Showing 51001 words to 54000 words out of 87802 words
baby ki taimakawa rayuwata ki daure ki sanarmin dalilin zubar da hawayenki idan ba haka zuciyata zata iya bugawa in fad'i in mutu! ".
Jin mahaifiyarta ta ambaci kalmar mutuwa yasa Nazifa ta d'ago kanta afirgice k'wayar idanunta kana hango tashin hankali da tsantsar damuwa cikinsu dak'yar tace"ko daina cewa zaki mutu ki barni Ummu rayuwata zata iya shiga cikin garari da matsananciyar damuwa! ".
Cikin tsananin tausayi da tsantsar k'aunar Nazifa hajiya Ramlat tace"Ok baby ki kwantar da hankalinki na daina fadar haka yanzu dai ki gayamin waye ya sakaki zubar da hawayen bak'in ciki!? ".
Nazifa da idanunta sukayi jajir akan kuka tace"Ummu ashe Yaseer azzalumi ne da mak'aryaci duk zamanmu dashi bai tab'a bak'antamin rai ba fiyeda yau, mu muna dubin akwai sauran sati biyu kafin auresa da Fauzeeya ashe jiya ya d'aura aure da ita bamuda labari! ".
Maganarta ta girgiza k'wak'walwar hajiya Ramlat ta mike tsaye da k'arfi hankalinta tashe sai kai da komo takeyi atsakiyar parlourn! Zuciyarta cunkushe take da tsagwaron k'iyayyar Fauzeeya da b'acin rai, saida ta gaji da zagayar parlourn ta dawo cikin natsuwarta ta zauna tace"anyah abinda kika fad'a gaskiya ne baby?".
"wallahi gaskiya nake gaya miki Ummuna idan kina shakku ko kwankwanto akan maganata ki tambayi Abbu ai nasan bazai rasa sanin komai ba".Inji Nazifa cikin yanayin damuwa da rashin kwanciyar hankali.
Hajiya Ramlat ta girgiza kanta cikin rashin yarda tace"wannan maganartaki abar bincike ce d'aukomin phone d'ina saman center table in kira Alhaji injiya daga bakinsa ".
Nazifa ta miko mata wayar da sauri hajiya Ramlat ta amsa tayi dialling nombar Alhaji Mu'azu kiran na shiga Alhaji Mu'azu ya kara akunnensa yace"hello Ramlat ya kike?".
"k'alau nake Alhaji ya business d'inka?".
"lafiya k'alau Alhmdulillahi".
"dama wani labari naji agari ana yadawa shine nace bari in tambayeka inji ko gaskiya ne".
"tambayeni hajiya ina saurarenki".
Hajiya Ramlat taja gwauron numfashi cikeda damuwa tace"wai anyi aurensu Yaseer! ".
Alhaji Mu'azu yayi murmushin dake k'ayatar da fuskarsa yace"eh mana gaskiyar zance ne anyi auren Yaseer da Fauzeeya jiya adalilin yadda aka fahimci ana son afirgita Fauzeeya tace ta fasa aurensa shiyasa aka d'aura auren daga sama babu zato ko tsammani ".
Rassss taji gabanta ya fad'i tsantsar tsoro da d'imaucewa ya ziyarci sassan jikinta da k'wak'walwarta gudun kada asirinta ya tono yasa tayi saurin cewa"subahanillah!Ubangiji ya tsare gaba su waye suke tsoratata Alhaji amma sun cika marasa imani da tsoron Allah!? ".
"Amin hajiya nima ban sani ba banji wanda yace ya sansu ba".
Sai yanzu hankalinta ya kwanta ta samu natsuwa cikin zuciyarta tace"to shikenan ubangiji ya k'ara tsare gaba sai anjima ".
"okay sai anjima d'in hajiya:.Yana k'arasa maganarsa ya katse wayar ya cigaba da harakokin business d'insa da yakeyi.
