Showing 57001 words to 60000 words out of 87802 words
shawarar irin hukuncin da zamuyi mata domin ki huce takaicinta".
Alokacin ne Nazifa taji sanyi aranta tace"nima ban d'auka da zafi ba aminiyata abinda zamuyi shine idan Yaseer ya fara fita office muje muyi mata dukan tsiya! ".
"kina ganin haka zaifi sauk'i maigadin gidanku yana fita ne?".
"kece dai shegen d'an sa ido kenan baya fita zuwa ko'ina Safiya idan har muka rutseta cikin parlourn bazaiji kuwwarta ba saboda bai cika ji sosai ba".
"to yayi ki kwantar da hankalinki zamuje mukai mata farmaki agida".
"bar shegiya damu take zancen".
*********************
Aroom d'in Fauzeeya ce take kwance saman gado bayan tafiyar Yaseer d'akinsa tana waya da Iya Kulu kakarta, sai sagarci da shagwab'a take zubawa kakarta ita kuma sai biye mata takeyi saboda tana matuk'ar k'aunarta fiyeda tunanin mai karatu.
Iya Kulu ce naji tace"Fauzeeya ya kishiyarki ina fatar kina zaune da ita lafiya tareda yi mata biyayya?".
Zumb'ura baki tayi tace"Iya halayyarta sai ahankali saboda gaskiya idan bana kai zuciyata nesa bazan iya hak'uri da halayyarta ba ita komai nata azafafe takeyinsa".
Iya Kulu taja nannauyar ajiyar zuciya tace"ki cigaba da hak'uri da halayyarta duk zafin kishi ne yake damunta sannan duk zagin da zatayi miki bance ki tanka mata ba karki kuskura ki biye mata ku tayarwa da mijinku hankali domin kishi ba hauka bane".
"da yardar Allah bazan ma biye mata Iya mu dinga fad'a kamar karnuka mak'wabta su lek'o ta katanga suna kallonmu".
"yauwa d'iyar albarka ashe dai kinada fahimtar yadda rayuwa ke tafiya".
"haba Iya karki maidani k'aramar yarinya sosai ai nasan komai fa".
"shikenan Fauzeeya acigaba da hak'uri zaman aure saida juriya da hak'uri yake k'arko"."Ba komai Iya ai hak'uri ya zamo wajibi agareni muddin inason in zauna lafiya da mijina"."ubangiji yayi miki albarka sai anjima"."To Amin ina gaida babana"."Zaiji 'yar baba".Iya Kulu tana k'arasa maganarta ta katse wayar murmushin jin dad'i k'unshe afuskarta.
Ahankali ta mik'e tsaye ta fad'a d'akin baba Labaran dayake zaune shida Inna Munari suna sakarwa juna bak'ak'en maganganu, tana shiga bata fahimci fad'a sukeyi ba tace"Labaran d'iyarka Fauzeeya tana gaidaka".Baba Labaran ya washe baki cikin farin ciki da k'aunar 'yarsa yace"Allah sarki d'iyar albarka yaushe kukayi waya da ita Iya"."Yanzu yanzun nan na gama waya da ita".Har baba Labaran ya bud'i baki zaiyi magana kenan Inna Munari ta katse masa hanzari taja tsoki mtsssssss cikin matuk'ar hassada da bak'in ciki shimfid'e k'arara afuskarta tace"dallah kuyimin shiru kunzo kun cikamin dodon kunne da surutun banza! Kuna wani zancenta saikace d'iyar gwal idan surutu zakuyi ku ficemin ad'aki kaida munafukar uwanka! ".
Iya Kulu ta rik'e baki tana k'ara jinjinawa rashin mutunci irin na Inna Munari yayinda baba Labaran ya hasala da zagar masa uwa da tayi, zuciyarsa ta kawo awuya wani irin d'aci da zogi zuciyarsa keyi mugun kallo yayi mata wanda saida d'iyan hanjin cikinta suka motsa yace"Munari yanzu saboda bakida albarka mahaifiyartawa kike zagi?".
Inna Munari tace"na zageta kayi abinda zakayi!".Ta fad'a cikin rashin kunya da rashin sanin darajar uwar miji.
Baba Labaran zai sake magana kenan Iya kulu ta girgiza masa kai tace"k'yaleta indai akaina ne duk abinda mutum yakeyi barinsa yakeyi indai duniya ce wanda baizo bama jiransa takeyi !".Tana rufe bakinta ta fice daga cikin d'akin ta koma nata d'aki,Baba Labaran yajuyo ya kalli k'wayar idanun Inna Munari yace"kinci darajar mahaifiyata dayau saina yi miki mugun duka acikin gidan nan".
