Showing 27001 words to 30000 words out of 87802 words

Chapter 10 - SAKACI BY MUGIRAT MUSA

05 Jul 2024

4231

hajiya Ramlat, ganin itace yasa ta fad'ad'a fuskarta da fara'a da murna tace"hajiya Ramlat kece agidana sannu da zuwa".
"nice Sadiya".Tace cikin matuk'ar b'acin rai.
Hajiya Sadiya tayi murmushin dake k'ayatar da fuskarta tace"ki zauna mana bari in kawo miki ruwa kisha".
Cikin kakkausar murya tace"dakata Sadiya! Na hutassheki ba ruwa nazo sha ba".
Tsantsar mamaki da al'ajabin maganarta ne ya wanzu afuskar hajiya Sadiya cikin rashin kuzari tace"mi ya kawo wannan maganar Ramlat to idan bazaki sha ruwa ba miye dalilin zuwanki?".

Hajiya Ramlat ta gyara tsayuwarta cikin matuk'ar takaicin Sadiya tace"dalilin dayasa nazo gidanki akan munafikin d'anki Yaseer zai k'ara aure! Idan banda rainin wayo ya rasa wacce yake so aduk fad'in garin nan sai Fauzeeya yarinyar da Nazifa ta raineta da hannunta, wannan ai cin amana ne da kuma zalunci! ".

hajiya Sadiya tayi murmushin mai k'unshe da bak'in ciki da tsantsar takaici sannan ta musk'uta tace"yanzu akan Yaseer zai k'ara aure shine kika zo har cikin gidana domin ki gayamin magana!".

"abinda yafi wannan maganar zafi zan iya gaya miki saboda dasa hannunku keda mijinki acikin wannan auren, to wallahi baku isa ba kunyi kad'an ku tozartamin d'iya mu bamu gaji zama da kishiya ba mu kad'ai mu gadi zama agidan mazajenmu".

"hmmmm zancen banza kenan atunaninki ita kishiya gadon zama da ita akeyi ne? Kinyi gurguwar fahimta Ramlat sannan eh mu muka goyi bayan Yaseer ya k'ara aure saboda ba haramun bane saboda haka ki ficemin daga cikin gida banason rashin mutunci! ".

"babu inda zanje har sai na amayar da abinda yake cikin cikina to ki sani ko kin koreni ba zanje ko'ina ba, sai munyi masifa da bala'i acikin gidan nan saboda na fahimci bak'ar munafukar mata kike! ".

"to karki fita zauna kiyimin d'ibar albarka Ramlat wawuyar banza! ".

Hajiya Ramlat ta iso wurinta cikin matuk'ar hasala tace"uwarki ce wawuyar banza dangin tsiya! ".

Hajiya Sadiya tace"naji dai duk zagin da zakiyimin ko ajikina saboda na fahimci duk zafi da rad'ad'in za'ayiwa d'iyarki kishiya yake damunki aure kam babu fashi saiya auri Fauzeeya! Ko zaku had'iyi zuciya ku mutu sai anyi saboda haka kuba zuciyarku hak'uri da dangana".

"haka kikace Sadiya!? ".

"na fad'a da babbar murya! ".

Hajiya Ramlat ta rike k'ugu cikin son tashin hankali da fitina tace"ina tabbatar miki ko Yaseer ya auri Fauzeeya bazai tab'a samun kwanciyar hankali ba har abada sai munga abinda ya turewa buzu nad'i! ".

"kije kiyi duk abinda zakiyi ubangiji ya fiki mahaukaciya wadda batasan ciwon kanta ba! ".

Hajiya Ramlat ta tunkaro wurinta gadan gadan ta kawo mata wawura da nufin tayi mata illa hajiya Sadiya ta sunkuya k'asa hannun hajiya Ramlat ya bugi cushion, ta mik'e tsaye cikin matuk'ar zafin nama ta kwasheta da mari biyu masu k'yau wanda asanadiyyar haka saida tayi taga taga zata fad'i ubangiji kawai ne ya kareta bata fad'i k'asa ba dafe kuncinta tayi cikin zafi da rad'ad'in mari tace"Sadiya kika mareni!? ".

