Showing 12001 words to 15000 words out of 87802 words

Chapter 5 - SAKACI BY MUGIRAT MUSA

05 Jul 2024

4233

yace "sannu uwata!".

Fauzeeya tayi murmushin dake fallasa asirin k'yawonta tace"ina ni ina zama mahaifiyarka yah Yaseer ka daure ka gayamin gaskiyar abinda ya had'aku".

Numfashin takaici ya sauke mai tattare da bak'in ciki da b'acin rai yace"Fauzeeya tun lokacin da Nazifa ta fara wannan tsinannen business ta daina kulawa dani tareda bani hak'k'ina na auratayya, rayuwarta gaba d'aya ta chanza yanayinta ya sake ta koma kamar ba Nazifar da muka shud'e shekaru da ita muna soyayya ba, kullum cikin b'atamin rayuwa take da haddasamin bak'in ciki da k'uncin rayuwa.................. ".Kwashe labarin duk irin abubuwan da Nazifa takeyi masa marasa dad'i da k'unsamai bak'in ciki ya gaya mata komai babu abinda ya b'oye mata.
Yana kai k'arshen labarinsa idanun Fauzeeya suka cicciko da hawayen matuk'ar tausayinsa cikin sanyin murya tace"tabbas Aunty batayi maka adalci ba arayuwa amma ka daure ka cigaba da hak'uri da halayyarta wata rana zata daina".
Yaseer yayi ajiyar zuciya yace"ai hak'urin nakeyi da ita saboda haka ki bani dama in tura magabatana gidanku asa mana ranar aure".
Fauzeeya ta rufe fuskarta cikin kunya tace"na baka dama ka turo ba komai ".Tana k'arasa maganarta ta fice daga cikin d'akin akunyace domin maganar tayi mata matuk'ar dad'i da sanyi azuciya.
Tana fita Yaseer yayi murmushi yace ji Fauzeeya wai kunyata akeji idan mukayi aure zaki aje batun kunya agefe".Yana kai k'arshen maganarsa ya kwararo addu'o'in neman tsari daga shaid'an yana shafawa ajikinsa, bada jimawa ba ya lumshe fararen idanunsa alamar barci yakeji nan da nan barci ya sacesa.
Acan room d'in Fauzeeya tana shiga to fad'a saman gadon fuskarta k'unshe da tsantsar farin ciki da annashuwa, wani irin sanyi da farin ciki ne ke yawo cikin jini da sassan jikinta hak'ik'a ta tabbatar ta riga ta fad'a cikin tarkon soyayyar Yaseer ji takeyi kamar ya zamo gobe za'a d'aura aurensu itada masoyinta, juye juye ta dingayi akan tsabar farin ciki da nishad'i hankalinta kwance barci yayi awon gaba da ita batare data ankara ba..........
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

_Duk mai buk'atar cigaban novel d'ina *RASHIN SO* ya tuntunb'eni ta wannan nombar 08163650557._

*PAGE 8*


Da tsakar dare Nazifa ta isa bakin get gidansu ta danna horn da k'arfi getman ya sheko ya wangale mata get d'in, yana budewa ta kunna hancin motarta aparking lot ta parker ta fito rataye da handbag d'inta a kafad'arta, sanya key tayi ta kulle motar ta nufi cikin parlourn ahanzarce ta isa tsakiyar filin parlourn babu kowa tsit direct room d'in daya kasance mallakinta tun tana budurwa ta nufa,tana shiga ta iske d'akin duk yayi k'ura da datti cire mayafinta tayi ta aje saman drower handbag d'in ma ta aje akan drower, towel k'arami ta d'auko da ruwa abucket ta zuba dattol cikin ruwan ta fara goge wardrobe, drower da gadon duka saida ta gogesu tasss sannan ta fad'a cikin bathroom ta wanke towel d'in fess ta shanya a k'arfen dake cikin bathroom d'in ruwa ta watsa ajikinta ko zataji sanyi azuciyarta saboda marin da Yaseer yayi mata yayi matuk'ar b'ata mata rai tareda sanya d'aci da zogi azuciyarta, tana kammala wankan ta fito d'aure da towel ajikinta sharp sharp ta shafa lotions d'in dake kan mirror ta ciro doguwar riga mara nauyi ta sanya ajikinta, kwantawa tayi saman gadon ta jawo blanket ta rufe jikinta yayinda har cikin jini da magudanar jikinta wani irin abu ne ya tokare mata a k'irji, addu'o'i ta karanta ta shafa ajikinta ta lumshe idanunta cikin bak'in ciki da tafasar zuciya dak'yar ta samu ta runtsa akan tarin damuwa..
____________________
Da gari ya waye da safe Nazifa ta tashi tayi sallar asuba tana gama sallah ta fara gyara d'akin lungu da sak'o saida ta gyareshi tsab sannan ta kunna turaren wuta tareda fesa room freshner, k'amshi mai ratsa zuciya duk ya gauraye cikin d'akin gaba d'aya sannan ta shiga cikin bathroom tayi wanka, tana fitowa daga cikin toilet ta zauna saman kujerar dake fuskantar dressing mirror ta fara tsantsara kwalliyarta mai k'yau da kallo, ta mike tsaye tareda ciro atamfarta orange da pink colour ta sanya yayi mata cifcif ajiki ta kawo turarurka ta feshe jikinta dasu, sannan ta nufi hanyar zuwa parlourn gidansu tun daga nesa ta hango iyayenta zazzaune wurin dinning table suna yin breakfast, k'arasowa wurinsu tayi ta gaishesu amsa mata sukayi cikin sakin fuska tareda yi mata kallon mamaki dayake breakfast sukeyi shiyasa basu ce mata uffan ba, hakan ne ya bata damar jan kujera ta zauna ta d'ibi nata abincin ci sukeyi atsanake har suka kammala suka goge bakinsu da tissue paper.