"na zata kasheni zakayi ba iya duka zaka tsaya ba!".
Baba Labaran yace"bani duk kasheki saboda bakiji ance ina kashe mutane ba kwakkwaran mataki zan d'auka akanki".Inna Munari ta d'aga muryarta k'warai tace"ahayyyeehhh duk abinda zakayi kaje kayi bana tsoronka bana tsoron duk wani shege ko d'an iska agarin nan ".Baba Labaran ya gyad'a kansa cikin b'acin rai yace mata "zan nuna miki iskancinki k'arami ne Munari saina saina fasa miki rub'abb'en bakinki "............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 34*
Inna Munari tayi k'yafci cikin matuk'ar zafin rai tace"ba nice da rub'abb'en baki ba mai tsamiya ce mai baki da wari!".Baba Labaran ya kalleta da idanunsa da suka kad'a sukayi jawur adalilin b'acin rai da jifansa da takeyi da kalamai masu iya tarwatsa zuciya zama guda jan numfashi yayi mai d'aci yace"mahaifiyata ce mai warin baki Munari?"."Eh mana na fad'a sai mi ko akwai hukuncin da zaka iyayimin ne?.Baba Labaran ya girgiza kansa alamar a'a sannan ya furta"babu abinda zan iya miki".Gama maganarsa keda wuya yaja k'afafunsa yabar d'akin akumbure zuciyarsa sai suya da tsantsar zafi takeyi masa amma dole ya daure ya cigaba da sha'anin gabansa.
Inna Munari tana ganin ya fice daga cikin d'akin ta mik'e tsaye ta harhad'o kayayyakinta masu dauda wuri d'aya, ta kwasa ta nufi tsakiyar filin gidan domin ta wawwake kayanta ruwa ta d'ebo afamfo ta ciccika bokitaiya da robobi manya ta dawo ta zauna ta fara wanke kayanta atsanake..
Da tsakar dare su baba Labaran suna kwance saman katifa sun fara barci can Inna Munari ta sanya k'afafunta ta shuri baba Labaran aciki, cikin barci yaji zafi ya farka yana fahimtar itace ta shuresa dayake yanada takaicinta cikin matuk'ar hasala sosai yace"keeee wace irin jakar mace ce da baki iya yin kwana cikin natsuwa ba!?".Makin taga daga ita saishi cikin d'akin tayi shiru sai tace"ai ba'a tab'a yin jaka guda d'aya saidai jakuna! ".Baba Labaran ya nad'e wandonsa cikin matuk'ar b'acin rai ya rufeta da duka Inna Munari ta saki rikitaccen kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro, cikin zafin rai yake dukanta can yaja ya tsaya yace"gobe ki sake zagina ko zagin mahaifiyata kiga irin hukuncin da zanyi miki na rantse da girman Allah idan kika sake na fara dukanki sai kinyi fitsari da tutu awando!".Inna Munari bata sake cewa k'ala ba gudun kada ya k'ara tumurmusarta cikin d'aki babu mai cetonta shiyasa jikinta yayi lak'was tsananin fargaba da tsantsar tsoro ne ya shiga cikin zuciyarta farat d'aya, baba Labaran kwanciyarsa yayi ya barta zaune tana risgar kukanta ganin zata dameshi da kukan munafurci yasa ya daka mata tsawa yace tayi masa shiru ko ya k'ara mata! Jikinta yana kad'uwa da k'yarrrma tasa hannu ta rufe bakinta saida taci kukanta harta k'oshi sannan ta kwanta hawaye sai shatata sukeyi saman fuskarta...
*********************
*BAYAN SATI BIYU*
Yaseer ya fara zuwa office ranar girkin Fauzeeya tunda safe take tashi bayan sallar asuba ta aza masa ruwan zafi ta juye abucket, idan ta surka da ruwa masu sanyi saita tayasa cire tufafinsa ta kaishi har cikin bathroom yayi wanka, ta fito ta cigaba da gyaran bedrooms da parlour saita tsabtace lungu da sak'o na cikin gidan sannan ta fad'a cikin kitchen tana k'ok'arin had'a breakfast.