"an mareki Ramlat abinda yafi mari ma zan iyayi miki idan baki kiyayeni ba! ".

Cikin kunya da matuk'ar tafasar zuciya hajiya Ramlat tace yayinda idanunta suka kad'a sukayi jajir akan tsantsar takaici da k'unar zuciya"tabbas zakiyi nadamar marina da kikayi arayuwarki saina haddasa miki tashin hankali da fitinar rayuwa sai kin gwammacewa kid'i akan karatu! ".K'arasa maganarta keda wuya taja k'afafunta ta fice daga cikin gidan da sauri kamar zata tashi sama akan sauri.

Hajiya Sadiya ta d'aga muryarta da k'arfi tace"shashasha duk abinda zakiyi kije kiyi ina jiranki ko gobe kika sake tako k'afarki gidan nan da sunan rashin mutunci sai nayi miki abinda yafi wannan! Sakaryar uwa wadda tayi sanadiyyar tab'arb'arewar tarbiyar d'iyarta ".Haka dai hajiya Sadiya ta cigaba da fad'a tana sabbatunta kamar ta ari bakin kura saboda abinda hajiya Ramlat tayi mata ya matuk'ar k'ona mata rai da sanya bak'in ciki azuciyarta.

____________________

Rai b'ace hajiya Ramlat ta dawo cikin gidan mijinta cikin matuk'ar b'acin rai da zafin zuciya ta rasa abinda yakeyi mata dad'i aduniya sai zagayar d'akinta takeyi, kallo d'aya zakayi mata ka gane tana cikin matsanancin hali da matuk'ar damuwa.
Ta dad'e tsaye shiru can dai tayi ajiyar numfashi ta jawo phone d'inta tayi dialling nombar Nazifa tana shiga tayi receiving call tace"hello Ummu barka da yau".

"barka dai baby Nazifa ya kike yasu Sameer? ".

"lafiya k'alau suke".

Hajiya Ramlat ta musk'uta tace"dama abinda yasa na kiraki domin in sanardake naje gidan iyayen Yaseer na isko hajiya Sadiya munyi kacha-kacha nida ita uwa kuturu kaka makaho! Saboda haka gidan kakar Fauzeeya kawai ya rage inje mu fafata nida ita ".

Nazifa tayi tsallen murna kamar tana gaban mahaifiyarta wani irin dad'i da sanyi ne ke kwaranya cikin jini da sassan jikinta cikin matuk'ar nishad'i tace"agaskiya Ummu kin sanyani cikin matuk'ar farin ciki baki tab'a burgeni ba irin yau ba shiyasa nake k'ara sonki ".

Hajiya Ramlat taja dogon numfashi tace"karki damu zan iyayi komai akanki muddin ina raye babu ke babu kukan bak'in ciki har abada ".

"Allah sarki uwa mai dad'i ina godiya gareki mahaifiyata ".

"ba komai ki gaidamin dasu Sameer ".

"OK zasuji".Tana k'arasa maganarta taji hajiya Ramlat ta katse wayar murmushi k'unshe afuskarta cikin farin ciki ta dubi fuskar Safiya tace"kinji abinda Ummu ta gayamin Safiya? ".

Safiya ta girgiza kanta alamar a'a tace"sai kin fad'a".

