Showing 45001 words to 48000 words out of 87802 words
mu hak'ura da juna, bayan kinsan na riga nayi matuk'ar nisa cikin tarkon k'auna da matsananciyar soyayyarki ke atunaninki za'a iya raba hanta da jini ne? To ki sani aure babu fashi sai an d'aurashi idan zugoki akeyi domin ki fasa aurena ki koma kice musu maganarki batayi tasiri azuciyata ba".
Fauzeeya ta fashe da rikitaccen kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro tana rusar kukan fargaba tace"ka fahimceni yayana ba nufina inki aurenka ba akwai abinda nake hangowa muddin muka auri juna babu mu babu kwanciyar hankali! ".
"mi nene kika hango wanda nina kasa hangowa?".Inji Yaseer cikin rashin fahimtar maganarta.
"ka bani dama mu tattauna mu fahimci junanmu yah Yaseer".
Yaseer yayi doguwar ajiyar zuciya cikin sanyin murya da lalama yace"ina jinki ki gayamin gaskiyar dalilin dayasa kikace mu hak'ura da junanmu?".
Hannunta ta sanya ta share hawayenta tsab sannan ta nisa tana kuka ta gaya masa abubuwan da suka faru da ita daga farko har k'arshe komai ta gaya masa, amma banda gaya masa ainahin su waye suka turosu ba saboda batason ta haddasa fitina da tashin hankali atsakaninsa da matarsa Nazifa tasan duk abinda yakeyi takeyi komai dad'ewa sai asirinta ya tonu.
Tana kai k'arshen labarinta hawaye suka cigaba da gangarowa kamar an bud'e famfo cikin sanyin jiki da tsantsar tausayinta yah Yaseer ya mik'a mata handkchief ta share hawayenta, sannan ya dubeta cikin tausayawa yace"kiyi hak'uri my Fauzee da farko ban fahimceki bane shiyasa na daka miki tsawa ashe kinada babban dalilinki da hujja mai k'arfi na cewa mu hak'ura da juna, ki daina kuka ki kwantar da hankalinki da yardar Allah babu abinda zai faru sai alkhairin Allah ".Fauzeeya ta goge fuskarta tace"dole hankalina ya tashi yaya fyad'e fa ya tashi yimin in halaka dan Allah ka nemo mana wata mafitar kafin su kasheni kowa ya huta! ".Hankalin Yaseer ya d'unguma zuciyarsa ta girgiza amma saiya daure yace mata "ki daina fad'in zasu kasheki mana hankalina k'ara tashi yakeyi zuciyata k'una takeyi da yardar Allah zan nemo mana wata fahimta kinji masoyiyata ".Fauzeeya ta gyad'a kanta alamar gamsuwa da maganarsa tace"ba komai saina ji wace irin shawarar ka yanke awaya ".Yaseer yace "OK zakiji ni zuwa gobe kinji nizan wuce zuwa gida ".Fauzeeya ta musk'uta tace"ba kace akwai maganar da kakeson yi da Adama ba "."Babu lokaci sai gobe zanyi maganar da ita ".Yana rufe bakinsa ya shige cikin motar suka tadda motar suka nufi hanyar zuwa gida yayinda Fauzeeya ta juya da gudu ta fad'a cikin gidan babanta saboda gudun kada masu bibiyarta su kamata su cika burinsu akanta..............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 27*
Su Yaseer suna barin bakin k'ofar gidansu Fauzeeya suka nufi hanyar zuwa gidan Abduljalal, tafiya sukeyi cikin natsuwa har suka iso bakin get gidansa Yaseer ya parker motarsa ya dubi fuskar Abduljalal yace"sai gobe zamu sake had'uwa friend".Abduljalal yayi saurin kallonsa yace"ina kuma zakaje bazaka bari har kaci abinci ba?"."Kaidai Jalal wata lalura ce ta kunno kai wadda nakeson inga naga k'arshenta kafin ta bayyana".Abduljalal ya firfito da idanunsa yace"kai kuwa wace irin lalura ce da zata sanya maka damuwa haka naga gwargwado kafi k'arfin komai arayuwarka?".Numfashi Yaseer ya sauke ya d'an murmusa domin ganin ya b'oye damuwarsa yace"yanzu ba lokacin surutu bane ka bari idan na dawo zan gaya maka gaskiyar abinda ake ciki".
"ba damuwa Yaseer saika dawo ubangiji yasa adace".Cewar Jalal cikin tausayi da k'aunar abokinsa.