Idan ta kammala ta juye ruwan zafin aplask ta d'auka takai saman dining table ta jajjerasu, sannan ta koma cikin room d'in koda ta shiga ta hango Yaseer tuni ya fito yana shiryawa cikin tsadadden yadinsa mai k'yau ya kawo turare ya feshe jikinsa dashi hula ya sanya akansa yana kallon kwalliyarsa cikin dressing mirror, yayinda Fauzeeya ta iso wurinsa tana jifansa da kallon soyayya tace"kayi k'yau yayana shiyasa ina kishin ka fita da wannan kwalliyar domin kada wata ta ganka ta k'yasa".
Yaseer yayi murmushinsa mai ma'ana yace"haba dai my Fauzee miye abin kishi aciki aini tuni na mallaka miki makullin zuciyata ta yadda babu macen da zata iya bud'eta ta shigo ciki".Fauzeeya ta sanya hannunta ta gyara masa hularsa cikin shauk'in so tace"gaskiya naji dad'in yadda ka bani babban matsayi arayuwarka nima ka sani da sonka nake rayuwa dashi zan mutu azuciyata".
Yaseer yaji matuk'ar dad'in kalamanta agogon dake mak'ale ahannunsa ya duba yace"ina godiya sosai da kulawa lokaci yana tafiya nizan wuce office kada inyi late".
"breakfast d'in fa yah Yaseer?".
"zanyi a office".
"shikenan hubby amma dan Allah karka bar kanka da yunwa".
"bazan bari ba dear".Yana isa wurin kofa ya sanya hannunsa ya fice daga cikin d'akin.
Murmushin farin ciki ne shimfid'e k'arara afuskarta numfashi ta sauke tace"Allah sarki mijina farin cikin rayuwata saika dawo".
Daga cikin d'akin ta fito ta dawo parlour ta zauna tareda kunna kallo ta fara yi hankali kwance, kallo d'aya zakayi mata ka gane tana cikin jin dad'i da kwanciyar hankali saboda duk abinda takeso gwargwado Yaseer yana siyowa ya kawo mata.
*********************
Acikin katafaren had'add'en office mai d'auke da ni'imtaccen k'amshi mai dad'i na hango Yaseer zaune saman kujera ga takardu nan birjik agabansa sai aiki yakeyi cikin k'warewa da natsuwa, agefensa computers da newspapers saman teburin.
aiki yakeyi babu kama hannun yaro zuciyarsa cikeda matuk'ar farin ciki da tsantsar soyayyar Fauzeeya daya kanainaye zuciyarsa zama guda, ya dad'e sosai yana aiki saiga sallamar Abduljalal ya bud'e k'ofar ya shigo cikin office d'in direct ya iso wurinsa yaja kujerar dake fuskantar Yaseer ya zauna, Yaseer ya amsa sallama tareda bashi hannu sukayi musabaha Abduljalal ya jaye hannunsa yana murmushi k'unshe afuskarsa yace"ango kasha k'amshi mijin Nazifa angon Fauzeeya gwarzon namiji mai wuyar samu".
Yaseer ya dago fararen idanunsa ya dubi fuskar Abduljalal yana dariyarsa mai k'yau yace"gaskiya abokina ka iya kirari sosai da ace ka zama mawak'i daka samu kud'i sosai".Yace azolaye.
"ka daina zolayata Yaseer gaskiya yanayinka ya chanza akwanakin nan sai haske da k'yallin amarci kakeyi amarya ta iya kula dakai yanzu kasan kayi aure".
Yaseer ya ajiye bironsa saman desk yace"kamar ko kasan ta iya kula dani Jalal alal hak'ik'a ayanzu kam nayi sa'ar samun mace ta gari, yanzu hankalina kwance banida wata damuwa saboda duk abinda nakeso amaryata tana yimin gwargwadon iyawarta".
"kayyyy gaskiya nayi matuk'ar maka murna ubangiji ya baku zuri'a d'ayyiba masu tausayinku".
"Amin Jalal kaima ina alfahari dakai saboda kaine ka jajirce ka bani shawarar yadda zanyi in kare kaina daga fad'awa cikin tarkon shaid'an! Nasan da babu kai da tuni na jefa rayuwata cikin matuk'ar halaka".
"ba komai Yaseer ai zaman tare ne idan ban baka shawarar kirki ba ai ban cika abokinka na gari, kuma idan na k'yaleka ka afka cikin sab'on Allah ka sani nima inada kamasho na zunubi aranar gobe k'iyama idan har nayi sakacin daka fara aikata mugayen ayyuka to na munafurceka kuma bana daga cikin abokai nagari".
