Showing 39001 words to 42000 words out of 87802 words

Chapter 14 - SAKACI BY MUGIRAT MUSA

05 Jul 2024

4241

fad'a da komai hajiya Ramlat ta bari ya bata k'yautar akwatin saboda hajiya ma cece mai bak'in rowa da son abin wani ita tanason taci naka amma nata kam baya ciyuwa.

Tana kammala had'a kayanta tsab Nazifa ta sanya agaba suka nufi parking lot suna isa suka bud'e k'ofar motar Nazifa ta zauna, itama ta zauna tareda jawo k'ofar motar ta rufe sannan ta danna horn da k'arfi getman ya sheko da gudu ya wangale musu k'ofar get d'in suka fice daga cikin gidan da sassarfa.

Nazifa tafiya sukeyi sannu ahankali cikin yanayin natsuwa har suka iso unguwar daidai bakin get d'in gidan, danna horn tayi fififififi maigadi yazo da sauri ya wangale mata k'ofar get d'in ta kunna hancin motarta daidai tsakiyar filin gidan harta isa parking lot ta parker motarta, tana parkerwa ta fito suka fito atare daga cikin motar Tasallah ta d'auki akwatinta saman kai ta wuce gaba, yayinda Nazifa take biye abayanta har suka iso cikin parlourn suna isowa wurin cushion suka zazzauna suna ajiyar numfashi.

Alokacin ne Nazifa ta juyo ta dubeta cikin yanayin gajiya tace"Tasallah".
"na'am hajiya".Tace cikin girmamawa da ladabi.
Nazifa ta gyara muryarta tace"daga yau kin fita daga mai aikin hajiyata kin koma 'yar aikina ina fatar zaki rik'eni hannu bibbiyu cikin ladabi da amana, sannan ina ja miki kunne da gargad'inki akan banason shisshigi da shiga cikin abinda bai shafeki ba kuma nan da sati uku mijina zai k'ara sabon aure saboda haka ko amaryar ta shigo cikin gidan nan babu ke babu ita har abada!Idan na samu labarin cewa ko maganar arzik'i kikayi mata abakin aikinki! ".

Rasssss fad'uwar gaba ya ziyarceta tsantsar fargaba ne ya bayyana k'arara afuskarta cikin mutuwar jiki tace"da yardar Allah hajiya zan kasance mai biyayya agareki muddin muna tare dake".

"good Tasallah haka nakeson ji abakinki ubangiji ya bamu zaman lafiya ya kauda duk wata fitina atsakaninmu".

"Amin hajiya ko akwai aikin da zanyi miki ne yanzun nan?".

Nazifa tayi hamma alamun tana jin matuk'ar yunwa ta kishingid'a bayanta akan cushion tace"babu aikin da zakiyimin saidai ki girkamin abu mafi sauk'i inci saboda ina jin yunwa".

Tasallah ta tashi tsaye tace"babu damuwa hajiya ina kitchen d'in yake?".

Nazifa ta nuna mata da yatsa daidai saitin kitchen d'in tace"kibi inda kikaga yatsar hannuna take fuskanta"."To hajiya".Tana rufe bakinta taja k'afafunta ta nufi cikin kitchen ta fara kichaniyar dafa jallof d'in taliya taji kayan cikin rago ciki, k'amshin girkinta duk ya gauraye cikin gidan da zagayensa ko'ina k'amshi sai tashi yakeyi, babu jimawa ta kammala girka dahuwar tafiyar ta juye cikin k'aramar kula ta aza saman tire ta d'auko ahannunta ta nufi cikin parlourn.
Tana isowa wurin Nazifa ta duk'a har k'asa ta aje tiren sannu ahankali domin kada abincin ya watse, sannan ta koma gefe k'asan carpet ta zauna Nazifa ta musk'uta tace"ki koma kitchen ki d'auko plate biyu sannan ki had'omin da lemun gora da ruwa idan zaki fito".

Ta tashi sannu cikin yanayin natsuwa tace"to".
Ta nufi hanyar zuwa kitchen ta d'auko plate biyu sannan ta bud'e frizer ta d'auko lemun gora da ruwan, ta fito daga ciki ta k'araso wurin Nazifa dake zaune kamar gimbiya ta aza k'afarta d'aya saman d'aya, Tasallah ta russuna ta aje mata goran lemun da ruwa akan tire sannan ta mik'a mata plates d'in ahannunta tace"gasu".

"OK godiya nake".

Nazifa ta sanya hannu ta bud'e murfin kular ta d'ibawa Tasallah abincin itama ta d'ebi iyakar wanda zata iya cinyewa, sauran abincin daya rage ta sanya murfin kular ta rufe tace"kizo ki d'auki naki abincin".

