wani yaro mak'wabcinsu Fauzeeya ya aikesa cikin gidan saboda ya kirata, yaron ya juya ya shiga cikin tsakiyar filin gidan ya hangota zaune saman kujera tana wanke wanke yayinda Iya Kulu ke kishingid'e saman tabarma, gaidasu yayi cikin ladabi sannan ya mayarda hankalinsa kacokam wurin Fauzeeya yace"Aunty Fauzeeya ana miki sallama awaje".
Fauzeeya ta dubesa tace"waye Nafi'u?".
"nima ban sanshi ba amma da mota yazo".Cewar Nafi'u ya juya zai fice kenan Fauzeeya tace"kace masa ina zuwa".Saboda ta fahimci Yaseer ne yazo wurinta.
"zan gaya masa".Inji Nafi'u ya fice daga cikin gidan da sassarfa.
Zumbur ta mike tsaye tana kallon fuskar Iya Kulu tace"Iya Yaseer ne yazo wurina".
"to ayi fira lafiya".
"Allah yasa".
Fauzeeya ta fad'a cikin d'akinta ta gyara fuskarta da powder ta shafa lipstick abakinta tareda chanza tufafin dake jikinta ta sanya wasu, bata dad'e ba ta fito daga cikin d'akin ahanzarce ta nufi wurin Yaseer dake bakin k'ofar gidan.
Jingina jikinsa yayi ga motarsa yana tsaye yana jiranta daga nesa ya hangota tana tafiya cikin yanga da natsuwa tsura mata idanunsa yayi cikin shaukin so yana k'are mata kallo, daga can yake jifarta da kallon soyayya ita kuma sai murmushin dake k'ayatar da fuskarta takeyi domin ganin Yaseer agabanta ya wanke dukkan cutar dake cikin zuciyarta,isowa wurinsa tayi ta gaidashi cikin ladabi ya amsa mata cikin fara'a.
Kallon k'auna yayi mata yayinda ya k'awata fuskarsa da murmushi yace"my Fauzee ina farin cikin k'ara saduwarmu akaro da dama nakan kasance cikin tunaninki da sonki azuciyata".
Fauzeeya ta rausayar da kanta cikin murna da annashuwa tace"soyayya wata abace mai sanyaya zukatan masoya babbar farin cikina akowane lokaci na ganni gani gaka ka sani har abada kaine ruhina".
"idan idanuna basuyi tozali da k'yak'k'yawar fuskarki ba har zazzab'in k'auna yake kamani tabbas kin zamo ginshikin rayuwata, da za'a iya bud'e zuciya dana bud'e miki zuciyata domin ki k'ayyade adadin k'aunarki dake gudana cikin jini da magudanar jikina".
Tabbas kalamansa sunyi matuk'ar tasiri azuciyarta yayinda wani irin abu yake kwaranya cikin jini da k'ofofin jikinta, tsantsar murna da farin ciki ne kwance cikin k'wayar idanunta langwab'e kanta tayi tace"k'aunarka tuni ta mamaye zuciyata babu wani gurbi da waninka zai iya shiga cikinta saboda babu abunda nakeso da muradi saikai yah Yaseer".
Yaseer yaji matuk'ar dad'in kalamanta har cikin tsoka da jinin jikinsa farin ciki da nishad'i ne kwance cikin k'wayar idanunsa,cikin yanayin murna yace"hmmm tabbas na yarda da soyayyarki gareni to ya bayan rabuwa?".
"lafiya k'alau Alhmdulillahi".
"haka nakeson ji to nazo miki da akwatin tufafinki suna bayan boot d'in mota".
"OK ba damuwa".
Yaseer bai sake cewa komai ba ya bud'e bayan boot ya d'auko mata akwatinta kiran wani yaro yayi daya gifto ta gabansu, yabashi d'ari biyar tareda umurtarsa daya shigar mata akwatin cikin gidansu yaron yayi godiya sannan ya d'auki akwatin ya shigar da ita cikin gidan.