Nazifa ta langwab'e kanta tace"yanzu Ummu ke gayamin cewa taje har gidansu Yaseer ta ciwa munafukar uwarsa mutunci wadda ta d'aure masa gindi ya k'ara aure! ".Safiya ta bushe da dariyar mugunta can ta tsagaita tace"kice kenan an fafata rigima da hayaniya atsakaninsu kenan! Hmmmmmm naso ace agabana sukayi fad'a ".Nazifa ta kalli k'wayar idanunta tace"keji ki da wata magana idan gaba gareki akayi fad'an mi zakiyi? ".Safiya ta bintsire baki tace"kallonsu zanyi mana".
Nazifa ta girgiza kanta tace"ina ruwan mai kallon video kenan".
"ai fad'a yafi video dad'in kallo Nazifa ".
"haka kika fad'a kenan k'awata "."Haka yake Nazifa d'iyar Ummu ".Ta fad'a azolaye cikin wasa............

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 17*



Nazifa tayi murmushinta mai k'yau tace"fad'i ki k'ara fad'a nice guda ba k'ari".Safiya ta karkace baki tace"awurin Ummunki ko ba'a wurin Yaseer ba".Nazifa ta harareta da wasa tace"kedai bak'ya rabo da zolaya wallahi har awurinsa ni kad'aice cikin fadar zuciyarsa Fauzeeya matsayin photo kawai na d'auketa ba komai ba"."kayyyy kina wata magana fa Nazifa karfa ki ganeta k'aramar yarinya ki mata kallon batasan aikin da take ba kinsan hausawa sunce d'an hakin daka raina shike tsone maka idanu! ".
Nazifa tayi mata wani irin kallo mai nuni da zafin kishi tace"ya isa Safiya! Maganarki tana b'atamin rayuwa fa taya zaki kalli tsabar idanuna kice Fauzeeya zata iya bani mamaki wato na fahimci dad'i kikeji azuciyarki za'ayimin kishiya! ".
Safiya ta marairaice fuskarta tareda had'e hannunta wuri d'aya alamar rok'o tace"kiyi hak'uri Nazifa niba haka nake nufi ba karki yiwa maganata gurguwar fahimta, taya zanji dad'i adalilin za'ayi miki kishiya ai duk abinda ya sameki ya sameni Aminiyata".
Sai alokacin ne Nazifa taji zuciyarta tayi sanyi damuwarta ta ragu tace"ok na fahimceki komai ya wuce".
Safiya ta aza hannunta saman cinyoyinta tace"ki kwantar da hankalinki ko Yaseer ya auri Fauzeeya zamu shirya mata tuggu da makirci har sai tabar gidansa da k'afafunta dole ba domin son ranta ba".

Nazifa ta k'ara gyara zamanta tace"to ta yaya kike tunanin zan iya fitar da ita da k'arfi daga cikin gidan Yaseer? ".
Safiya ta kalleta cikin fara'a tace"idan akayi auren zan sanardake tuggun dana shirya mata amma fa abin sirri ne daga ni sai ke sai Allah".

Jijjiga kanta tayi tace"nasan da haka Aminiyata".

"ki bari idan lokaci yayi zakiji abinda nake shirya mata tana ruftawa cikin tarkon da zamu d'ana mata to babu ita babu Yaseer tana ji tana gani zai rubuta mata takardar saki ya bata! ".

Nazifa tayi murmushin dake bayyana hak'ora tace"Safiya kenan bakida sauk'i cikin lamarinki komai cikin tsari kike yinsa".

"nice wasa ko aikina kedai ki zuba idanu kiyi kallo".

"ai idan lokacin yazo zanyi kallo Safiya".
Cigaba da maganganunsu sukayi cikin natsuwa yayinda sai mayarda zancen Fauzeeya sukeyi suna shawarar yadda zasu b'ullowa al'amarin, domin ganin sun cimma burinsu da tarwatsa farin cikin Yaseer da Fauzeeya.

