Showing 54001 words to 57000 words out of 87802 words

Chapter 19 - SAKACI BY MUGIRAT MUSA

05 Jul 2024

4238

iya jefa kanki cikin wahala! "."Ai duk abinda nayi maka kai kaja Yaseer saboda haka ka fitarmin daga cikin d'aki domin niba Fauzeeya bace! ".Yaseer ya musk'uta yace"awurina dake da ita duk d'aya kuke Nazifa babu bambanci ".Nazifa tayi charap tace"karya ne da bambanci wallahi! ".Yaseer ya mayarda hankalinsa kacokam wurinta yace cikin sanyin murya da neman sulhu"ki gayamin bambancin dana fara nunawa atsakaninki da Fauzeeya please karki cuci kanki ki gayamin gaskiya ni kuma nayi miki alk'awarin zan baki hak'uri tareda gyara duka kuskurena "..............

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

_Jinjina da godiya mai tarin yawa ga bro Hassan Atk alkhairin Allah ya riskeka har inda kake yayana._


*PAGE 32*


Nazifa ta yamutsa fuskarta tareda bintsire baki zuciyarta cunkushe take da tsagwaron k'iyayyar Fauzeeya da bak'in cikin rayuwa, wani irin zogi da k'una takeyi mata yayinda k'asan ranta wani irin k'ololon bak'in ciki da tsantsar damuwa ya tokare mata a k'irji shiru tayi na mintuna k'alilan kamar baza tayi magana ba sai can ta nisa cikin zafin rai tace" kasan an mayarda aurenka kusa amma baka gayamin ba saboda ka nunamin banida wata daraja da kima awurinka, na tabbatar da kana sona da baka b'oyemin cewar an matso da auren kusa ba yanzu dai nasan matsayina awurinka babu komai ai".Yaseer yayi saurin kallonta yana girgiza kansa cikin rashin jin dad'in kalamanta yace"karkiyimin gurguwar fahimta mana nima banida masaniya akan maida aurena da akayi kusa ba wannan maganar daga magabatanmu ce ba nine nace amatso da auren kusa ba".Nazifa ta bintsire baki zuciyarta cunkushe take da tsagwaron b'acin rai da zafin zuciya tace"k'arya kake Yaseer babu yadda za'ayi ad'aura maka aurenta saida saninka saboda haka ka daina yimin k'unbiya-k'unbiya da cikani da dad'in baki domin bazasu tab'a tasiri azuciyata ba".
Yaseer ya musk'uta cikin bak'in cikin maganarta yace"bazaki tab'a tausasa kalamanki zuwa gareni ba Nazifa wato dai nine mak'aryaci? ".

"kaima kasan duk wanda yaji wannan maganartaka yasan k'arya kakeyi".

Yaseer ya tashi tsaye domin ya tabbatar idan ya cigaba da sauraren bak'ak'en maganganunta zasu iya samun sab'ani atsakaninsa da ita, saboda Nazifa bata tauna magana kafin ta furtata kallonta yayi ya b'oye damuwarsa yace"tunda na lura lalama batayi dake nizan wuce zuwa d'akina duk hanyar da zaki bi ki b'atawa mutum rai kin sani Nazifa, amma ya kamata ki sani ita zuciya ba komai ne take iya jurar agaya mata ba".Yana k'arasa maganarsa yaja k'afafunsa yabar d'akin Nazifa zuciyarsa sai tururin zafi da k'una takeyi masa adalilin rashin iya magana irin na Nazifa.
Harara tabi bayansa dashi har ya fice dogon tsoki mtssssssssss taja kamar bakinta zai tab'o ceiling tace"jishi harni zaizo yana yiwa k'arya da maganganun banza waishi adole ya k'ara sabon aure da sannu zan k'ara bayyana maka muguwar halayyata, daga kai har ita sainayi maganinku acikin gidan nan saina sanyaku cikin k'unci da bak'in cikin rayuwa! Saina haddasa muku tashin hankali da tarwatse duk wani farin ciki naku".Tana kammala yin maganarta ta koma tayi kwanciyarta saman hamshak'in gadonta tareda jawo blanket ta rufe jikinta dayake su Sameer tareda 'yar aiki Tasallah suke kwana.

