Showing 36001 words to 39000 words out of 87802 words
zaune cikin d'akinta ita kad'ai tana waya dasu Baura tareda basu wani irin aiki wanda bata bari naji zancensu ba, ta jima tana waya dasu kafin daga k'arshe ta kashe wayarta tana sak'a da warwara azuciyarta, shiru tayi cikin matsananciyar damuwa adalilin za'ayiwa d'iyarta Nazifa kishiya can saiga Alhaji Mu'azu ya shigo tsakiyar room d'in hannunsa rik'e da briefcase wurinta ya isa ya zauna dak'yar ta bud'i bakinta tayi masa sannu da zuwa, ya amsa mata fuskarsa ayalwace cikin yanayin gajiya a office ya kalleta yace"hajiya lafiyarki k'alau kuwa naga duk jikinki yayi sanyi mike damunki?".
hajiya Ramlat ta d'ago idanunta ta kalli mijinta tace"haba Alhaji ya kakemin irin wannan tambayar bayan kasan da cewa Yaseer zaiyiwa yarinyata kishiya to akan mi bazan damu, kai ya kamata kaje ka yiwa mahaifinsa magana akan su jaye maganar auren Yaseer da Fauzeeya idan ba haka ba saidai ya rubutawa Nazifa takardar saki! ".
"ohhh yanzu na fahimci damuwarki Ramlat akan mijinki 'yarki zai k'ara aure shine kika d'auki damuwa da rashin kwanciyar hankali kika sanya azuciyarki, to bari kiji ni babu ruwana cikin wannan lamari idan zuwa zakiyi da kanki ki gayawa Yaseer wannan mugun batu to na baki izni kije".
"inje ina Alhaji kuma?".
"gidan Yaseer d'in nake nufin kije da kanki".
"gidan surukin nawa zakace inje salon in jawa d'iyata gori da walak'anci tun yanzu! ".
Alhaji Mu'azu ya gyad'a kansa yace"oh to nine kika mayar wawa amma ke gashi kince gidan surukinki ashe kinada kunya ban sani ba".
"inada kunya mana mi ka d'aukeni ne Alhaji?".
"masifaffiya na d'aukeki".
hajiya Ramlat taji matuk'ar haushin maganarsa cikin yanayin takaici tace"nagode daka d'aukeni mahaukaciya! ".
"ban ambaci hauka cikin wannan al'amarin ba saboda haka kada ki kuskura ki k'agamin sharri da k'azafi".
"k'aga k'azafi da sharri aikina ne".
"yiwa kanki fata na k'warai Ramlat".
____________________
Agidan baba Labaran ya shigo faram faram cikin tsakiyar filin gidan ya iske Inna Munari tanata balbalin masifa bisa kwakciyar masifa,tana ganinsa ta k'ara d'aga muryarta tana balbaleshi da masifa baba Labaran shiru yayi yana sauraronta har ta gaji tayi shiru can yace mata"Munari mi yake faruwa ne da kiketa fad'a tun d'azu keda waye?".
"nida bak'ak'en munafukan mak'wabtanmu ne da suke yimin arashi da habaice-habaice akan Fauzeeya zatayi aure wai tabarni cikin wahala da talauci! ".
Baba Labaran yayi murmushi yace"haba Munari ki dinga hak'uri da mutane kinsan rayuwar duniyar sai ahankali duka duka idan kikayi duba da lura duniyar gaba d'ayanta guda nawa take?".
"bazan iya hak'uri ba Labaran saboda sun sakamin maganganu masu zafi da k'una azuciya harda cemin sukayi wai Fauzeeya mai kud'i zata aura ba talaka ba".
"ki daina daukar jita jitar mutane da gulma Munari wallahi ina jiye miki ranar da zakiji kunya agaban jama'a ki natsu ki daina yin wasu abubuwa marasa k'yau ".
Inna Munari ta tashi tsaye tana kakkab'e zanenta da yayi k'ura tace"nifa ka dameni da surutun banza inada aikin da zanyi sai anjima ".Baba Labaran ya girgiza kansa cikin rashin dace da mace ta gari yace"ubangiji ya shiryeki Munari ".Inna Munari tana shirin shigewa d'akinta ta k'yaro masa magana cikin raini tace"aini ashirye nake Labaran saidai inyi maka fatar shiriya ".Tana kammala maganarta ta fad'a cikin room d'inta tareda rufe k'ofar da k'arfi kaji gwaffff zad k'ara da k'arfi.
