Showing 48001 words to 51000 words out of 87802 words
daban da niyar gobe bayan an d'aura auren arabawa abokan arzik'i.
Washegari da safe misalin k'arfe goma daidai na safe babu zato ko tsammanin da yawa daga cikin mutane sukaji d'aurin auren _Yaseer Taheer da amayarsa Fauzeeya Labaran_ wanda dubban mutane suka shaida d'aurin aurensu amasallacin dake unguwarsu.
Mutanen unguwar sunyi matuk'ar mamakin yadda aka k'ara matso auren kusa tareda yi musu fatar alkhairi da addu'ar ubangiji ya basu zuri'a d'ayyiba, ko'ina ga duba kawunan mutane ne birjik babu laifi mutane sun taru da yawa bayan an gama d'aurin auren lafiya mutane suka fara watsewa, bayan mutane sun ragu ango Yaseer ya dinga gaisawa bakinsa ya kasa rufuwa akan tsantsar farin ciki da murnar da yake ciki mara misaltuwa.
Acan gidansu baba Labaran kuwa Iya Kulu sai hidima da d'awainiya da jama'a itada Adama, komai sune jagora cikin al'amarin auren Fauzeeya saboda Inna Munari ko nan da can bataje ba kuma matan dake sintiri suna shigowa idan suka gaidata bata amsawa, haka dai suka shareta suka cigaba da sha'anin gabansu yayinda zuciyar Inna Munari tayi bak'ik'irin sai zafi da k'una takeyi mata ta rasa mi yakeyi mata dad'i aduniya, domin kayan dake jikin Fauzeeya kallo d'aya tayi musu ta fahimci tsadaddin gaske ne tun anan zuciyarta ta tsinke gabanta ya bada dummmmm! Hankalinta yayi k'ololuwar tashi fargaba da tsantsar hassada ne kwance cikin k'wayar idanunta.
Haka bikin ya kasance cikin k'oshin lafiya da wadatar zuci har dare yayi su Adama suna manne da amarya, bada jimawa ba saigasu Iya Kulu da dangin mahaifiyar Fauzeeya sun shigo cikin d'akin sunata yi mata wa'azi da nasihar dake ratsa tsoka da zuciyar mai sauraro, an dad'e ana nasihar tabi umurnin mijinta Fauzeeya sai rusar kukan bak'in cikin rabuwa da gida takeyi yayinda cikin k'ark'ashin zuciyarta farin ciki ne fal aranta, lallashinta sukeyi suna bata maganganu masu dad'i saida sukaga tayi shiru can sukaji tsayuwar mototin abokan ango Yaseer, lullub'eta da mayafi sukayi suka ja hannunta suka nufi parking lot da ita anan suka taras da mototin suka, yayinda Iya Kulu sai sharar kwallar rabuwa da jikanyarta takeyi wadda take matuk'ar so da k'auna.
Shisshigewa matan sukayi cikin mototin abokan ango Yaseer suka danna horn maigadi ya wangale musu get d'in suka fice daga cikin gidan da sauri, acikin mota Fauzeeya sai zubar da kwallar rabuwa da iyayenta takeyi saboda daidai da rana d'aya bata tab'a yin nesa dasu ba, amma gashi yanzu asanadiyyar aure zatayi nesa da kakarta da kkuma mahaifinta hmmm aure kenan babu inda baya kai mace.
Babu dad'ewa suka iso unguwar daidai bakin get d'in gidan Yaseer wanda ya k'ara k'awata gidan da chanza masa sabon painting, danna horn sukayi da k'arfi getman ya shek'o ya wangale musu get suka kunna hancin motarsu cikin tsakiyar filin gidan tareda parkerwa aparking lot, mata da mazan da suka rako amarya zuwa gidan mijinta suka firfito daga cikin motar rududududu kamar diyan kadai suka rankaya suka nufi hanyar da zata sadasu da parlour, kafin su kutsa kai cikin gidan saida suka saka amaryar tayi addu'a tareda fad'awa da k'afar dama.
Suna isowa tsakiyar parlourn babu kowa tsit kakeji suka d'unguma suka fad'a d'akin dayake mallakinta ita Fauzeeyar, tura k'ofar d'akin sukayi suka afka cikin d'akinta suna shiga suna dube dube da kalle kalle kamar k'auyawa domin tsari da k'awatuwar d'akin ya burgesu da basu sha'awa matuk'a, saboda k'yawo da had'uwarsa ya tafi da imaninsu zagaye ciki da wajen gidan sukayi da kallo har suka gaji sannan suka dawo wurinta suka cigaba da lallashinta da gaya mata kalamai masu sanyi da ratsa zuciyar mai sauraro.
