Showing 3001 words to 6000 words out of 87802 words

Chapter 2 - SAKACI BY MUGIRAT MUSA

05 Jul 2024

4234

ragu yayinda Fauzeeya ta tsurawa k'yak'k'yawar surarsa idanu tana yi masa kallon k'urilla,shidai bai lura da ita ba abinda yasha masa kai kawai yakeyi .

Fauzeeya sai kallonsa takeyi tana k'udurta abubuwa da dama cikin zuciyarta wani irin shauk'in soyayyarsa da tsantsar k'aunar Yaseer sai fisgarta yakeyi, burinta bai wuce ace ya furta mata kalmar so ba amma tasan hakan yanada matuk'ar wuya wai gurguwa da auren nesa.

*********************
Nazifa ce naga tayi wanka bayan sallar isha'i ta ciro kayan barcinta masu shara shara yayinda su Sameer suna d'aki daban wanda suke barci suda Fauzeeya,kwantawa tayi saman k'asaitaccen gadonta ta fara karanto addu'o'in neman tsari daga sharrin masu sharri ta jima tana kwararo addu'o'in sannan daga baya ta shafa afuskarta ta jawo blanket d'inta ta lullub'e ko'ina ajikinta, ta lumshe idanunta kenan ta fara barci saiga shigowar Yaseer cikin d'akinta sanye da kayan barcinsa mara nauyi jikinsa sai tashin k'amshin turarensa yakeyi, direct wurin Nazifa ya nufa yana isa wurinta ya zauna saman gadon yana murmushin dake k'ayatar da fuskarsa ya shafi gefen fuskarta tareda kwantawa ya rungumota ajikinsa, jin ta fad'a ajikin mutum yasa ta falko dayake batayi nisa cikin barcinta ba.

Ganinsa kusa gareta yasa Nazifa ta yamutsa fuskarta ta jaye jikinta daga nasa Yaseer ya jawo hannunta ya sanya cikin nasa yace"lafiya kike wani jaye jikinki anawa kamar kin fini? ".Nazifa tayi hamma alamar barci ne ke cikin idanunta tace"ka tafi zuwa d'akinka barci nakeji daddyn Sameer ".Yaseer yayi mata wani irin kallo mai nuni da bata isa ba cikin kakkausar murya yace"babu inda zanje ayau sai kin bani hak'k'ina dake rataye saman wuyanki Nazifa kina cutar da rayuwata kina cin amanata wannan sauyin yanayin da kike nunamin ya isheni! ".
Dummmm taji fad'uwar gaba ya ziyarceta wani irin abu ne ya tokare mata a k'irji cikin tsinkewar zuciya da tsantsar fargaba tace"wai miyasa kakeson b'atamin rai Yaseer waikai wani irin mutum ne da baya gajiya dayin abu d'aya? ".Yaseer yayi murmushin dake bayyana hak'ora yace"haka zaki fad'a kice bana gajiya dayin abu d'aya alhalin rabon daki bani hak'k'ina na auratayya harna manta Nazifa, nifa cikakken namijne lafiyayye dole in buk'aci mace amma miyasa kikeson jefa rayuwata cikin had'ari!? ".

Nazifa ta aza hannunta saman kai tace"kayyyy Yaseer nifa gaskiya ban faye son namiji mai yawan buk'ata ba dan Allah ka rabudani barci nakeson yi".Cikin d'acin rai da zafin kalamanta yace"hmmm rayuwarki tana bani matuk'ar mamaki Nazifa ki kalli tsabar idanuna kicemin na faye yawan buk'ata alhalin ko hak'k'ina bak'ya bani "."Naji dai bana baka kaje wurin wadda zata iya baka abunda kakeso nifa ka dameni zaka sani ciwon kai! ".Yaseer ya tashi tsaye yana girgiza kansa cikin jimami da tsantsar takaici azuciyarsa yace "shikenan zan wuce in barki kiyi barci Nazifa sannan ki sani duk abinda kikeyi ubangiji yana sama yana kallonki ".Yana rufe bakinsa yaja k'afafunsa ya fice daga cikin d'akin fuskarsa k'unshe da tsantsar b'acin rai da bak'in cikin rayuwa..............