Ganin ta shige cikin d'akinta yasa baba Labaran ya shuri takalminsa ya sanya a k'afafunsa ya nufi wurin majalisarsu ta dattijawan unguwar, yana isa ya iske sun taru mak'il sai firarsu sukeyi cikin natsuwa zaunawa yayi ya tsoma bakinsa aka cigaba dayin firar dashi.
Mai keke napep ne na gani ya tsaya abakin k'ofar gidan Iya Kulu mai tsamiya Adama ce ta fito daga cikin napep d'in bayan ta biyasa kud'insa ta fad'a cikin gidan da sallama abakinta, Fauzeeya tana jin muryarta ta iso da sauri suka rungume junansu cikin so da tsantsar shak'uwa suna manne da juna dak'yar suka rabu Fauzeeya taja hannunta sai cikin d'aki suka zazzauna saman gadon Iya Kulu na da.
Adama ta saukar da numfashi murmushi k'unshe afuskarta tace"amarya amarya kinyi wuyar gani fa".
"haka kikace Adama ina kika fito naga hannunki da k'aramar leda? ".Adama ta rausayar da kanta tace"kasuwa naje na biyo ta gidanmu na d'auko kayana kala biyu saboda mu fara shirye shiryen abubuwan da duk zamuyi ranar aurenki ".
"kin cika zumud'i Adama har yanzu fa akwai sauran kwana goma sha uku fa ".
"keee Fauzeeya baiyi wani sauri ba kinsan ance mai shirin shiga ruwa tun atudu yake shiryawa ".Fauzeeya ta saki dariya tace"lamarinki da ban dariya kinsan wai Nazifa tazo har cikin gidan nan sunyi mana rashin mutunci itada k'awarta Safiya ".Adama ta karkace baki tace"kee Fauzeeya sunzo fa?".............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 22*
Fauzeeya ta juya idanunta cikin iyayi tace"kina mamaki ne akan maganata to ki daina mamaki saboda duk inda kike zato da tsammani Nazifa ta wuce nan!"."Amma matar nan batada hankali saikace gareta aka fara yin kishiya to da suka zo mi sukayi muku?".Cikin d'acin rai Fauzeeya ta chanza yanayin fuskarta tace"mugun kashi Safiya ta bani har na tashin hankali! ".
Adama ta rik'e bakinta cikin mamaki tace"Fauzeeya kina aikin mi ta jibgeki abanza da yofi? ".
"kedai bari ai bata jibgi banza saboda nayi matuk'ar alk'awarin bazan tab'a k'yaleta ba saina rama wata rana".
Adama ta gyad'a kanta tace"yanzu naji maganar k'warai ya kamata kam ki rama kada taci bulus taji dad'i".
"barni dasu har ita Nazifan saina koya musu hankali da sannu zasu fahimci cewa duniya makaranta ce mai jujjuyawa akowane lokaci".
Adama tace"gaskiya kam bani labarin yadda abin ya kasance atsakaninku?".
Fauzeeya ta musk'uta cikin yanayin d'acin rai ta kwashe labarin rikicin da sukayi ta gaya mata babu abinda ta b'oyewa Adama, saboda ta yarda da ita da bata amana domin shak'uwarsu da amintakarsu ta wuce zaton mai karatu .
Tana kammala gaya mata labarin rayuwar Adama ta b'aci idanunta suka chanza colour akan takaici dak'yar tace"kina cikin matuk'ar tashin hankali saifa kin tashi tsaye kin daina nuna musu tsoronsu akan fuskarki idan ba haka ba kashinki ya bushe, sannan ki kwantar da hankalinki saimun rama abinda sukayi miki zasu gane cewa d'an hakin daka raina wata rana shike tsole maka idanu".
"ai bazan tab'a k'yaleta ba Adama saina gurji bakin shegiyar matar nan data tashi ciremin boob's in mutu ko in nakkasa ".
Adama ta k'yalk'yale da dariyar mugunta harda rik'e ciki akan dariya 😄tace"aranar kinga mutuwa kusa gareki afilin wuri ubangiji ne ya ceceki daga kaidinta".
"hmmmm aranar naga mutuwa tsirara Adama wasu matan basuda imani da tsoron Allah arayuwarsu! ".
"kinada babban aiki agabanki saifa kin nuna mata kin fita iya fitsara da rashin kunya sannan zamanku zai daidaita ku zauna lafiya, saboda mata da kike gani wasunmu bamuda hankali da imani ai yanzu an daina yayin *KISHIN JAHILCI* da bak'in kishi domin yanzu kai ya waye".
