Showing 15001 words to 18000 words out of 87802 words

Chapter 6 - SAKACI BY MUGIRAT MUSA

05 Jul 2024

4226

kam yafi miki rufin asiri".Tana ida maganarta taja k'afafunta ta fice daga cikin parlourn ahanzarce.

Fauzeeya tabi bayanta da harara taja tsoki mtssss tace"aikin banza wawuyar mace kawai mijinki kam saina auresa inga abinda zaki iyayi min, ai kin riga kinyi *SAKACIN* dazan k'wace miki miji kina ji kina gani babu abinda zaki iyayi yara kuma idan na barsu da yunwa kizo ki dafa musu ai yaranki ne ba nawa ba sakaryar mace kawai! ".
Tana kammala maganarta ta mik'e tsaye tareda nufar d'akin dayake mallakinta, tana shiga ta fad'a saman gado sai murmushin jin dad'i takeyi saboda ganin Yaseer ya amince zai aureta.

**********************
Yaseer yana isa gidansu getman ya shek'o ya wangale masa get d'in ya kunna hancin motarsa ciki tareda parker ta aparking lot, fitowa yayi daga ciki ya sanya key ya kulle motar sannan ya tunkari k'ofar da zata sadashi da parlour, da sallama ya shiga cikin parlourn yayinda ya hango iyayensa zazzaune saman cushion suka amsa masa sallamarsa, yana isowa wurinsu yayi mazauni saman carpet d'in dake k'awace cikin parlourn ya gaida iyayensa suka amsa masa cikin sakin fuska, can ya nisa cikin matsananciyar damuwa yace"Abi dama akwai maganar da nakeson in sanardaku kafin in yanke hukunci akai".

Alhaji Taheer ya kalli hajiya Sadiya itama ta kallesa can suka had'a baki wurin cewa"muna saurarenka".

Yaseer ya daure cikin natsuwarsa yace"dama inason in sanardaku cewa aure nakeson in k'ara nan bada jimawa ba saboda ina bukatar k'ara aure".

Su Alhaji Taheer sukayi shiru suna tunani da nazarin maganarsa kowanensu da abinda yake sak'awa azuciyarsa, can suka saukar da numfashi Alhaji Taheer ya dubesa cikin lura da hangen nesa yace"Yaseer aure kakeson k'arawa a ina ka samu yarinyar da kakeso?".

"Abi ba bak'uwa bace awurinku kun santa ba wata bace illa Fauzeeyar dake yiwa Nazifa ayyukan gida".

Alhaji Taheer ya sake maimaita sunan afili yace"Fauzeeya kuma wannan yarinyar da bata kammala secondary school ba mai yiwa matarka ayyukan gida ?".

"itace Abi ai ta kusa kammala secondary school yanzu SS2 take going to SS3".

"to ita tana sonka ne kun daidaita kanku ne kafin kazo kayimin wannan maganar?".

Yaseer yayi murmushi yace "eh mana gaskiya muna son junanmu".Ya fad'a cikin 'yar kunya.

Alhaji Taheer yayi doguwar ajiyar zuciya cikin nazari yace"karka damu zanje nida abokina mu nema maka aurenta amma sai ka bani address d'in gidansu idan mukaje unguwarsu".

"eh to rafin atiku shine sunan unguwarsu sannan gidan kakarta na sani da kunce agwada muku gidan Iya Kulu mai tsamiya za'a kaiku har gidanta".

"na fahimta jibi idan ubangiji ya kaimu lafiya zamuje nemar maka aurenta".

Wani irin sanyi da tsananin farin ciki ne ya kwaranya cikin jini da k'ofofin jikinsa murmushi ne kwance cikin yalwatacciyar fuskarsa cikin matsananciyar murna yace"nagode ubangiji ya k'ara d'aukaka Abi".

"Amin ya rabbi Yaseer karka damu duk abinda zai sakaka farin ciki shi zanyi domin samun kwanciyar hankalinka".

Alokacin ne hajiya Sadiya tayi ajiyar zuciya cikin sanyin murya tace"yanzu Alhaji ka goyi bayan ya k'ara aure bayan kasan wani k'arin nauyi ne?".

"to Sadiya ya kikeson inyi masa so kike inbarshi ya shiga cikin wani matsananciyar damuwa?".

Hajiya Sadiya tace"ganin nayi kamar bai wani jima da k'ara aure ba duka duka yaran Nazifa biyu fa".

"to ai Allah bai hana ba koda ace yaranta d'aya".