Hajiya Ramlat ta juyo ta dubeta cikin zafi da k'unar zuciya tace"abinda kika fad'a gaskiya ne Nazifa tabbas Yaseer yayi amfani da wayo da tunani irin na yaran zamani ya yaudaremu domin ya hango cewar idan ba'a yi auren da wuri ba zamu iya wargaza komai, kishakuruminki d'iyata ki barni dasu ko sunyi auren basu tsira daga sharrina ba domin bazan tab'a barin su samu kwanciyar hankali da natsuwa ba arayuwarsu! ".
Alokacin ne Nazifa taji damuwar dake k'unshe zuciyarta ta ragu tayi narai narai da fuskarta tace"shikenan Ummu amma dan girman Allah kar kiyi musu hukunci mai sauk'i saboda yarinyar fitsararriya ce batada kunya na tsaneta fiyeda tunaninki! ".
"hak'uri zakiyi ki daina fitar da kishinki agaban Yaseer domin kada wani abu ya sameta ya dinga zarginki kinji Nazifa komai asannu hankali ake binsa domin ganin mun cimma burinmu da nasara".
"ba komai Ummuna zan dinga b'oye kishina agabansa amma na tsani in bud'e idona inga yarinyar nan amatsayin kishiyata! Ji nakeyi kamar in dab'a mata wuk'a ga k'ahon zuciya ta mutu in huta da ganin bak'ar kishiya annobar gari".
Hajiya Ramlat ta rik'e hannunta cikin lallashi da natsuwa tace"kidai cigaba da hakuri komai yayi farko yanada k'arshe baby domin haka kibi komai asannu".
**********************
Su Yaseer suna shigewa cikin d'akin sukayi masauki sai saman gado suna yiwa junansu kallon soyayya, Yaseer ya mannata a kirjinsa yana shafar lallausan gashinta mai d'auke da sinadaran k'amshin mayukan gashi, kaunarta sai fisgarsa yakeyi yana lumshe fararen idanunsa cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa, ita kuma sai k'ara narkewa ajikinsa takeyi tana lahewa kamar mage numfashi Yaseer ya sauke yace"my Fauzee ina matuk'ar k'aunarki azuciyata sonki ya riga yayi min illa cikin zuciya tareda mamaye ruhi da rayuwata".
Murmushin jin dad'i takeyi saboda kalamansa sunyi matuk'ar tasiri azuciyarta sai yawo yakeyi cikin jini da bargon jikinta kallon so tayi masa tace"k'aunarka gareni bazata misaltu ba domin ka riga kayi dashe tuntuni afilin rayuwata,babu mai iya tuge dashen da kayi azuciyata saboda ya riga ya yad'u ".
"naji dad'in yadda kike k'aunata Fauzeeya ki sani har abada Yaseer naki ne ke d'in tawace sonki nake rayuwa dashi nake mutuwa, ina k'ara tabbatar miki babu wadda zata samu gurbi azuciyata saike *ABAR SONA* farin cikin rayuwata soyayyar gaskiya nakeyi miki masoyiyata".
Fauzeeya tace"nima haka k'aunar da nakeyi maka bayada iyaka da adadi mijina saboda haka zan cigaba da tarairayarka tareda sanyaka cikin farin ciki da nishad'i mara misaltuwa".
Yaseer ya k'ara k'ank'ameta ajikinsa yana aika mata zazzafan sak'onni ta ko'ina ita kuma sai tsoro da kakkaucewa takeyi saboda ta tsorata da lamarinsa, ganin hankalinta atashe yasa yake binta sannu ahankali yana gigita mata k'wak'walwarta da tunaninta .
Saidai yaga ta zauce da ficewa daga cikin hayyacinta sannan ya fara biyan buk'atarsa yana kukan dad'i, Fauzeeya sai nishin zafi da rad'ad'i takeyi domin ba wani dad'i takeji ba.
Sannu ahankali naja k'afafuna na k'ara gaba domin kada inyi tozali da abinda yafi k'arfina.