"Amin Jalal".Jan k'ofar motarsa yayi ya kulle ya nufi hanyar zuwa gidan iyayensa yayinda Abduljalal ya girgiza kansa cikin yanayin gajiya ya juya ya shiga cikin gidansa, abakin k'ofar parlour ya had'u da matarsa Rufaila ya rungumeta suka ida k'arasawa atsakiyar parlourn.
*********************
Yaseer ya shigo cikin tsakiyar filin gidan ya parker motarsa fitowa yayi daga cikin motar ya sanya mata key ya kulle, da sauri ya isa tsakiyar parlourn da sallama d'auke abakinsa su hajiya Sadiya suna zaune itada mijinta suna firarsu cikin fara'a da kwanciyar hankali.
Alhaji Taheer ne ya amsa masa sallamar cikin k'auna da soyayya isowa wurinsu yayi ya gaishesu, suka amsa masa cikin yanayin k'auna sannan Yaseer ya zauna k'asan carpet tareda lank'washe k'afafunsa, kallonsa kawai sukeyi suna nazarinsa na wani lokaci can Alhaji Taheer yayi gyaran murya yace"Yaseer mike tafe da kai ko maganar aurenka ce ta kawoka?".
"ai shine na gani Alhaji ya shigo yayi shiru bai sanardamu komai ba".Inji hajiya Sadiya cikin taushin murya.
Yaseer ya sauke gwauron numfashi cikeda damuwa da rashin kwanciyar hankali ya duk'ar da kansa k'asa yace"Abi Ummi auren nan nawa nakeson idan dason samu ne ayishi da wuri".
Alhaji Taheer ya kalli fuskar hajiya Sadiya itama ta kallesa maganarsa ta basu matuk'ar mamaki, amma dayake sun hango yanada dalili mai k'arfi dayasa ya tunkaresu da wannan maganar, shiyasa Alhaji Taheer ya fara cewa"ban gane ayi aurenku da wuri ba duka duka ai saura sati biyu ad'aura maka aure Yaseer?".
Hajiya Sadiya ta musk'uta tace"kayi mana bayanin abinda kake nufi ta yadda zamu fahimta".
Yaseer yayi shiru na tsawon lokaci ya rasa yadda zasu d'auki maganar zasu amince ko basu amince ba, shine abinda yake tunani cikin ransa ganin tunani baya kawo k'arshen matsala dole ya furta"wato Ummi abinda baku sani ba shine kwata kwata bana samun kulawa da hak'k'ina dake rataye awuyan Nazifa, sannan gashi ana firgitamin Fauzeeya akan matuk'ar bata rabudani ba zasu iya kasheta jiya ma ubangiji ne ya tsareta da tuni sunyi raping d'inta..................." .Yaseer saida ya sanar musu duk abinda Fauzeeya ta gaya masa babu abinda ya b'oye musu, saboda shima atakure yake ya matsu yayi aure ya huta da yawan sha'awa da mafarke mafarke na banza da yofi.
Bayan ya gama sanar musu irin cin kashi da tozarcin da Nazifa takeyi masa tareda gaya musu rashin mutunci da d'ibar albarka, salati iyayensa suka saka kusan atare suna salallami sun jima suna mamaki da al'ajabin halayyar Nazifa mara k'yawo sannan Alhaji Taheer yayi ajiyar zuciya yace"kayyy amma Yaseer kanada zurfin ciki sosai miyasa tun farko baka sanarmin ba domin amagance matsalar da wuri?".
Hajiya Sadiya ta hararesa tace"ina ko zai gaya maka tunda son mace ya rufe masa idanu! Ashe so tayi ta kasheka kowa ya huta Yaseer gaskiya anan kam ka nuna wauta saboda miye baka k'ara aure ba tuntuni?".
"hajiya yarinyar nan batada tarbiya da tausayi ta yaya zata fifita business d'inta akan mijinta, wannan ai rashin nazari da tunani ne irin haka shi yake kawo rashin jituwa atsakanin miji da mata!".
Hajiya Sadiya ta bintsire baki tace"aishi mutunci gadonsa akeyi Alhaji to Nazifa bata biyo halin babanta ba wurin hajiya Ramlat ta d'auko,saboda itace ta sangartata tareda b'ata mata tarbiya ta yadda bata ganin daraja da kimar mutane".
Alhaji Taheer yace"haka ne gaskiyar zancenki to yanzu dai tunda an fara kawowa ita Fauzeeyar hare-hare bari insa amatso da auren kusa kada mak'iya su tarwatsa auren Yaseer! ".