Fauzeeya ta musk'uta tace"Adama ki aje wannan maganar gefe har yanzu mafi akasarin mata suna yin wannan bak'in kishi da nuna tsagwaron jahilci".
"haka ne gaskiyar zance amma har gobe ana samun matan kirki masu zuciyar alkhairi".
"Adama kin fad'i gaskiya ubangiji ya bamu kishiyoyi nagari".
"amin amin Fauzeeya k'awata ta kaina".
"nice babbar Aminiya ta hannun dama".
Fauzeeya tayi dariya yayinda Iya Kulu da taje gidan baba Labaran ta dawo cikin b'acin rai da zafin zuciya, kallo d'aya zakayi mata ka gane rayuwarta k'unshe take da bak'in ciki ganinta yasa Adama ta russuna ta gaidata dak'yar Iya ta amsa mata cikin k'unar zuciya.
Su Nazifa suka fito adayan d'aki suka koma na kusa gareshi domin kada su takurawa Iya Kulu, da wayo Fauzeeya ta sance jikinta ta dawo wurin kakarta domin taji abinda ya b'ata mata rai, tana shiga ta iske Iya Kulu zaune saman tabarma tayi tagumi cikin matsananciyar damuwa da takaici Fauzeeya ta isa kusa gareta tasa hannunta ta jaye mata hannu tace"Iya mi yake damunki da naga kin shigo rai ab'ace?".
Iya Kulu ta juyo ta dubeta da k'wayar idanunta da suka chanza colour akan takaici dak'yar ta bud'i bakinta tace"kedai bari Munari bazata tab'a gamawa da duniya lafiya ba saboda naje gidan wurin d'ana Labaran akan maganarki aurenki, bayan na shiga da sallama abakina ko amsawa batayi ba ina kallonta tana kallona babu gaisuwar arziki! Daurewa nayi na tambayeta ina Labaran yake ai in gaya miki matar nan yadda kikasan gunki haka ta zama saboda raini da walak'anci, dana sake tambayarta tsoki taja min tareda juyar kanta wani b'angare daban kinga kenan ko kallona bata sonyi, haka nayi ta tsayuwa da k'afafuna ko wurin zama bata bani ba saboda batada albarka".
Fauzeeya ta marairaice fuskarta cikin tsananin tausayi da jimamin abinda Inna Munari tayiwa kakarta wadda batada wanda ya fita a fad'in duniyar nan, cikin mutuwar jiki da tattausan lafazi mai kwantar da zuciyar mai sauraro tace"ki k'yaleta Iya kiyi hak'uri duk abinda mutum yakeyi aduniya wata rana dole ya daina, sannan duk abinda kayi sai anyi maka indai duniya ce ta ishi kowa wando da riga".
Iya Kulu tayi huci mai tattare da d'acin rai da zafin zuciya tace"ai nasan duk abinda Munari ta shuka saita girbi abinta indai duniya ce zata gani da idanunta budurwar wawa ce!".
Fauzeeya ta rausayar da kanta tana murmushi tace"tabbas gaskiya ne Iya".
" yi tafiyarki zuwa wurin Adama kada taga kin dad'e sosai".
"to Iya".Tana kammala maganarta ta mik'e tsaye ta fice daga cikin d'akin Iya Kulu ta koma wurin babbar aminiyarta Adama suka cigaba dayin firarsu cikin fara'a da kwanciyar hankali.
*********************
Nazifa da Safiya suna zaune suna firarsu tareda cin arish da k'wai yayinda mijin Safiya Haidar ya fito cikin shirin fita zuwa kasuwa, yana isowa gab dasu yayiwa Safiya murmushin k'auna yace mata"dear zanje kasuwa".
Zumbur Safiya ta tashi tsaye da sauri cikin yanga da yauk'i tace"ok farin cikina bari inyi maka rakiya to".
Ta juya ta kalli fuskar Nazifa tace"minti biyu Nazifa ina zuwa".
Nazifa zaune tayi cikin tsananin mamaki da al'ajabin yadda jikin Safiya ke rawa da kad'uwa adalilin taga mijinta, sannan kuma taga harda kallon soyayya Haidar ke jifarta dashi yayinda itama tana mayar masa da martanin kallonsa.
Har parking lot Safiya tayi masa rakiya tareda bud'e masa mota cikin matuk'ar ladabi da girmamawa, Haidar ya shiga cikin motar ya zauna da murmushi k'unshe afuskarsa cikin tsagwaron soyayyar matarsa yace"dear nizan tafi mi kike buk'ata inzo miki dashi idan na dawo? ".
