Showing 84001 words to 87000 words out of 87802 words
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 49*
Alhaji Taheer ya sake cewa"zaku iya tafiya gidanku saina nemeku".Su Yaseer suka mimmik'e tsaye sukace"mun barku lafiya Abi"."OK ubangiji ya kaiku gida lafiya".Inji Alhaji Taheer, Yaseer ya bud'i baki yace"amin ya rabbi".K'arasa maganarsa keda wuya suka fice daga cikin parlourn direct parking lot suka nufa suka shige cikin mota .
Ganin sun wuce yasa hajiya Sadiya ta dubi fuskar Alhaji Taheer tace"Alhaji miyasa ka bashi umurnin bayan bai maida matarsa ba?".
"akwai abinda nake hangowa Sadiya kibi komai sannu ahankali"."shikenan Alhaji duk abinda kace haka za'ayi".
*********************
*BAYAN KWANA BIYU*
Fauzeeya ce zaune saman kujera tayi jugum sai tunanin rayuwa takeyi sakin da Yaseer yayiwa Nazifa yayi matuk'ar yi mata zafi da ciwo azuciya, saboda batason ace sanadinta ne aka saki Nazifa sallamar Yaseer ne ya katse mata tunani ya iso wurinta tareda jingina jikinsa anata yace"my Fauzee lafiya mi yake damunki?".Fauzeeya tayi rau rau da idanunta cikin zullumi tace"please yaya dan Allah idan akaina ne ka maida uwar 'ya'yanka banason su Sameer su taso ace nice nayi silar fitar mahaifiyarsu daga cikin gidan ubansu".
Yaseer ya numfasa cikin so da tsantsar k'aunarta yace"shine abinda yasa kika shiga cikin damuwa my Fauzee kenan?".
Fauzeeya ta d'ago idanunta ta kallesa tace"shi kad'ai ne yake damuna mijina wallahi hankalina bazai tab'a kwanciya ba har sai ka maida ita d'akinta".Yaseer ya dafa kafad'arta cikin tattalin so yace"ki kwantar da hankalinki babyna nayi miki alk'awarin zan maida Nazifa so nake kawai ta gane kuskurenta".Fauzeeya tayi murmushin dake k'ayatar da fuskarta tace"har kasa naji sanyi azuciyata mijina".
Yaseer yaja hannunta sukayi masauki saman gadonta ya kwanta saman k'afafunta suna jin numfashin juna, wani irin sinadarin so da tarairaya junansu sukeyi Yaseer ya shafi cikinta daya fara fitowa yace"banason kina saka damuwa cikin zuciyarki saboda banason abinda yake cikin cikinki ya samu matsala domin aduniya zan iyayi miki komai saboda ki kasance cikin matuk'ar farin ciki da annashuwa".
Fauzeeya tayi murmushin daya bayyana fararen hak'oranta tace"ina alfahari dakai mijina domin ka zamo hasken idaniyata annurin zuciyata har abada kaine sirrin ruhina".
Yaseer yace"gaskiya nayi matuk'ar dace da samun matar kirki abar ado ga kowane d'a namiji da soyayyarki nake rayuwa dashi nake mutuwa".
Agidan hajiya Hamamatu ce zaune itadasu hajiya Ramlat da d'iyarta Nazifa suna zantawa akan yadda zasu b'ullowa al'amarin komawa gidajen mazajensu, hajiya Hamamatu ya nisa tace"yanzu abinda zakiyi ki kira Alhaji Taheer aminin Mu'azu yayi masa magana ko za'a samu ya maidake d'akinki".
hajiya Ramlat taja numfashi mai tattare da bak'in ciki da tsantsar damuwa ta rausayar da kanta tace"wallahi abin yana damuna Aunty na rasa yadda zanyi in koma gidan mijina".