"haba Alhaji idan aka matso da auren duk shirin da nayi da abinda nake shiryawa bazai yiyu ba kawai dai abarsa yadda yake ".
"hajiya kenan akwai abinda na hango wanda kika kasa hangowa yanzu dai bari inyi magana da Alhaji Mu'azu".
"miye ka hango Alhaji?".
"zaki fahimta nan gaba kad'an Sadiya kinsan komai sannu ahankali ake binsa".
"naji ba matsala duk abinda yafi zama alkhairi ubangiji ya tabbatar".
"Amin amin haka ya kamata ki fad'a".Yana kammala maganarsa ya zaro phone d'insa a aljihunsa tareda dialling nombar Alhaji Mu'azu kiran na shiga Alhaji Mu'azu ya d'auka suka gaisa, bayan sun gaisa ne yake sanar masa akan su had'u ahanya daidai roundabout way.
Alhaji Mu'azu ya nuna masa ba damuwa su had'u d'in suna gama maganarsu Alhaji Taheer ya katse wayar ya kallesu yace"Yaseer ka shirya duk abinda ake ciki zan kiraka awaya karka manta ka kashe wayarka ".
"to Abi bazan manta insha Allahu".Inji Yaseer cikin ladabi da biyayya.
Alhaji Taheer ya fice daga cikin gidan da sauri ya nufi parking lot tadda motarsa yayi ya danna horn maigadi ya wangale masa get da sauri ya fice daga cikin gidan, yayinda Yaseer ya tashi tsaye ya zauna wurin mahaifiyarsa alokacin ne hajiya Sadiya tace"Yaseer miyasa koni da nake mahaifiyarka baka tab'a fad'amin irin abubuwan da Nazifa keyi maka ba?".
Yaseer ya rausayar da kansa yace "kiyi hak'uri Ummi da farko na zata zata chanza halayyarta ne shiyasa nayi shiru ban gaya miki ba".
"na fahimceka son amma dan Allah karka k'ara boyemin irin matsalolin da kake fuskanta a gidanka saboda idan kana sanarmin zansan yadda zan b'ullowa al'amarin kaji ko?".
"afuwan Ummina bazan sake b'oye miki komai duk abinda ake ciki zan dinga sanar miki".
"ba komai ubangiji yayi maka albarka".
"Amin Ummi".
___________________
Su Alhaji Mu'azu suka had'u bakin roundabout way suka shige cikin mota guda tareda parker dayar motar agefen titi, sannan suka rankaya suka nufi hanyar unguwarsu Fauzeeya tafiya sukeyi ahankali har suka iso daidai bakin k'ofar gidan Iya Kulu mai tsamiya, tambayar mutane sukayi ina Iya Kulu taje dayake sun aika yaro cikin gidanta yace musu batanan, wani saurayi ne yayi musu jagora har bakin k'ofar gidan baba Labaran yace musu bari ya shiga cikin gidan da sallama da k'arfi, Iya Kulu ta amsa masa tace"wa kake nema Isuhu?".
Isuhu yace mata"sallama akeyi dake Iya Kulu".
"bak'i nayi kenan kace musu su shigo ciki gida Isuhu ".Tace tareda fitowa da tabarma daga cikin d'akinta ta shimfid'a a k'asa tayi zaune Isuhu ya juya ya fice daga cikin gidan.
Isuhu ya isa wurinsu Alhaji Mu'azu yace "ance ku shiga ciki Alhaji"."To mungode sosai d'an samari ".Cewar Alhaji Taheer tareda ciro kud'i daga cikin aljihunsa yaba Isuhu kud'in ya amsa yayi godiya yayi tafiyarsa inda zaije .
Su Alhaji Mu'azu suka kunna kansu tsakiyar filin gidan suka iso wurin Iya Kulu dake zaune saman tabarma itada baba Labaran, gaishe -gaishe sukayi atsakaninsu sannan Alhaji Mu'azu ya koro mata bayanin abinda suke buk'ata akan ta bari gobe ad'aura auren Yaseer da Fauzeeya, baba Labaran ya kalli fuskar Iya Kulu itama ta dubeshi can suka daina kallon juna sukayi shiru na mintuna kad'an babu motsin da kakeji saina kaji.
