Showing 60001 words to 63000 words out of 87802 words

Chapter 21 - SAKACI BY MUGIRAT MUSA

05 Jul 2024

4246

tantsama tantsama ai daga gani babu tambaya zuk'ar abinsa yakeyi adole shi ga jarababbe".

Fauzeeya taji matuk'ar zafin k'azafin da sukeyi mata harda jifarta da kalmar mazinaciya idanunta suka cicciko da ruwan hawaye kamar zata fashe da kuka,kasa cewa komai tayi saboda tana masifar tsoronta har zuciyarta.

Safiya ta bintsire baki tareda yi mata kallon k'urilla can tace"ai daga gani babu tambaya tun awaje yarinyar nan ta fara bin mazan banza shiyasa kikaga k'ugunta ya bud'e sosai".

Nazifa tayi nuni da hannunta zuwa wurin Fauzeeya tace"duk iskancinta ubanta Labaran ko sonta bayayi saboda tun mahaifiyarta tana raye yake walak'antata akan Inna Munari, in tak'aice miki har bak'in cikin ubanta ya kashe uwarta amma yanzu kinga tazo ta auremin miji domin ta fitar dani daga cikin gidan ko ta halin k'ak'a! ".

Safiya tace"wannan ne kuma bata isa tayi kad'an itadai zata bar gidan bake ba saboda itace ta fara iskoki ba kece kika iskota ba".

Nazifa ta kalli fuskar Safiya tayi mata alamu da idanunta ta taso Safiya ta tashi tsaye ta k'araso wurinta tace"muna b'ata lokaci fa Nazifa ya kamata muyi abinda ya kawomu mu wuce".

"haka za'ayi kafin lusarin mijinki ya riskemu anan".Cewar Safiya cikin matuk'ar makirci da azuzanci irin nata.

Fauzeeya cikinta ya bada k'ululululu duk dayake bata fahimci inda maganarsu ta dosa ba amma ta hak'ik'ance ba alkhairi bane ya kawosu wurinta, gadan-gadan suka tunkari wurin Fauzeeya wadda take zaune saman carpet atsorace take kallonsu tana cewa"lafiya Aunty mi yake faruwa ne wai?".

"uwarki ce ke faruwa 'yar iskar yarinya wadda ta gama rabon mutucinta atiti! ".Inji Nazifa azafafe.

Fauzeeya ta dinga ja da baya su kuma suna k'ara tunkararta babu alamun tausayi ko rahama afuskarsu, ganin tayi tabbas da gaske akwai mugun nufin dake cikin zuciyarsu yasa tayi wuf zata tsere Safiya ta rik'ota cikin matuk'ar zafin nama da b'acin rai tace"ke atunaninki zaki iya yi mana wayo ki gudu to babu inda zakije sai munyi dukan tsiya jikinki yayi tsami sannan zaki fahimci cewa kishi damu ba alkhairi bane! ".Fauzeeya ta tsure tayi wuru wuru da idanunta tsagwaron shakku da tsantsar firgici ne ya shimfid'u saman fuskarta alokacin ne tururin zafi da k'una ya ziyarceta cikin matuk'ar mamakin maganarta tace"kuyi hak'uri Aunty dan Allah kada ku cutardani saboda banyi muku komai ba!".Cikin suk'uwa da tafasar zuciya Nazifa tayi mata dundu abaya da k'arfi wanda asanadiyyar haka saida ta durkushe k'asa ta saki rikitaccen kuka mai ban tausayi wani irin rad'ad'in ciwo ne ya ziyarci k'wak'walwarta da rayuwarta hawaye masu zafi sai sintiri sukeyi afuskarta.
Alokacin ne Nazifa ta juyo ta dubi fuskar Safiya tace"rik'emin ita bari in d'auko bulala in zane mata jiki".
"to yi sauri ki fito".Fad'ar Safiya saboda ita atsorace take nunawa ne kawai batayi domin tasan idan har Yaseer yazo ya taras da aika-aikar da suke yiwa amaryarsa zai iya sanarwa mijinta Haidar ita kuma ta tsani duk wanda zai iya kawo mata cikas arayuwa, Nazifa ta shige cikin room d'inta saigata ta fito rike da sharb'eb'iyar dorina ahannunta tsirara tana isowa wurinta batayi wata wata ba ta yankawa Fauzeeya bulalar ajikinta ai kuwa nan da nan ta saki razananniyar kuwwa da k'ara tana zubar da kwallar zallar takaici da tausayin rayuwarta.