Yaseer ya rungume hannayensa saman k'irji ya dubeta yace"to yanzu inason inji yadda kikeson tsarin d'akinki ya kasance saboda kinga bikinmu sai k'ara matsowa yakeyi?".
Fauzeeya ta duk'ar da kanta cikeda matuk'ar kunya tace"duk yadda ka tsara yayimin".
"a'a ki fad'i ra'ayinki kada ki bari kunya ta cuceki".
"Allah yayana duk abinda kayi daidai ne ta b'angarena babu matsala kar kaji komai annurin zuciyata".
Yaseer ya saukar da numfashi yace"to tunda kin kasa fad'in ra'ayinki zaki iya turomin text message awaya in gani".
"kayyyy yaya Yaseer kawai kayi abinda kaga yafi maka sauk'i basai ka wahalar da kanka ba wallahi".
Yaseer ya aza yatsarsa saman leb'b'ensa yace"shittttt banason in k'ara jin wata magana daga cikin bakinki muddin ba ra'ayinki zaki fad'a ba akan abunda nake so".
"afuwan masoyina na daina".
"my Fauzee ni zan wuce zuwa gida ko akwai abinda kike buk'ata?".
"babu abinda nake bukata ubangiji ya kaika gida lafiya".
"amin babyna".Yana k'arasa maganarsa ya shige cikin motarsa ya k'ara gaba yayinda Fauzeeya ta juya ta shige cikin tsakiyar gidan.
*********************
*BAYAN WATA BIYU*
Alokacin ne ya rage saura wata d'aya da d'aurin auren Yaseer da Fauzeeya, yayinda duka b'angarori biyu suka dinga shirye -shiryen aure babu kama hannun yaro.
Nazifa ce zaune tayi tagumi cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali wanda ya bayyana k'arara afuskarta, zuciyarta sai zogi da k'una takeyi mata yayinda k'asan ranta wani irin tururin zafi da suya yake mata ji take kamar zuciyarta ta buga ta mutu ta huta da takaicin duniya! Akwanakin nan tunda taga auren Yaseer ya k'ara kusantowa ta d'auki bak'in ciki da tsantsar damuwa ta sanya azuciyarta babu abinda yakeyi mata dad'i aduniya, da tsakar dare dak'yar da sud'in goshi take samun b'arawon barci ya saceta domin kwata kwata batada natsuwa da walwala arayuwarta.
Tana zaune tana tunanin tun farkon had'uwarta da Yaseer har zuwa aurensu, saiga sallamar k'awarta Safiya ta shigo tsakiyar parlourn da sassarfa tana isowa wurinta ta jaye mata hannun da tayi tagumi dashi tace"miya sameki k'awalli wai miye kika saka azuciyarki har yake damunki haka!?".
Alokacin ne Nazifa ta juyo ta dubeta cikin zafi da k'unar zuciya tace"haba Safiya miyasa kikeyimin irin wad'annan tambayoyi bayan kinsan babu abinda yake damuna illa zafi da rad'ad'in kishiya!".
Safiya ta kalleta cikin tausayawa tace"ki daure ki rage yawan saka damuwa da bak'in ciki azuciyarki domin gudun saka rayuwarki cikin hatsari!".
"ya kikeson inyi da rayuwata Safiya wallahi ina cikin matuk'ar damuwa da rashin kwanciyar hankali bana barci cikin dare akan tsantsar fargaba da zullumi kullum zuciyata cunkushe take da tsagwaron takaicin rayuwa! ".
Safiya ta rik'e hannunta cikin sanyin jiki da tattausan lafazi mai kwantar da zuciyar masoya tace"nasan damuwarki aminiyata yanzu abinda za'ayi kije ki d'auko gyalenki muje gidan kakar Fauzeeya muci musu mutunci tun yanzu su fara nadamar bawa Yaseer d'iyarsu! ".
Nazifa taja numfashi mai tattare da d'acin rai da tafasar zuciya ta mike tsaye tace"to bari in fito yanzu".Tana rufe bakinta ta nufi cikin room d'inta domin ta k'ara kintsa jikinta.