Yaseer ya dubi fuskar hajiya Sadiya amarairaice yace"Ummi ki taimaka ki bani goyon baya in k'ara aure saboda ina buk'atar mace mai bani tsantsar kulawa da soyayyar gaskiya".

Kallon tausayawa da k'aunar d'anta tace"Yaseer na amince da aurenka ubangiji ya sanyawa aurenka albarka ya baka zuri'a d'ayyiba ya nuna mana lokacin lafiya".

"Amin ya rabbi "Inji Alhaji Taheer.

"zaka iya tafiyarka Yaseer karkaji komai da yardar Allah zamuje nemar maka aurenta".Cewar Alhaji Taheer yayinda Yaseer ya tashi tsaye ya russuna yace"na barku lafiya".Yana k'arasa maganarsa ya fice daga cikin parlourn direct wurin parking lot ya nufa, tunda getman ya tsinkayosa daga nesa ya wangale masa get ya fice daga cikin gidan ta ya nufi wani wuri.
*********************
Fauzeeya ta chanza tufafinta ta sanya doguwar riga mai adon flowers red da white ta shafa powder da lipstick abakinta, turarenta ta fesa ajikinta ta rataya a kafad'arta ta fito daga cikin room d'inta ta fita daga cikin bakin get gidan.
Tana isa waje ta tari mai keke napep ya tsaya sukayi jinga suka biyasa kud'insa ta zauna cikin kujerar napep d'in, tana zama mai keke napep ya tadda napep d'insa ya tambayeta wace unguwar zai kaita tayi masa kwatancen inda zai kaita.
Tafiya sukayi mai nisa har suka iso cikin unguwar daidai bakin k'ofar gidan kakarta Iya Kulu nan ta tsayardashi ya tsaya, ta fito daga cikin napep d'in ta juya ta shige cikin tsakiyar gidan mai keke napep ya tadda napep d'insa ya k'ara gaba inda zaije.
Tana isa tsakiyar filin gidan babu kowa Fauzeeya ta isa cikin d'akin Iya Kulu ta hangota zaune tana sauraren labaran duniya a rediyo, jin motsin tafiyar mutum yasa Iya Kulu yasa ta kashe rediyon ta kalli Fauzeeya da murmushi k'unshe afuskarta tace"maraba da 'yan unguwar birni".Fauzeeya ta iso wurinta ta zauna gab da ita tace"yauwa Iya na sameki lafiya? ".Iya Kulu ta kalleta tace"lafiya k'alau nake ya mutanen gidanku ?""Duk lafiya k'alau suke Iya sunce agaisheki"...........

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 10*


Iya Kulu tace"ina amsawa Fauzeeya".Fauzeeya ta kalleta cikin fara'a da kwanciyar hankali tace"Iyata"."Na'am Fauzeeya d'iyar albarka".Fauzeeya ta langwab'e kanta cikin shagwab'a tace"inason inyi wata muhimmiyar magana dake saboda haka ki bani aron hankalinki domin mu tattauna cikin natsuwa".Iya Kulu ta gyara zamanta ta mayarda hankalinta kacokam wurin Fauzeeya tace"kar kiji komai Fauzeeya fad'amin sirrin dake cikin zuciyarki saboda bakida wadda ta fini aduniya".Fauzeeya tayi murmushinta mai k'yau tace"dama maganar dazan sanardake shine na samu mijin aure".Ta fad'a cikin kunya da tarbiya.
Iya Kulu ta girgiza da jin kalamanta cikin matuk'ar mamaki tace"da gaske kike fad'a kin samu mijin aure!?".
"Allah da gaske nakeyi Iya kuma yace in gaya muku zai turo magabatansa atsaida lokacin auren".Iya Kulu ta d'aga hannu sama tayi gud'a tace"ayyirurihhhh nanayehh Allah mun gode maka daka nunamin wannan ranar ta farin ciki wa nene saurayinki a ina kuka had'u?".
Fauzeeya ta musk'uta cikin yanayin farin ciki tace"Iya ba kowa bane yace yana sona illa Yaseer mijin Aunty Nazifa".
Rassss gaban Iya Kulu ya fad'i hankalinta yayi k'ololuwar tashi fargaba da tsantsar tsoro ne suka bayyana k'arara afuskarta cikin mutuwar jiki tace"anya Fauzeeya aurenki da Yaseer zai yiyu kuwa ganin nayi kamar cin amana ne da zalunci? Ita fa ta raineki tun kinada shekara goma aduniya har zuwa girmanki ki rasa da irin abinda zaki saka mata dashi sai aure mata miji wannan sam ba halacci bane! ".
Fauzeeya ta b'ata fuska tace"yanzu dai Iya mi kike nufi nufinki bazan auri yah Yaseer ba!?".
"gaskiyar zance bazan lamunta da aurenki dashi ba ko sunzo zan fad'a musu suyi hak'uri wannan auren bamai yiyuwa bane".