Sun jima zaune sun sakata tsakiyarsu wata daga cikin wad'anda suka kawo amarya ta shigo tsakiyar d'akin tace musu abokan ango sunce su fito akwai maganar da zasuyi dasu, matan suka tashi tsaye suka fito daga cikin d'akin amarya direct parlour suka nufa.
Suna isa parlourn suka iske ango Yaseer da tawagar abokansa zazzaune saman cushion sai tsiya da tsokanarsa sukeyi ana dariye dariye, Yaseer washe baki kawai yakeyi yana jin dad'i nasihar da sukayi masa tareda umurtarta akira musu amarya da suyi mata nasiha, wata cikin matan ce ta mik'e tsaye ta fad'a d'akin Fauzeeya amarya. Duk abinda akeyi Nazifa tana cikin d'akinta kwance batada labari kuma Allah bai bata ikon ji hayaniya da maganganun mutane ba hankalinta kwance take barci da minshari domin batayi tsammanin mijinta yayi aure ayau ba.
Babu wani dad'ewa saiga budurwar ta fito daga cikin d'akin amarya yayinda Fauzeeya take biye abayanta har suka k'araso cikin mutane fuskarta lullub'e da mayafi ta samu saman cushion ta zauna tana zama abokan Yaseer 'yar nasiha mai ratsa b'argo da jinin jiki sannan suka mimmik'e tsaye suda 'yan kawo amarya suka fice daga cikin parlourn direct wurin mototinsu suka isa suka shisshiga tareda tadda mototinsu zuwa nufar gida...........
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 29*
Ganin mutane duk sun watse yasa Yaseer ya mik'e tsaye agajiye ya sanya key a k'ofar parlourn sannan ya dawo wurin Fauzeeya yana mata kallon so da tsantsar farin ciki, ji yakeyi duk abinda yake damunsa na tsawon lokaci ya gushe murmushi k'unshe afuskarsa ya kashe murya yace"my Fauzee ki tashi mu tafi d'aki muyi alwala mu godewa ubangiji daya nuna mana wannan ranar farin ciki".Fauzeeya ta kalleta cikin mayafinta idanunta duk sun kumbura akan yawan kuka tace"yaya ka barni anan parlour in huta duk na gaji sosai wallahi".Kallon tausayawa yayi mata yace"oyahh muje d'aki ki kwanta ki huta kinji matata anan baza kiji dad'in barci ba".Mak'e kafad'arta tayi cikin shagwab'e fuskarta zatayi magana kenan yah Yaseer ya sungumeta ya nufi cikin room d'in da ita, bai ajeta ko'ina ba sai saman gado ita Fauzeeyar duk kunyarsa ta kamata ji takeyi kamar ta nutse cikin k'asa.
Yaseer baice mata uffan ba ya fad'a cikin bathroom ya watsa ruwa ajikinsa tareda d'auro alwala ya fito yace"ki shiga toilet kiyi alwala".Fauzeeya ta mik'e tsaye batare da gardama ba ta fad'a cikin bathroom ta d'auro alwala tareda lullubo mayafi ajikinta, isowa wurinsa tayi ta iske har ya shimfid'a musu sallaya biyu kabbarta sallah yayi tabi bayansa har saida sukayi rakaa biyu suka sallame, addu'o'i suka dinga kwararowa daga baya suka shafa addu'ar afuskarsu kamar an tsikari Yaseer ya mik'e tsaye ya nufi parlour ya d'auko ledodin da abokansa suka kawo masa adazu.
Yadda yabar Fauzeeya hakanan ya iskota bata motsa ko nan da can gab da ita ya zauna suna jin numfashin juna,sannan ya bud'e leda d'aya kaza ce k'atanya aciki da madarar gora biyu masu sanyi fara cin kazar yayi yana lumshe fararen idanunsa alamar abin yayi matuk'ar dad'i kenan, sake debowa yayi ya nufi bakin Fauzeeya da naman ta kauda kanta gefe cikin lallashinta da tattausan lafazi mai dad'i yace"haba madarar zuciyata ki taimakamin kici kazar nan ko zan samu natsuwa da sa'ida arayuwata kinji".
"na k'oshi yaya Yaseer".
"ko kin k'oshi ina buk'atar kici ko kad'an ne saboda banason ki kwana da yunwa".
"zanci tunda ka takuramin".