Ruwan bulalle kawai sukayita zuba mata ajiki tana tsalle da ifface -ifface kamar zautacciya risgar kukanta takeyi jikinta sai k'yarrrma da kad'uwa yakeyi kafkafkaf yayinda ta had'a gumi alokaci guda! Tasallah dake lab'e abayan cushion tana lek'onsu jikinta sai mazari da makarkatar tsoro yakeyi cikinta sai k'ugin firgici yakeyi nan da nan gumi ya dinga tsattsafowa yana tsiyaya ajikinta!.
Cigaba daba Fauzeeya ruwan bulalle ta ko'ina ajikinta sukayi saida sukayi mata lik'is da matsiyacin duka sannan suka ja suka tsaya mayarda numfashin gajiya da nishi, ita kuma gata ak'asa kwance shame shame a carpet batada kwalin ceto jikinta duk yayi jajir kwancin bulala ne bayyane afatarta rud'u rud'u zad tausayi dak'yar take fitarda numfashin wuya da galabaita! Wani irin azababben zafi da rad'ad'in ciwo jikinta yakeyi tabbas ta k'ara tabbatarwa ayau idan Nazifa ta samu sa'arta zata iya kasheta kowa ya huta domin duk yadda take zato ko tsammani ta wuce tunaninta haki ta dingayi sannu sannu hawaye sai sintiri sukeyi afuskarta kamar an bud'e famfo.

Nazifa ta nunata da yatsa tace"ba kin zab'i kiyi rayuwar aure da mijina ya ciki kamar yadda yake cina kin matsu ayi aure ya zura miki jijiyarsa cikin k'ugunki alokacin da kina waje, to wlh ki shirya tarbon bala'i da masifa arayuwarki kinyi bankwana da farin ciki da jin dad'i har abada kin gwammaci ki kasance cikin k'unci da uk'ubar rayuwa".

Tasallah tana sauraren duk irin kalaman da suke fitowa daga cikin bakinsu, tanason tazo ta k'waci Fauzeeya ahannunsu amma bazata iya domin tasan hakan zai iya sa asirinta ya tono!. Nazifa ta musk'uta cikin yanayin mugunta tace"yanzu ki jirani in d'auko wuk'a in yanke mata boob's kowa ya huta".

Safiya tayi saurin kallonta domin ta gasgata abinda ta fad'a cikin idanunta ta hango gaskiyar lamari cikin matuk'ar razana tace"da kin k'yaleta haka domin ta jigata sosai Nazifa ko so kike mijinki ya riskemu? ".

"bazan iya k'yaleta ba saboda nasha alwashin saina nakkasata ko wancan karon dak'yar tasha ahannuna da tuni labari yasha bamban".

"naji je ki d'auko wuk'ar ina jiranki ko gobe! ".

"bazaki duk jirani zuwa gobe ba ina zuwa yanzun nan zan fito akitchen".Nazifa tana rufe bakinta taja k'afafunta ta shige cikin kitchen d'in.
Tana ficewarta Fauzeeya ta d'ago idanunta da suka kumbura akan yawan kuka dak'yar tana cize baki tana nishi ta tashi zaune, marairaice fuskarta tayi cikin rauni tace"Aunty Safiya dan girman Allah ki ceceni ki taimakamin in gudu cikin d'akina kada matar nan ta iskoni ta salwantamin da rayuwa wlh so takeyi ta kasheni inbar duniya! ".Safiya ta harareta tace"taya zan barki ki gudu idan ta tambayeni ince mata kin gudu!? Wannan maganar bazata tab'a yiyuwa ba".