Safiya ta shagwab'e fuskarta cikin sagarci tace"duk abinda ka siyomin zanyi farin ciki mijina amma dan Allah karka dad'e waje sosai, wlh idan ka fita waje hankalina baya kwanci har sai naga ka dawo cikin gida".
"saboda kishi ko my dear?".
Murmushi ta sakar masa tace"eh mana ai kishi gaskiya ne ko nayishi farin cikina".
"OK insha Allahu zan dawo da wuri kinji matata".
"shikenan ubangiji ya kaika lafiya ya dawomin dakai cikin k'oshin lafiya".
"Amin ya rabbi my Sofeeya".Yana k'arasa maganarsa ya rufe murfin motarsa ya tadda motar maigadi ya wangale masa get ya fice daga cikin gidan da gudun tsiya.
Safiya ta juya ta koma cikin tsakiyar parlourn wurin Nazifa da tayi jugum tana mamakin yadda taga Safiya tana tarairayar mijinta tareda bashi tsantsar kulawa na musamman, zaunawa Safiya tayi kusa gareta da murmushi kwance cikin fuskarta tace"lafiyarki k'alau kikayi shiru Nazifa?".
Nazifa taja gwauron numfashi cikeda damuwa da mamaki tace"kedai wani abu ne ya bani mamaki tareda d'aure tunanina da rikita k'wak'walwata".
Safiya taja numfashi tareda yi mata wani irin kallo wanda ita kad'ai tasan ma'anarsa sannan tace"ke kuwa mi nene ya d'aure miki tunani da rikita k'wak'walwarki?".
Nazifa tace"yanzu naga kina tarairayar mijinki da bashi tsantsar kulawa bayan kinsha gayamin cewar bak'ya bashi kulawa da basa hak'k'insa dake rataye awuyarki adalilin kada kiyita haihuwa kiyi saurin tsufa, yanzu kuma sai naga zancenki ya bambanta da abinda idanuna sukayi tozali dashi yanzu! ".
Safiya ta karkace baki cikin sanyin murya tace"Nazifa kenan ai saboda ganin idanun mutane ne yasa nake nuna masa kulawa da tsantsar soyayyar gaskiya, domin mutane da kike gani idan baka iya tako da tafiyar da rayuwarka cikin tsari da dabara ba zasu iya kaika su baro abanza!".
Nazifa tayi shiru tana tunani da nazarin maganarta na tsawon mintuna can ta nisa tace"gaskiya kinyi tunanin daya kamata Safiya amma shine baki sanarmin abinda kikeyiwa mijinki ba nima in dingayin yadda kikeyi ".
"afuwan my k'awata ayi hak'uri na manta ne shiyasa ban gaya miki ba".
"ba komai ai Safiya tunda yanzu naga yadda kike tafiyar da rayuwar aurenki nima zan dinga kwatantawa agidan mijina da yardar Allah".
"hakan ya dace kiyi aminiyar k'warai".
"da yardar Allah zanyi iyakar bakin k'ok'arina wurin ganin al'amurran gidana sun daidaita".
"Allah yasa komai ya daidaita Nazifa".
"Amin ya rabbi k'awata nizan wuce zuwa gidan mijina idansu Khalifa suka dawo school ina gaidasu".Cewar Nazifa bayan ta mik'e tsaye.
"to zasuji ina gaida 'ya'yana su Sameer".
"zan mik'a sakon gaisuwarki zuwa garesu".
"OK ba damuwa".
Nazifa tana k'arasa maganarta taja k'afafunta ta fice daga cikin gidan Haidar ta shige cikin motarta ta nufi gidan iyayenta, batayi doguwar tafiya ba ta iso bakin get d'in gidansu danna horn tayi maigadi ya wangale mata get d'in ta kunna hancin motarta ciki tareda parker motar aparking lot .
Tana parker motar ta fito sannu ahankali rataye da handbag d'inta a kafad'arta cikin yanga da matsananciyar damuwa ta nufi cikin hanyar da zata sadata cikin katafaren parlournsu, tana isowa tsakiyar parlourn ta isko babu kowa sai k'arar TV aparlourn direct wucewa tayi ta nufi room d'in mahaifiyarta, bud'e k'ofar d'akin tayi ta afka cikin filin d'aki ta iske hajiya Ramlat zaune saman gado tana waya zaunawa Nazifa tayi tana kallon mahaifiyarta har ta k'arasa wayarta, sannan ta juyo ta dubi fuskar Nazifa cikin nazari tace"ya naga kin rame akwanakin nan baby Nazifa ko kuwa duk k'arin auren da Yaseer zaiyi ne ya sakaki cikin matuk'ar damuwa da tashin hankali? Ki kwantar da hankalinki zan san yadda zanyi in wargaza auren nasu muddin ina numfashi aduniya bazaki tab'a walak'anta ba saboda haka ki cire komai azuciyarki".