"wato Jalal Nazifa taso jefa rayuwata cikin matuk'ar halaka tareda nuna mini hanyar da zata kaini cikin wutar jahannama, domin kwata kwata ire iren abubuwan da takeyimin sun sab'a shari'a tareda wuce gona da iri amma kaga yanzu na kawo idanu na saka mata duk abinda zatayi taje tayi tayi ita ta sani babu ruwana".
"duk da haka bazaka k'yaleta ba nasiha zaka dinga yi mata har ubangiji yasa ta gyara halayyarta saiku zauna lafiya, kasan su mata da kake gani saida lallashi da tattausan lafazi mai dad'i yake sanya ka shawo kansu fad'a ko tsauri baya saka su chanza yanayin halayyarsu".
"tabbas gaskiya ne Jalal".
Abduljalal ya gyad'a kansa cikin sanyin hali yace"saboda haka karkayi tunanin bazata shiryu ba ita shiriya ta ubangiji ce zai iya shiryata akowane lokaci ya dace kabi komai ahankali".
"ba damuwa zanbi komai asannu ubangiji yayi mana jagora cikin lamarinmu".
"Amin ya rabbi dan Allah ka had'e kan matanka wuri d'aya banda nuna bambanci atsakaninsu ".Cewar Abduljalal cikin iya magana.
"zanyi iyakar bakin k'ok'arina wurin ganin na daidaita adalci atsakaninsu da yardar Allah ba za'a samu wata matsala ta gefena ba".
"hakan yayi nizan koma office d'ina na barka lafiya".
"OK thanks".
Abduljalal ya tashi tsaye ya fice daga cikin office d'in Yaseer ya koma nashi office domin ya k'arasa sauran ayyukan dabai kammala ba, yayinda yabar Yaseer zaune yana cigaba da aikinsa domin so yake ya samu ya kammala da wuri kafin lokacin tashinsa yayi a office..
*********************
Fauzeeya ce na hango cikin kitchen tana kichaniyar aza abincin dare saboda so take ta kammala da wuri ta huta, tukunyar tuwon semonvita ta fara azawa ruwan data saka aciki suna tafasa ta tuke tuwon ta sanya cikin kula madaidaiciya, sannan ta aza tukunyar miya tayi jajjagen kayan miya ta kawo ta zuba cikin tukunya k'amshi duk abinda ya gauraye cikin gidan gaba d'aya,ta kawo magugguka ta zuba cikin miyar ta koma gefe tayi zaune saman kujera tana jiran miyar ta nuna.
Ta jima zaune miyar tayi ta sauke k'asa ta juye cikin k'aramar kula sannan ta d'auko babban tire ta aza kulolin saman tire, sannan ta fice daga cikin kitchen d'in ta nufi dining table ta jajjerasu samansa sannan ta shiga cikin d'akinta, murmushi shimfid'e afuskarta ta jawo phone d'inta tana danna yayinda ta shiga contact ta turawa mijinta sak'o kamar haka:
_Mijina ina fatar kana cikin walwala da yalwar farin ciki azuciyarka, akowane lokaci idanuna suna marmarin in sake yin tozali da k'yak'k'yawar fuskarka hancina yana muradin jin k'amshinka, fatana shine in ganka gani gaka soyayyarka sai k'ara kwaranya yakeyi aruhina shauk'in so sai nuk'urk'usar zuciyata yakeyi, ka sani har abada *SOYAYYAR GASKIYA* nakeyi maka dakai zan rayu mu mutu tare alkhairin ubangiji ya riskeka aduk inda kake yayana._
_Karka manta da cewa ina matuk'ar k'aunarka arayuwata zuciyata mallakinka ce._
Tana kammala rubutawa ta turawa Yaseer cikin wayarsa sannan ta cire tufafinta ta fad'a cikin bathroom domin ta tsabtace jikinta taji sanyi azuciyarta.
Yaseer yana zaune saman kujera yana harhad'a takardar da kayayyakinsa cikin briefcase domin ya tafi gida ya iske farin cikin rayuwarsa, yana tsakar kwashewa saiga text message d'in ya shigo cikin wayarsa kuka phone d'insa tayi alamar sak'o yayi shigo sanya hannunsa yayi ya zaro phone d'insa ya bud'e text message d'in da Fauzeeya yana karantawa.
Tsantsar farin ciki da k'aunar Fauzeeya ne k'unshe afuskarsa wani irin sanyi da tsananin murna yake bin jini da magudanar jikinsa tabbas text message d'inta yayi matuk'ar yi masa dad'i azuciya, alal hak'ik'a ya sadak'ar yanzu yayi matuk'ar dace da mace ta gari abar alfahari ga kowane d'a namiji.........