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 3*


Yaseer yana fita daga cikin d'akin Nazifa ya fad'a cikin d'akinsa cikin zafi da k'unar zuciya akan yawan damuwa har wani irin duhu duhu yake gani cikin idanunsa, dak'yar ya kwanta saman gadonsa yayinda hawayen nadama da takaicin Nazifa suka dinga sintiri asaman k'yak'k'yawar fuskarsa,wani irin tururin d'aci da zogi zuciyarsa keyi ya rasa miyasa Nazifa ta kasa fahimtarsa ya rasa miyasa bazata bashi kulawa shida yaransa ba,ya rasa abinda ta nema ta rasa acikin gidansa dazai sa ta dinga neman kud'i har ya zamo sanadiyar tarwatsewar farin cikin gidansa dana yaransa.
Juye-juye ya dingayi saman gadon zuciyarsa cunkushe da tsantsar bak'in ciki da damuwa ya rasa miyake masa dad'i aduniya,hak'ik'a yayi nadamar auren Nazifa arayuwarsa saboda bata nuna masa tsagwaron k'auna da tsantsar *SOYAYYAR GASKIYA* blanket ya jawo ya lullub'e jikinsa yanata faman tunane-tunane dak'yar ya samu barci mai nauyi yayi awon gaba dashi.

____________________
Washe gari da safe misalin k'arfe shida da rabi 6:30am na safe Fauzeeya ta farka daga barci bayan sallar asuba, ta fad'a kitchen ta had'a breakfast ta d'auko komai ta jajjera saman dinning table, sannan ta nufi cikin d'aki ta shiga cikin bathroom tayi wanka direct wurinsu Sameer taje ta tayardasu daga barci, Sameer ta fara shiga dashi cikin toilet tayi masa wanka sannan tazo ta dauk'i Sameera tayi mata wanka tass tareda lullub'e mata jiki da towel, itace ta shiryasu cikin school uniform d'insu sky blue and white itama ta shirya cikin uniform d'inta na secondary school, tana kammala shiryawa taja hannunsu suka nufi dinning table anan suka isko Nazifa da Yaseer suna yin breakfast babu mai magana daga cikinsu..
Fauzeeya ta jawasu Sameer kujera suka zazzauna sannan itama ta zauna serving d'insu tayi suka fara yin breakfast,sun d'an jima suna cin abincin atsanake cikin kwanciyar hankali sannan daga baya suka jaye hannayensu alamar sun k'oshi, alokacin ne Yaseer ya kalli agogon dake mak'ale ahannunsa yace"kun shirya kufa nake jira".
Fauzeeya tace"eh mun shirya".Tareda rik'e lunch boxes biyu nasu Sameer ahannunta.

Nazifa ce ta wurga mata harara kamar idanunta zasu fad'o daga cikin idanunta tace"Fauzeeya ina zakije alhalin baki kammala gyaramin bedroom d'ina ba?".

Fauzeeya ta marairaice fuskarta kamar zatayi kuka saboda tasan ba k'aramin aikin Nazifa bane ta hana mata zuwa school, cikin tattausan lafazi tace"kiyi hak'uri Aunty idan na dawo anjima zan gyara miki".

"yanzu nakeson kije ki gyaramin kafin jikinki ya gaya miki anjima".

Yaseer dayake rik'e da briefcase d'insa kamar bazaiyi magana ba amma ganin tana son b'ata musu lokaci dole yace"ki bari idan ta dawo daga school ta gyara miki idan bazaki iya barin ta dawo ba ki gyara da kanki ai kinada hannuwa".Yana k'arasa maganarsa ya tisa k'eyarsu Fauzeeya agaba suka nufi parking lot.

Kukan motar Yaseer taji alamun sun fice daga cikin gidan kenan Nazifa ta musk'uta cikin takaicin abinda Yaseer yayi mata tace"zaki zo ki sameni saina ci ubanki Fauzeeya!".Tana kammala maganarta taja k'afafunta ta shige cikin d'akinta batare data tsaya gyara bedroom d'inta ba ta fad'a bathroom sharp sharp tayo wanka ta fito d'aure da towel ajikinta, wurin mirror ta nufa ta jawo lotions ta shafa kayan kwalliya ta d'auko ta tsantsara kwalliyarta mai k'yau sannan ta ciro lace light brown colour ta sanya ajikinta fitted gown ce, takalmi da gyalenta duk kalarsu d'aya ta sanya handbag d'inta ta rataya a kafad'arta tareda jawo k'ofar d'akinta ta rufe.

Parking lot ta nufa direct domin taje gidan k'awarta Safiya maigadi yana hangota ya wangale mata k'ofar get d'in, Nazifa ta sanya key ta bud'e motar ta shiga cikin yanga tadda motarta tayi ta fice daga cikin gidan da masifaffen gudu kamar zata tashi sama, hanyar unguwarsu Safiya ta nufa domin atare suke yin harakar kasuwancinsu cikin rufin asiri.