Nazifa ta langwab'e kanta cikin shagwab'a tace"Ummu abin ne da ciwo arayuwa ace kamar ni wai Yaseer zai yiwa kishiya aida kunya adinga nuna ni agari ana kiran inada kishiya! ".Hajiya Ramlat ta musk'uta cikin zafi da k'unar zuciya tace"ki kwantar da hankalinki nace miki kibarshi muga iya gudun ruwansa zan nuna masa shi k'aramin k'waro ne ita kuma zata gane batada wayo wallahi!".
"nifa so nake idan ta aureshi ta tozarta da walak'anta arayuwarta ta yadda zata tsani rayuwa akan mutuwa saboda so nake ta shiga cikin k'unci da matsananciyar rayuwa! ".Hajiya Ramlat ta fashe da dariyar k'eta can ta tsagaita tace"duk yadda kikeso haka zanyi babyna kinsan aduniya babu abinda nakeso sama dake domin ke kad'aice na haifa arayuwata adalilin haka bazan bari bak'in cikin d'a namiji ya halakaki ba ".Nazifa ta rungume mahaifiyarta cikin tsananin farin ciki da murna tace"kayyy Ummuna shiyasa nake k'ara fitinannen sonki saboda yadda kike k'aunata yafi gaban misali "............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 23*
Hajiya Ramlat ta saki murmushin jin dad'i tace"soyayyar da nake miki tsayawa iyakanceta ma b'arnar baki ne".Nazifa ta jaye jikinta ana mahaifiyarta tana wani langwab'ewa adole gata d'iyar masu kud'i tace"shiyasa nake alfahari dake akowane lokaci Ummu ina Abbu yaje ne naji banji motsinsa ba?".Hajiya Ramlat ta kalleta ta sakar mata murmushi tace"yana k'asar Dubai wurin kasuwancinsa".Yamutsa fuskarta tayi tace"shine baki gayamin ba sai yanzu to idan ya dawo ki gaya masa cewa ya k'ara min jari business d'ina ya k'ara habb'aka sannan ina buk'atar achanzamin kayan d'aki"."Ayyah kiyi hak'uri kwata kwata na manta ne shiyasa ban sanardake kuma zan isar da sak'onki zuwa garesa"."Yauwa hajiyata daban kike ko acikin iyaye sai an tona za'a iya samun irinki".
hajiya Ramlat tace"Nazifa akwaiki da dad'in baki wallahi"."Ba wani dad'in baki sai gaskiya Ummu"."To naji yanzu dai waye zai dinga yi miki ayyukan gida da share share idan Fauzeeya ta shigo? Saboda nasan baki iya yin aiki mai wahalarwa".Nazifa ta bintsire baki tace"har yanzu ban samu 'yar aiki ba Ummu ko zaki barmin Tasallah ne ta dawo gidana da aiki".Hajiya Ramlat ta harareta da wasa tace"hmmm sannu sarkin wayo idan na baki ita ina zan samu wata 'yar aiki mai kirki da tarbiya kamarta?".
Nazifa ta marairaice fuskarta cikin lallashi da dad'in baki tace"haba dai hajiyata ki barmin ita mana idan kikayiwa Inna Manga magana zata samo miki wata mai kirki".
"kidai bari insa asamo miki sabuwa mana".
Nazifa ta girgiza kanta alamar a'a sannan tace"banason sabuwa ni Tasallah nakeso".
"to naji nabar miki ita bari in kirata".
"yi zamanki Ummuna basai kin kirata ba da kaina zanje d'akinta in d'auketa mu wuce tare".
"ba matsala tunda kinyimin k'wacen 'yar aiki Nazifa ubangiji ya baku zaman lafiya".
"zaki samu wata Ummuna".
Firarsu suka cigaba dayi cikin natsuwa da soyayyar uwa da d'iya Nazifa ta jima sosai agidan tana d'ebewa hajiya Ramlat kewa,sannan daga baya ta mik'e tsaye ta shiga cikin room d'in dayake mallakin Tasallah ta bata umurnin ta kwaso kayanta su wuce, batare da gardama ba ta had'a kayayyakinta da duk wani abu da takeso ta saka cikin akwatin da Alhaji Mu'azu ya siyo mata, koshi da