*********************

*BAYAN KWANA UKU*
Agidan Iya Kulu suna zaune itada Fauzeeya suna cin tuwon shinkafa da miyar sure yayinda zabbi da kaji sai yawo sukeyi atsakar gidan.
Alokacin ne Iya Kulu ta dubi Fauzeeya tace"Fauzeeya".
"na'am Iya".Cewar Fauzeeya.
Iya Kulu ta musk'uta cikin yanayin farin ciki tace"nayi magana da babanki Labaran yacemin ya siyo miki wasu kayayyakin aure sannan anjima kije gidan ki k'ara siyo duk abinda kikeson siya".
Fauzeeya ta zumb'ura baki tace"to Iya amma agaskiya ni ina tsoron Inna Munari domin matar nan batada mutunci bata ganin kowa da gashi akai ".
Iya Kulu taja tsoki mtsssssss tace"ina ruwanki da matarsa kedai idan kikaje wurinsu duk abinda tace miki bance ki kulata ba saboda nima ba ragamin takeyi ba".

"hmmmmmm Iya matar nan ta baba sai addu'a saboda ta fita daga cikin hayyacinta".

"duk abinda takeyi Fauzeeya iskanci ne tana cikin hayyacinta rainin hankali ne da walak'anci amma ba komai duk abinda mutum yakeyi aduniya wata rana dole yabarsa indai duniya ce ta ishi kowa riga da wando wanda baizo bama jiransa takeyi".

"wannan zancen naki haka yake Iyata".

Har Iya Kulu ta bud'i bakinta kenan zatayi magana saiga hajiya Ramlat ta shigo da wasu k'atti majiya k'arfi mutum biyu kadaran majaran, tafiyarsu sukeyi cikin isa da k'asaita kodasu Iya Kulu sukaga mutane cikin gidan gabansu ya fad'i rasssss hankalinsu yayi k'ololuwar tashi fargaba da tsantsar tsoro ne ya bayyana k'arara afuskarsu cikinsu sai k'ugi yakeyi tsuuuuuuuu k'ululululu zad tausayi, suna isowa wurinsu hajiya Ramlat taja k'aramar kujera ta zauna tana jifarsu da walak'antaccen kallo tace"Kulu ina fatar kin ganeni?".

Iya Kulu ta tsorace da gigicewa cikin tsinkewar zuciya tace"eh na ganeki kece hajiya Ramlat mahaifiyar Nazifa wadda ta raini Fauzeeya".

"da k'yau ashe baki manta dani ba".

"eh mana hajiya ban manta dake ba".Tace cikin yanayin firgici da d'imauta! .

Hajiya Ramlat taja dogon numfashi tace"dalilin daya kawoni gidanki Kulu wato ita rayuwa da kike gani duk yadda ka amince da mutum ka bashi amana sai yaci amanarka, idan banda kuna butulu kwad'ayayyu taya zaku d'auki Fauzeeya kuba Yaseer wannan ai zalunci ne da *BUTULCI* !Saboda haka abinda nakeso gareki kiyiwa d'anki Labaran magana akan awarware maganar aurensu tun muna shaidar juna kafin duniya ta jimu".

Dummmm gaban Iya Kulu ya fad'i hankalinta ya d'unguma zuciyarta ta tsinke! Tsagwaron tashin hankali ne da tsantsar tsoro ya bayyana k'arara afuskarta cikin mutuwar jiki ta rausayar da kanta tace"kiyi hak'uri hajiya banida masaniya akan abinda yake faruwa! ".

"rufemin baki banason munafurci! Idan har ke bakida masaniya akan abinda yake faruwa ai ita Fauzeeyar duk abinda yake faruwa ta sani, bari kiji tsohuwa billahillahi banida mutunci ko tausayi matuk'ar akan Nazifa ne domin haka na baku sati d'aya tak kuje kuyi duk yadda zakuyi awarware baikonsu! ".

Alokacin ne hajiya Ramlat ta juya b'angaren Fauzeeya cikin kakkausar murya tace"ke kuma na dawo gareki muddin kinason kanki da zaman lafiya da kwanciyar hankali ki fita daga cikin sha'anin mijin 'yata! Idan banda lalacewa da mutuwar zuciya kaf garin nan ki rasa wanda kikeso sai Yaseer hmmmm tabbas d'an Adam butulu ne kayi masa alkhairi ya saka maka da sharri ".