Fauzeeya ta aza hannunta saman kai ta b'are baki tanata kuka wiwiwi hawayen takaici sai sintiri sukeyi saman fuskarta cikin tsananin bak'in ciki da guguwar soyayya tace"wayyo wayyo Allah na rok'eki Iya kiyi hak'uri ki barni in auri Yaseer wallahi idan ban auresa ba zan iya mutuwa, wayyo na rasa mai sona cikin wannan duniyar da mahaifiyata tana raye da babu mai yimin irin wannan rik'on sakainar kashi".Tana kammala maganarta ta sake rushewa da kukan haushi harda kwantawa k'asa tana birgima kamar zautatta.

Ganin Fauzeeya ta yamutse ta fice cikin hayyacinta yasa hankalin Iya Kulu ya d'unguma jikinta yana rawa hawayen tausayi sai gangaro mata sukeyi daga cikin idanunta, da sauri ta isa wurin Fauzeeya tasa hannu ta tayarda ita a k'asa tace"tashi kinji yi hak'uri d'iyar albarka da yardar Allah zaki auri Yaseer babu wanda ya isa ya hana miki aurensa sai Allah".Jin kalaman da Iya Kulu ke fad'a yasa Fauzeeya ta daina birgima ta tashi zaune hawaye yab'e yab'e afuskarta tace"da gaske Iya kin amince da aurena dashi?".

"da gaske nake fad'a mana kina zaton zanyi miki k'arya ne Fauzeeya aure kam ai kamar an d'aurashi".
Nan Fauzeeya taji hankalinta ya kwanta tasa hannu ta share hawayen dake saman fuskarta cikin tsananin murna tace"naji dad'i Iya shiyasa nake sonki saboda kina sona da k'aunar duk abinda nake so".

"affff idan ban soki ba wa nakedashi aduniya bayan ke da mahaifinki yanzu dai aramin wayarki in kira babanki yasan duk abinda ake ciki".

Cikin yanga Fauzeeya ta sanya hannu cikin handbag ta ciro phone d'inta dialling nombar mahaifinta tayi sannan ta mik'awa Iya Kulu wayar ahannunta, Iya Kulu ta amshi wayar ta kara akunnenta dayake taji tana ringing can baba Labaran ya d'aga wayar yace"Assalamu Alaikum".
"Wa'alaikas Salam Labaran kana ina yanzu?".
B'angaren baba Labaran yace"a'aaaa Iya ce ina yini".
"lafiya k'alau nake".
"masha Allahu ina kasuwa Iya".
"to idan ka fito daga cikin kasuwa kazo gidana ka sameni".
"ba damuwa Iya ina nan tafe".
"to sai kazo".Tana k'arasa maganarta ta mik'awa Fauzeeya wayarta tace"ki kashe saboda ni ban iya irin wannan wayar mai kamada madubi ba".
Fauzeeya ta katse wayar tana k'yalk'yalar dariyar k'eta tace"keyyyy Iya akwaiki da ban dariya ba madubi ake cewa ba touching screen ake cewa".
"tuching sikiri kike nufi aini ban sani ba? ".Inji Iya Kulu tana son koyon yadda ake fad'a.
Fauzeeya ta sake fashewa da dariya harda rik'e cikinta akan dariya 😂 dak'yar ta tsagaita da yin dariyar tace"ke kam Iya kinada ban dariya wallahi to tunda baki iya ba ki daina fad'a".

Iya Kulu ta hasala da harzuk'a tace"kefa matsalata dake shegen dariyar tsiya uban wa ma ya siya miki waya?".

Fauzeeya ta shanye dariyarta ganin Iya ta hasala tace"mijina Yaseer ya siyamin".

"to mai miji Allah ya sanya Alkhairi".

"Amin Iyata".Inji Fauzeeya.
Firarsu suka cigaba dayi suna jiran zuwan baba Labaran mahaifin Fauzeeya bada jimawa ba saiga sallamarsa ya shigo cikin d'akin, Iya Kulu ta amsa masa cikin walwala fuska asake isowa wurin mahaifiyarsa yayi ya zauna Fauzeeya ta gaidashi cikin yanayin tsoro da shakku dak'yar ya amsa mata yana kallon yadda ta chanza ta koma kamar bashi ya haifeta ba.
Daga baya ya juyo ya fuskanci Iya Kulu yace"Iya gani lafiya kike kirana?".