"ai dole in takura miki saboda bana muradin amaryata ta zauna da yunwa".Yana rufe bakinsa ya yago naman ya saka mata abaki ta dinga tauna da ci kamar bataso ayangace, shima ya sanya abakinsa haka ya cigaba dayi idan yaci ya bata har saida suka nak cikinsu ya d'auka,sannan suka kawo madarar gora suka sha tareda yin gyatsa alamar sun k'oshi kenan, bathroom suka fad'a suka wanko bakinsu suka fito atare hannunsa mak'ale dana amarya mai dad'in suna wato Fauzee baby.
Adaren ranar Yaseer ya gurji amarcinsa shida Fauzeeyarsa saboda duk wata sha'awa da yakeda saida ya kauda ita akanta, alokacin Fauzeeya tasha kuka da sambatu mara adadi domin ba k'aramar wuya da galabaita tayi ahannunsa ba daga baya ma saida yaga numfashinta yana shirin d'aukewa sannan ya saurara mata, kallon yayi cikin matuk'ar tausayi da tsantsar k'auna yana lallashinta da gaya mata kalamai masu dad'i da sanyaya zuciyar masoya, yayinda a k'ark'ashin zuciyarsa wani irin tsantsar farin ciki da annashuwa ke kwaranya cikin jini da k'ofofin jikinsa, shi kansa ya kasa tantance wani irin yanayi yake ciki domin bakinsa ya kasa rufuwa saboda ni'imar daya kwasa ajikin amarya Fauzeeya, cigaba da lallashinta da tarairayarta yakeyi yana shafar k'yak'k'yawar fuskarta har barci ya d'auketa shi kuma ya fad'a cikin bathroom yayi wankan tsarki tareda d'auro alwala, yana fitowa ya shimfid'a sallaya ya dinga jero nafiloli na godiya ga ubangiji daya mallaka masa Fauzeeya amatsayin matarsa ta sunnah.
*********************
Da Asuba Yaseer ya sanya mata ruwan zafi sannan ya tayar da ita daga barci sai b'ata fuska takeyi kamar zatayi kuka, lallashinta yakeyi ya sanya hannu ya sungumeta sai cikin bathroom acan ya cire mata tufafinta tana hawayen shagwab'a sannan ya sanyata cikin ruwan zafi yana gasata, Fauzeeya kuka kawai takeyi kamar ana yankan naman jikinta ruwan suna rage zafi ya koma sanya mata wasu masu zafi domin ta gasu da k'yau.
Jikinta ko'ina zafi da rad'ad'i ya ratsashi saboda Yaseer ya nuna mata shi gwarzon namiji ne wanda ya jima yana buk'atar mace, saida ya gasa Fauzeeya ya tabbatar data gasu sannan ya umurceta data fito daga cikin ruwan, shagwab'e fuskarta tayi tana wani kakkare surar jikinta Yaseer yana lura da ita k'asan zuciyarsa farin ciki sai kwaranya yakeyi murmushi ya sakar mata batare da yace uffan ba ya ficewarsa.
Ganin yayi tafiyarsa yasa Fauzeeya ta fito d'aure da towel ajikinta hannunta rike da tufafin data shiga dasu bathroom, iskesa tayi zaune shiru yana danne dannen phone d'insa fuskarsa k'unshe da annuri da fara'a, direct wurin dressing mirror ta nufa ta zauna tana shafa lotions ajikinta kayan kwalliyarta ta jawo ta fara tsantsara kwalliyarta mai tsananin k'yawo, ta jima tana k'awata k'yak'k'yawar fuskarta da make up sannan daga k'arshe ta gama ta d'auko had'ad'd'iyar doguwar rigarta mai adon stones light green colour ta zura ajiki, d'an kwalin ta yafa a kafad'arta cikin yanga da natsuwa Yaseer yana kallon duk wani motsinta ta gefen wutsiyar idanunsa, yayinda yakejin wani irin sinadarin so da shauk'in soyayyarta sai k'ara ninkuwa yakeyi azuciyarsa.
Ganin ta kammala shiryawa yayi mata alamar tazo da yatsarsa gaban Fauzeeya ya fad'i rasssss cikin sanyin jiki ta isa wurinsa, zaunar da ita yayi saman cinyoyinsa yana shinshinar k'amshin turarenta itadai shiru tayi batace komai ba domin tana gudun yace zai sake nemanta, can Yaseer ya kalleta da shanyayyun idanunsa masu k'ara narkar da zuciyarta yace"kinyi k'yau amaryata".