Fauzeeya dai noce kanta tayi k'asa batare mata uffan ba saboda gudun tasa k'attin mazan su afka mata, shiyasa ta dinga kwararo addu'o'in neman tsari cikin zuciyarta saboda gudun abinda zaije ya dawo.

Jikin Iya Kulu yana k'yarrrma da kad'uwa cikinta sai k'ugin tsoro yakeyi k'ululululu bakinta yana rawa tace"karkiji komai hajiya da yardar Allah zuwa gobe da kaina zanje in samu mahaifinta Labaran domin awarware komai kiyi hak'uri munsan munyi kuskure kinji ".

Hajiya Ramlat ta mik'e tsaye yayinda su Baura suke tsaye k'yam kamar gumaka jira kawai sukeyi hajiya Ramlat ta basu umurnin su afkawasu Fauzeeya, murmushin mugunta hajiya Ramlat ta saki tace"naji uzurinki Kulu wannan maganar ba rok'onku nakeyi ba umurni ne na baku idan kunbi ku zauna lafiya idan baku bi ba rayuwarku tana cikin had'ari da tashin hankali! ".

Mayarda kallonta tayi wajensu Baura tace"Baura muje gida zamu dawo wata rana".

"da girman kujerarki hajjaju".Cewar Baura ya russuna mata cikin girmamawa.

Hajiya Ramlat ta shiga gaba tana tafiya guda guda cikin gadarar ita d'in hajiya ce matar Alhaji, yayinda su Baura ke take mata baya kamar gimbiya da bayinta haka suka fito daga cikin gidan Iya Kulu suka shisshige cikin motarta, Baura shine ya zauna mazaunin driver d'an uwansa yana gefensa nan da nan suka tadda motar suka nufi hanyar zuwa gidan Alhaji Mu'azu.

*********************
Su hajiya Ramlat suna fita daga cikin gidan Iya Kulu ta kalli fuskar Fauzeeya afirgice tsantsar tsoro da d'imaucewa ne kwance cikin k'wayar idanunta k'arara fuskarta ta bayyanar da damuwa, zuciyarta ta tsinke jikinta duk ya mutu cikin yanayin damuwa tace"Fauzeeya muna cikin tsaka mai wuya ya zamuyi!? ".

Fauzeeya ta zumb'ura baki cikin matuk'ar tsoro da matsananciyar damuwa kallo d'aya zakayi mata ka gane tana cikin firgici! Sashen jikinta duk yayi lak'was cikin sanyin jiki tace"bansan yadda zamuyi ba Iya amma maganar gaskiya bazan iya rayuwa idan babu Yaseer ba saboda soyayyarsa ta riga tayimin illa azuciya, tabbas cutar so batada magani har sai zuciya ta mallaki abunda take so taya kike tunanin zan iya fitar da sonsa azuciyata?".

Iya Kulu ta harareta da wasa tace"dallah ni kin dameni da surutun banza ni ina nasan ma'anar kalaman da kike magana, yanzu dai kina nufin duk abinda zasuyi mana bazaki tab'a iya rabuwa da Yaseer? ".

Fauzeeya ta gyara zamanta tace"gaskiya bazan iya rabuwa da yah Yaseer ba! ".

Iya Kulu ta rik'e bakinta tace"ohhhh ni Kuluwa tabbas zamani ya chanza ke yanzu Fauzeeya ki kalli tsabar idanuna kicemin bazaki iya rayuwa saida Yaseer ba, to idan suka dawo mi kikeson ince musu ko kuwa so kike hajiya ta sanya akashemu!? ".

"ki daina damuwa da maganarta Iya babu abinda zasu iya yi mana sai abinda ubangiji ya k'addaro".

"ke yarinya ce Fauzeeya bakisan abinda nake hangowa ba".