Bata dad'e sosai ba ta fito sanye da mayafinta handbag tana rataye a kafad'arta tana isowa wurinta tace mata"Safiya na kammala shiryawa muje".
Zumbur Safiya ta tashi tsaye tace"to k'awar arzik'i".
Atare suka jera da juna suka nufi parking lot suna isowa wurin motar Nazifa ta sanya key ta bud'e motar sannan suka shiga ciki suka zazzauna tareda danna horn maigadi ya wangale musu get d'in,Nazifa ta saita motarta saman kwalta suka nufi hanyar zuwa unguwarsu Fauzeeya.
**********************
Tafiya sukeyi cikin mota sannu ahankali har suka iso cikin unguwar daidai bakin k'ofar gidan Iya Kulu mai tsamiya suka parker motar tareda fitowa daga cikin motar kusan tare, jerewa da juna sukayi suka shiga cikin tsakiyar filin gidan yayinda suka isko Fauzeeya tana shafa powder afuskarta Iya Kulu tana gefenta tana kallonta cikin so da tsantsar k'aunar Fauzeeya, cikin gadara da tak'ama suka iso wurinsu fuskarsu amurtuk'e babu alamun fara'a ko annuri basuyi musu sallama ba balesu Iya Kulu su amsa.
Jin motsinsu yasa Iya Kulu ta d'ago fuskarta idonta ya sauka akansu cikeda matuk'ar mamaki take k'are musu kallo, yayinda cikin k'ark'ashin zuciyarta yakeyi mata zogi gabanta sai dukan uku uku yakeyi saboda tayi imani da cewa ba alkhairi bane ya kawosu!.
Tsaye sukayi k'yam saman k'afafunsu kamar sojawa Safiya tayi musu kallo mai tattare da raini da rashin kunya tace"keee tsohuwa wurinki muka zo fa! ".Cikin rashin girmamawa da tarbiya ta fad'i haka.
Iya Kulu ta musk'uta cikin yanayin fad'uwar gaba tace"lafiya 'yar nan mi nayi miki?".
"ina fa lafiya tunda jikanyarki Fauzeeya take neman jefa rayuwarki cikin hatsari da matsalar rayuwa!".
Fauzeeya jugum tayi tana kallon ikon Allah domin taga k'arfin halinsu afilin wuri mamaki da al'ajabi ya sanya ta kasa yin kwakkwaran motsi, takaici da haushinsu ne kwance cikin k'wayar idanunta wani irin tururin zafi da tafasa zuciyarta keyi domin ita arayuwata ta tsani cin mutunci da walak'anci arayuwa.
"assha 'yar nan mi Fauzeeya tayi muku ne da take neman jefani cikin hatsari sanardani abinda yake faruwa!? ".
Karkad'a jikinta tayi tace"wato ke baki gane ko mu su waye ba?".
"ban gane ba baiwar Allah".Inji Iya Kulu cikin magana sanyi sanyi.
Safiya zata bud'i bakinta ta sake magana kenan Fauzeeya tayi charap ta rigata magana tace"Iya su Nazifa kishiyata ce baki ganeta ba!? ".
Dummmmm gaban Nazifa ya fad'i tsantsar mamaki da tafasar zuciya ne ya wanzu k'arara afuskarta saboda Fauzeeya ta bata mamaki yadda ta ambaci sunanta gatsau, babu kunya bale tunani harda kiranta da kishiyarta lallai ta d'auko ruwan dafa kanta zata nuna mata ta fita zama tantiriyar k'warai domin tayi alk'awari azuciyarta saita haddasa mata fitina arayuwa tareda tarwatsa duk wani farin ciki nata.
Iya Kulu ta chanza yanayin fuskarta daga fara'a zuwa murtuk'ewa tace"lafiya miye ya kawoku cikin gidan nan ko kunzo ne ku d'aura daga inda uwarki Ramlatu ta tsaya!".
Nazifa ta harzuk'a da zagin da Iya Kulu ta jefa mata cikin zafin rai tace"keee bak'ar munafukar tsohuwa karki kuskura ki k'ara zagina! Azzaluma maciya amana butulu kawai daku ubangiji ya tsine muku albarka keda banzar jikanyarki! ".