Tasallah tazo ta d'auki nata abincin ta koma inda ta zauna da farko fara cin abincin takeyi cikin natsuwa da kamala, itama Nazifa tuni ta fara bawa cikinta hak'k'insa domin kada yunwa tayi mata illah.

**********************
Safiya kuwa tana nan zaune bayan ficewar Nazifa gidanta kallo kawai takeyi tana mamaki wauta da rashin wayo irin na Nazifa, idan banda batada hankali ta yaya take d'aukar nasiharta bayan babu dangi uwa bale na baba, amma Nazifa ta bata amana da sakankancewar ita d'in *SOYAYYAR GASKIYA* takeyi mata alhalin ak'ark'ashin zuciyar Safiya babu wadda ta tsana fiye da Nazifa saboda ta kasance d'iyar masu kud'i wadda ta taso cikin gata da dukiya, hakan ne yasa ta k'udurta azuciyarta sai tayi sanadiyyar tab'arb'arewar farin cikinta da tarwatsa duk abinda yake sakata cikin nishad'i.
Wato abinda Nazifa bata sani ba Safiya tana matuk'ar hassadarta da kuma son ganin bayanta domin ganin takeyi Nazifa ta zarceta da komai na rayuwa, hakan ne yasa take nuna mata k'auna azahiri amma abad'ini ko jaki yafi ta daraja da kima a idanun Safiya saboda ita bata k'i awayi gari ace an sakota ba saboda tsantsar k'iyayya da tsagwaron hassada.

Hmmmmmm amma dayake Nazifa irin matan nan ne masu saurin bada amana da yarda da mutum farat d'aya, shiyasa bata fahimci cewa Safiya ba son gaskiya takeyi mata kunsan hausawa sunce *SANIN MASOYI* sai ubangiji Allah tabbas wannan maganar haka yake babu k'arya acikinta.

_Abin nufi da lura anan shine duk yadda kike da mutum karkiyi saurin basa yarda da amana, domin wata rana zai iya cin amanarki da ha'intarki ya gudu ya barki cikin k'unci da k'angin rayuwa._

**********************
Washegari su Fauzeeya suka shirya itada k'awarta Adama zasuje kasuwa kenan Iya Kulu sai tsokanarsu takeyi tana cewa bazasu barta ita kad'ai cikin gidan ba, saita bisu duk inda zasuje yayinda Adama sai dariyar zolaya takeyi tana cewa"babu inda zaki bimu adinga nunamu agari ana cewa mun wahalar da tsohuwar mutane".

🤩Iya Kulu ta gyara d'aurin zanenta cikin iyayi da kwakwazo tace"ke rabani da shirmen banza ko don na kwana biyu zakiyi mini wani irin gani gani, to dubeni da k'yau babu abinda zaki gwadamin ahalin yanzu dai sai k'urciya da wauta".

Adama ta bintsire baki tace"amma fa kin kasheni Iya ni zaki had'a dake "..Iya Kulu ta rausayar da kanta cikin kicifi da azuzanci tace"fad'amin abinda zaki gwadamin idan ba tsawo ba kamar fal wire hanci kamar butar shayi ".😁😁

Fauzeeya ta fashe da dariyar mugunta harda hawaye suka fito mata adalilin dariyar k'eta dak'yar ta samu ta had'iye dariyarta tace"wannan dramar bazata tab'a k'arewa ba irin wannan shammata haka Iya gaskiya koki daina bamaso ""Kee mai k'irar 'yan yunwa waya kasa dake bale ki kwasa? ".
Itama Adama ta rama dariyar da Fauzeeya tayi mata tace"wallahi Iya ke iya shammata sosai yi sauri ki kintsa mu wuce lokaci yana tafiya fa".Fauzeeya ta murmusa tace"to aini Iya ta wuce tunani wlh "."K'warai kuwa na wuce tunanin dukanku saboda jikokina kuke ".

"ai mun sani Iyarmu ".Inji Adama tana dariya k'asa k'asa domin kada Iya Kulu taga ta maisheta madari. Fauzeeya ta fito cikin d'akin tana tafiya guda guda cikin natsuwa kallon fuskar kakarta tace"mu zamu tafi Iya mizan siyo miki idan naje? ".Iya Kulu ta kallesu cikin tsananin so da k'aunarsu ta rausayar da kanta tace"basai kun siyomin komai ba d'iyan nan burina shine ubangiji ya kaiku lafiya ku dawo cikin aminci ".Hak'ik'a sunji dad'in addu'arta har cikin jini da k'ofofin jikinsu murmushi k'unshe afuskarsu sukace"amin amin ".Rungumeta sukayi cikin tsantsar farin ciki da k'aunar Iya Kulu.