*********************
Yaseer yana kwance d'akinsa ya kwanta saman gado cikeda damuwa da zafin kalaman Nazifa saboda maganganunta sun sanya k'una da tsantsar rad'ad'i azuciyarsa, bedshit ya jawo ya lullub'e jikinsa yana tunanin farkon had'uwarsa da Nazifa da yadda sukayi soyayya kafin aurensu kamar su cinye junansu,haka ma bayan sunyi auren sunyi soyayya tareda nuna junansu tsantsar kulawa da k'auna amma kamar kar ta had'u da k'awarta Safiya duk ta chanza tsarin rayuwarta da halayyarta.
Juye juye ya dingayi agadon domin kwata kwata barci yak'i zuwar masa dak'yar yake fitar da numfashi mai d'auke da tsantsar damuwa da b'acin rai can dai barci mai nauyi yayi awon gaba da shi.

**********************
Washe gari tunda safe Fauzeeya ta tashi bayan tayi sallar asuba ta share room da parlournta tareda mopping d'insu alokaci guda, sannan ta nufi cikin kitchen ta had'a musu breakfast ruwan zafin ta juye aplask ta rufe, ta d'auka taje saman dinning table ta jajjerasu ta sake komawa ta aza ruwan wanka masu yawa ta juye cikin bucket babba d'auka tayi ta nufi room d'inta.
Tana shiga ta iske Yaseer zaune yayi shiru da yin tagumi kamar marayen da baida uwa ko baba, direct bathroom ta nufa ta surka ruwan da ruwa masu sanyi suka zamo masu d'umi fitowa tayi daga ciki ta isa wurinta mijinta cikin matuk'ar tausayi da yanayin damuwa ta kallesa tace"haba yayana mi yake damunka da har zaka zauna kana tagumi sannan jiya nayi jiranka banga ka kirani ba?".

Jaye hannunsa yayi yaja gwauron numfashi cikeda damuwa kallo d'aya zakayi masa ka gane yana cikin takaici da k'unar zuciya, dak'yar ya samu ya had'iye wani irin abu mai matuk'ar d'aci azuciyarsa yace"kiyimin uzuri my Fauzee damuwa ce ta saka banzo gareki ba jiya ina fatar zakiyimin afuwa".
zaunawa tayi gab dashi kamar zasu shige cikin jikin juna tace"ka daina saka damuwa da bak'in aranka muddin akan Aunty Nazifa ne ya dace ka saba da halayyarta tuntuni saboda kunsan halin juna kun saba da juna, sannan matuk'ar ina tare dakai babu kai babu rayuwar b'acin rai mijina domin kaine rayuwata soyayyarka ta riga tayimin babbar illah azuciyata".

Yaseer yayi murmushi yana tsura mata idanunsa cikin sanyin zuciya da gushewar b'acin rai yace"zanyi k'ok'arin ganin na daina shiga cikin damuwa kinji domin kada na sakaki adamuwa kema".
Langwab'e kanta tayi tana wani kashe murya tace"damuwarka damuwata ce saboda haka ka daina tunanin idan na ganka cikin wani hali bazan shiga cikin damuwa ba,yanzu dai bari mu cire tufafinmu muyi wanka daga baya muyi breakfast".

"OK my Fauzee".Inji Yaseer yana jifarta da kallon soyayya da k'auna.

Tufafinta ta cire ta d'aura towel ajikinta sannan ta tayashi cire nasa tufafi suka fad'a cikin bathroom manne da juna, suna shiga ciki suka cire towel suka dinga cud'ayar junansu cikin shauk'in so da tarairaya, sun dad'e sosai suna wanke sassan jikinsu da lungu sannan suka d'oraye jikinsu suka fito daga cikin bathroom sai murmushi sukeyiwa juna.

Akan gado sukayi masauki Fauzeeya ta d'auko lotion da kayan kwalliyarta ta dawo wurin Yaseer, saida ta shafe masa jiki da lotion sannan itama ta shafe jikinta tareda yin kwalliyarta mai tsari kaya marasa nauyi ta mik'awa Yaseer ya zura ajikinsa itama ta ciro atamfarta awardrobe lemon green colour ta sanya ajikinta yayi matuk'ar yi mata cifcif da haskaka fatar jikinta, shidai sai kallonta yakeyi yana murmushi domin ba k'arya Fauzeeya k'yak'k'yawa ce ta had'u ta ko'ina komai yaji, tana gama shiryawa tayi tsaye agabansa cikin yanga tace"yaya kalleni da k'yau nayi k'yawo sosai?".

Murmusawa yayi yace"wow!My Fauzee agaskiya ban tab'a tozali da k'yak'k'yawar mace ba irinki kinyi k'yawo sosai bari inyi miki picture awaya".

Fauzeeya taji matuk'ar dad'in maganarsa gyara tsayuwarta tayi tace"ok yi sauri ka d'aukeni picture sai muje parlourn muyi breakfast yunwa nakeji".