Fauzeeya ta langwab'e kanta tayi narai narai da idanunta cikin zullumi da fargaba tace"wayo zakiyi mata Aunty kice mata na tureki kin fad'i shiyasa nayi galaba akanki na tsere ".

"bazanyi ba gara ki hakura da rok'ona! ".

Fauzeeya ta fashe da kuka ta fara magiya da rok'onta akan ta ceci ranta ta bari ta gudu cikin d'akinta, tasan idan Nazifa ta cimmata aparlour zata iya halakata abanza akan bak'in kishi da tsagwaron k'iyayya! Har yau bata d'ebe ran Safiya zata iya barinta ta shige cikin d'aki tace"ki taimakamin idan kika ceceni duk abinda kike buk'ata zanyi miki! ".Sai alokacin ne Safiya ta musk'uta tace"na amince zan barki ki gudu cikin d'akinki amma bisa sharad'i guda"."Mi nene sharad'in fad'i koma miye nayi matuk'ar yi miki alk'awarin zan zanyi ".Safiya ta yamutsa fuskarta tace"sharad'in shine duk rintsi duk wuya idan mijinki ya tambayeki akan su waye sukayi miki shegen duka kada ki kuskura ki ambaci sunana idan kika ambaci sunana saina yi miki abinda har abada bazaki tab'a mantawa dani ba! "."Jikinta yana rawar tsoro tace"wannan shi yafi komai sauk'i awajena "..............

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 36*


Safiya taji matuk'ar tausayinta akaro na farko har cikin zuciyarta tace"tashi kiyi sauri ki shige d'akinki kada ta riskeki anan babu kuma ruwana"."To nagode sosai Aunty ubangiji ya rufa miki asiri duniya da lahira".Tana k'arasa maganarta ta mik'e tsaye ta fad'a d'akinta da sauri tareda sanya sakata ta rufe d'akinta.
Safiya tayi kwance rigiggine saman carpet cikin makirci da shahara akan azuzanci tana fitar da numfashin munafurci, can saiga Nazifa tik'is tik'is rike da sharb'eb'iyar wuk'a ahannunta ta iso tsakiyar parlourn taga Safiya kwance rai ahannun Allah tana nishi da sauri ta yassuwa wuk'a k'asa ta taimaka mata ta jinganar da ita acushion tana yi mata sannu tace"Safiya ta yaya hakan ya faru ina Fauzeeyar take ban ganta ba aparlour".

Nishi takeyi dak'yar tace"tunkud'eni tayi ta shek'a da gudu cikin d'akinta!".

Ta hasala sosai cikin k'unar zuciya tace"lallai yarinyar nan ta cika hatsabibiya irin yadda tayimin afarko shine tayi miki tabbas saita walak'anta cikin gidan nan tunda ni take yiwa yawo da hankali!".

Safiya ta logaye kamar da gaske tace"taimakamin mubar cikin gidan nan kafin mijinki ya dawo asirinmu ya tonu! ".

"to.. to.. sannu ubangiji ya baki lafiya".Tana k'arasa maganarta ta taimaka mata ta dafa kafad'ar Safiya ta mik'e tsaye tana cize baki da lumshe idanunta, jan hannunta tayi suka fice daga cikin gidan da sauri abakin get suka shige cikin motar Nazifa ta sakata cikin motarta suka fice daga cikin unguwar da matsiyacin gudu..

Tasallah dak'yar taga sun fice daga cikin gidan ta fito daga inda take b'oye duk jikinta yayi sharkaf da zufa tana isowa tsakiyar parlourn ta hango wukar da Nazifa ta d'auko akitchen, ta mance da ita k'asa sanya hannunta tayi ta d'auketa ta nufi kitchen da ita ta adana wurin daya dace.
Tana aje wuk'ar ta fito daga cikin kitchen d'in ta fad'a da sassarfa cikin d'akinta ta sanya key saboda gudun kada su Nazifa su sake dawowa taga abinda yafi k'arfinta,kwantawa tayi saman gadonta tana jinjinawa rashin mutuncin Nazifa da rashin imani irin nata...