"nagode sosai".
Yaseer ya muskuta yace"yanzu muje parlour kiyi breaskfast saboda nasan kina jin yunwa".
Narkewa Fauzeeya ta k'ara ajikinsa tace"waye ya kawo mana abinci ko kaine ka girka?".
Jan karan hancinta yayi cikin matuk'ar k'auna yace"a'a bani na girka ba Ummi ce ta aiko driver ya kawo mana tun d'azu".
"OK yaya Aunty Nazifa taje shago ne?".
"tsoronta kikeji ne to bataje ba? ".Ya fad'a azolaye murmushi k'unshe afuskarsa.
Fauzeeya tayi fari da idanunta cikin murna tace"ni kam bana tsoronta tambaya ce kawai nayi maka".
Yaseer yayi murmushin dake bayyana hak'ora yace"kedai fad'i gaskiya ga naira biyar".
"Nak'i d'in".Tace cikin wasa da sagarci.
Yaseer ya sauketa ajikinsa sannu ahankali yaja hannunta suka fice daga cikin d'akin suka isa tsakiyar parlourn.
Suna isa parlourn direct wurin dinning table suka nufa suka zazzauna saman kujerun dake kewaya dasu, aplate d'aya Fauzeeya ta zuba musu abinci suna ci suna jifar junansu da kallon soyayya da k'auna, haka dai suka cigaba da breaskfast d'in har suka kammala suka koma cikin parlourn manne da juna.
Yaseer sai aikin shafar ko'ina ajikinta yakeyi yana lumshe fararen idanunsa alamar yana matuk'ar jin dad'in abin, saiga Nazifa ta shigo tsakiyar parlourn kanta yana kallon tiles dake malale cikin parlourn dagowar da zatayi idanunta ya sauka akansu!.
Cikin firgici da tsantsar kad'uwa akan abinda mugun tozalin da idanunta sukayi gabanta ya bada dummmmm hankalinta yayi k'ololuwar tashi fargaba da tsantsar tsoro ne ya bayyana k'arara afuskarta, cikin zullumi da fargaba ta isa wurinsu idanunta har nauyi nauyi sukeyi mata tace"Yaseer mi ya kawo Fauzeeya gidanka shin tun kafin ayi aurenku kun fara iskanci da juna to ai ku daure har ad'aura auren kafin ku tsira mana tambada cikin gida!? ".
Murmushin mugunta Yaseer yayi yana rungume da Fauzeeya ajikinsa ya kalli fuskar Nazifa cikin nazari da tunani yace mata"ba iskanci mukeyi ba Nazifa na manta ban sanardake cewa jiya aka d'aura aurena nida amaryata Fauzeeya mai sona da son duk wani farin ciki nawa ".
Hak'ik'a maganarsa ta soki k'ahon zuciyarta tareda sanya zafi da rad'ad'in kishiya aranta narai narai tayi da fuskarta kwallar zallar takaici da bak'in ciki nek'wayar suka taru cikin k'wayar idanunta, jiri ne yake neman kwasheta ta fad'i aamma saita isa wurin bango ta dafashi cikin suyar zuciya tace"tabbas biri yayi kamada mutum saboda baka sona baka k'aunata shine baka gayamin cewar jiya za'a d'aura aurenka da Fauzeeya ba hmmmm lallai ka nunamin kai munafuki ne butulu yayinda matarka ta kasance azzaluma maciyiya amana to ku jira ku gani hak'k'ina saiya fita akanku! ".
"Nazifa kenan kina bani matuk'ar mamaki idan kina wad'ansu maganganu aini banci amanarki ba kece kikaci amanata tareda tashi jefani cikin halaka, saboda bana samun duk wata kulawarki hak'k'ina dake rataye awuyanki bak'ya bani, to yaya kikeson inyi idan ba in k'ara aure ba domin inga na tseratar da kaina daga fad'awa cikin tarkon shaid'an? ".
Fauzeeya ta k'ara lahewa a faffad'an k'irjinsa ta dubi fuskar Nazifa cikin sanyin murya da lalama tace"nima banci amanarki ba Aunty Nazeefa kice kika cuci kanki kika kasa bawa mijinki tsantsar kulawa da soyayyar gaskiya, kika fifita business dinki akan mijinki da 'ya'yanki ni miye nawa aciki saboda na auri Yaseer kece kikayi *SAKACI* arayuwarki har na samu damar shigowa gidanki amatsayin kishiyarki! ".