Ta jima tana tafiya cikin motarta har ta iso bakin get d'in gidan mijin Safiya wato Haidar awaje ta parker motar,sannan ta fito daga cikin motar rataye da handbag d'inta a kafad'a sanya key tayi ta kulle motar ta isa wurin get d'in ta bud'e k'ofar ta shiga cikin tsakiyar filin gidan, babu kowa afilin gidan direct ta shiga cikin tsakiyar parlour hango Safiya tayi zaune tana dudduba kayayyakin da aka aiko musu irinsu dogayen riguna, handbags, shoes, hijabbai, turaren d'aki dana fesawa ajiki da dai sauran kayayyakin da ba'a rasa ba.
Jin takun tafiyar mutum yasa Safiya ta d'ago idanunta suka fad'a cikin na Nazifa zumbur ta mik'e tsaye ta iso wurinta ta rungumeta, fuskarta k'unshe da farin ciki mara misaltuwa dak'yar suka jaye jikinsu ana juna Safiya taja hannunta suka iso saman cushion suka zazzauna, suna zama Safiya ta kalleta cikin fara'a tace"'k'awata kinsha hanya bari in kawo miki ruwa ki jik'a mak'oshinki".

Zata mik'e kenan Nazifa ta rik'eta tace"ki barshi kawai Safiya bana jin k'ishirwa".

"ayi haka k'awata?".

"ba komai ni nace ki barshi".Inji Nazifa yayinda take gyara zamanta.

Safiya ta k'ara bud'e kayayyakin tana kallon fuskar Nazifa tace"kinga kayayyakin da aka kawo mana sunyi matuk'ar k'yawo sosai".

Nazifa tayi murmushi tace"gaskiya sunada k'yawo ba laifi".

Safiya ta numfasa tace"yanzu dai bari in d'auko gyalena mu wuce can shago gaba d'aya domin na fahimci ke ashirye kikazo".

Nazifa ta musk'uta cikin yanayin damuwa tace"kedai Safiya wani abu ke damuna cikin raina wallahi".
Safiya ta tattaro natsuwarta ta mayar kacokam wurin Nazifa cikin sanyin jiki tace"ayyah k'awata mi yake damunki?".

Nazifa ta marairaice fuskarta kamar zatayi kuka tace"Yaseer ne yake yawan damuna akan bana bashi kulawa shida yaransa na rasa yadda zan b'ullowa al'amarin".

Safiya ta yamutsa fuskarta tareda bintsire baki tace"bak'ya bashi kulawa yake fad'a to mi yakeson kiyi masa? So yake ki zauna gida kada kiyi sana'a ki nemi na kanki inyaso sai abinda ya gadama ya baki, ki daina damar da kanki akan maganarsa saboda kwata kwata wannan maganar bata ko kawo kallo ba! ".

"hmmmmmm kedai Safiya harda cewa yakeyi duk abinda ya biyo baya in kuka da kaina".

"dallah shareshi babu abinda zai biyo baya sai alkhairi".

Nazifa tayi ajiyar zuciya tace"shikenan k'awata zan dinga shareshi".

"aiko ni da kike gani Nazifa mijina Haidar yashamin complain akan in daina wannan business d'in in tsaya in kula dashi da yaranmu na nuna masa nikam bazan iya daina business d'in dayake kawomin kud'i ba, yacemin kenan nafison kud'i akansa na shareshi har ya gaji da ji nini ya k'yaleni".

Nazifa ta rik'e baki tace"ashe kice kema mijinki ba baya ba wurin complain ubangiji yayi musu sauk'i".

"ai duk jirgi d'aya ya d'aukosu Nazifa bansan dalilin dayasa mazan yanzu basa son cigaban matansu ba".

"haka suke mafi akasarinsu yanzu dai je ki d'auko mayafinki mu wuce zuwa shagon".

Safiya ta mik'e tsaye tace"to bari in shirya".Tana rufe bakinta ta nufi d'akinta domin ta yafa mayafinta da shigarta cikin d'aki, ta shafa powder tareda feshe jikinta da turare sannan ta yafa mayafi kalar kayanta ta fito daga cikin d'akin ta iso wurin Nazifa dake zaune tana jiranta, tana isa wurinta ta kalli Nazifa tace"na shirya wuce muje ko".

Nazifa ta mike tsaye suka fito daga cikin parlourn direct bakin get suka nufa inda Nazifa ta parker motarta, sanya key Nazifa tayi ta bud'e motar sannan suka shiga ciki suka zazzauna tareda tayarda motar suka d'auki hanyar da zata kaisu katafaren shagonsu.