**********************

Fauzeeya tana fad'awa cikin d'akin ta cire tufafinta ta aza ruwan zafi ta juye abucket ta zuba ruwa masu sanyi ta fad'a cikin bathroom domin ta gasa jikinta, domin duk jikinta tsami da ciwo yakeyi mata zuciyarta cunkushe take da tsagwaron takaicin abinda sukayi mata da kuma ja musu Allah ya isa yafi shurin masaki! Ta dad'e tana gurza dukkan sassan jikinta sannan ta d'oraye jikinta ta fito d'aure da towel direct wurin dressing mirror ta zauna murza lotion kawai ta shafa powder da lipstick abakinta, rigarta ta ciro adrower ta zura sannan tayi kwance rigiggine saman gado hawayen bak'in ciki sai kwaranya sukeyi afuskarta, ji takeyi duniyar gaba d'ayanta tayi mata bak'ik'irin ji takeyi kamar ta kashe aurenta ta huta da bak'in ciki da tsantsar takaicin rayuwa, alal hak'ik'a ta lura wasu matan basuda imani da tausayi ko kad'an azuciyarsu sannan muddin akan kishiya ne zasu iya aikata koma miye arayuwarsu..

Yaseer ya danno hancin motarsa tsakiyar filin gidan tareda parker motar aparking space, sannu ahankali ya fara zura k'afafunsa awaje cikin tafiyar mazantaka da k'asaita briefcase d'insa ya d'auko ya maida k'ofar ya rufe ya sanya key, direct cikin parlourn ya iso babu kowa dakinsa ya wuce ya cire tufafinsa ya fad'a bathroom ya sakarwa kansa shower wanke yakeyi amma zuciyarsa tana wurin Fauzeeyarsa abar kaunarsa, yana gama wanka ya fito d'aure da towel lotion ya shafa ajikinsa ya jawo turarurkansa ya feshe jikinsa dasu jalabiyarsa dark green colour ya jawo ya zura ajikinsa, cikin so da tsantsar muradin son ganin Fauzeeya ya fito daga ciki ya nufi room d'inta cikin shauk'in so da begenta zuciyarsa sai azalzalarsa takeyi akan yaje gareta.

Yana tura k'ofar room d'in ya shiga ciki zaune ya ganta tana karatun labarai na ban dariya aphone d'inta jin alamar an shigo yasa ta d'ago kanta idanunta suka fad'a cikin nasa murmushi ta sakar masa, ta mik'e tsaye ta aje phone d'in ta iso wurinsa ta fad'a saman k'irjinsa cikin matuk'ar k'auna da soyayyar gaskiya Yaseer ya k'ank'ameta yana shafar k'yak'k'yawar fuskarta tsurawa fuskar juna sukayi ido sukayi na mintuna k'alilan kamar an tsikareta ta numfasa tace"sannu da dawowa yayana".
Yaseer ya lumshe idanunsa can ya bud'esu tarrrr akanta wani irin sinadarin so yake nuk'urk'usar zuciyarsa yace mata"yauwa my Fauzee ya hidimomin gida?".

"k'alau yaya".
Yaseer ya jayeta ajikinsa yaja hannunta sukayi masauki saman gadonta suna ajiyar zuciya kallonta yayi yace"ke kad'aice cikin gidan nan ko?".

"mi ka gani dear?".

"naga banji motsin kowa ba".

Fari da idanunta tayi ta kwanta saman k'afafunsa tace"bani kad'aice bace cikin gidan nan saidai ban sani ba ko Tasallah ta fita".

Yaseer yayi murmushi k'unshe afuskarsa yace"ok na fahimta yanzu bari in baki ajiyata".