Alokacin ne Alhaji Mu'azu mahaifin Nazifa ya kalleta cikin k'auna da soyayya yace"baby yaushe kika shigo cikin gidan nan har kikayi wanka ina yaranki?".
Nazifa ta marairaice fuskarta kamar zatayi kuka tareda kallon b'angaren hajiya Ramlat mahaifiyarta tace"Abbu Yaseer ne ya koroni jiya da tsakar dare daga cikin gidansa! ".
Dummmmm gabansu Alhaji Mu'azu ya fad'i zuciyarsu ta tsinke cikin yanayin tashin hankali da damuwa suka had'a baki wurin cewa"akan wane dalili baby zai koroki!?".
Nazifa tayi rau rau da idanunta hawaye suka cicciko cikin k'wayar idonta tace"akan wai ina yawan zuwa shagona sayar da kayayyaki shine yazo yanata zagina abin bai ishesa ba domin ni ko uffan bance masa shine ya mareni tareda rufeni da duka kamar jaka, Abbu Ummu ni wallahi wannan auren ya isheni kullum cikin zagina yakeyi da aibantaku! ".Tana rufe bakinta ta rushe da kukan munafurci wiwiwi kamar wadda ake yankan naman jikinta.
Hak'ik'a abinda Nazifa ta gayawa iyayenta yayi matuk'ar b'ata musu rai da sosa zuciyarsu kallo d'aya zakayi musu ka hango tsananin b'acin rai da bak'in ciki k'unshe cikin fuskarsu, sunyi shiru kowane da abinda yake k'ullawa cikin zuciyarsa dakyar hajiya Ramlat ta tattaro dauriya da natsuwarta tace"amma Yaseer ya cika shegen yaro taya zai dinga dukanki da marinki an gaya masa ke baiwar uwarsa ce ko ta ubansa! Lallai za'ayi tashin hankali da masifa awannan karon saboda bazan d'auki irin wannan sakarcin ba wannan ai salon zalunci ne ".
Alhaji Mu'azu ya sauke numfashi ya sassauta murya k'asa k'asa yace"Ramlat ki daina cika baki tukun ki bari akira mijinta yazo ya fad'i abinda ya had'asu".
"ai dama nasan haka zakace Alhaji d'iyar tawa k'waya tak aduniya yana neman kashemin ita, to gaskiya bazan d'auki duka da zagi akan yarinyata ba saboda haka ka kirasu hajiya Sadiyan da mijinta suzo suji aika aikar da d'ansu yakeyi! ".
"haba hajiya ki bari mubi komai asannu mana".
"bazan bari duk abinda zai faru ya faru so nake ayita ta k'are! Bazai mayarmin da d'iya jaka ba ni nasan zafin da naji alokacin nak'udarta ina gangaran mutuwa saboda haka ka kirasu suji abinda d'an iskan d'ansu yakeyi, idan ba bak'in ciki ba miye ruwansa da business d'inta shi ya bata jari ne dazai d'auki hassada da bak'in ciki ya sanya azuciyarsa? ".

"Allah ya huci zuciyarki Ramlat kiyi hak'uri zan kirasu amma dan girman Allah na rok'eki idan sukazo ki bari ayi komai cikin fahimta da natsuwa kada ki aza mana tijara da masifa ".