____________________

K'arfe biyu daidai Fauzeeya ta dawo daga school yayinda ta iskosu Sameer wad'anda suka dawo tun k'arfe d'aya dai-dai, tana dawowa uniform d'inta kawai ta cire ta d'aura towel ajikinta sharp sharp ta watsa ruwa ta fito daga cikin bathroom d'in doguwar rigarta ta sanya mai adon stones red, sannan tayiwasu Sameer wanka ta shiryasu cikin kayansu masu k'yawo direct kitchen ta nufa tana kichaniyar had'a musu abinci shinkafa da miyar stew taji naman kaza k'amshin girkinta duk ya gauraye cikin gidan gaba d'aya.

Ta dad'e tana k'ok'arin ganin abincin ya dahu yana dahuwa ta juye shinkafar cikin kula madaidaiciya miyar ta zube cikin k'aramar kula, sauran kayayyakin data b'ata ta wankesu tasss ta adanasu a ma'adaninsu wanke hannuwanta tayi cikin ruwa masu tsabta, sannan ta d'auki kulolin ta nufi wurin dinning table dasu ta jajjera samansa sannan ta shiga cikin d'akin ta iskesu Sameer sunata wasanninsu.

Kallonsu tayi cikin sha'awa tace"ku tashi muje kuci abinci yarana".

Atare suka mimmik'e tsaye sukace"to Aunty Fauzeeya".

Fauzeeya taja hannunsu suka nufi cikin parlourn direct wurin dinning table suka isa suka ja kujeru suka zazzauna tareda jawo plate agabansu,serving d'in kowa tayi itama ta zauna ta fara cin abinci ci sukeyi atsanake har suka kammala cin abincin suka xare hannayensu, Fauzeeya ta tattaro plates d'in taje ta wankesu tasss akitchen ta adanasu cikin kwando.

Dawowa wurinsu tayi taja hannunsu suka dawo parlour suka zazzauna Fauzeeya ta kunna musu TV suka fara kallo, sun jima axaune saiga sallamar Yaseer ya shigo hannunsa d'auke da briefcase su Sameer suka shek@o da gudu suka fad'a ajikinsa suna yi oyoyo oyoyo daddy, dak'yar Yaseer ya jayesu ajikinsa yaja hannunsu suka iso saman cushion ya zaunar dasu Fauzeeya tayi masa sannu da zuwa ya amsa mata agajiye, direct room d'insa ya nufa domin ya watsa ruwa ajikinsa yaji sanyi ya jima kad'an sannan ya fito da towel d'aure a k'ugunsa, yana fitowa ya nufi wurin wardrobe ya d'auko lotions d'insa yana shafawa ajikinsa yana lumshe idanu yana kammala shafawa ya zura jallabiyarsa ajikinsa, ya d'auko laptop d'insa yana operating d'inta yana daddannawa yana yin wani aiki bai jima da farawa ba saiga Fauzeeya ta shigo cikin d'akin da sallama abakinta hannunta rik'e da tiren abinci, tana isowa wurinsa ta aje tiren agabansa tace"ko akwai abinda kake buk'ata?".

Sai alokacin ne Yaseer yasan ta shigo dago fuskarsa yayi amurtuk'e yace"waye ya baki iznin shigowa d'akina idan ina ciki Fauzeeya!?".

Jikin Fauzeeya ya d'auki k'yarrrma da mazari gabanta sai bugawa yakeyi da k'arfi tace"kayi hak'uri daddyn Sameer ganin nayi ka dawo agajiye shiyasa nace bari in kawoma abinci maybe kana jin yunwa".

"Dakata! Nine nace miki ina jin yunwa? Nasha gaya miki duk lokacin da ina cikin d'aki ki daina shigowa ki bari har saina fita sannan ki shigo, idan badan inada sakaryar mata ba wane matsayi kikedashi awurina da har zaki shigomin d'aki ki daina please banason shisshigi".Fauzeeya ta langwab'e kanta tayi narai narai da idanu tace"haba yah Yaseer don kawai na kawo maka abinci shine nayi laifi to kayi hak'uri bazan sake ba kaji, banason rayuwarka ta b'aci asanadiyyata saboda haka bazan sake ba ".Tana k'arasa maganarta ta fice daga cikin d'akin.