hajiya Hamamatu ta dubi gefen da Nazifa take zaune cikin damuwa da tsantsar tashin hankali tace"tun farko duk abinda ya sameku laifinki ne Ramlat ta yaya zaki dinga d'aurewa yarinya gindi tana aikata abinda ta gadama tareda walak'anta rayuwar mijinta, wannan abin da kike gani bai dace ba 'yarki ce tayi *SAKACI* tun farkon zamanta da mijinta bata nuna masa k'auna da tsantsar soyayyar gaskiya bata jashi ajikinta ba kinga kuwa dole Fauzeeya taga k'ofar da zata shiga cikin zuciyar Yaseer tayi kane kane, to nidai shawarar dazan baki Ramlat ki sanarwa aminin mijinki duk abinda ake ciki wata k'ila yayi masa magana ya mayardake kina komawa nasan dole asa Yaseer ya maida Nazifa d'akinta ko domin saboda 'ya'yan dake tsakaninsu".
"da yardar Allah Aunty zanje har gidansa gobe in basu hak'uri sannan inyi masa maganar".
"hakan ya dace kiyi Ramlat kuma dan girman Allah idan kika koma gidan mijinki ki rok'esa gafara sannan ki gyara halayyarki kinji".
"zan gyara Aunty".
hajiya Hamamatu ta maida kallonta wurin Nazifa tace"ke kuma idan kika koma gidan mijinki kiyi masa biyayya ki zauna lafiya da k'awayenki banda biyewa zugin k'awayen banza, muddin kika kuskura na sakejin wani abu ya biyo baya da kaina zan iskoki inci mutuncinki! ".
Hawaye masu zafi sai shatata sukeyi afuskarta cikin nadama da biyewa son zuciya tace"bazaki sake jin komai ya fito daga gareni ba mommy".
"yauwa d'iyar albarka komai da kike gani arayuwar duniya sai kayi hak'uri kakecin riba bale mijinki yana sonki babu abinda ya rageki dashi mi zaisa ki dinga musgunawa rayuwarsa tareda shuka masa rashin mutunci, ki daina ba k'yau ko a addinin musulunci".
**********************
Washe gari da safe misalin k'arfe takwas da rabi Nazifa ta tashi daga barci bayan tayi wanka taci breakfast, ta fad'a cikin bathroom tayo wanka tareda suturarta mai k'yawo tufafin sunyi mata k'yau duk dayake ta soma ramewa saboda tana cikin matsanancin hali da tsantsar damuwa batada sukuni da walwala arayuwarta ta rasa abinda yakeyi mata dad'i aduniya, tana gama shiryawa ta zura hijabinta kalar tufafinta ta rataya handbag ta fito daga cikin room d'in ta nufi wanda mahaifiyarta take zaune ciki.
Tana iza k'ofar d'akin ta tsaya abakin k'ofar ta hango hajiya Ramlat zaune saman sallaya tayi tagumi kallon mahaifiyarta tayi cikin tausayawa tace"Ummuna".
"please ki rage yawan damuwa".
hajiya Ramlat ta jaye hannunta cikin sanyin jiki tace"zan rage baby ina zakije ne naga kinyi shirin fita?".
Murmushin da baikai zuci ba tayi tace"zanje gidan k'awata Safiya ne kwana biyu ta daina ganinta".
"hakan yanada k'yawo sai kin dawo to".
"OK Ummuna".Jan k'afafunta tayi ta nufi parking lot ta shiga cikin motarta ta zauna tareda ficewa daga cikin gidan da sauri.
____________________
Nazifa ta isa bakin get gidan Safiya ta parker motarta awaje tareda fitowa ta shiga cikin gidan maigadi ya gaidata, ta amsa masa cikin sakin fuska tareda yi masa k'yautar naira dubu biyu domin duniya ta fara yi mata karatun ta natsu godiya yayi mata ya dingayi mata addu'ar gamawa lafiya, tabbas taji dad'in addu'arsa sosai har cikin zuciyarta wucewa tayi ta isa bakin parlourn zata tura kenan taji k'ofa akulle knocking d'in k'ofar tayi, Safiya dake kwance shame shame ajikin mijinta tace"yes come in k'ofar abud'e take".
