Showing 24001 words to 27000 words out of 87802 words
saukar da numfashin d'aci da tafasar zuciya bak'in ciki da tsantsar takaici ne cunkushe cikin zuciyarta tace"kedai bari ina cikin tsaka mai wuya da matsanancin hali wlh yanzu ma saida na biya gidanmu na sanar mata halin da nake ciki!".
Safiya tayi tagumi da ajiyar zuciya tace"kardai kicemin hasashena ya zama gaske Nazifa".
Nazifa ta gyara zamanta cikin suyar zuciya k'asan zuciyarta sai ciwo da k'una yakeyi mata cikin takaici Tace"hasashenki ya zama gaske Safiya Yaseer aure zai k'ara kuma da Fauzeeya !".
Maganar ta razana jikin Safiya sosai cikin rawa da mazarin jiki tace"wace Fauzeeyar zai aura!? ".
Nazifa tayi mata wani irin kallo mai tattare da bak'in ciki tace"wace Fauzeeyar kika sani bayan wadda takeyimin ayyukan gida da kula da yarana! ".
Hak'ik'a maganar ta soki k'ahon zuciyar Safiya cikin fargaba da tsantsar tashin hankali dayake kwance k'arara afuskarta tace"ina lillahi wa inna ilaihirraji'una! Lallai na tabbata ayau namiji bayada tabbas yanzu Yaseer ya rasa wacce yakeso kaf garin nan sai Fauzeeya yarinyar da kika raineta ahannunki tun kina amarya tanada shekara goma ko sha d'aya, ya kamata ki tashi tsaye mu d'auki mummunan mataki akanta saboda ta gane cewa ba'a tab'a cin amanarki azauna lafiya! ".
"kema kenan kina goyon bayana akowane lokaci ".
"ina goyon bayanki d'ari bisa d'ari k'awata ai mun riga mun zama d'aya abokin kuka shi ake gayawa mutuwa! ".
"zansa mana ranar da zamuje gidan kakarta da ubanta muci musu mutunci har sai sunyi matuk'ar nadamar bada Fauzeeya ga mijina ".
"OK duk ranar da kika sanya ki gayamin muje muyi musu wankin babban bargo ".
"zan sanardake Safiya".
Cigaba da firarsu sukayi cikin natsuwa da damuwa cunkushe cikin zuciyarsu, maganar auren Yaseer kawai suke maimaitawa suna zagin Fauzeeya da iyayenta yafi gaban misali.
*BAYAN KWANA BIYU*
Aranar aka tura Yaseer a ma'aikatarsu cikin wad'anda zasuje wani aiki ajahar Kataina har na tsawon sati guda, aranar dak'yar suka rabu shida Fauzeeya saboda yarinyar tana matuk'ar sonsa da nuna masa tsantsar soyayyar gaskiya, ab'angaren Nazifa bata wani damu ba akan zaiyi tafiya saboda dama tun farko akwai abinda ta k'ulla azuciyarta, tana ganin ya fice daga cikin gidan ta fashe da dariyar mugunta saida tayi dariyar mai isarta sannan ta tsagaita dayin dariyar ta tunkari room d'in Fauzeeya gadan gadan babu annuri afuskarta cikin zafin rai da k'unar zuciya .
Fauzeeya tana zaune saman gado itadasu Sameer su suna wasa ita tana karatun novel cikin phone d'inta mai suna *JINKIRIN ALKHAIRI* kwatsam! Taji motsin tafiyar mutum ya shigo cikin d'akinta ta d'ago kanta da sauri sai taga Nazifa ce cikin tsinkewar zuciya tace"Aunty kece wani aiki zanyi miki ne!? ".Gabanta yana dukan uku uku saboda kallo d'aya tayi mata ta gane ba alkhairi bane ya kawota d'akinta.
Nazifa ta girgiza kanta alamar a'a sannan ta mayar da kallon gefensu Sameer tace"ku tashi ku fita ku bamu wuri zamuyi magana da ita! ".Sameer ya langwab'e kansa yace"mom wasa fa mukeyi ".
Daka musu rikitacciyar tsawa da hargowa tayi tace"nace ku fice daga cikin d'akin nan! ".Kafin ta rufe bakinta suka mimmik'e tsaye suka shek'a da gudu saboda sun matuk'ar firgita da razana akan tsawar da tayi musu.
