Showing 63001 words to 66000 words out of 87802 words
fad'a cikin room d'insa sai kai da kawo yakeyi rungume hannunsa yayi saman k'irji jijiyoyin kansa suka mimmik'e tsaye rud'u rud'u! Zarya ya dingayi yana neman irin hukuncin daya kamata yayiwa Nazifa duk dayake batasan yasan cewa itace ta kori Fauzeeya ba alokacin daya amince da soyayyarta, batasan baba maigadi ya bashi labarin irin cin mutunci da walak'ancin data shuka masa awannan ranar tabbas ya dace yayiwa abin tufkar hanci idan ba haka ba Nazifa zata iya tarwatse masa aure yarinyar taji tsoro ta gudu ta koma gidansu! "Kayyyy bazai tab'a yiyuwa ba dole in takawa mata burki ta fahimci na gane duk makirci da k'ulle k'ullen da takeyi"...........
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 37*
Dak'yar Yaseer ya saisaita natsuwarsa ya kwanta saman gadonsa yana jiran dawowar Nazifa yau ayita ta k'are! Saboda ya hak'ik'ance da cewa bazata tab'a daina aikata abinda takeyi ba domin ya hango bak'in kishi da son fitina kwance afuskarta akowane lokaci, so takeyi ta zauna ita kad'ai cikin gidansa domin bata tab'a tsammanin zai iyayi mata kishiya ba *ARAYUWA*,bazai yarda ta kore masa Fauzeeya ba domin ayanzu bayan iyayensa babu abinda yake so da tsantsar k'auna fiye da ita ta zamo ginshik'in rayuwarsa da garkuwarsa ta yaya zai iya rayuwa babu ita, tabbas rashinta aduniyar so bazai tab'a yiyuwa ba saboda zuciyarsa zata iya bugawa ya mutu ta sace zuciyarsa da k'yautatawa da bashi tsagwaron kulawa tareda tsantsar *SOYAYYAR GASKIYA*,tunanin rayuwa ya dingayi yana mamakin yadda al'amurran duniya suke jujjuyawa kamar waina.
*********************
Dayake Nazifa tasan sharrin data k'ulla itace bata dawo cikin gidan ba sai bayan sallar isha'i tana dawowa ta fad'a cikin bathroom ta watsa ruwa ajikinta, ta jima tana wanke sassan jikinta sannan ta fito daga cikin toilet d'in d'aure da towel direct kujera ta jawo ta zauna tana shafa manshafi, tana gama shafe jikinta ta jawo rigar barci mara nauyi ta zura ajiki ta dawo saman gadonta ta aza kanta saman pillow, lullub'e jikinta tayi da blanket ta fara lumshe idanunta alamar barci yanason saceta, can taji an bud'e k'ofar d'akin an shigo bud'e idanunta cikin sannu ahankali tana kallon fuskar mijinta, Yaseer ya iso wurinta gab da ita ya zauna yana k'are mata kallo ciki d'acin rai yace mata"tashi zaune zamuyi magana".
Nazifa tayi hamma alamun barci takeji sosai cikin idanunta tace"ka fad'i duk maganar da zaka fad'a barci nakeji".
"ki tashi maganar mai matuk'ar muhimmanci ne zamuyi".Inji Yaseer zuciyarsa cunkushe da tsantsar damuwa da b'acin rai.
"nifa bazan iya tashi ba ka fad'amin abinda zaka fad'a".
Yaseer ya kauda kansa daga barin kallonta cikin tsananin takaici da k'unar zuciya yace mata"mi Fauzeeya tayi miki da zaki jibgeta kamar baiwar gidanku!?".
Jin ya sakota gaba da tambaya yasa hankalinta yayi k'ololuwar tashi fargaba da tsantsar tsoro ne ya bayyana k'arara afuskarta, zuciyarta ta tsinke gabanta ya dinga dukan uku uku b'oye fargabanta tayi tace"itace ta gaya maka na duketa da bakinta!?".
"ko d'aya karki zargi yarinyar mutane samuna akayi har cikin office aka gayamin ina zaune banida masaniyar abinda yake faruwa ".
"idan ba itace ta gaya maka to waye ya gaya maka!?".
"baki isa ki tsiyeni da tambaya ba Nazifa abubuwan da nake samun labarin kina aikatawa sun isheni gaskiya! Haka wancan karon da naje katsina kika bata kashi sannan kika koreta tabar gidan da matsiyacin gudu, ki gyara halayyarki domin bazan tab'a yarda ki kashemin aure ba saboda babu abinda kikeyimin cikin gida daga kici ki kwanta da safe kije shago babu abinda kika iya".
Maganarsa ya soki k'ahon zuciyarta ta mik'e zaune tana harararsa kamar k'wayar idanunta zasu fad'o tace"eh banida wani amfani agidanka saina ci na kwanta tunda ta wanke gabanta ta baka kasha ai dole ka fad'i haka Yaseer, kuma na fahimci cewa babu munafikin dake kai maka gulmata sai shegen matsiyacin maigadinka da babu abinda ya iya sai tsabar munafurci da kashe aure".