Yaseer ya jawo wayarsa dake kusa gareshi ya shiga cikin camera ya fara d'aukarta photona kala kala har guda hud'u sannan ya aje phone d'in agadonta yace"na gama muje parlourn".

"to yayana mijina".

Atare suka jera da juna yayinda Yaseer ya mak'ala hannunsa cikin nata tamkar d'iyarsa suka fito tareda jawo k'ofar d'akin suka rufe, suna shiga cikin tsakiyar parlourn direct wurin dinning table suka nufa suka zazzauna saman kujerun dake kewaya Fauzeeya ta tashi sannu ahankali ta zuba musu arish aplate d'aya tareda had'a masa tea mai kauri cikin cup ta aje agabansa itama ta had'a nata ta zauna ta fara cin arish ahankali tana shan tea ayangace, cin abinci kawai sukeyi bakajin maganar kowanensu saida suka k'oshi sannan suka mik'e tsaye zumbur suka dawo cikin parlourn suka zazzauna saman cushion Fauzeeya rungume ajikinsa.

Yaseer sai shafarta sassan jikinta yakeyi yana lumshe fararen idanunsa yace"kayyy fatarki akwai laushi wlh".Fauzeeya sai langwab'ewa ajikinsa takeyi tana wani shagwab'a tace"yayana kenan ina naga laushin fata fararen fata fatarsu tafi laushi".Yaseer ya harareta da wasa yace"to zageni ina namiji ina ni ina laushin fata"."Haka kake gani amma nasan kanada fata mai k'yau yaya".
Yaseer ya d'aga mata gira yace"naji muje d'aki in baki wani irin abu mai dad'i".

Mak'e kafad'arta tayi cikin sagarci tace"nak'i wayon mi zaka bani idan mukaje d'aki?".

Kanne idonsa d'aya yace mata "lada zaki samu".
"ka bari zuwa anjima yaya kaga yanzu ina buk'atar hutu".

Yaseer yace mata"idan baki tashi mukaje ba zan amshi hak'k'ina anan".

Fauzeeya ta ware idanunta cikin matuk'ar mamakin kalamansa murmushi k'unshe afuskarta tace"kana fara cewa ka nemeni aparlour bayan akwai yara dasu Aunty Nazifa cikin gidanka".

"to tunda kina tsammanin bazan iya ba bari in nuna miki".
Zumb'ura baki tayi tace"karma ka fara yah Yaseer banaso".

"kinaso mana my Fauzee".

Yaseer yana rufe bakinsa ya sanya hannunsa cikin rigarta yana mammatsa boob's d'inta cikin matsananciyar buk'ata yana lumshe idanunsa tareda fitar da numfashi, alokacin ne Fauzeeya ta dinga girgiza kanta alamar ya daina domin batason wani ya gifto yaga irin abinda yakeyi mata, kakkaucewa ta farayi ganin yayi tanason kwafsa masa shiyasa ya k'ara mannata a k'irjinsa ya fara tsotsar bakinta.
Can saiga Nazifa ta shigo tsakiyar parlourn kai tsaye batare data ankara dasu ba idanunta suna kallon tiles, d'agowar da fuskarta zatayi idanunta ya sauka akansu da suke rungume da juna Yaseer sai kissing d'inta yakeyi da sauri sauri, Nazifa tsaye tayi turus ta fara salallami tace"subahanillah !Mi zan gani ni Nazifa iskancin naku bai isheku a d'aki ba sai kunzo cikin parlour".

Sai alokacin ne su Yaseer suka dawo cikin hayyacinsu suna ajiyar numfashi tareda jaye Fauzeeya ajikinsa, saida ya natsu yace mata "miye na wani saka salati Nazifa sai kace kinga muna aikata zina !?".

Wani irin d'aci da bak'in ciki ne ya kwaranya azuciyarta idanunta har duhu duhu suke gani akan tsantsar kishin mijinta da k'iyayyar Fauzeeya tace"ai bakuda maraba da mazinata Yaseer domin duk abinda kakeyi da ita cikin d'aki bai isa ba sai kunzo tsakiyar parlourn inda zan iya ganinku saboda ku turamin damuwa da bak'in ciki azuciya, wannan shine adalcin da kake ik'irarin zakayi atsakaninmu!? ".Yaseer da Fauzeeya duk jikinsu yayi matuk'ar sanyi akan kalamanta domin tasan ko itace baza taji dad'i idan taga Nazifa manne ajikin mijinsu ba yana aika mata zazzafan sak'onni, Yaseer yayi nannauyar ajiyar zuciya yace "kiyi hak'uri bamusan baki tafi shago ba Nazifa".Hawaye ne masu zafi suka wanke fuskar Nazifa cikin matuk'ar b'acin rai da tafasar zuciya ta jijjiga kanta tace"hmmmmmmm wannan maganar ba gaskiya bane cin fuska ne"............