"abinda my Fauzee ta fad'a gaskiya ne Nazifa kinyi sake shiyasa tayi miki sakiya ".
Cikin matuk'ar zafin rai da hargowa Nazifa ta zaburo musu da k'arfi kamar zata dakesu tace"keeee k'aramar karuwa ki kiyayeni wlh idan ba haka ba zanyi miki shegen duka!Inga ubanda yace ki saka bakinki idan ina magana da mijina!? ".Yaseer ya d'aga mata hannu yace"karki kuskura ki dakarmin mata kako bana nan".Fauzeeya ta rausayar da kanta cikin shagwab'a tace"ki gyara maganarki kice mijinmu yanzu kam mu biyu ne dashi kinji masifaffa! ".
"Kulu mai tsamiya ce masifaffa kinji Fauzeeya wato na lura dai so kukeyi kuyimin taron dangi keda bak'in munafikin mijinki! Bazan tab'a damuwa saboda kafin kuyi aure saida kuka dandani dad'in juna shiyasa kuka lakewa junanku, 'yan buro uban sheguna munafukan azzalumai tsakanina daku ubangiji ya isa! ".Yaseer ya hasala sosai da irin yadda Nazifa ke zaginsu cikin matuk'ar b'acin rai yace"munji dai duk abinda zakice mana babu matsala ubangiji yafi ki saboda haka kiyi tafiyarki inda zakije banason rigima da neman tashin hankali! ".Nazifa ta rike k'ugunta tace"babu inda zanje har saina amayar da abinda yake cikin cikina ".Yaseer yace"to idan bazaki tafi ba yita zama kaike d'aya ".Yana rufe bakinsa ya sungumi Fauzeeya suka nufi hanyar zuwa room d'insa suka bar? Nazifa atsaye sai balbalin masifa takeyi tana zage zage bakinta har kumfa yake fitarwa akan tsantsar fitina da tashin hankali irin nata...............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 30*
Saida Nazifa tayi fad'an ta gaji sannan taja k'afafunta ta nufi hanyar room d'inta tana shiga ta wawuro mayafinta ta nufi parking lot, alokacin idanunta har rufewa sukeyi akan tsantsar bak'in ciki da tsagwaron kishin dake cin zuciyarta hawaye sai zubowa sukeyi asanadiyyar Yaseer ya munafurceta tareda b'oye mata ajiya za'a d'aura aurensu, tana isowa parking lot ta sanya key ta bud'e motar sannan ta fad'a ta zauna tareda danna horn da k'arfi getman ya sheko ya wangale mata get, ta fice da matsiyacin gudu daga cikin gidan domin zuciyarta cunkushe take da tsananin damuwa da rad'ad'in kishiya, tafiya takeyi tana risgar kukanta cikin mota babu mai lallashinta ji takeyi duniyar gaba d'aya tayi mata bak'ik'irin! Gwamma mutuwa ta risketa akan irin wannan matsanancin halin data shiga zafi da k'unar zuciya takeji cikin ranta yayinda taji kamar an aza mata dutsi akan zuciya saboda wani irin nauyi da yanayin da takeji azuciyarta.
Haka dai ta cigaba da tafiya tana kuka ga hawaye kwance yabe yabe saman fuskarta alokacin ne tururin zafi da k'una zuciyarta keta yi harta iso cikin unguwarsu kuka takeyi mai ban tausayi, awaje ta parker motarta tareda shiga cikin gidan batare da sallama tafiyar sauri sauri takeyi harta isa tsakiyar parlourn ta hango hajiya Ramlat azaune tana shan tea ahankali, da gudu Nazifa ta isa ajikinta ta rungumeta tana zubar da kwallar zallar takaici daga sama hajiya Ramlat taji mutum ya rungumeta, ai kuwa harta tsorata da farko sai daga baya ta gane d'iyarta ce Nazifa jin kukanta yasa hankalin mahaifiyarta ya d'unguma zuciyarta ta tsinke gabanta sai luguden tsoro da fargaba yakeyi mata, bubbuga bayanta tayi alamar lallashi ta tattaro dauriya da natsuwa ta sanya azuciyarta cikin tausayawa tace"ki daina kuka baby just tell me what is happen to you?".
Nazifa ta k'ara volume d'in kukanta cikin bak'in ciki da tsantsar takaicin rayuwa ta kasa sanarwa mahaifiyarta dalilin kukanta, ganin bata gaya mata komai ba hajiya Ramlat ta sake tambayarta cikin tsinkewar zuciya da damuwar ganin yarta k'waya tak aduniya tana kuka"please