Daga baya suka jaye jikinsu ana Iya Kulu suka juya zasu nufi hanyar zuwa kasuwa kenan Iya Kulu sai d'aga musu hannu takeyi alamar bye bye 👋 kwatsam! Wata irin kafirar guguwa ta bayyana da k'arfi suuu suuu suuu hankalinsu ya d'unguma zuciyarsu ta tsinke, gabansu sai dukan uku uku yakeyi domin tuni fargaba da tsantsar tsoro ne ya bayyana k'arara afuskokinsu, cikin Fauzeeya ya d'uri ruwa guguwar ta jima tana kewayarsu can dai ta d'auke cak! Su Baura sukayi musu k'awanya cikin sihiri da shahara akan tsafi...........

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 24*


Ganin mutane har kusan hudu sun sakasu atsakiya tun anan suka k'ara tsurewa da rikicewa cikinsu ya d'uri ruwa jikinsu sai k'yarrrma da kad'uwa yakeyi kafkafkaf, ji sukeyi kamar ace k'yat su zura da gudu kallo d'aya suka yiwa su Baura suka kauda kai saboda sun hango matuk'ar rashin imani da rashin tausayi a k'wayar idanunsu,Baura ya fito gabansu yana k'arewasu Fauzeeya kallo da idanunsa jajir kamar gauta rikitacciyar tsawa da hargowa ya daka musu wadda asanadiyyar haka saida suka shiga rud'u da rikicewa zama guda nan take Iya Kulu ta fashe da rikitaccen kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro hawaye sai shatata sukeyi saman fuskarta tace"bayin Allah ku dubi girman Allah ku gaya mana dalilin daya kawoku cikin gidan nan! ".
Yaran Baura suka wurga mata muguwar harara yayinda Baura ya bud'e k'atanyar muryarsa mai kamada kukan jaki yace"keeee tsohuwa! Kiyi mana shiru banason tambayar banza ko yanzu na lahira yafi ki jin dad'i ".
Iya Kulu jikinta yana mazari da k'yarrrma ta duk'ar da kanta k'asa zuciyarta sai d'ar d'ar d'ar takeyi yayinda su Fauzeeya tuni sunyi sharkaf da gumi sai tsiyaya yakeyi ajikinsu ji sukeyi kamar su b'ulla ta cikin k'asa su gudu, saboda sun sadak'ar da cewa babu alkhairi azuk'atan wad'annan mutane domin dubi d'aya zakayi musu ka gane babu tausayi ko rangwame k'unshe afuskokinsu!.

Baura ya k'ara murtuk'e fuskarsa kamar wanda yaga kashi cikin yanayin rashin imani yace"wa cece Fauzeeya acikinku?".

Dummmm gabansu ya buga tsantsar tsoro da tsinkewar zuciya ne ya ziyarci sassan jikinsu da zuciyarsu sunyi shiru sun kasa bashi amsa asanadiyyar sun shiga cikin matsananciyar damuwa da fargaba!Da Baura yaga sun kasa magana ya amshi wuk'a ahannun yaronsa guda ya tunkaro wurinsu Adama gadan gadan babu alamun rahama da tausayi cikin k'wayar idanunsa, suna ganin ya tunkarosu sai ya zamana Adama ta kalli Fauzeeya itama ta kalleta cikin hautsinewar ciki Adama ta saki rikitaccen kuwwa da razananniyar k'ara ta fara rok'onsa tana cewa"dan Allah kayi mana rai kada ka kashemu! Mun tuba munbi Allah kayi hak'uri".

Baura ya aza yatsa saman bakinsa yace"shittttttt yimin shiru ko yanzu in dab'a miki wuk'a saman zuciya ki mutu abanza bakida masu yi miki addu'ar neman gafara aduniya! ".

Adama ta sanya hannunta ta rufe bakinta domin kada kukan ya fito fili had'iye wani abu tayi cikin zuciyarta, Fauzeeya kuwa ta kasa yin kwakkwaran motsi adalilin ta shiga cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa!.

Baura yayi tsaye yana kallon fuskarsu amurtuk'e cikin bak'in rai da mugun nufi ya sake cewa"wa cece Fauzeeya atsakaninku ku biyu?".