Nazifa ta tura k'ofar ga mamakinta taga ta bud'e ta kunno kai tsakiyar parlourn idanunta sukayi tozali da Safiya manne ajikin mijinta gabanta ya fad'i rasssss kanta ya k'ulle tunaninta ya rikice! Cikin mutuwar jiki ta k'araso wurinsu ta gaida Haidar ya amsa mata fuskarsa asake jaye jikinta tayi anashi sannan Haidar ya mik'e sannu ahankali ya fice daga cikin parlourn, alokacin ne Safiya tayiwa Nazifa kallon raini tace"k'awata kinyi wuyar gani ashe ana ganinki kwana biyu kin b'oye".
Nazifa ta zauna saman cushion cikin matuk'ar damuwa tace"kedai dole ki jini shiru Safiya wata matsala ce ta kunno kai arayuwata".
Safiya ta mayarda hankalinta kacokam wurin Nazifa cikin jimami tace"to Allah yasa dai ba wata babbar matsala bace mi yake faruwa ne? ".
Nazifa ta marairaice fuskarta cikin tsananin takaici da tsantsar tashin hankali tace"kedai bari Safiya Yaseer ya cuceni yaci amanata ya sakeni saki d'aya! ".
Rasssss faduwar gaba ya ziyarceta tsantsar farin ciki da murna ne kwance cikin k'wayar idanunta wani irin kallo ta jefeta dashi tace"ya sakeki Nazifa!? ".
Nazifa ta girgiza kanta cikin zafin rai tace"eh mana da gaske ya sakeni! ".
Safiya ta fashe da dariyar mugunta Nazifa tayi saurin kallonta cikin tsananin mamaki da tsantsar takaicin dariyarta tace"amma Nazifa kinyi wauta tun farko da kika amince dani! ".
Nazifa taji hankalinta ya d'unguma zuciyarta ta tsinke gabanta ya dinga dukan uku uku tace"Safiya mi kike nufin da nayi wauta dana amince dake ki fitar dani daga cikin duhu zuwa haske ban fahimci inda maganarki ta dosa ba?".
Safiya ta bintsire baki tareda yamutsa fuskarta cikin tsananin hassada da tsantsar bak'in ciki tace"yanzu kuwa zan fahimtar dake ta yadda zaki Nazifa tun farkon had'uwata dake bana k'aunarki ko kad'an azuciyata domin kin mallaki duka dukiya ,mijin nagari, iyayenki sunada arzik'i sannan suna matuk'ar k'aunarki azuciyarsu kinyi mini fintinkau ta ko'ina arayuwarki,kin amince dani tareda saurin bani amana shiyasa na samu galaba akanki sainayi ta zugaki kina yiwa mijinki rashin mutunci ni kuma ina yiwa mijina biyayya tareda banbasa tsantsar soyayyar gaskiya saboda haka ki tashi ki ficemin daga cikin gida domin *DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA* shi ruwa kan doka babu abinda ya shafeni da mijinki ya sakeki tunda ba nawa ne ya sakeni ba! ".Fauzeeya ta dubeta cikin zafi da rad'ad'in kalamanta hawayen bak'in ciki da tsantsar damuwa sai sintiri sukeyi afuskarta cikin zafin rai tace"ina lillahi wa ina ilaihirraji'una! Na bani na lalace ni Nazifa kin cuceni Safiya kin zugani na sab'awa umurnin mijina kin kaini kin baro cikin nadama, tsakanina dake Allah ya isa ban yafe miki ba".Safiya ta harareta tace"karki yafemin d'in sakaryar mace wadda batasan abinda ake nufi da *SOYAYYAR GASKIYA* ba ke azatonki sonki nakeyi yanzu ki ficemin daga cikin gida banason ina mu'amala dake domin kada ki zamo silar mutuwar aurena! ".Nazifa tana sharar hawayenta tace"tabbas shiyasa duk abinda mutum zaiyi ya dinga sara yana dubin bakin gatarinsa kaicona ni Nazifa na biyewa shawarar muguwar k'awa da rud'in duniya na afka cikin tarkon nadamar arayuwa! ".