Ta d'ago fuskarta da sauri tace"wace irin ajiya kuma yaya?".

"auuu ke bakisan irin ajiyar dazan baki ba?".

Ta girgiza kanta alamar eh mana bata sani ba Yaseer yasa hannu ya tallabo fuskarta yana jifarta da kallon k'auna, yayinda cikin k'ark'ashin zuciyarsa soyayyarta ta riga tayi kane kane aransa bayada wani buri illa ya kasance da ita har k'arshen rayuwarsa.
Bud'a baki yayi yace"ina nufin in baki ajiyar d'a ko d'iya acikin mararki".

Sa hannu tayi ta rufe fuskarta cikin kunya tace"kayyy yaya bakada kunya fa".
Yaseer ya juya yana kalle kalle kamar yana neman wani abu aroom d'in yace"ina kunyar take ne in kamota in d'aure yanzu nan?".

Fauzeeya ta jaye hannunta saman fuskarta tace"ba'a ganinta mana".
"OK na zata ana ganinta ne".

"ba'a gani nace maka".

Tashi zaune Fauzeeya tayi Yaseer ya dinga bin fatar jikinta da kallo tsab can yaji gabansa ya buga da k'arfi zuciyarsa ta bashi cewa akwai abinda ya faru bayan yaje office, jikinta yaga yayi rud'u rud'u da kuma ja cikin matuk'ar dabara da wayo yace"my Fauzee muga hannunki".
Batare data kawo tunanin komai azuciyarta ba ta mik'a masa hannunta rik'ewa yayi yana nazari da tunani, zanenta ya d'aga yaga nan ma yayi rudu rudu da kwancin bulala hankalinsa ne ya tashi gudun bayason ya zargi abinda bai gani ba yasa yace"miyasa jikinki yayi jawur haka?".

Kamar daga sama taji ya jefo mata wannan tambayar jikinta ya dinga k'yarrrma tsantsar fargaba da zullumi ne ya bayyana afuskarta, amma saboda ta iya tako tayi k'ok'arin yalwata fuskarta da murmushi tace"babu abinda yasa jikina yayi jawur ina ganin sauyin yanayi ne".Tace tana duk'ar da kanta k'asa domin bazata iya kallon cikin k'wayar idanunsa ba ta gaya masa k'arya.

"oyahh d'ago idanunki ki kalleni ki gayamin abinda kika fad'a yanzu".

Runtse idanunta tayi zuciyarta tana fat fat fat cikin tsoro tace"bazan iya ba dan girman Allah kabar zancen ya wuce".

"awurinki ya wuce ba ki gayamin gaskiyar abinda yake faruwa cikin gidan nan bayan wucewata!?".

Fauzeeya ta dafe kanta cikin rashin son yawan tambaya tace"babu abinda ya faru dear".

"shikenan zanyi bincike in gano abinda ya faru bayan tafiyata sannan ki kalleni da k'yau niba k'aramin yaro bane irinki da zaki sharamin k'arya in yarda, duk abubuwan da kike b'oyemin suna dawowa kunnena ina sharewa ne domin banason in tada fitina cikin gidana".

Tayi rau rau da idanu tace"please yaya kabar maganar ta wuce kasan ubangiji ya la'anci mai tada fitina adoron k'asa".Naji shin in tambayeki ne ko bakida gaskiya cikin wannan al'amarin ne da kike k'umbiya k'umbiya da magana cikin zuciyarki kin dameni da magiya fa?".

"ba haka bane nidai kabar maganar nace".

"Fauzeeya kenan ke k'aramar yarinya ce bakisan ciwon kanki ba shiyasa kike fad'ar wannan maganar, karki manta ke d'in amana ce awurina matuk'ar ina numfashi bazan lamunci abinda zai cutarmin dake ba kalli yadda jikinki yayi rud'u rud'u na kwancin bulala kamar na auro jaka! Yanzu misali idan danginki suka kawo miki ziyarar ba zata suka riskeki ahaka mi kike tunanin zasu d'aukeni? Azzalumi mai dukan matarsa saboda haka bazan lamunci irin haka amayarmin dake kamar baiwa! ".