Suna ficewa ta mayar da kallonta ga Fauzeeya wadda ta gama firgita da lamarin Nazifa cikinta sai k'ugin tsoro yakeyi k'ululululu zad tsoro! Nazifa tayi mata walak'antaccen kallo tace"keeee don kutumar uwarki kina jin dad'in zaki auri mijina ya ciki kamar yadda yake cina kin matsu ayi aure ya zura miki jijiyarsa cikin k'ugunki! To ayau zaki gane ke k'aramar shed'aniya ce saina babance miki tsakanin aya da tsakuwa! "..............😢
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 15*
Fauzeeya ta razana da firgicewa akan kalamanta tun anan ta fara zubar hawaye tana rok'on Nazifa cikin tsananin tsoro domin tasan ayau babu mai k'watarta ahannunta sai Allah, tana kuka cikin tsinkewar zuciya tace"dan girman Allah Aunty Nazifa kiyi hak'uri karki cutardani wallahi indai yah Yaseer ne na hak'ura da aurensa! ".Nazifa ta banka mata harara kamar idanunta zasu fad'o a k'asa tace"k'arya kikeyi bak'ar munafuka dama daga gani ya saba cinki idan bana nan shiyasa kika lik'e masa saboda kinsan dad'in maza".Sharri da k'azafin da tayi mata yayi matuk'ar cin mata rai da sanya bak'in ciki da tsantsar rad'ad'i azuciyarta amma saita daure tace"duk abinda zaki fad'a ki fad'a idan har zaisa kiji sanyi azuciyarki amma dan girman Allah kiyi hak'uri Aunty".
"yimin shiru idan kika k'ara kirana da Aunty saina tsinka miki mari! Da kin d'aukeni yayarki da bazakiyi gigin auren mijina amma dayake shaggun iyayenki kwad'ayayyu ne shiyasa zasu had'a aurenki da Yaseer domin ku samu abin duniya! ".
Fauzeeya ta girgiza kanta cikin yanayin fargaba tace"ba haka bane Aunt...........".Kasa hak'uri Nazifa tayi ta k'arasa maganarta ta rufe da shegen duka ko'ina ajikinta ji kakeyi dim dim dim dim, ai kuwa nan take Fauzeeya ta saki kuwwa da kururuwar neman agaji amma ina babu kowa cikin gidan daga ita sai Nazifa da yaranta!.
Cigaba da dukanta takeyi kamar ta samu jaka saida tayi mata lik'is da d'an banzan duka sannan ta tsaya tana mayarda numfashi da haki wuk'ar data b'oye cikin zanenta ta d'auko tace"yau cikin gidan nan saina nakkasaki inga ta yadda auren zai yiyu! Saina yanke miki nonuwa in tura wuk'a akasanki inga ta yadda zai aureki!".
Duk dayake Fauzeeya tana cikin matsanancin hali hakan baisa hankalinta yak'i tashi ba zuciyarta ta girgiza jikinta duk tsami da ciwo yakeyi mata, saboda ba k'arya ta daku sosai cikin kad'uwa ta gurfana ak'asa saman gwiyoyinta hawaye masu zafi sai shatata sukeyi saman fuskarta tace"karki nakkasani Aunty na tuba na bar miki mijinki bazan auresa ba!".
"bayan kinga mutuwa k'iri k'iri ba shiyasa kike cewa kin fasa aurensa to bazan tab'a yarda da maganarki ba, ayau saina cire miki nonuwa inga iyakar iskanci k'asanki kuma saina sa wuk'a na hudeshi ya zamo kamar na wadda maza suka cita! ".
Ganin tana rok'onta tana botsarewa yasa Fauzeeya ta tabbatar zata iya aikata abinda take fad'a tunanin yadda zata gudu takeyi, can taji Nazifa ta chapki nonuwanta wuk'a rik'e ahannunta Fauzeeya ta k'ara gigicewa da d'imaucewa tana kuka kokuwa ne ya kaure atsakaninsu ita Fauzeeya tana ceton ranta ita kuma Nazifa tana son yanke mata boob's!.
Cigaba da kokuwa sukayi kowaccesu tana son cimma burinta akan 'yar uwarta dayake k'arfinsu ba d'aya ba Nazifa ta sake jujuyata ta fyad'a atiles kaji gwammmm!Wani irin rikitaccen zafi da rad'ad'i ne ya ziyarci sassan jikinta da k'wak'walwarta ai batasan lokacin da tayi k'ara tace"wayyo ni Allah Fauzeeya na shiga uku jama'a kuzo ku taimakeni zata kasheni akan toshewar basira da *KISHIN JAHILCI*!".