Safiya ta zaburo mata cikin hargowa tace"duk abinda zaki fad'a kije kiyita fad'a nace ki ficemin agidan miji kafin inzo in fitardake da k'arfi! ".Nazifa tana kuka tace"ni kika cuta Safiya!? "."Na cuceki duk ubanda zaki fad'awa kije ki gaya masa naci amanarki sai mi wa yace ki bani amana kin amince dani!? ""Haka zaki fad'a bayan na taimakeki alokacin da kike buk'atar taimako ba komai kije duniya ce da sannu zakiga sakayyar da zata biyo baya! ".Safiya ta iso gab da ita tace cikin matuk'ar b'acin rai "babu abinda zan gani sai alkhairi muguwar aniyarki ta biki duk kika shiga aduniya! ".Tana rufe bakinta taja hannun Nazifa nufin ta fitar da ita waje da k'arfi Nazifa sai turjewa takeyi tana son tasa taurin kai, Safiya janta tayi k'ik'ik'ik'ik'i kamar karya harta fito da ita cikin tsakiyar compound d'in gidan ta wunlata k'asa kaji bifffff sai k'asa! Wani irin rikitaccen zafi da rad'ad'in ciwo ne ya ziyarci sassan jikinta da k'wak'walwarta asanadiyyar haka saida ta saki rikitaccen k'ara da gigitacciyar kuwwa! Kwance tayishame shame k'asa Safiya tayi k'yafi tace"idan kika sake zuwa gidana saina nakkasaki! ".Tana kammala maganarta taja k'afafunta ta shige cikin parlour..................
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*THE END*
*PAGE 50*
Bayan shigewarta gida Nazifa ta mik'e tsaye dak'yar tana kakkab'e dattin jikinta da sauri ta fice daga cikin gidan, yayinda ta isa bakin motarta ta bud'e k'ofar motarta ta shige tareda ficewa daga cikin unguwar.
hajiya Ramlat tayi shirinta na kamala ta shige cikin motarta batayi doguwar tafiya ba,ta iso bakin get d'in gidan ta parker motarta awaje fitowa daga cikin motar ta shiga cikin tsakiyar filin gidan babu kowa awaje domin maigadi yana cikin yana lazimi, tana isowa bakin k'ofar parlourn ta shiga cikin parlourn ahanzarce ta iskesu Alhaji Taheer zazzaune saman cushion suna firarsu cikin fara'a da nishad'i,saiga sallamar hajiya Ramlat ta shigo tsakiyar parlourn cikin matuk'ar kamala da kunya amsa mata sukayi cikin natsuwa da sakin fuska sannan tayi masauki saman cushion, bayan sun gaggaisa hajiya Ramlat ta noce kanta cikin d'aci da tsantsar takaicin rayuwa tace"Alhaji wurinku nazo fa".
Hankalinsu suka mayar kacokam wurinta Alhaji Taheer yayi murmushin dake fallasa asirin kyawonsa yace"muna saurarenki hajiya Ramlat".
"nazo ne in nemi gafararku akan abinda ya faru nasan nayi matuk'ar kuskure arayuwata, musamman ke hajiya Sadiya akwanakin baya nazo har nan na shuka miki rashin mutunci akan abinda bakida laifi saboda haka na rok'eku kuyafemin ba domin halina ba".Tace yayinda kwallar zallar takaici suka cicciko cikin k'wayar idanunta wani irin d'aci da zogi cunkushe azuciyarta!.