Cikin tsinkewar zuciya da tattausan lafazi tace"baza suce komai domin sunsan aure bauta ne kuma shi nakeyi".

Yaseer ya sance jikinsa ahankali ya mik'e tsaye yace"kwata kwata bakida gaskiya cikin maganarki saboda haka nizan wuce zuwa d'akina domin kada in cigaba da sauraronki rayuwata ta b'aci ".Yana kammala maganarsa yaja k'afafunsa ya fice daga cikin d'akin yabar Fauzeeya hankalinta atashe gabanta sai luguden tsoro da fargaba yakeyi mata saboda tasan idan ya gano gaskiyar zance zaiyi mata fad'ar k'aryar da tayi masa sannan kuma wutar gaba da k'iyayya zata k'ara haddasa atsakaninta da Nazifa, addu'a takeyi azuciyarta ubangiji yasa babu wanda yaga lokacin da suke dukanta,kwantawa ta jawo pillow ta aza kanta samansa kenan ta nasa azuciyarta Yaseer yanada labarin cewa matarsa itace ta koreta alokacin data komai gidan kakarta Iya Kulu mai tsamiya....

Yaseer yana fita room d'inta bai zarce ko'ina ba sai abakin k'ofar d'akin Tasallah 'yar aiki tura k'ofar yayi sannu ahankali kamar mara gaskiya saboda bayason Fauzeeya ta ankara da abinda zaiyi, azaune ya hango Tasallah tsaye yayi nesa da ita yana k'are mata kallo cikin matuk'ar damuwa ya kira sunanta"Tasallah".

Tasallah jin an kira sunanta yasa ta waigo tace"na'am yallab'ai".Cikin kunya da ladabi tana wasa da yatsun hannunta domin yayi matuk'ar yi mata kwarjini bazata tab'a iya kallonsa ba.

Ajiyar zuciya yayi cikin matuk'ar tsantsar takaici da damuwar dake shimfid'e afuskarsa yace"bayan wucewata office miye ya faru!? ".

Dummmm gabanta ya fad'i tsantsar tsoro ne ya bayyana afuskarta cikin sanyin jiki tace"babu abinda ya faru".

"keee! Karki nemi kiyimin yawo da hankali fa ki gayamin gaskiyar al'amari fa banason k'arya!".

Jikinta yana makarkata cikin yanayin zullumi hawaye suka wanke mata fuska alokaci guda tace"zan gaya maka gaskiyar zance yallab'ai amma dan Allah karka bari hajiya tasan nice na gaya maka domin nasan idan ta sani abakin aikina!"."Calm down bazan gaya mata komai ba ki kwantar da hankalinki babu wanda zaiji abinda kika gayamin".Tasallah ta gyara zamanta cikin firgici tace"d'azu ina bayan cushion neman k'afar takalmina daya bace to alokacin Auntyn yara tana jajjera kuloli saman dining table saigasu hajiya sun shigo babu ko sallama cikin tsakiyar parlourn................... ".Labarin duk irin maganganun da sukayi da dukanta da sukayiwa Fauzeeya duk saida ta gaya masa babu abinda ta b'oye, saida ta dasa aya zuciyarsa ta cika fam da bak'in ciki da tsantsar takaicin duk'ar masa mata da sukayi wani irin d'aci ya had'iye mai matuk'ar d'aci mak'wat a mak'oshinsa idanunsa suka kad'a sukayi jajir akan tsantsar b'acin rai da tsantsar zuciya, kallonta yayi ita duk ta tsorata da chanzawar yanayinsa cikin matuk'ar b'acin rai yace"nagode sosai da kika gayamin gaskiya Tasallah".Yana ida maganarsa ya zare jikinsa ya fice daga cikin d'akinta.

Fuuuuu ahasale ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login