Ganin shirun zaiyi yawa yasa Alhaji Mu'azu ya sake cewa"ya kamata kuyi tunanin wannan maganar idan ba'a yi auren nan da wuri ba rayuwar yaranmu zata iya shiga cikin matsanancin hali da had'ari! Amma nasan muddin aka d'aura auren shikenan k'aryar munafurci da ture ture ta k'are ".Alhaji Taheer ya gyad'a kansa yace"maganarka hak'k'un ce Mu'azu saboda haka ku bamu had'in kai mu aiwatar da wannan auren inasa ran akwai alkhairi acikinsa ".
Iya Kulu ta sassauta murya cikin natsuwa da kamala tace"nidai na gamsu da maganarku kuma na amince gobe ad'aura auren ubangiji ya sanya alkhairi ya kuma kauda duk wata fitina atsakaninsu".
Sukace"amin ya rabbi".
Juyawa sukayi suna kallon fuskar baba Labaran domin suji ta bakinsa, ganin sun mayarda kallonsu gareshi yasa baba Labaran yayi murmushi k'unshe afuskarsa yace"tabbas kunyi tunani mai k'yau tareda hangen nesa babu matsala ta wajena nima na amince da yarda gobe ad'aura auren Yaseer da Fauzeeya, ubangiji Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba ".
Su Alhaji Mu'azu suka washe baki tamkar gonar auduga tsantsar farin ciki da murna ne kwance cikin k'wayar idanunsu, kallo d'aya zakayi musu ka gane sunji dad'in yadda su Iya Kulu suka amince da maganarsu hannu bibbiyu cikin girmamawa da karamci.
Mik'ewa tsaye sukayi sukace zasu tafi baba Labaran ya tashi tsaye yabi bayansu har bakin k'ofar gida inda suka parker motar, suna isa Alhaji Taheer ya bud'e murfin motar shi kuma Alhaji Mu'azu ya zaro kud'i ya sanya cikin tafin hannun baba Labaran yace"gashi ka k'ara cikin hidimar aure gobe ".Baba Labaran ya amshe kud'in yana kwararo musu godiya da addu'ar gamawa lafiya da duniya Alhaji Mu'azu ya dubesa cikin tausayawa yace"ka daina yi mana godiya nayi maka ne domin Allah".Yana rufe bakinsa ya shige cikin motar Alhaji Taheer ya tadda motarsa suka nufi hanyar zuwa gida yayinda baba Labaran ya juya ya koma ciki..............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 28*
Baba Labaran yana shiga cikin gidan ya fad'a d'akin da Iya Kulu ke zama ciki saboda bayason Inna Munari taga ya samu kud'i, domin duk yadda zatayi ta lura da inda ya aje kud'in ta zara ta sani tayi ilmi wurin fagen sata da dad'in baki matuk'ar taga mutum da kud'i, shiyasa akowane lokaci idan ya d'an samu kud'i yake b'oyewa tareda kaffa kaffa da abinsa saboda yana tareda b'arauniya.
Zaune saman sallaya ya isko Iya Kulu tana jan casbaha samun wuri yayi zauna kusa gareta harta kammala abinda takeyi,tana k'arasa abinda takeyi ta juyo ta dubesa tace"Labaran ya akayi ne?".
Baba Labaran ya duk'ar da kansa cikin ladabi da biyayya yace mata"dama bak'in da mukayi ne suka bani kud'i shine nace bari in kawo miki ki ajiye idan buk'atarsu ta taso sai kuyi amfani dasu".Ya zaro kud'in daga cikin aljihunsa yaba Iya Kulu ta amsa tana juya kud'in murmushi k'unshe afuskarta cikin sanyin murya tace"babu damuwa Labaran ubangiji yasa ka gama da duniya lafiya".
"amin Iya sannan dan girman Allah ina rok'onku duk abinda nayi miki abaya kiyafemin wallahi ayanzu na gane kuskure na fahimci cewa uwa uwa ce ba kowa ke amsa sunan ba, sannan duk Munari ce ke k'ulla makirci da zugani inayi muku wasu abubuwan marasa dad'i".
Iya Kulu ta rausayar da kanta cikin farin ciki da murnar shiriyar d'anta kallo d'aya zakayi mata ka gane tayi matuk'ar farin ciki hak'oranta abayyane tace"na yafe maka Labaran ubangiji ya yafe mana baki d'aya amma inason ka sani ita mace da kake gani tafi shaid'an lahani da fitina arayuwa, domin tasan duk yadda zatayi ta rabaka da 'yan uwanka da mahaifiyarka ta sani ni abin har mamaki yake bani saboda wasu matan basuda tunani da nazarin rayuwa, saboda idan mace tanada nazari da tunani baza tayi k'ok'arin ta raba mijinta da mahaifiyarsa da 'yan uwansa saboda hakan zai iya jefa rayuwar mijinki cikin halaka tareda nuna masa hanyar shiga wutar jahannama".