*********************
Nazifa ta fice daga cikin gidansu ta nufi gidan Safiya babbar aminiyarta tana isa bakin get maigadi ya wangale mata get d'in ta kunna hancin motarta aparking lot, ta fito daga ciki ta sanya key ta kulle motar handbag d'inta rataye a kafad'arta direct cikin parlourn ahanzarce.
Tana shiga cikin tsakiyar parlourn ta hango Safiya zaune tana goge kayanta da iron yayinda agefenta Khalifa ne yake wasa da k'anensa Idris, sallama Nazifa tayi ta iso wurinta cikin sakin fuska tace"k'awata yau kuma guga kawai kikeyi ".
Safiya ta waigo murmushi k'unshe afuskarta cikin murna tace"a'aaaaa Nazifa kece sannu da zuwa eh mana goga nakeyi".
"yauwa Safiya ya yaranki? ".
"k'alau suke gasunan kusa gareki suna wasa Nazifa ".Tace alokacin ne ta k'arasa goge tufafinta ta iso wurin Nazifa ta zauna gab da ita.
Nazifa ta juya fuskarta gefensu Idris tace"lallai kuwa sai wasanninsu sukeyi cikin farin ciki kurciya mai dad'i daga gani zaka fahimci basusan miye damuwa ba".
Safiya ta fashe da dariya tace "da abin dariya kike Nazifa su yara mi suka sani balantana damuwa ta auresu damuwa sai wanda ya mallaki hankalinsa take ziyarta, ya mijinki Yaseer ina fatar yanzu ya rage yawan takura miki?".
Jin ta ambaci sunan Yaseer yasa k'ololon bak'in ciki da tsantsar takaicin dake cikin zuciyarta ya shimfid'a saman fuskarta alokacin ne tururin zafi da suyar zuciya ya mamaye zuciyarta dak'yar ta cire komai azuciya tace"kedai bari k'awata Yaseer kwata kwata ya fita daga cikin sha'anina saidai ya auri Fauzeeya batare da sanina ba".
Nuna damuwarta Safiya tayi afili tace"what!kikace mijinki ya auri Fauzeeya baki sani ba?".
Nazifa ta gyad'a kanta cikin zafin rai da tafasar zuciya tace"tabbas jiya anyi aurensu ".
"Ina lillahi wa ina ilaihirraji'una! Lallai Yaseer ya cika butulu wato saida ya auri Fauzeeya saboda ya nuna miki halinsu na maza ".Bak'in ciki ne ya tokare mata a k'irji domin Safiya ta sosa mata inda yakeyi mata k'aik'ayi cikin matuk'ar b'acin rai da tsantsar damuwa tace"kiba wani labari Safiya Yaseer yana can manne ajikinta kamar zasu cinye junansu ni abin ma matuk'ar mamaki yake bani wlh sannan yana d'auremin kai ".Safiya taji matuk'ar dad'in kishiyar da akayiwa Nazifa wani irin farin ciki da murna ne ke nuk'urk'usar zuciyarta amma dayake ta kware wurin munafurci da azuzanci, afuska ta marairaice cikin rashin walwala tace"hmmmm gaskiya yaci amanarki bai k'yautawa rayuwarki ba".............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 31*
Nazifa tayi rau rau da fuskarta ta bintsire baki tace"yaci amanarsa kansa duk abinda yayimin na cutarwa ko yaci da hak'k'ina shida rabbis samawati".Safiya ta girgiza kanta alamar gamsuwa da maganarta tace"haka ne kowa ya gyara ya sani kuma kowa ya b'ata shida Allah".
"sudai suka sani nasan yanzu yana can yana caccakar d'iyar mutane kinsan amatse yake koda ya auri Fauzeeya".
Safiya tayi murmushinta mai k'yau tace"keee Nazifa kin iya sharri ta yaya kikasan yana can yana kwasar dad'in Fauzeeya?".Nazifa tayi saurin kallonta tace"hmmm kina mamakin yadda akayi na sani ne to ki daina mamakina yadda nasan mijina bayada hak'uri idan yaga mace ta zamo mallakinsa, saiya fanshe duk sha'awar da yakeyi mata domin amatse yake ba wani kulawa nake bashi ba".