Fauzeeya ta mik'e zumbur tsaye tace"yadai tsine miki albarka keda annobar uwarki k'atanyar banza wadda bata baki tarbiyar kirki ba! ".Nazifa ta zaburo da k'arfi cikin zafin zuciya ta kawowa Fauzeeya wawura nufin ta mangareta zama guda cikin zafin nama Fauzeeya ta kauce mata tareda kwashe k'afafunta kaji ribbb Nazifa ta fad'i kasa!Asanadiyyar haka saida ta saki rikitaccen k'ara da gigitacciyar kuwa saboda wani irin zafi da rad'ad'in ciwo ne ya ziyarci sassan jikinta da k'wak'walwarta!..........
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 21*
Ganin irin abinda ya faru ga Nazifa yasa Safiya ta shek'o da matsiyacin gudu ta tunkud'e Iya Kulu data tashi tsaye saboda ta shige cikin d'akinta, gwaffff kaji Iya Kulu takai k'asa sai kukan zafi da k'unar zuciya takeyi 🤣🤣.
Fauzeeya tana ganin Safiya ta ture kakarta har ta fad'i ta tunkari wurin Safiya gadan gadan babu alamun tsoro afuskarta, tana isowa ta kawowa Safiya bugu ta kauce da sauri tareda kai mata dundu abayanta, jin zafin da Fauzeeya tayi ne yasa ta rungumi Safiya suka kachame da fad'a kamar yara k'anana bugun junansu kawai sukeyi cikin bak'in rai da mugun nufi, Safiya ta lura idan bata nunawa Fauzeeya wayo na shekaru ba zata iyayi mata shegen duka.
Shiyasa nan da nan wata dabara ta fad'o mata arai ta samu ta shammaci Fauzeeya ta rik'eta gagam ahannunta tayi mata shegen dukan daya sanya ta galabaita alokaci guda, dukan cikinta Safiya ta dingayi cikin rashin tausayi saida taga numfashinta yana batun d'aukewa sannan taja ta tsaya tana mayarda numfashin gajiya kamar wadda tayi abin k'warai.
Wurin Nazifa ta nufa dake kwance shame shame a k'asa duk jikinta ya b'aci da k'asa ta taimaka mata ta tashi tsaye tana cize baki, cikin ciwo da rad'ad'in fad'uwar da tayi dafa kafad'ar Safiya tayi ta kalli Fauzeeya dake kwance k'asa hawayen takaici ne yab'e yab'e saman fuskarta tace"wannan abinda ya faru dake somin tab'i ne akan wanda zai iya faruwa dake nan gaba nasha alwashin duk kika auri Yaseer sai kinga tasku da walak'anci iri iri arayuwarki! Domin saina miki abinda yake har abada bazaki tab'a mantawa dani ba".
Fauzeeya tana kwance cikin galabaita domin ta daku iya dakuwa ahannun Safiya numfashin wuyar da tasha kawai take fitarwa ahancinta, cikin tafasar zuciya ta tofar da miyau tace"duk abinda zakiyi Nazifa kije kiyi ubangijin sammai da k'assai ya fiki kuma yana kallonki sannan k'aryarki tasha k'arya kice zaki walak'antamin rayuwa saidai mu gwabza da juna aga mai gajiya ya sakewa d'aya ".
"kina ma kwancen amma bakinki bai mutu ba".Cewar Nazifa cikin matuk'ar mamakin k'arfin hali irin nata.
Safiya ta dubi fuskar Nazifa tace"bari in k'ara dukan shegiya".
"a'a k'awata barta kawai aita jibgu kuma akwai wata rana zamu sake dawowa".
"shikenan tunda kince in kyaleta".Inji Safiya.
Jan hannun Nazifa tayi zasu wuce kenan suka tsinkayo muryar Fauzeeya tana cewa"kuzo ku kasheni idan kun cika manyan marasa imani wallahi ko zaku had'iyi zuciya ku mutu aurena da darling Yaseer babu shakka sai anyisa! ".