Baba Labaran ya natsu yana sauraren kalamanta cikin matuk'ar sanyi jiki da nadamar abubuwan daya aikata abaya, kwallar zallar takaici ne suka taru cikin k'wayar idanunsa wani irin abu ke yawo cikin jini da gangar jikinsa, dakyar ya bud'i baki yace"amin Iya insha Allahu zan dinga kiyayewa abinda ya faru bazai sake faruwa ba".
Iya Kulu tace"Allah yasa d'in Labaran".
"amin Iya".Firarsu sukeyi na tsakanin uwa da d'a saiga Inna Munari ta shigo buzut babu ko sallama abakinta, tana isowa wurinsu tayi musu walak'antaccen kallo mai tattare da raini da iko tace"Labaran kaifa nake jira tun d'azu kazo inason magana dakai".
"yana wurin koyon sallama Munari".Inji baba Labaran cikeda jin haushinta da tsanar halayyarta.
Tsaye tayi saman kansu cikin rashin mutunci tace"ban gane kana wurin koyon sallama mi kake nufi!? ".
"ban sani ba Munari ki fice daga cikin d'akin nan ki bamu wuri ina tattaunawa ne da mahaifiyata! ".
Alokacin ne Iya Kulu tace cikin matuk'ar lallashinta da lalama tace"kiyi hak'uri ki bamu minti goma mu k'arasa maganarmu kinji Munari".
Inna Munari ta hasala da suk'uwa tace"dallah yimin shiru ko yanzu jikinki yayi tsami bak'ar munafukar tsohuwa ai duk abinda yakeyimin kece kika d'aure masa gindi da zugashi".
Baba Labaran ya mik'e zumbur cikin matuk'ar b'acin rai idanunsa suka chanza colour sukayi jajir adalilin zagin data yiwa mahaifiyarsa wadda ita kad'ai ce ta rage masa aduniya, cikin azama da zafin rai ya kwasheta da maruka har kusan hud'u kaji kauuu kauuu kauuu kauuu jere ga juna! Asanadiyyar haka Inna Munari ta saki razananniyar kuwwa da kururuwa ta zura da gudu zanenta ya fad'i k'asa daga ita sai under sicket, saboda duk ta rikice da d'imaucewa akan zafi da rad'ad'in marin da baba Labaran yayi mata d'an kwalin dake saman kanta ya cire batare data ankara ba 😆😆.
Da gudu ta fad'a cikin d'akinta ta sanya sakata saboda ta rikice da ficewa daga cikin hayyacinta, shatin yatsun hannun baba Labaran ya bayyana b'aro b'aro afuskarta wani irin d'aci da zogi zuciyarta keyi gabanta sai fad'uwa yakeyi fat fat fat!.
Ganin ta fice da gudu yasa Iya Kulu ta b'ata fuska cikin damuwa tace"Labaran kanason mu shirya da k'yau?".
"eh mana Iya babu wanda bayason ya shirya da mahaifiyarsa matuk'ar ya kasance d'a nagari".
"to idan har kanason mu shirya kada ajimu kada ka kuskura ka k'ara marin Munari haba ya kakeson mayarda matarka kamar jaka! ".
Baba Labaran ya sassauta murya cikin tattausan lafazi mai dad'i domin aduniya babu ya tsana yanzu fiyeda b'acin ran Iyarsa, numfashi ya sauke yace"kiyi hak'uri Iya bazan k'ara ba amma naga fa zaginki tayi shiyasa nayi mata hukunci".
"kai ta zaga ne Labaran!? ".
"a'a ke ta zaga Iya bani ba".Ya fad'a cikin mutuwar jiki.
"to tunda ni take zagi karka kuskura ka k'ara d'aga hannunka da sunan marinta kaji na gaya maka".
"bazan sake ba nayi matuk'ar kuskure".
"yauwa yaron albarka komai ya wuce".
*********************
Aranar ne duka b'angarori biyu sukayi shirye shiryen aurensu Yaseer zama guda tareda sanarwa 'yan uwa da abokan arziki, amma ba kowa suka sanarwa ba saboda basason azo atayarwa ango da amarya hankali, anyi oder d'in abinci daga restaurant daban