Safiya ta gyara zamanta tace"tafdijam kice abuk'ace yake da mace karkiga laifin yadda yake mak'alewa jikin Fauzeeya domin so yake ya samu natsuwa awurinta".
Nazifa ta banka mata harara tace"to agaisheki 'yar iya magana nifa banason kina saka mini maganganu da wayo da wayo masu zafi abin yana b'atamin rai tareda k'onamin zuciya Safiya, amma ba komai domin kinga ina yawan zuwa gidanki ne shiyasa kike neman walak'antani! ".
Safiya ta dakatar da ita cikin lallashi tace"nifa wasa nakeyi miki amma kiyi hak'uri karki rik'eni cikin zuciyarki".
"haka akeyin wasa da sakawa mutum magana yadda kika gadama".Inji Nazifa cikin matuk'ar b'acin rai.
"nace kiyi hak'uri nayi kuskure haba k'awata miyasa wai bakisan wasa ba nifa da kike ganina banason ina bawa mutum hak'uri yana k'ara tunzura rayuwata b'aci takeyi".
Nazifa ganin rayuwar Safiya tana son b'aci yasa tace"na hak'ura komai ya wuce".
"yauwa ko kefa Nazifa ki rage saurin d'aukar zafi mana duka duniyar nan guda nawa take?".
"zan daina Aminiyata Haidar ya fita ne naji tunda na shigo cikin parlourn nan banga giftawarsa ba?".
"kedai ya fita wlh kinsan zama baya tab'a yiyuwa ga talaka saiku d'iyan masu kud'i".
"ai yanzu babu mai kud'i babu talaka kowa tashi tsaye yakeyi ya nemi na kansa saboda babu wanda kika tab'a gani ya samu da kwance Safiya, saboda haka ki godewa Allah duk halin da kika tsinci kanki domin wani yana can yana neman samu ko rabin matsayinki".
"gaskiya ce maganarki idan zakiyi duba karki dubi wadda ta fiki ki dubi wadda kika fi saboda ki k'ara godewa ubangiji da ni'imar da yayyi gareki".
"haka ne Safiya bari inje gida sai gani na biyu idan ubangiji ya yarda".
"ubangiji ya yarda tun yanzu zaki tafi bazaki bari kici abinci ba".
Nazifa ta gyad'a kanta tace"ana can ana jirana gida wata rana zan ci k'awata".
"uhmm to ki shafamin kan yarana".
"OK".Nazifa ta fice daga cikin parlourn direct bakin get ta nufa tareda shigewa cikin motarta.
*********************
*BAYAN KWANA BIYU*
Fauzeeya ce na hango cikin kitchen bayan ta kammala wanke wanke tana kichaniyar dafa abinci yayinda Tasallah 'yar aiki ke tayata, saboda maigidan ne ya umurceta idan taga matarsa tana ayyukan gida ta dinga tayata sunayi atare, aikinsu sukeyi cikin natsuwa saigasu Sameer sun shigo da gudu suna wasar guje-guje.
Fauzeeya sai kallonsu takeyi cikin so tana murmushi k'unshe afuskarta yayinda suka iso wurinsu suka fad'a cikin Fauzeeya cikin k'auna da shakuwa, rungumesu tayi daga baya ta jaye jikinta anasu tace"ku natsu fa ku daina yin mugun wasa kada kuji ciwo".
"mun bari Aunty".Inji Sameer.
Sameera ta make kafad'arta cikin rashin jin magana tace"nikam saina rama bugun da yayimin sannan zan bari".
Fauzeeya ta dubi fuskar Sameer tace"mi tayi maka da zaka doketa?".
"Aunty ki k'yaleni da ita k'arya takeyimin".
Zumbura baki Sameera tayi tace"kaine mai k'arya bani ba".