"amma kasan abin da ciwo mutum ya walak'anta maka d'iya wannan ai salon *RASHIN SO* ne".
"na fahimci abinda kikeji azuciyarki amma dai ki daure kinji kada ki bani kunya agaban mutane".
"tunda ka matsa na hak'ura kirasu suzo da d'ansu ayi komai agabansu".
"to hajiya".Yana rufe bakinsa ya d'auko phone d'insa a aljihunsa yayi dialling nombar Alhaji Taheer mahaifin Yaseer wayar tana shiga ta fara ringing, batare da b'ata lokaci ba Alhaji Taheer yayi receiving call d'insa yace"Assalamu Alaikah Alhaji Mu'azu".
"Wa'alaikas Salam Alhaji ya gida ya iyalinka?".
"k'alau suke ya naka?".
"lafiya k'alau suke Alhaji Taheer dama dalilin dayasa na kiraka saboda kazo kaida matarka da Yaseer akwai matsalar data kunno kai atsakanin Yaseer da Nazifa".
"subahanillah! To karka damu gamunan zuwa yanzun nan harda Yaseer d'in".
"OK no problem sai kunzo".Yana kai k'arshen maganarsa ya katse wayar k'it ya mayarda hankalinsa kacokam wurin hajiya Ramlat yace mata"kiyi hakuri gasunan tafe hajiya".
Hajiya Ramlat tace"naji ba damuwa".
Nazifa dake zaune saman carpet ta shagwab'e fuskarta tace"Ummu kuce suyi zamansu nifa gaskiyar zance bazan koma gidan Yaseer ba na gaji da halayyarsa kullum k'unsamin bak'in ciki yakeyi so yake ya kasheni tun kafin lokacina yayi! ".
"ki daure kinji Nazifa 'yancinki mukeson k'watar miki ai ko sunzo ba dole bane ki koma hardai idan muka fahimci zaluntarki yakeyi".

Nazifa ba haka taso ba har cikin zuciyarta domin tasan idan Yaseer ya fad'i gaskiyar abinda takeyi masa kashinta ya bushe, b'oye damuwa da fargaba tayi cikin zuciyarta tace"to Ummu babu damuwa".

"ko kefa d'iyar k'warai".Inji hajiya Ramlat.
Firarsu suka cigaba dayi cikin kwanciyar hankali kamar basuda wata damuwa azuciyarsu, babu dad'ewa saiga sallamarsu Alhaji Taheer sun shigo cikin tsakiyar parlourn Alhaji Mu'azu ya mike tsaye yayi musu iso zuwa saman cushion sannan suka kira 'yar aikinsu Tasallah ta kawowasu Alhaji Taheer drinks da ruwa atire ta dire agabansu ta fice da sauri daga cikin parlourn.

Ruwan kawai suka iya sha sannan Alhaji Mu'azu yayi gyaran murya cikin dattijantaka yace"dama dalilin dayasa muka taru awannan lokaci ba komai bane illa Nazifa ta kawo mana k'ararka Yaseer na cewa ka doketa da marinta, ko zaka iya sanar mana musabbabin abinda ya had'aku fad'a?".

Yaseer ya d'ago idanunsa ya kalli fuskar Nazifa alokacin ne gabanta ya bada rasss zuciyarta ta tsinke, tsoro da fargaba ne ya bayyana k'arara akan fuskarta cikin dakewa Yaseer yace"Abbu ita ya kamata ta k'ara maimaita abinda ta gaya muku ina yi mata".

Alhaji Taheer yace"wannan zancen naka gaskiya ne Yaseer".
Alhaji Mu'azu ya mayarda kallonsa gefenta yace"Nazifa ki sake maimaita irin abubuwan da kika gaya mana cewa mijinki yana yi miki agaban kowa".

Jikinta yana mazari da kad'uwa alamun rashin gaskiya ne ya bayyana k'arara acikin k'wayar idanunta bakinta yana rawa tace"Abbu ....na..... gaya muku du....kana da ma....rina yakeyi kullum ya mai.....dani jakarsa.....".

"ke gama naki bayanin ne Nazifa? ".Inji Alhaji Mu'azu.

"eh mana Abbu na gama".