Sudai basu ce mata komai ba suka fice daga cikin gidan suka shige cikin motar yayinda Safiya ta zauna mazaunin driver, ta tadda motar suka nufi hanyar chemist domin adubi lafiyar jikin Nazifa kada wata matsala ta biyo baya.
**********************
Su Safiya suna ficewa daga cikin gidan Fauzeeya ta mik'e tsaye dak'yar ta taimakawa Iya Kulu cikin dauriya tana cize baki, da taimakon Allah ta kai Iya Kulu cikin d'akinta ta zaunar da ita saman gado itama ta zauna tana kallon fuskar kakarta cikin tausayi tace"kiyi hak'uri Iya akan abinda ya faru nasan duk abinda ya sameki nice sanad.........".
Iya Kulu ta katse mata hanzari da sauri tace"shitttttt ki daina cewa haka Fauzeeya ko kad'an bakida laifi cikin wannan al'amarin duk abinda ya sameni k'addara ce saboda haka ki kwantar da hankalinki tuni na mik'awa Allah lamarina".
"shikenan na daina fad'ar haka ubangiji yayi mana jagora cikin lamarinmu".
"Amin amin Fauzeeya".
____________________
*BAYAN SATI BIYU*
Saura sati biyu ad'aura auren Yaseer da amaryarsa Fauzeeya yayinda tuni ya kammala had'a lefe akwati set biyu aka kai gidan Iya Kulu, ana kai kayan lefen Iya Kulu ta basu umurnin ajuyo da akwatunan domin batason baba Labaran ya fahimci ko wane irin miji zata aura.
Haka dai aka juyo da lefen wurin Yaseer tareda gaya masa abinda kakar tace bai nuna b'acin ransa saboda shi mutum ne mai sauk'in kai da hangen nesa, sauran lefen ya kwasa ya kaiwa babban telan mata wanda akeji dashi agarin ya bashi kayan ya d'inke mata kafin biki, saida ya biyasa kud'insa k'asa bai biyosa ko naira biyar ba sannan ya fice daga cikin shagon.
Nazifa da Safiya ne saman gado sunyi jugum cikin matuk'ar damuwa kallo d'aya zakayi musu ka gane basa cikin farin ciki da walwala, musamman Nazifa wadda ake shirin yiwa kishiya daga sama bayan ta riga ta saba ita kad'ai agidan mijinta, hawaye masu zafi sai gangara sukeyi afuskarta wani irin d'aci da zogi ne azuciyarta mara adadi, gabanta sai suya da zafi yakeyi mata adalilin zuciyarta cunkushe take da tsagwaron takaici da bak'in cikin rayuwa, ganin ta shiga kogin tunani yasa Safiya ta bugi bayanta da k'arfi tayi firgigit ta dawo cikin hayyacinta can ta nisa tace"yadai Safiya?".
Safiya taja dogon numfashi tace"naga kinyi shiru tun lokacin da Yaseer ya kawo miki kayan fad'an kishiya bakice komai ba".
Juyar da kanta tayi b'angare daban tace"mi zance k'awata bayan Yaseer ya riga ya gama da rayuwata tunda har zaiyimin kishiya abar k'i da tsana ga kowace d'iya mace!".
"daurewa zakiyi Nazifa ki dinga b'oye kishinki agaban mijinki da mutane saboda kada su sami damar da zasu k'ara ki gaba idan wani abu ya biyo baya zasu iya zarginki".
Nazifa ta jijjiga kanta alamar gamsuwa da maganarta tace"gaskiya kinada basira da kaifin tunani Safiya ba damuwa da yardar Allah zan dinga b'oye kishina saboda kada wani abu ya faru mutane su zargeni".
"wannan bashida ance idan bakiyi taka-tsan-tsan ba Nazifa kinsan mutanen yanzu akwaisu dasa ido da k'walelecewa kai baka damu da mutum ba amma shi yana nan yana saka maka idanu baya sonka ".
"tabbas Safiya maganarki hak'k'un ce babu k'arya haka yake".
**********************
Hajiya Ramlat ce