Suka tsinkayo muryar mahaifiyarsu tana cewa"Sameer har yanzu bakuga Tasallah bane da kuka tsaya wasar banza".
"mom mun ganta gatanan tafe yanzu".Cewar Sameer cikin masifar tsoron mahaifiyarsa saboda idan sukayi mata laifi ba k'aramin duka takeyi musu ba, shiyasa suke shakku da matuk'ar tsoronta basu cika yi mata laifi sosai.
Tasallah da taji abinda Sameer ya fad'a gabanta ya fad'i hankalinta ya d'unguma kallonsa tayi tace"ke kasan tun d'azu mahaifiyarka ta aikoka ka kirani shine baka gayamin ba saida naji da kunnena ".
"to ai yanzu kinji da kunnenki saboda haka karki dameni! ".
Tasallah ta bishi da kallon mamaki afuskarta tace"ni kake cema karki in dameka? ".
Sameer baice mata k'ala ba yaja hannun Sameera suka fice daga ciki suka shige d'akin mahaifiyarsu, tsaye sakatoto Tasallah tayi tana nazari da mamaki maganarsa amma sai Fauzeeya ta katse mata tunani tace"karki damu da maganarsa bale ta
dameki kinji saboda shi yaro ne ba'a kulawa da batunsa".
Numfashi ta sauke tace"haka ne Auntyn yara".
"wanke hannunki kije Aunty Nazifa tana kiranki kada ki k'arawa kanki laifi awurinta".
"to".Kawai tace ta sanya hannunta cikin ruwa masu tsabta tana wankewa tana kammala wankewa ta sanya ragga ta goge tareda fitowa daga cikin kitchen d'in.
**********************
Tana fitowa ta nufi hanyar zuwa room d'in Nazifa tana isa abakin k'ofar room d'in tayi knocking Nazifa dake zaune saman gado tace"ki shigo ciki mana kin wani tsaya abakin k'ofar d'aki kamar mutuniyar arzik'i ".Cikin sanyi jiki Tasallah ta shigo tsakiyar d'akin ta russuna cikin ladabi tace"gani hajiya ance kina kirana".
Nazifa tayi mata walak'antaccen kallo tace"na ganki ai mi kikeyi akitchen?".
Tasallah ta rasa irin amsar da zata bata jikinta yana mazari tace"ba komai nakeyi ba hajiya! ".
Daka mata razananniyar tsawa tayi tace"k'arya kikeyi bak'ar munafuka zaki gaya mini gaskiyar lamari ko saina koreki kin koma gidan matsiyacin ubanki da bayada komai sai tarin tsummokara! ".
Zuciyar Tasallah ta tsinke hankalinta yayi k'ololuwar tashi fargaba da tsantsar tashin hankali ne ya ziyarci sassan jikinta cikin rawar murya tace"yallab'ai..... ne... yace... idan... na.. ga... Aun...tyn yara tana.... aiki ....in.... din.....ga.... ta....yata".
Cikin matuk'ar hasala da b'acin rai Nazifa tace"shegiyar munafuka nice na d'aukoki aiki cikin gidan nan ko wani banzan yallab'ai da kika ambata!? ".Tasallah jikinta yana karkawa tace"ke kika d'aukoni aiki hajiya "."Saboda haka bari inyi miki kashedi da babbar murya daga rana mai kamar ta yau idan kika k'ara taya banzar matarsa aiki abakin zamanki cikin gidan ya k'are! Idan ba kin rainani ba taya zaki dinga yiwa kishiyata bauta bayan aduniya babu abinda na tsana sama da *KISHIYA*,to akwanakin nan zamu saka k'afar wando d'aya dani dake shege ya fasa 'yar kan durin uwa! ".
"na tuba hajiya kiyi hak'uri ".
"hak'urin mi zaki bani tunda dake ake had'a baki ana munafurtata acikin gidan nan saboda haka ki kiyayeni Tasallah kafin in shuka miki rashin mutuncin da bazaki tab'a mantawa dani ba".