Iya Kulu ta iso wurinsa gab dashi tace"nice Fauzeeya yar............ ".Yaronsa d'aya daga cikinsu bai bari ta k'arasa maganarta ba ya d'auketa da rikitaccen maruka guda hud'u masu k'yau wanda asanadiyyar haka saida ta wuntsila k'asa ta fad'i kaji d'immmmm jinta da ganinta suka d'auke cak na wucin gadi ta rasa awace duniyar ta tsumduma ta fice daga cikin hayyacinta hawaye masu zafi da k'unar rai sai sintiri sukeyi afuskarta.
Su Fauzeeya suna ganin irin abinda ya faru da Iya Kulu suka k'ara gigicewa da rikicewa kowaccesu zufa sai tsiyaya yakeyi ajikinta, wani irin abu mai matuk'ar d'aci Fauzeeya ta had'iye cikin mak'oshinta ta furta cewa"kuyi hak'uri ku daina marinta please kunga tsohuwa ce ba yarinya ba!".

Wani irin mugun kallo Baura ya jefeta dashi yace"karki nemi ki raina mana hankali aikinmu mukeyi".

Maimaitawa tayi afili domin ta kasa barin maganar cikin zuciyarta tace"mari ma yana daga cikin aikinku wannan bai dace ba bayin Allah kuji tsoron ubangijin sammai da k'assai ku sani duk zaluncin da kuka yiwa mutum aduniya agobe k'iyama sai Allah yayi masa muguwar sakayya ".

Yaran dai sauraren nasiharta kawai sukeyi Baura ne yayi k'arfin daka mata tsawa saboda bayason wa'azinta yayi tasiri azuciyarsa da zuciyar yaransa yace"ba wa'azi ya kawomu saurare ba saboda haka kibi ahankali ko yanzu kaifin wuk'ata tasha jininki! ".Yana rufe bakinsa yayiwa yaransa signal da ido babu b'ata lokaci naga sun zare belt d'insu ak'ugunsu suka rufesu Fauzeeya da matsiyacin duka kaji faufaufau basu ba ba Iya Kulu ba,dukansu kawai sukeyi cikin matuk'ar rashin imani da k'arancin tausayi su Iya Kulu sai kuka da kuwwar wuya sukeyi amma kaji shiru ko a mak'wabtan dake gab dasu basu jiyo kukansu ba, saida sukayi musu lik'is da duka numfashinsu yana batun d'aukewa sannan suka ja suka tsaya suna mayarda numfashi da hakin wuya.

Baura ganinsu Fauzeeya sun galabaita alokaci guda cikin zafin rai yace"don ubanku gobe ku sake k'yaleni idan ina tambayarku".
Nuna Fauzeeya yayi da hannunsa yace musu"ku tallabomin ita ku kaimin cikin d'akin kakarta in yaga mata rigar mutunci! ".

Suka russuna cikin ladabi sukace"to Oga angama".

Jin umurnin da Baura yaba yaransa yasa su Iya Kulu suka gigice da shiga cikin matsanancin halin da babu mai iya fitar dasu sai Allah, saboda yanzu duk sunsha wuya da galabaita ahannunsu Baura gashi sunji yace ya yagawa Fauzeeya rigar mutunci gashi basu iya tashi tsaye bale su gudu su ceci ransu, hawayen takaici sai gangarowa sukeyi afuskar Fauzeeya domin ta sadak'ar ayau ubangiji ne kawai zai kub'utar dasu ahannun wadannan azzaluman mutane!.
Tasan idan ya rabata da budurcinta yana wuya Yaseer ya aureta domin komai ma zai iya faruwa, yaran basuyi wata wata ba suka sungumi Fauzeeya suka kaita har cikin d'akin Iya Kulu har kan gadonta, suna ajiyeta suka juyo suka fito daga cikin d'akin saboda suba Ogansu wuri ya biya buk'atarsa su kuma tsaresu Iya Kulu domin kada su gudu!.

Su Iya Kulu kuka kawai sukeyi suna addu'a cikin zuciyarsu akan ubangiji ya kub'utar dasu daga hannun wad'annan bayin Allah, fatansu kada ubangiji yaba Baura sa'a akan Fauzeeya domin kada ya lalata mata rayuwa tareda tarwatsa duk wani farin cikinta.

Cikin d'aki kuwa Baura ne ya shigo yana k'yalk'yalar dariyar k'eta kallonta kawai yakeyi yana had'iyar miyau kamar wanda yaga soyayyar kaza 😂.
Tuni Fauzeeya ta k'ara rikicewa hawaye sai shatata sukeyi saman fuskarta cikin tsananin takaicinsa tace"na rok'eka kayi hak'uri kada ka tarwatsamin farin cikina tareda sakani cikin uk'ubar rayuwa! Haba bawan Allah idan laifi nayi maka ka yafemin bale nasan banyi maka laifin komai ba".