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 35*
Dak'yar ya saisaita kansa ya cigaba had'a kayayyakinsa cikin briefcase d'insa yana gama hadasu wuri d'aya, ya d'auki briefcase d'in tareda mayarda phone d'insa cikin aljihunsa ya jawo k'ofar office d'insa direct wurin daya parker motarsa ya nufa ya zaro key d'in ya sanya ya bud'e k'ofar motarsa ya shiga ya zauna tareda ajiye briefcase d'in mazaunin da babu kowa, kai tsaye ya tadda motarsa ya nufi hanyar zuwa gidansu domin yaga hajiyarsa wadda bayada kamarta aduk fad'in duniyar nan.
**********************
Su Nazifa suna tashi daga shago suka shiga cikin motar Safiya suka rankaya zuwa gidan Yaseer domin su ciwa Fauzeeya mutunci tareda tozartata abanza.
Gudu sukeyi saman kwalta domin kada Yaseer ya rigasu dawowa cikin gidan duk da Nazifa ta gaya mata baya dawowa da wuri amma tana gudun ya kamasu k'iri k'iri suka walak'anta masa 'yar mata, firarsu sukeyi suna tafiya har iso bakin get d'in gidan Yaseer Safiya ta parker motarta agaban gidan sannan suka fito daga cikin motar kusan tare suka jera suka shiga cikin gidan, baba maigadi yana zaune suka gifto ta gabansa suka wuce ko kallo bai samu ba bale ya samu darajar su gaidashi ya lura tun ranar da sukayi sa'insa da Nazifa, ta d'auki karan tsana da jin haushinsa ta sanya azuciyarta shi kuma bai damu da ita saboda yasan yarinyar batada mutunci bata ganin kowa da gashi akai sai ita, amma yasan duk abinda takeyi laifin iyayenta ne da suka sagartata tun farko bayansu yakebi da kallo har suka shige cikin parlour suka rufe k'ofar garammm da k'arfi!.
Su Nazifa suna shiga tsakiyar parlourn suka hango Fauzeeya sai jera kulolin abincin rana takeyi domin itace ta girka abincin saboda batason ana sakarwa Tasallah duka ayyukan gida,kulolin data sanya abincin dare ta jayesu gefe ta yadda mai hankali zai iya fahimtar akwai bambaci, kanta yana duk'e bataji motsin shigowarsu ba domin ba sallama sukeyi ba aikinta ta cigaba dayi harta gama ta juyo fuskarta dagowar da zatayi idanunta sukayi mata tozali dasu yayinda taji matuk'ar tsinkewar zuciya da damuwa alokaci guda zuciyarta ta dingayin luguden tsoro da fargaba ne ya bayyana k'arara afuskarta, daurewa kawai tayi ta b'oye fargabanta ta isa tsakiyar parlourn ta fad'ad'a fuskarta da fara'a da murmushi tace"a'aaaaa su Aunty har kun dawo sannunku da zuwa bari in kawo muku ruwa ku jik'a mak'oshinku".Zata juya kenan Nazifa tayi sauri dakatar da ita da k'arfi tace"bama jin k'ishirwa dawo kiyi zamanki 'yar gaban goshin miji".
Cikin mutuwar jiki Fauzeeya ta zauna k'asan carpet tana mimmik'e k'afafunta, Nazifa ta sake magana cikin matuk'ar b'acin rai da tsantsar tsanar kishiya tace"keeeee bak'ar kishiya wadda ta zamo annobar gari! Wurinki muka zo domin muyi miki hukuncin cin amana da butulcin da kikayi na auremin miji asanadiyyar kwad'ayi da dogon buri! ".
Gabanta ya fad'i hankalinta ya d'unguma zuciyarta ta girgiza cikin matuk'ar sanyin murya tace"Aunty miye dalilinku na zuwa wurina naga babu abinda yake shiga tsakanina dake na rashin mutunci?".
Safiya ta kalleta cikin haushinta da bak'in ciki tace"keee karki nemi ki raina mana hankali uban wa yace ki auri Yaseer dan ubanki? Wato anga mai arziki jar fata kin lik'e masa keba abin kunya bane awurinki adubeki adubeshi shine mijinki".
"ina ko zai zamo abin kunya awurinta Safiya ai ina gaya miki tun kafin ayi aurensu idan yaga bana nan yake cinta shiyasa ta mak'ale tace saishi, kalli fa boob's d'inta yadda suka k'ara cika sukayi