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 33*


Yaseer ya girgiza kansa cikin son gamsar da Nazifa ya sassauta murya cikin tattausan lafazi yace"ki fahimceni Nazifa banida niyar inyi miki cin fuska ko in tozartaki duk dayake bak'ya yimin irin abinda mata keyiwa mazajensu domin su k'yautata musu su sakasu farin ciki".Fauzeeya ta marairaice fuskarta kamar zatayi kuka tace"kiyi hak'uri Aunty akasi aka samu bamuyi haka ne ba do......... ".Daka mata tsawar da tayi ne ya katsewa Fauzeeya sauran maganarta taja bakinta tayi shiru saboda har gobe tana masifar tsoronta har cikin zuciyarta. Nazifa ta kalleta awalak'ance cikin kakkausar murya tace"kiyimin shiru ya ina magana da mijina zaki sakamin k'azamin bakinki mai wari da doyi! Wannan maganar ba huruminki bace ki bari inyi magana da tsarana".Yaseer ya logaye wuyansa cikin matuk'ar rashin son fitina yace"huruminta ne Nazifa amma tunda baki kasa da ita bazata sake magana ba"."Look at you kaga kenan kai kake d'aure mata gindi tana iya shegen data gadama idan ba raini ba ina fad'a tana fad'a".Yaseer yace"da tayi miki mi da zakice na d'aure mata gindi? Duka duka kwananta nawa agidan nan kinga nifa banason fad'a da tashin hankali acikin gidana babba yaja girmansa k'arami ya zauna ga kansa!".
Nazifa tayi k'yafci tace"kana nufin kenan ni bana jan girmana ko?"."Ban fad'a ba ke kika d'aukeshi ta wannan fassarar".Nazifa ta gama k'are musu kallo cikin matuk'ar nazari tareda tsagwaron bak'in kishi tace"ba komai zaku gane kurenku daga kai har ita 'yar iskar yarinya".Kammala maganarta keda wuya taja k'afafunta ahasale tabar parlourn ta nufi parking lot zata shiga mota taje shagonsu.

Tana wucewa Fauzeeya tayi rau rau da idanu kwallar zallar takaici ne ta taru cikin k'wayar idanunta alokacin ne Yaseer ya tallabo fuskarta yace"ya akayi ne my Fauzee miye ya b'ata miki rai?".

Tura bakinta tayi cikin sagarci tace"ba kaine ka wani rungumeni ba saida nace maka kar kayi kar kayi tun farko amma kayi kunnen uwar shaggu da maganata to gashinan Aunty ta ganmu da idanunta".

Yaseer ya d'aga kafad'arsa alamar ko ajikinsa bai damu ba yace"to sai mi idan ta ganmu aiba zina mukeyi ba?".

Fauzeeya tayi sakatoto da baki tana kallonsa cikin matuk'ar damuwa tace"hakama zaka fad'a bayan mune sanadiyyar b'ata mata rai".

"to mi kikeson in fad'a ki daina sakawa kanki damuwa? Duk abinda zanyiwa Nazifa baiko kama rabin wanda tayi mini ba saboda tun farko ta saka rayuwata cikin k'unci da bak'in cikin rayuwa! ".

"wannan ai ya riga ya wuce yayana ka daina tunawa".

"nasan haka my Fauzee magana ce ta kawo magana".

"OK barin in d'an kishingid'a barci nakeji"."Muje d'aki ki kwanta"."Nan ma ya isa".Tana rufe bakinta Yaseer ya sunkuceta kamar jaririya ya nufi room d'insa da ita..