Alhaji Mu'azu ya mayarda kallonsa wurin Yaseer yace"kai muke jira ka fad'i naka bayani".
Yaseer ya d'ago idanunsa suka fad'a cikin na hajiya Ramlat wani irin sak'on harara ta aiko masa kallo d'aya zakayi mata ka gane ta cika tayi fam kamar zata fashe akan takaicin Yaseer, noce kansa yayi a k'asa ya fara kwararo bayanin irin tasku da walak'ancin da Nazifa keyi masa, duk abubuwan da takeyi masa na rashin kunya da tozarci saida ya gaya musu yana kammala basu labarin suka hau salati da salallami, kowanensu sai tofa albarkacin bakinsa yakeyi dak'yar Alhaji Mu'azu ya samu suka tsagaita dayin surutu yace"agaskiya banji dad'in abinda kika aikata ba Nazifa kinsan bakida gaskiya kuma kika tako k'afarki gidan nan da sunan yaji! Ki tashi maza ki d'auko jikkarki kibi mijinki! ".Dole Nazifa ta mik'e tsaye tayi cikin d'akinta da sauri jikinta amace yayinda hawayen rashin samun nasara ke shatata afuskarta.

Alhaji Mu'azu ya k'ara da cewa "dan girman Allah Alhaji hajiya kuyi hak'uri da nasan itace batada gaskiya da ban saku kunzo ba, saboda haka kuyimin uzuri rashin sani ne wanda yafi dare duhu ".

"karka damu Alhaji ai duk d'an Adam mai kuskure ne arayuwa awurinmu bakada wani laifi saima mu gode maka saboda kayi k'ok'arin daidaita tsananin Yaseer da matarsa mun gode da wannan jajircewa naka ubangiji ya saka maka da mafificin Alkhairi ".Cewar Alhaji Taheer mahaifin Yaseer .

hajiya Sadiya tayi murmushin dake k'ayatar da fuskarta tace"bakayi mana laifin komai ba mune da godiya saboda kayi namijin k'ok'ari wanda dole ayaba maka".

"alal hak'ik'a naji dad'in yadda kuka fahimceni d'ari bisa d'ari lallai ku d'in mutanen kirki ne masu karamci da zuciyar alkhairi Allah ubangiji ya k'arfafa mana zumuncin dake tsakaninmu ya kauda duk wata fitina dake tunkaromu "."Amin amin ".Sukace sannan aka rufe taro da addu'o'i suka tsaya suna gaggaisawa da junansu can saiga Nazifa ta fito rataye da handbag d'inta a kafad'arta cikin matsananciyar damuwa da bak'in ciki, tana isowa wurinsu sukayi sallama da juna Alhaji Mu'azu ya rakasu har parking lot suka shige cikin motar suka fice daga cikin gidan, yayinda ya juyo ya dawo ya isko hajiya Ramlat zaune ita kadai cikin tsantsar takaici da b'acin rai.........
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 9*


Yana isowa wurinta ya zauna kusa gareta cikin taushin murya yace"lafiya Ramlat zaki b'ata ranki akan abinda ba abin damuwa bane?".Hajiya Ramlat ta musk'uta cikin takaici da k'unar zuciya tace"haka zaka fad'a kace ba abin b'acin rai bane ta yaya zaka d'auki yarinya kabasu bayan ya jibgeta alhalin bamu k'watar mata 'yancinta ba?".Alhaji Mu'azu ya girgiza kansa yace"ke kurma ce da baki tsaya kin saurari irin abubuwan da d'iyarki takeyi ba marasa dad'in saurare da k'yawo ba, ki gyara rayuwarki tareda jawa Nazifa kunne ta rik'e darajar aurenta hannu bibbiyu domin shine kimarta da darajarta".Hajiya Ramlat ta hararesa kamar idanunta zasu fad'o daga cikin k'wayar idonta tace"dakata Mu'azu! Karka nemi ka d'oramin laifin daba nawa ba mi kake nufi da in gyara rayuwata?".
"yauwa abinda nake nufi daki gyara rayuwarki saboda duk yadda Nazifa ta kwaso jiki ta dawo gida yaji saita gaya miki k'arya da gaskiya kina d'auka, to ki daina idan ba haka ba wata rana zata iya kunyataki cikin mutane wallahi".
"naji fa surutunka ya isheni idan ma ta kunyatani cikin mutane miye damuwarka? Inace nina haifeta ga cikina kuma d'iyata ce"."Hmmm matsalata dake bak'ya son gaskiya ko kad'an a rayuwarki "."Badai kai kanason gaskiyar ba bani ita in rik'e ahannuna".Cewar hajiya Ramlat cikeda son fitina da tashin hankali.
Alhaji Mu'azu ya tashi tsaye ya girgiza kansa yace"ubangiji ya shiryeki"."Amin idan da gaske kake".Ficewa yayi daga cikin parlourn batare daya sake sauraren irin kalmar da zata fito daga cikin bakinta ba d'akinsa ya shige yabarta aparlour.
Fad'a hajiya Ramlat ta dingayi ita kad'ai kamar taga Alhaji Mu'azun agabanta, bakinta har kumfa yake fitarwa akan tsantsar fitina da masifarta saida tayi fad'an ta gaji sannan taja bakinta ta tsuke.
____________________