Yaseer yayi shiru na tsawon lokaci yana nazarin maganarta can dai ya saukar da numfashi yace"hmmm Fauzeeya bazaki tab'a gane dalilin dayasa banason ki kusanceni ba ni kad'ai nasan abinda nakeji cikin zuciyata".Yana rufe bakinsa ya cigaba da aikinsa har ya kammala sannan ya jawo plate ya d'ibi abincin yana tsakura kad'an kad'an, can ya tsame hannunsa yasa ruwa ya wanke hannunsa leda ya bud'e ya ciro hollandia yasha domin yaji sanyin cikin zuciyarsa,yasha rabi ya ajiye sauran ya kwanta yanata tunanin rayuwarsa ta baya alokacin dayake cikin kwanciyar hankali da farin ciki, alokacin da baisan miye matsalar rayuwa wani irin yanayi yakejin kansa mai wuyar fassaruwa shi kansa yasan shi namiji ne mai yawan buk'ata da son akula dashi amma babu yadda zaiyi saboda baiyi dace da mace ta gari ba.........

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 4*


Fauzeeya tana fitowa daga cikin d'akin Yaseer ta nufi d'akin dayake mallakinta ta jawo mayafi ta yafa a kafad'arta, fitowa tayi ta wuce ta gabansu Sameer ta nufi hanyar fita daga cikin gidan tana isa waje ta tari mai keke napep tareda biyansa kud'insa inda zai kaita tayi masa kwatance,har suka iso unguwar da kakar Fauzeeya ta wurin uba suna isa bakin k'ofar gidan mai keke napep ya tsaya, Fauzeeya ta fito daga cikin napep d'in ta shige cikin gidan mai keke napep ya tadda napep d'insa ya k'ara gaba.
Fauzeeya tana isa tsakiyar gidan ta hango Iya Kulu zaune saman tabarma tana dama fura taji nono sai girgiza kanta takeyi,Fauzeeya ta iso wurinta da sallama abakinta ta zauna gab da kakarta Iya Kulu ta dubeta cikin mamakin dawowarta gida yanzu tace"Fauzeeya 'yar kaka ya akayi ne kika dawo gida yanzu ko wani abu ne yake faruwa?".
Fauzeeya ta shagwab'e fuskarta tareda bintsire baki tace"babu komai Iya kawai dai nazo ne domin in gana da k'awata Adama".
Iya Kulu ta rik'e baki tace"hmmm iyayin banza gareki Fauzeeya yanzu akan kinason ganin Adama ne shiyasa kikazo ganinta".
Fauzeeya ta zumb'ura baki tace"eh mana ke Iya kin cika ganin nisan da unguwar da muke zaune".
Iya Kulu ta harareta da wasa tace"unguwar da kike akwai nisa mana yanzu dai ya mutanen gidanku?".
Fauzeeya tace"lafiya k'alau suke".
Iya Kulu tana kammala dama furar ta d'ibawa Fauzeeya nata akofi tace"gashinan kisha idan kika gama shan furar sai kije gidansu".
Fauzeeya ta d'auki kofin furar ta kafa kai ta shanye furar sannan ta ciro kud'i abakin gefen zanenta ta mik'awa Iya Kulu dubu uku tace"Iya ga kud'i nan ki samu na cin goro".
Iya Kulu ta amshi kud'in cikin tsantsar farin ciki tace"kayyyy nagode sosai Allah ubangiji yayi miki albarka ya jik'an mahaifiyarki".
Fauzeeya taji dad'in addu'arta sosai har cikin zuciyarta da sassan jikinta tace"amin ya rabbi Iya nizan wuce zuwa gidansu Adama".
Iya Kulu tace"to..to.. d'iyar albarka idan kin koma gida ki gaida ubangidanki Yaseer".
Fauzeeya tayi murmushin dake tattare da bak'in ciki tace"zaiji da yardar Allah".Tana k'arasa maganarta taja k'afafunta ta nufi hanyar zuwa gidansu Adama.

**********************
Tana isa tsakiyar gidan ta hango Inna Amo mahaifiyar Adama da Adama zaune saman tabarma suna fisgar sure suna sanyawa cikin roba, Fauzeeya ta isowa wurinsu ta duk'a har k'asa ta gaida Inna Amo Inna ta amsa mata fuskarta asake tace"ya Iyarki Fauzeeya?".
Cikin kunya tace"lafiya k'alau take Inna".
Fauzeeya ta mik'e tsaye yayinda Adama ta tashi tsaye tana kallon fuskar Fauzeeya tace"mu shiga cikin d'aki Fauzeeya zaman gidan Yaseer ya amsheki fa".
Fauzeeya tabi bayanta suka shige cikin d'aki suka zazzauna saman gadon Inna Amo, alokacin ne Fauzeeya ta kalleta cikin fara'a tace"ban gane zama gidan Yaseer ba ya amsheni bayan kinsan ina cikin matsananciyar soyayyarsa?".
Adama ta saukar da numfashi tace"ina nufin kinyi k'iba kin k'ara k'yawo kina bani mamaki Fauzeeya taya kina zaune gidansa amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login