*********************
Nazifa tana fisgar motarta tana rusar kukan kishi da tsagwaron bak'in cikin abinda idanunta sukayi tozali dashi, wani irin zafi zuciyarta keyi ta rasa abinda yakeyi mata dad'i aduniya gwamma mutuwarta da ganin wannan mummunan ranar ta yau, tabbas idan bata yiwa abin tufkar hanci ba Yaseer zai iya haddasa mata hawan jini ko ciwon zuciya! Mafita ya dace ta nemo ta fitar da Fauzeeya ko ta halin k'ak'a daga gidan mijinta.
Tafiya takeyi ahankali tana neman yadda zata b'ullowa al'amarin amma ina ta kasa hango wata mafitar, babu jimawa ta kawo bakin get gidansu ta parker motarta awaje domin batason ta jima ciki tanason k'arasawa shago, fitowa daga cikin motar tayi ta fad'a cikin gidan da sassarfa maigadi ya gaisheta ta amsa masa ad'akile.
Shi dai bai lura da yanayinta ta wuce ta gabansa ta nufi hanyar da zata sadata da parlour tana tura k'ofar, ta hango hajiya Ramlat tana kallon news da sauri Nazifa ta isa wurinta ta fad'a ajikinta tana zubar da kwallar zallar kishi da tsagwaron takaicin rayuwa, hajiya Ramlat ta dinga bubbuga bayanta cikin lallashi da tausayin 'yarta ita kanta ta tabbatar kukanta yanada nasaba da mijinta shasshekar kukanta kawai kakejin yana tashi hajiya ta k'ank'ameta tace"kiyi shiru baby ki daina kuka waye ya tab'amin ke yanzu inje inci masa mutunci?

Nazifa tayi ajiyar zuciya tana sauke numfashi kad'an kad'an can ta furta baki tace"Yaseer ne agabana yake amfani da Fauzeeya domin ya sanyani cikin takura da b'acin rai! ".

Hajiya Ramlat ta zabura afirgice cikin matuk'ar razana tace"mi?Shi Yaseer d'in da iliminsa da komai yake aikata haka".

Nazifa ta musk'uta tace"Yaseer d'in da kika sani ada ayanzu ba shi bane Ummuna ya kamata ace anyi wani abu idan ba haka yarinyar nan so take ta fitar dani daga cikin gidan mijina ko ta halin k'ak'a, shiyasa nake ganin idan bamu d'auki kwakkwaran mataki akanta ba zata iya tarwatsamin farin cikina ta sanya 'ya'yana su zamo marayun k'arfi da yaji".

"shakuruminki Nazifa ki kwantar da hankalinki ki cire komai azuciyarki matuk'ar ina raye ban mutu ba babu ke babu kukan takaici, yanzu ki share hawayenki ki tafi shagonki zanyiwa su Baura magana akan su k'ulla mata gadarzaren da zata fad'a ciki inyaso Yaseer ya saketa ki huta da alak'ak'ai wadda ko ubanta ya gaza zama da ita! ".

Nazifa ta mik'e tsaye tana goge hawayen fuskarta tsab tace"ba komai Ummu saina ji kiranki awaya nizan wuce zuwa shago".

Hajiya Ramlat ta gyara zamanta tace"Ok ubangiji ya kaiki lafiya".

"Amin Ummuna".K'arasa maganarta ta fice daga cikin parlourn direct bakin get ta nufa ta shige cikin motarta ta nufi hanyar zuwa shagon..

**********************
Tana isowa bakin shagon ta parker motarta agefe tareda fitowa daga cikin motar rataye da handbag d'inta a kafad'arta, key ta sanya ta kulle motar ta k'arasa ciki taga Safiya tayi d'ad'd'aya saman kujera tana gyangyad'i alamar barci bai isheta ba, Nazifa ta isa wurinta ta dafa kafad'arta cikin tsoro tayi firgigit ta farko tace"a'aaaa sai yanzu kikazo shago miye ya tsayar dake haka? ".Nazifa ta zauna gab da ita cikin sanyin jiki tace"kedai bari Safiya yau nayi mugun gani! ".
Safiya ta razana da kad'uwa akan zancenta mummutsike idanunta tayi tace"subahanillah!K'awata mugun ganin mi kikayi? ".Nazifa ta sassauta muryarta ta yadda babu wanda zaiji abinda zata fad'a tace"Yaseer ne na kamashi aparlour saboda bak'ar jaraba da kwad'ayi yana cin Fauzeeya babu kunya! ".

Safiya tayi mata wani irin kallo tace"na zata wani mugun abun kika gani har kinsa gabana ya fad'i to ai ko ya cita matarsa ce saboda haka ki daina fadar irin wannan maganar".

"sannu uwata hanamin in fad'i abinda nakeso! ".Cewar Nazifa cikeda matuk'ar hasala da suk'uwa.

"aini ban isa in hana miki fad'in duk abinda kikeso ba amma ya kamata ki dinga tunani kafin ki furta magana amma nayi miki uzuri saboda nasan zafin kishi ne yake damunki".

"bazan yi tunani ba Safiya kafin in furta magana".

Saboda Safiya tasan inda ta ajeta yasa ta sauko cikin sanyi sanyi tace"yi hak'uri Nazifa bani nakai zomon ba rataya aka bani yanzu dai bari muyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login