Shurinta ta dingayi da k'afafunta har saida ta fashe mata baki da jini fuskar Fauzeeya duk ta kumbura taji jajir saboda ta galabaita da shan matuk'ar wuya ahannun Nazifa, akwancen ma ta tunkarota da wuk'a tsirara ahannunta gadan gadan zata yanke mata boob's, Fauzeeya tana hankalceta da ita tana isowa zata aitawar da mugun nufinta Fauzeeya tasa k'afarta d'aya ta shureta ta fad'i k'asa kafi gwaffff! Wani irin zafi ya ziyarci sassan jikinta Fauzeeya tayi wuf cikin matuk'ar zafin nama ta fito daga cikin d'akin ta ranci na kare kamar zautatta, su Sameer suna zaune parlour tazo ta wuce ta gabansu suna cewa Aunty Aunty lafiya amma ina Fauzeeya tayi nisa batajin kira.
Haka ta isa wurin maigadi daga ita sai kayan jikinta babu takalmi bale d'an kwali baba maigadi yana ganin ta fito afirgice ya kalleta cikin razana yace"lafiya Fauzeeya mi akayi ne!?".
Fauzeeya sai numfashin wuya da haki takeyi dak'yar ta bud'i bakinta tace"ka taimakeni baba Aunty Nazifa zata kasheni! ".
Cikin kad'uwa da razana afuskar baba maigadi yace"mi kikayi mata ne da zata kasheki!? ".
"babu lokacin baka amsa kadai taimakeni wata rana zan gaya maka".
"to babu damuwa ".Baba maigadi ya shiga cikin d'akinsa ya d'auko wani zane mai kamada mayafi ya bata sannan ya ciro kud'i cikin aljihunsa d'ari biyar ya bata yace"ki rufe jikinki da wannan zane sannan kud'in ki tari mai keke napep ya kaiki gida"."To nagode sosai baba ubangiji ya saka maka da mafificin Alkhairi".Tana rufe bakinta ta fice daga cikin gidan da sauri domin kada Nazifa ta iskota ta halakata abanza akan bak'in kishi!.
Tana ficewarta baba maigadi ya zauna saman teburin da yake zaune cikin tausayin Fauzeeya, bada jimawa saiga Nazifa ta fito ayamutse tana neman Fauzeeya kanta ya kumbura a inda ya bugi k'asa k'arasowa tayi wurin maigadi tace"baba ina Fauzeeya? ".
"ke kuwa miyasa kike nemanta!? ".
Babu kunya bale tsoron Allah tace"sata tayimin! ".
Baba maigadi yayi saurin kallonta arazane domin ya gano gaskiyar abinda take fad'a k'wayar idanunta ya tsurawa kallo na tsawon lokaci yana karantar abinda yake cikinsu, hango rashin gaskiya yayi cikinsu sannan yaja numfashi yace"yanzun nan ta fice da gudu da farko inace ma ko maciji ta gani ta shek'o ashe sata tayi miki".Yace kamar ya yarda da zancenta.
Nazifa tayi k'yafci cikin tsananin takaici da rashin nasarar cika mugun nufinta akan Fauzeeya Tace"shikenan ta tsira yanzu amma gamona da nata wani karon ba k'yau saboda wallahi saita biyani kud'ina data sata! ".
"hak'uri zakiyi hajiya saboda Fauzeeya k'aramar yarinya ce bisa gareki".Inji baba maigadi.
Wani irin matsiyacin kallo tayi masa mai nuni da walak'anci tace"ba zanyi hak'uri ba ko zaka biyani kud'ina data sace ne sannan yanzu Fauzeeya data gama lalacewa atiti ita kake kira da yarinya, shin in tambayeka ko tare kuka had'a baki kaida ita kuka sacemin kud'i ko tana baka jikinta kana kwasar dad'inta ne shiyasa kakeson kareta?".
Dummmmm gaban baba maigadi ya buga da k'arfi kalamanta sun soki k'ahon zuciyarsa cikin jikinsa sai zafi yakeyi masa tun ranar da ubangiji ya haliccesa ba'a tab'a k'aga masa k'azafin da yayi masa ciwo irin wannan ba ,cikin matuk'ar b'acin rai da tafasar zuciya yace "dakata yarinya! Daga kawai na baki hak'uri kike neman ki k'agamin sharri da k'azafi ke wace irin zuciya ne dake da bakida tausayi bakisan darajar d'an Adam, ki kalleni da k'yau ahaife na haifeki da kike neman yimin rashin kunya! ".
Nazifa ta rik'e k'ugunta tana karkad'a jikinta cikin rashin tarbiya ta tofawa baba maigadi miyau afuskarsa tace"munafikin banza na k'aga maka sharri duk abinda zakayi kaje kayi kuma ubangiji yayimin tsari da matsiyaci kamarka ya haifeni wanda bayada komai sai tulin talauci da tsiya! "..