"da yardar Allah bazan sake ba"."Ki sake ma kiga irin hukuncin da zanyi miki babu tausayi bale imani acikinsa! ".Inji Nazifa Tasallah ta marairaice fuskarta kamar zatayi kuka tace"nayi miki alk'awarin bazan sake ba hajiya ".Nazifa ta harareta tace"tashi tashi ki b'acemin da gani makirar k'auye ace ni in d'aukoki aiki amma wata k'atanyar banza ke cin amfaninki".Tana k'arasa maganganunta Tasallah ta mik'e tsaye ta fice daga cikin d'akin da sassarfa tana sharar kwallar zallar takaici domin ita arayuwarta ta tsani cin mutunci da tozarci!.
Akitchen Fauzeeya harta kammala girka abincin rana ta saka cikin babbar kula ta rufe tareda kwasar kulolin tana jerawa adinning table zad tsari da k'awatuwa, bayan ta gama jerawa ta koma cikin kitchen ta had'a lemon juice ta kawo ta aza saman dinning table ta nufi hanyar zuwa room d'inta.
Tana isowa room d'inta ta cire tufafinta ta fad'a cikin bathroom domin ta watsa ruwa ajikinta taji sanyi ta jima tana gurza dukkan sassan jikinta sannan ta d'oraye jikinta ta fito d'aure da towel, kai tsaye saman gadonta tayi masauki ta d'auko lotion da kayan kwalliyarta ta fara shafawa ajikinta sannan ta fara yin kwalliyarta mai k'yau cikin natsuwa, gama kwalliyar keda wuya ta ciro atamfarta mai k'yau d'inkin riga da sicket yayi mata cifcif tareda bayyanar da k'yawon surarta turare ta feshe jikinta dashi, ta jawo pillow ta kishingid'a bayanta akansa ta jawo phone d'inta tana danne dannenta tana murmushi, kallo d'aya zakayi mata ka gane tana cikin jin dad'i da kwanciyar hankali saboda babu abinda ta nema ta rasa awurin mijinta Yaseer.
____________________
Bayan sallar la'asar Yaseer ya dawo daga office hannunsa rik'e da briefcase direct room d'insa ya fad'a yayi wanka atoilet ya fito ya shafa lotions ajiki tareda zura jalabiyarsa black colour ajikinsa, fitowa yayi daga ciki yaja k'ofar ya rufe direct room d'in uwargida sarautar mata ya nufa wato Nazifa.
Yana tura k'ofar room d'in ya shiga ya hangota kwance shame shame saman gado fuskarta tana kallon ceiling ta fad'a cikin kogin tunani, girgiza kansa yayi yana nazarinta cikin tausayawa domin ya hango damuwa da tsantsar tashin hankali a k'wayar idanunta isa wurinta yayi ya shafi boob's d'inta cikin shauk'in so, firgigit Nazifa ta dawo cikin hayyacinta tana masa wani irin kallo mai d'auke da ma'anoni da yawa tace"lafiyarka zaka shigomin ciki d'aki batare da ka nemi izinina ba? ".Dariya ya sanya mata yace"kinada abin dariya nida gidana da matata kice saina nemi izininki ".Acewarsa cikin wasa da zolayarta. Nazifa ta bintsire baki tace"to ai naga nan ba d'akin Fauzeeya bane bale kayi wani yi mini tink'aho da gadara".Yaseer ya kalli fuskar Nazifa cikin nazari yace"ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne ohhh na fahimta kin fara kishina ne ashe dai kina sona har yanzu? ".Nazifa ta tashi zaune tace"akan mi zanyi kishinka bayan ka nunamin kai babban munafuki ne ko acikin munafukkai ka zarce kowa ".Yaseer ya Juyar da kansa gefe yace"ki tauna kalamanki kafin ki fitar dasu Nazifa nifa mijinki ne kisan irin kalaman da zasu fito daga cikin bakinki kafin ki furta saboda zaki