"'yan mata bazan fice daga cikin gidan nan ba har saina cika umurnin da aka bani saboda haka ina shawartarki akan ki bani had'in kai muyi abinmu cikin lalama da rufin asirin ,idan ba haka ba zanyi amfani dake ta k'arfi inyi miki kaca-kaca har sai kin kasa motsi! ".

Fauzeeya tayi wuru wuru da idanunta cikin razana da kad'uwa akan zancensa tace"umurni kace an baka ni kuwa miye na tarewa wani/wata da zasu nemi nakkasamin rayuwa!?".

"tabbas umurni ne aka bani in lalata miki rayuwa kiyi nazari da tunani mai k'yau ai duk yadda kike aduniya bak'ya rasa mak'iya da mahassada".

Fauzeeya tayi shiru na mintuna kad'an can su hajiya Ramlat da d'iyarta Nazifa suka fad'o mata arai cikin sub'utar baki tace"su hajiya Ramlat ne suka turoka ka lalatamin rayuwa wayyo ni na shiga uku na lalace wannan wace irin *RAYUWA CE* mai tattare da k'unci da bak'in cikin rayuwa? Duniya ina zaki damu ubangiji ya Allah ka kub'utar dani daga hannun wannan azzalumin bawa naka! ".Tace da k'arfi ta yadda zaiji abinda ta fad'a.

Kallonta yayi cikin harzuka da suk'uwa yace"ni kike kira da azzalumi!? ".

Cikin tsantsar tsoro tace"yi hak'uri bada kai nake ba".

"dawa kike to!? ".Yace atsawace cikin zafin zuciya.

"bada kowa nake ba".

"'k'arya kikeyi! ".Yana rufe bakinsa ya nufi wurinta gadan gadan da nufin yayi amfani da ita ko ta k'arfin tsiya ne Fauzeeya ta rikice da d'imaucewa hankalinta yayi k'ololuwar tashi fargaba da tsantsar tsoro ne ya bayyana k'arara afuskarta, kuka ta fashe dashi wiwiwi domin tasan ayau babu mai k'watarta ahannunsa sai ubangiji majina ce ke tsiyaya ahancinta domin zama d'aya ta rikice ta fice daga cikin hayyacinta!. Duk da yadda yaga ta shiga cikin damuwa baisa Baura yaji ko d'igon tausayinta azuciyarsa ba.

Baura yana isowa wurinta ya kawo mata chapka da nufin lokaci guda yayi amfani da ita alokacin ne Fauzeeya ta kauce cikin zafin nama domin ta lura idan ta tsaya sanyi zanyi mata illah, ganin ta kaucewa harin daya kawo mata yasa ya hasala da harzuk'a ya sake kawo mata chapka akaro na biyu Fauzeeya ta sake kaucewa tana ja da baya da baya.

Shi kuma sai binta yakeyi yana dariyar mugunta har suka kakai k'arshen bangon d'akin,suna kai k'arshen bango Baura ya kawowa boob's d'inta chapka ya damki d'aya ahannunsa rikitaccen zafi taji nan da nan ta saki kuka rik'ewa yayi da k'arfi cikin mugunta saboda ya kwad'aitu da ita domin so yake yaji ni'imarta, kallon kasan d'aki takeyi tana kuka can ta samu ta shammaceshi ta gantsara masa cizo ahannu yayi kuwwa tareda sakinta! Ai kuwa nan da nan ta zura da gudu ta fice daga cikin gidan kamar walkiya yayindasu Iya Kulu dake kwance kasa ganin Fauzeeya ta gudu yasa suka tunkud'e yaran Baura suka shek'a da gudu .

Kaji gwaffff yaran Baura sunkai k'asa wani irin fitinannen zogi da rad'ad'i ne ya ziyarci sassan jikinsu da magudanar jininsu suna numfashin wuya saiga Baura ya fito arikice cikin d'akin yana cewa "ku kamota ! Ku kamota!! ".Sai alokacin ne yaga yaransa kwance cikin mayuwacin hali ya daka musu tsawa suka mik'e tsaye zumbur yace"dan uwarku ku bisu ku kamosu idan ba haka ba saina kasheku dukanku sakarkarun banza da yofi!. ".Kafin ya rufe bakinsa har sun fice daga cikin gidan sunbi bayansu Iya Kulu ko zasu hango ko kurarsu amma ina sunyi musu fintikau, saida suka zagaye kaf garin da k'afafunsu suka sha iya wuya amma ko walkiyarsu basu gani daga baya suka yanke shawarar su dawo su sanarwa Ogansu abinda ake ciki.........

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login