Baba maigadi ya shafi miyan data shafa masa afuskarsa yace cikin tsanar walak'anci "keee yanzu ni kike tofawa miyau afuskata saboda bakida albarka!? ".
Nazifa tayi clapping d'in hannunta 👏 tayi dariyar rainin hankali tace"an tofa maka miyau Barau kaine d'ebabben albarka wanda uwarsa ta mutu da takaicinsa".
Jin ta ambaci sunansa yasa baba maigadi yayi murmushin takaici ya dubeta yace"hmmmm hak'ik'a mahaifiyarki bata baki tarbiyar k'warai ubangiji ya tsine miki albarka yarinya! ".Nazifa tayi charap tace"yadai tsine maka albarka halan kai mahaifina ne da zaka tsine mini albarka dan kutumar ubanka idan Yaseer ya dawo saina sa ya sallameka kabar gidan nan tunda ba gidan ubanka bane! ".Tana kammala maganarta taja k'afafunta fuuuuu ta nufi cikin parlourn akumbure.
Kallon bayanta baba maigadi ya dingayi yana cewa "hmmmmmm wannan yarinyar iyayenta sunyi matuk'ar hasara domin basu bata tarbiyar kirki ba ".Yana k'arasa maganarsa yaja bakinsa ya tsuke yana jinjinawa rashin mutuncin Nazifa da rashin kunyarta, sak'e sak'e ya dingayi azuciyarsa cikin matuk'ar b'acin rai da zafin cin mutunci. ...
____________________
Fauzeeya tana fita daga cikin gidan Yaseer ta samu mai keke napep ya kaita har cikin unguwarsu a k'ofar gidan kakarta Iya Kulu mai tsamiya ya sauketa ta biyasa kud'insa ta juya ta shige cikin gidan yayinda mai keke napep d'in ya tadda napep d'insa ya k'ara gaba.
Fauzeeya tana isa tsakiyar filin gidan ta hango Iya Kulu zaune saman tabarma tana tsintar k'asa cikin shinkafa sallamar Fauzeeya ne yasa ta d'ago kanta tareda amsa mata sallamar, ganin jikanyarta ayamutse yasa hankalin Iya Kulu ya tashi zuciyarta ta girgiza cikin matuk'ar fad'uwar gaba tace"Fauzeeya lafiya kika zo haka kamar wadda aka koro? Ji yadda kika shigo tamkar mahaukaciya! ".Fauzeeya ta isowa wurinta cikin firgici da d'imuwa tace"Iya Aunty Nazifa ce ta koroni da wuk'a ahannunta tsirara! ".
Iya Kulu ta firfito da idanunta waje cikin matuk'ar tsoro da d'imaucewa akan kalamanta tace" wuk'a ta koroki da ita halan ta haukace ne!?".
Fauzeeya tayi murmushin takaici tace"bata duk haukace ba Iya tsabar hauka ne da bak'in kishi harda cewa takeyi saita yanke mini boob's taga yadda Yaseer zai aureni ahaka ".Iya Kulu tayi wuru wuru da idanunta mamaki da Al'ajabi ne kwance afuskarta k'arara cikin tsoro tace"amma agaskiya Nazifa ta haukace batada hankali! Wato so tayi ta kashemin ke tun kafin lokacinki yayi hmmmm ta Allah ba tata ba muguwar aniyarta ta bita !".
"Iya taji labarin aurena da za'ayi da Yaseer shine tace saita nakkasani! ".
Iya Kulu tayi tagumi cikin zullumi tace"afff ai wannan zancen banza halan saboda ita kad'ai aka halacci Yaseer ai namiji mijin mace hud'u ne saboda haka saidai tayi hak'uri ta rungumi k'addara aure kam babu fashi sai an d'aurashi! ".Fauzeeya ta jaye mayafin da baba maigadi ya bata ta nunnunawa Iya Kulu jikinta tace "duba ki gani Iya mugun kashi ta bani harda shurina kamar ta samu jaka ".Iya Kulu ta gyad'a kanta cikin matuk'ar b'acin rai tace"eh tabbas so tayi ta kashemin ke hak'ik'a Nazifa ta fifita daga cikin hayyacinta! "."Idan kinma ga yadda mukayi kokuwa da ita saina baki tausayi saboda nasha matuk'ar wuya ahannunta jikina duk tsami da ciwo yakeyi............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 16*
Iya Kulu ta kalleta cikin matuk'ar tausayawa tace"ayyah ubangiji ya sawwak'a jikinki kam duk yayi rud'u rud'u da ja akan duka, yanzu dai abinda za'ayi shine ki shiga wurin dafa abinci (kitchen)ruwan zafi yana nan saman murhu ki juye abokiti kiyi wanka".Fauzeeya tayi doguwar ajiyar zuciya cikin rad'ad'in ciwo tace"to Iyata ina godiya sosai da soyayyarki gareni".Iya Kulu ta sake kallonta tace"ki daina yimin godiya Fauzeeya hak'k'ina ne in kula dake saboda aduniya bakida wanda ya fini sai mahaifinki, shi kuma matarsa ta mallakesa sai yadda tayi dashi Allah ubangiji dai ya daidaita mana al'amurranmu"."Amin ya rabbi Iya".Inji Fauzeeya ta mik'e tsaye ta nufi cikin kitchen bokitin dake gefe ta d'auko ta juye ruwan zafi abokiti tareda surkawa da ruwan sanyi.