Iya Kulu ta girgiza kanta Tace"dama dalilin dayasa na kiraka domin in sanar maka cewa Fauzeeya ta samu mijin aure jibi insha Allahu zai turo magabatansa atsaida lokacin aure".

Baba Labaran ya firfito da idanunsa awaje alamar mamaki yace"to madallah Iya waye yake sonta da aure?".

Iya Kulu dayake tasan halin matarsa sarai dole tayi masa k'aryar cewa"a'a ba kowa bane illa mai saida fetur cikin jarkoki yana samun d'an abinda zai iya d'aukar nauyin kansa".

"to shikenan na amince Iya idan ya turo magabatansa jibi sai aturosu gidana ayi komai cikin fahimta da natsuwa babu matsala da yardar Allah".

"Allah ubangiji yayi maka albarka zaka iya tafiyarka Labaran".

"Amin amin".Yace bayan ya tashi tsaye yayi musu sallama tareda ficewarsa daga cikin gidan.

Sai alokacin ne Fauzeeya ta saukar da numfashi tace"Iya bari in lek'a gidansu Adama mu gaisa".
"to babu damuwa sai kin fito".
Fauzeeya ta fito daga cikin gidan ta nufi hanyar gidansu Adama tana isa ta kunna kai sai cikin tsakiyar gidan hango Adama tayi tsaye tana shanya kayayyakin data gama wankewa yanzu, jin sallamar mace ne yasa ta amsa ta waigo ganin Fauzeeya yasa ta shek'o da gudu suka rungume junansu, daga baya suka jaye jikinsu ana juna Adama taja hannunta sai cikin d'aki ta zaunar da ita saman gado itama ta zauna tace"Fauzeeya manyan gari ashe ana ganinki?".
"ana ganina Adama kune manyan gari".

Adama tayi murmushinta Tace"hmmm ya kwana biyu kin b'oye kinyi wuyar gani ya labarin Yaseer masoyinki?".

Fauzeeya ta gyara zamanta farin ciki kwance cikin k'wayar idanunta tace"kedai shine nazo in gaya miki albishirinki k'awata".
"goro fari tasss".
Fauzeeya tayi wani fari da idanunta cikin murna da annashuwa tace"Yaseer ya amince zai aureni jibi insha Allahu za'a tsaida lokacin aurenmu ".

Hak'ik'a Adama tayi matuk'ar mamakin maganarta cikin matsanancin mamaki ta furta baki tace"kayyyyy Fauzeeya na tayaki murna ubangiji ya nuna mana lokacin aurenki lafiya".

"Amin Adama bakiji yadda nake cikin farin ciki ba na matsu in auresa in huta da walak'ancin Nazifa".

"tafdijam! Kice akwai aiki agabanki Fauzeeya anya zaki iya kishi da matarsa Nazifa naga alamar zatayi masifaffen *KISHIN JAHILCI*.

"babu ruwana ko kishin hauka zamuyi ai itace tayi *SAKACI* da k'yak'k'yawan mijinta son kowa k'in wanda ya rasa har na gani inaso saboda haka ni haukar kishinta baya tab'a damuna saina gyara mata zama da koya mata hankali!".

"ai irin wad'annan matan marasa kulawa su suke jawa kansu kishiya da gangan saboda rashin nunawa miji so da tsantsar kulawa agaskiya wurin ga ta nuna wauta da rashin sanin darajar miji".

Fauzeeya ta yamutsa fuskarta tareda bintsire baki tace"ai sai kin gani da idanunki zaki k'ara tabbatarwa da batada kulawa ga miji da yaranta kullum cikin fad'a suke itadashi ko barci batayi ad'akinsa yana gabas tana yamma yana kudu tana arewa "."Ke Fauzeeya da gaske bata kwana dakinsa? Amma wannan matar tayi nisa batajin kira kishiya kawai ce zata gyara mata zama ".Fauzeeya ta kalli fuskar Adama tace"kina tunanin zan gaya miki abinda banida masaniya akai? To ranar nan da bakinsa ya gayamin bata kwana ad'akinsa ".

"hmmmmmm amma Nazifa tayi wayon banza kenan yanzu atakure yake daya k'ara aure Fauzeeya amma Yaseer yanada matuk'ar hak'uri da dangana rayuwarsa zama da irin wannan matar sai mutum yakai zuciyarsa nesa ".

"haka ne gaskiya ai naga hakurinsa k'awata ".