Alhaji Taheer ya dubi hajiya Sadiya itama ta kallesa sukayi jugum cikin nazari da tunani sunkai minti goma babu wanda yace uffan daga cikinsu, can dai Alhaji Taheer ya kalli fuskar hajiya Ramlat cikeda lumana yace"Ramlat ki sani baki tab'a yimin laifin komai ba koda ace kinyimin na yafe miki domin duk d'an Adam tara yake bai cika goma sannan duk mai rai baya wuce aikata kuskure".
hajiya Ramlat tasa hannu ta share kwallar data taru cikin k'wayar idanunta afaikace cikin matuk'ar mutuwar jiki tace"nagode ubangiji ya k'ara girma".
"amin ya rabbi".Cewar Alhaji Taheer.
hajiya Ramlat ta juya ta kalli b'angaren hajiya Sadiya cikin marairaicewa tace"kiyafemin Sadiya naji bakice komai ba ko............... ".
hajiya Sadiya ta katse mata hanzari ta taso daga inda take zaune ta sanya hannunta cikin tafin hannun hajiya Ramlat, murmushi ta sakar mata ta girgiza kanta cikin tausayawa rayuwarta tace"ki daina rok'ona gafara 'yar uwata tuni na yafe miki domin ban rik'eki azuciyata ba saboda nasan duk d'an Adam ajizi ne, kinga kenan komai ya riga ya wuce har abada bana tuna baya".
"gaskiya ku d'in mutane ne masu zuciyar alkhairi da halacci arayuwa tabbas idan mutum yabiku da sharri saiku saka masa khairi".
hajiya Sadiya ta musk'uta tace"karki manta da cewa akwai ragowa atsakaninmu babu komai mijina da naki aminan juna ne sannan gamu surukan juna duk abinda kikaga mutum yana yi da sannu zai daina saboda duniyar nan *RAYUWA CE* mai k'unshe da k'alubale da darussan rayuwa".
Murmushi mai ciwo tayi tace"haka ne dama inason in gaya muku mijina ya sakeni saki d'aya saboda nasan Alhaji Taheer bayada labari shine nace bari inzo in sanar masa dan girman Allah ya taimaka ya sanya bakinsa domin mijina ya maidani d'akina, wallahi nayi matuk'ar nadama dana sanin irin abubuwan dana aikata rayuwata alal hak'ik'a na cuci 'yata tareda silar tab'arb'arewar tarbiyarta amma yanzu na fahimci cewa *DUNIYA MAKARANTA* ce mai d'auke da classes na d'aukar darasin rayuwa! "
"ina lillahi wa ina ilaihirraji'una! ".Suka fad'a kusan atare.
Hankalin Alhaji Taheer ya d'unguma zuciyarsa ta girgiza daurewa yayi yace cikin damuwa yace"akan wane dalili ya sakeki Ramlat!? ".
hawayen bak'in ciki sai gangarowa sukeyi afuskarta wani irin tururin zafi da k'una zuciyarta keyi dak'yar ta bud'i bakinta tace"saboda Yaseer ya saki Nazifa shine yace nice sanadin mutuwar aurenta!".
"amma gaskiya wannan abin baiyi dad'i ba Alhaji Mu'azu bai k'yauta ba".Inji hajiya Sadiya cikin matuk'ar jimami da zafin sakin da yayiwa hajiya Ramlat.
Alhaji Taheer ya jijjiga kansa tareda yin huci mai tattare da d'acin rai da tsantsar takaici yace"Mu'azu bai k'yauta miki ba amma kiyi hak'uri karki damu ki koma gidan da kike zaune da yardar Allah komai zai dawo daidai".
"shikenan nagode sosai Allah ubangiji yabar zumunci".
"amin amin".
Saida ta tsaya suka tab'a yin fira sannan tayi musu sallama ta dawo gidan yayarta Hamamatu, koda ta dawo ta iske Nazifa tanata rusar kukan takaici da bak'in cikin rayuwa kamar zata shid'e akan tsantsar damuwa, da sauri ta isa wurinta ta rungumeta ajikinta tana bubbuga bayanta alamar lallashi cikin tausayawa tace"kiyi shiru ki daina kuka 'yata *DUKKAN TSANANI* yana tareda sauk'i saboda haka ki rungumi k'addararki hannu bibbiyu tareda fawwalawa ubangiji lamarinki komai yayi farko yanada k'arshe miye silar sanyaki zubar da hawaye baby? ".