Suna komawa gida Yaseer ya shige cikin d'akinsa baice mata komai ba yayinda Nazifa ta fad'a cikin nata room d'in cikeda matuk'ar haushin mijinta, tana shiga cikin room d'inta ta ciro phone d'inta cikin handbag tareda dialling nombar Safiya, wayar tana fara ringing Safiya ta d'aga wayar tace"hello k'awata kina ina tun d'azu nake kiranki amma wayar bata shiga?".
Nazifa ta musk'uta tace"kedai bari Safiya Yaseer ya koreni jiya da tsakar dare gidansa shiyasa kika jini shiru".
"Ayyah Nazifa gaskiya abubuwan da mijinki yakeyi miki sunyi yawa, yanzu dai abinda za'ayi kizo shago ina jiranki zamu tattauna".

"to ba matsala besty idan na watsa ruwa yanzu zan fito".

"to sai kinzo".Tana k'arasa maganarta ta katse phone d'in yayinda Nazifa tayi ajiyar zuciya mai tattare da bak'in ciki da takaicin mijinta, cire tufafinta tayi ta fad'a cikin bathroom domin ta tsabtace jikinta.
Ab'angaren Yaseer yana shiga cikin room d'insa ya chanza tufafinsa ya fesa turare, fitowa yayi zai fice daga cikin parlourn sukayi karo da juna shida Fauzeeya d'ago idanunsu sukayi suka fad'a cikin na juna murmushi ya sakar mata yace"my Fauzee dama kina cikin gidan nan shine ba ko magana?".
Fauzeeya ta rausayar da kanta tace"kayi hak'uri yah Yaseer tun d'azu ina cikin ina kichaniyar had'a lunch shiyasa bansan daka dawo ba".
"OK my Fauzee na fahimceki don't worry nizan fita yanzu".
Ta yakune fuskarta cikin sagarci tace"haba yaya tun yanzu zaka fita har ina farin cikin na samu abokin fira".

"zan dawo bada jimawa ba yanzu ma abinda zaisa na fita yanada muhimmanci sosai, duk dai abinda ake ciki zan sanardake kinji".
"ba komai ubangiji ya tsaremin kai aduk inda ka shiga a fad'in duniyar nan".

Alal hak'ik'a yaji matuk'ar dad'in addu'arta har cikin zuciyarsa da sassan jikinsa kallon k'auna yake jifarta dashi yace"amin amin my Fauzee".
Tana tsaye ya wuce ta gabanta ya nufi parking lot anan taji alamun ya tadda motarsa ya fice daga cikin gidan, alokacin ne ta isa tsakiyar parlourn ta zauna saman cushion tana zaune saiga Nazifa ta fito rataye da handbag d'inta a kafad'arta cikin had'ad'd'iyar kwalliya mai ban sha'awa wani irin tsadadden lace ne ta sanya ajikinta wanda kallo d'aya zakayi masa ka gane an kashe naira wurin siyensa.
Ta gaban Fauzeeya ta gifto zata wuce tana isowa gab da ita ta yamutsa fuskarta cikin tsananin isa da gadara tace"Fauzeeya zan fita sauran idansu Sameer suka dawo ki barsu da yunwa sannan iyakarki da mijina ki basa abinci banda wani yi masa kallon k'urilla da shegun idanunki kamar *MAYYA*!".

Fauzeeya ta kauda kanta cikin jin haushin kalamanta da kishinta domin tana masifar son Yaseer dayi masa kishi mai tsabta tace"Aunty su yaran ne suka sanardake ina barinsu da yunwa?".

"ai ko basu gayamin ba biri yayi kamada mutum saidai ke kici ki k'ara manyan k'ugu da boob's amma yarana sai ramewa sukeyi".

"hmm ubangiji ya baki hak'uri nidai nasan yadda nake kulawa dasu Sameer ko 'ya'yan cikina ne iyakarsa kenan".

"rufemin baki! Banason jin wasu surutunki na banza kuma kada ki kuskura ki dinga shigewa mijina ajiki ma'ana ko magana ban amince kiyi dashi ba idan kunne yaji gangar jiki ta tsira! ".

Fauzeeya ta noce kanta a k'asa tace"da yardar Allah hakan bazaima faru ba Aunty".

"da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login