D'aukar bokitin tayi ahannunta ta nufi makewayin dake cikin gidan acan ta cire tufafinta ta fara gasa jikinta da ruwan zafi ko zogi da rad'ad'in da jikinta keyi zai ragu, bayan ta kammala gasa jikinta da k'yau sannan tayi wankanta ta fito d'aure da zane ajikinta rigarta rike ahannunta.
Direct room d'in Iya Kulu ta fad'a ta jawo manshafi ta shafe jikinta dashi sannan ta shafa powder afuskarta, dayake tufafinta duk suna gidan Yaseer da Nazifa ta korota babu abinda ta samu ta d'auko akan tsantsar tashin hankali da rikicewa saboda taga mutuwa k'iri k'iri afilin wuri!.
Wata tsohuwar atamfa ce ta d'auko ta sanya ajikinta sannan ta fito daga cikin d'akin ta isa wurin Iya Kulu, Iya tana ganinta ta girgiza kanta tace"keee miya kaiki sanya tsohuwar atamfa?".
Fauzeeya ta b'ata fuska cikin shagwab'a tace"banida wasu tufafi anan gidan duka kayana suna gidan yaya Yaseer gashi yanzu banida ikon zuwa can gidan ta kasheni! ".
Iya Kulu ta musk'uta tace"wai ina Yaseer yaje ne alokacin da abubuwan nan suka faru? ".
"katsina yaje jiya ayau shine tayimin wannan walakanci da tozarci ".
Iya Kulu ta gyad'a kanta tace"ai nasan da yana nan wa cece ita da har zata tozartaki k'aryarta tasha k'arya! ".
"tabbas sa'a ta samu da baya nan shiyasa ta samu galaba akaina".
"hmmmmmm tayi haukarta ta gama sai kin auri Yaseer ko zuciyarta bugawa zatayi ta mutu babu abinda ya shafeni! ".
"ai Iya ko akan ire iren abubuwan da Aunty Nazifa tayimin saina auri mijinta inga k'arshen haukarta kuma daga yanzu bazan sake yarda tana jibgata ba saboda ba baiwar gidansu bace ni! ".
"tabbas maganarki gaskiya ne Fauzeeya".
**********************
Agidan iyayen Nazifa hajiya Ramlat ce ta shirya cikin suturarta mai k'yawo domin taje gidansu Yaseer ta ciwa hajiya Sadiya mutunci,bayan Alhaji Mu'azu ya fita office tayi shigar alfarma direct parking lot ta nufa ta bud'e murfin motar ta shiga ta zauna mazaunin driver agefe ta aje handbag d'inta sannan ta danna horn da k'arfi getman ya shek'o ya wangale mata get d'in, ta kunna hancin motarta awaje tahau saman kwalta tanata sharar gudu kamar zata tashi sama.
Bata wani jima ba ta isa bakin get gidan Alhaji Taheer parker motarta agaban gidan ta fito daga cikin motar rataye da handbag d'inta a kafad'arta, maigadi ya lek'o ta k'aramin rami ta nan yaga hajiya Ramlat tsaye zata fara knocking d'in k'ofar get d'in kenan ya bud'e mata k'ofar tareda russunawa yace"hajiya barka da zuwa".
Hajiya Ramlat ta yamutsa fuskarta cikin isa da gadara tace"lafiya k'alau".Tana k'arasa maganarta taja k'afafunta ta nufi hanyar da zata sadata da parlourn dake cikin gidan.
Tana isa bakin k'ofar parlourn ta tura sannu ahankali zaune saman cushion ta hango hajiya Sadiya tana karatun hisnul muslim k'arasawa tayi wurinta tana mata wani irin kallo mai tattare da raini da tsagwaron takaici, hajiya Sadiya taji k'amshin turare shiyasa ta d'ago kanta idanunta suka fad'a cikin na