Dak'yar Nazifa ta had'iye kukanta wani irin abu ke yawo cikin jini da gangar jikinta tarin damuwa yayi mata k'abe k'abe cikin zuciyarta ta rasa abinda yakeyi mata dad'i aduniya! Alal hak'ik'a ta tabbatar da duk inda kake mak'iyinka yana nan tare dakai sannan ba kowace k'awace abar yarda wadda zata rik'eki da zuciya d'aya tareda yi miki tsantsar *SOYAYYAR GASKIYA* ba.
Idanunta duk sun kumbura akan yawan kuka ta nisa tace"Ummu nayi matuk'ar nadamar yarda da Safiya da nayi arayuwata duk abinda nakeyiwa mijina itace take zugani ashe ita ladabi da biyayya takeyiwa mijinta Haidar! Tabbas ta cuceni kuma sai ubangiji Allah yayi mana hisabi atsakaninmu saboda bazan tab'a yafe mata har abada".
hawaye suna sintiri afuskar hajiya Ramlat tace"tabbas kin had'u da tuggun makirar k'awa arayuwarki Nazifa saidai abinda zance idan ubangiji ya k'addari komawarki gidan mijinki ki kiyaye babu ruwanki da kwashe kwashen k'awaye domin mafi akasarin aurarrakin dake mutuwa yanzu duk asanadin k'awaye ne! ".Nazifa ta kalli mahaifiyarta cikin dashasshiyar muryarta da ba'a ji tace"bazan k'ara yarda da kowace shegiyar k'awa domin duniya tayi mini karatun ta natsu".
**********************
Aranar da hajiya Ramlat tazo gidan Alhaji Taheer ta sanar masa mijinta ya saketa aranar ne ya kira Alhaji Mu'azu ya nuna b'acin ransa da kuskurensa, saboda maganar gaskiya baiji dad'in sakin da yayi mata ai akwai ragowa idan aure yakai wani munzali sai hak'uri da dangana, Alhaji Mu'azu bashi hak'uri yayi tareda maida aurensa da hajiya Ramlat.
da safe suka koma itada d'iyarta Nazifa gidan Alhaji Mu'azu yayinda har yanzu Nazifa ta kasa sakewa domin ita ta tuna da cin amanarta da Safiya tayi rayuwarta b'aci takeyi zuciyarta k'una takeyi, mahaifiyarta ce ke lallashinta tana bata kalamai masu sanyaya zuciya haka dai ake samu ashawo kanta dak'yar ta rage damuwa da kukan takaici da tsantsar tashin hankali arayuwa, akwanakin nan da tayi gidansu duk ta rame tayi baki adalilin b'acin rai da tsantsar damuwa, ganin d'iyarta tana cikin matsanancin hali yasa hajiya Ramlat take yawan nafila da rok'on ubangiji ya kawo mata mafitar alkhairi.
*BAYAN WATA GUDA*
Alokacin ne Nazifa tayi wata d'aya cifcif da komawa gidan mahaifinta to ranar ne Yaseer ya maida aurensa da ita, jin ya maida aurensa mahaifinsa ya taso k'eyarsa gaba suka zo har gidan Alhaji Mu'azu akayi musu nasiha mai ratsa b'argo da jinin jikin d'an Adam sannan daga k'arshe ya dawo da Nazifa gidansa, koda su Sameer sukaga mahaifiyarsu suka rungumeta cikin matuk'ar kewa da soyayya tsakanin uwa da d'a Fauzeeya tana tsaye tana kallon ikon Allah cikeda tsagwaron tausayawa, sun jima k'ank'ame ajikinta sannan daga baya ta jayesu d'agowar da zatayi idanunta suka fad'a cikin na Fauzeeya murmushi suka sakarwa juna Fauzeeya tayi mata sannu da zuwa ta amsa fuskarta asake,