Fauzeeya ta matso kusa ga Iya Kulu ta sanya hannunta cikin tafin hannun Iya cikin so da k'aunar kakarta tace"Iya ki kwantar da hankalinki kisa azuciyarki dukkan abinda ya samu bawa muk'addari ne daga Allah, sannan duk abinda ubangiji ya rubuta cikin kundin k'addarar mutum to sai ya sameshi saboda haka nina mik'awa Allah lamarina ".

Iya Kulu ta girgiza kanta alamar gamsuwa da kalamanta tace"kin koyi abinda ya dace saboda kin dogara ga ubangijin talikkai saboda haka nima na share da zancenta".

"yauwa Iyata yanzu naji maganar gaskiya shiyasa nake masifar sonki".

"Nima ina sonki Fauzeeya".

____________________

Agidan iyayen Fauzeeya Inna Munari ce takeyin surfen hatsi domin ta samu na dama kunu tab'arya ce ahannunta tana dakawa cikin turmi ji kakeyi dim dim dim yana tashi, d'aurin k'irji ne ajikinta babu ko riga tana dakan ne baba Labaran ya shigo tsakiyar filin gidan da sallama, Inna Munari ta aje tab'aryar saman k'aramar kujera sannan ta kwashe hatsin cikin kwano.

Bayan ta gama kwashewa hatsin ta isa wurin da baba Labaran ya shimfid'a tabarma ta zauna gab dashi tace"Labaran har ka dawo?".
Baba Labaran yace"eh Munari wallahi na gaji sosai yanayin sai ahankali".
Inna Munari tayi masa wani irin kallo tace"ka jika da wata magana kaida kakeda aure ina kai ina cewa ka gaji to ai banga abinda ka fara siya mata ba na aure".

"kee karki matsamin duk abinda nake dashi shi zan kai mata gidan matsiyacin mijinta da bayada kud'i!".
Inna Munari ta fashe da dariya tace"lallai Labaran da shegen kwad'ayi da buri kake dama so kayi ace diyarka ta samu mai kud'i ko? To Fauzeeya batada kashin arzik'i saina tsiya tun tana k'aramarta ba wani farin jini ne da ita saboda haka ka rungumi k'addara 'yarka babu mijin daya dace da ita sai talaka! ".

Hak'ik'a kalamanta sun matuk'ar sosa masa rai da sanya k'una azuciyarsa amma dayake Inna Munari tafi k'arfinsa saboda masifaffiyar gaske ce yace mata"nagodewa ubangiji daya bani d'iya ko batada farin jini ba wani abu bane wani yana nan yana neman haihuwar ido rufe bai samu ba".
Arikice Inna Munari ta kallesa domin kuwa maganarsa ya soki k'ahon zuciyarta tareda sanya zafi da rad'ad'i azuciyarta cikin matuk'ar b'acin rai tace"Labaran ni kakeyiwa gorin haihuwa!? ".

"ba gori nayi miki ba magana ce Munari".

Cikin harzuk'a ta jijjiga kanta tace"ahaka ake magana ka kalli tsabar idanuna kayimin gorin haihuwa saboda ni ban tab'a haihuwa ba!? ".

"nace miki ba haka nake nufi ba! ".Inji baba Labaran.
Inna Munari taja numfashi mai tattare da bak'in ciki da zafin maganar da baba Labaran ya saka mata, sak'a da warwara ta dingayi azuciyarta saboda maganarsa ba k'aramin zafi yayi mata azuciya ba............


_Muje zuwa dai masoyana ku cigaba da bina sannu ahankali domin jin yadda zata kasance atsakaninsu._🥰🥰

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu.*

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 18*


Baba Labaran yana ganin Inna Munari ta hasala da maganarsa tsantsar takaici da k'unar zuciya ne kwance cikin k'wayar idanunta k'arara zuciyarta sai zogi takeyi mata, sufsufsuf ya sance jikinsa sannu ahankali ya fice daga cikin gidan Inna Munari bata lura

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login