"tabbas yayi hak"uri Fauzeeya ".Cigaba da tattaunawarsu sukayi cikin natsuwa da kwanciyar hankali dayake Inna Amo ta fita gidan mak'wabta yin kitso.
**********************
Baba Labaran yana fita daga cikin gidan Iya Kulu mahaifiyarsa ya nufi hanyar zuwa gidansa yana isa ya afka cikin tsakiyar filin gidan ya hango Inna Munari matarsa tana ba kaji hatsi suna ci sallama yayi ta amsa adak'ile, ya shigo cikin gidan wurinta jikinsa amace saboda babu abinda yake tsoro da shakku aduniya fiye da ita, ganinsa yasa ta k'ara tsuke fuskarta tana jifarsa da muguwar harara tun daga nan yasha jinin jikinsa ya langwab'e kansa cikin sanyin murya yace"lafiya dai Munari waye ya b'ata miki rai kike b'ata fuska haka? ".Dak'yar ta iya furta cewa "kaine Labaran ka b'atamin rai ta yaya inata jiranka tun d'azu ka kawomin nama in dafa inci amma ka nemi wuri kayi zamanka "."Ayyah ubangiji ya huci zuciyarki ba laifina bane Iya ce ta kirani akan maganar auren Fauzeeya ".Dummmm gabanta ya buga amma sai tayi murmushin da baikai zuci ba tace"to ta samu mijin aure ne? Madallah amma nayi matuk'ar farin ciki da jin wannan maganar taka".Ta rufe bakinta ta d'auko tabarma cikin d'aki ta shimfid'a abakin k'ofar d'akin tace"zauna ka bani labarin a ina to ta samu mijin aure? ".Baba Labaran ya zauna ya lank'washe k'afafunsa itama ta zauna kusa gareshi tana jiran taji irin amsar da, zata fito daga cikin bakinsa..........

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 11*


Alokacin ne baba Labaran yayi ajiyar numfashi tareda kallon fuskar Inna Munari cikin shakku da firgici yace"wani mai saida fetur ne abakin titi yace yana sonta shiyasa Iya ta kirani d'azu take gayamini ke miye shawararki?".Inna Munari taji hankalinta ya kwanta damuwarta ta gushe saboda ita duk azatonta Fauzeeya mai kud'i ne zai aureta ashe matsiyaci ne, barin komai tayi cikin zuciyarta ta fad'ad'a fuskarta da fara'a tace"amma gaskiya nayi matuk'ar farin cikin jin wannan maganar na amince ubangiji ya sanya Alkhairi".Baba Labaran ya samu natsuwa na ganin Inna Munari bata balbaleshi da fad'a cikin murna yace"amin jibi zai turo magabatansa atsaida lokacin aurensu saboda haka gobe ki tunamin in siyi kayan cefane masu dama".
Inna Munari ta karkace baki tace"zan tuna maka yanzu dai mik'omin naman da nace ka siyomin".
"to".Yace tareda sanya hannu cikin aljihunsa ya ciro ledar k'unshin nama ya mik'a mata ta amshe ba ko godiya.
Jikinta yana rawa da mazari ta bud'e k'unshin ledar ta fara cin naman da sauri sauri kamar mahaukaciya shidai sai kallonta yakeyi yana mamakin halayyarta da rashin natsuwarta, 😂 amma dayake yana masifar tsoronta babu halin yayi mata magana yanzu su barkace suyita fad'a har mak'wabta suji su lek'o ta katanga, haka ta cigaba da cin naman harta kammala cinyewa ta sud'e takardar naman tass akan tsabar kwad'ayi da shegen buri 😜.
**********************
Fauzeeya tana fita daga cikin gidansu Adama ta koma wurin kakarta Iya Kulu ta bata k'yautar dubu goma Iya Kulu tayita saka mata albarka, sannan tayi mata bankwana ta dawo gidan Yaseer tana dawowa ta fad'a cikin kitchen ta d'ora tukunyar abincin rana tsaye take bata samu ta zauna ba saida ta kammala girka sakwara da miyar stew taji kifi d'anye, sai ta mulmula sakwarar cikin ledodi ta sanya akula miyar ma a k'aramar kula ta zube ta kwashe komai ta wankesu tasss sannan ta kwashi kulolin ta nufi wurin dinning table ta jajjerasu samansa.

Fauzeeya ta juya ta shige cikin d'akinta ta watsa ruwa ajikinta taji dad'i lace d'inta ta sanya pink colour ta murza d'aurin d'an kwalinta mai k'yawo, turare ta feshe jikinta dashi ta sake gyara d'akin ta chanza sabon zanen gado, nufar parlour tayi ta jawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login