"ba wannan maganar na tambayeki ba yanzu dai ina miki kashedi da gargad'i ne akan kada ki sake dukan matata!".
"sannu mai manta kasanni banida kowa daga saman icce aka sassak'oni".
"ke kika fad'i abinki bance ba iyakar abinda nace miki shine kija girmanki ki fita sabgar Fauzeeya! Wannan irin duka da kikayi mata so kike ki kasheta akaimu police station arufe nifa banason kishin hauka da soyayyar k'arya duk abinda nayi miki asanadin sakacinki ne! ".
"malam naji zaka iya tafiya kabarmin d'akina barci nakeson yi!".Tace cikeda matuk'ar tarin damuwa da bak'in cikin gaya mata maganganu da yakeyi son ransa asanadin Fauzeeya.
"ko baki fad'a ba ya zama dole in fita domin ba wani abu zaki bani ba bale kiyimin jan rai da yanga, kuma abinda kike hanamin ki jik'a aruwa kisha idan zaki iya jefa shiyasa ubangiji yayimin fasahar k'ara domin in samu mai matuk'ar k'aunata da sona da gaskiya wadda akowane lokaci zata iya rayuwa dani batare data gujeni ba".Kammala maganarsa keda wuya ya fice daga cikin d'akin ya rufe mata k'ofar d'aki da k'arfi kaji gwarammmm adalilin haka saida ta firgita da lamarin Yaseer! Hak'ik'a taji matuk'ar haushin maganarsa cikin yanayin takaici hawaye suka gangaro mata afuskarta ta sanya hannunta tana sharewa rayuwata a b'ace zuciyarta acunkushe da abubuwan marasa dad'i.
Yaseer ya koma wurin Fauzeeya yayinda har barci ya fara fisgarta yana hawa saman gadon ya jawota ya rungumeta yana shinshinar k'amshin turarenta, jin ta fad'a ajikin mutum yasa ta bud'e idanunta taga shine sannan ta k'ara manne masa domin taji dumin jikinsa addu'o'in neman tsari ya dinga karantawa yana tofe musu jiki, ya jima yana karantawa sannan daga k'arshe ya gama ya k'ara blanket ya lullubesu ciki barci ne ya sacesu babu zato ko tsammaninsu.
**********************
Da k'arfe biyar da rabi na safe Yaseer ya farka daga barci ya tayar da itama atare suka mik'e tsaye suka fad'a cikin bathroom sukayi brush tareda d'auro alwala, suna fitowa Yaseer ya wuce zuwa masallacin dake cikin unguwar ita kuma ta shimfid'a sallaya ta kabbarta sallah,tana gama sallah ta mike tsaye ta linke sallaya ta aje saman kan mirror direct kitchen ta fad'a ta had'a musu breakfast ta d'auko ta jajjera a dinning table ta wuce zuwa room d'inta.
Koda ta shigo ta iske har mijinta Yaseer yayi wanka ya shirya cikin tufafinsa masu k'yau, ya kawo turarurka ya feshe jikinsa dasu Fauzeeya ta sakar masa murmushi tace"har ka shirya yayana gaskiya ka had'u ba k'arya".
Rausayar da kansa yayi yace"Ok ina matuk'ar godiya da yabo".
"ya naga kayi saurin shiryawa?".
Ya dubi agogonsa yace"fita zanyi banason inyi late".
"breakfast d'in fa?".
"zan samu abinda zanci acan".
Shagwab'e fuskarta tayi cikin marairaicewa tace"ka daure kaci ko kadan ne banason yunwa tayi maka illah".Yaseer ya lakaci kumatunta yace"yunwa bazata tab'a yimin illah saboda inada kud'i kinga kuwa yadda za'ayi inbar kaina da yunwa".
Fauzeeya ta jijjiga kanta cikin gamsuwa da maganarsa tace"ba komai muje inyi maka rakiya har wajen motar".
Bai sake magana ba ta d'auki briefcase d'insa ta rataya a kafad'arta sannan suka jera atare hannunsu mak'ale da juna, suna fitowa a d'aki suka iso cikin parlour zaune suka ga Nazifa tayi tagumi da hannunta abubuwan duniya duk sun taru sun cunkushe mata azuciya kallo d'aya zakayi mata ka gano bata cikin nishad'i ko walwala ga bak'in kishin mijinta dayake azalzalar zuciyarta, gashi kuma tana ji tana gani an amshe mata asanadiyyar sakacinta ta tabbatar tunda har ya fara yi mata fad'a adalilin Fauzeeya wata rana ma zai iya korarta asanadiyyarta saboda haka ta k'udurta azuciyarta wannan karon baza tayi mata da sauk'i so takeyi ayita ta k'are Fauzeeya tabar mata gida ta wala ta b'ararraje daga ita sai yaranta.
Sak'a da warwara ta dingayi azuciyarta domin so take burinta ya cika Fauzeeya tabar mata mijinta ta huta da takaicin duniya da k'unci.
Ta gabanta suka wuce komai batace musu har suka k'arasa parking lot Yaseer ya sanya key ya bud'e k'ofar motarsa ya shiga ya zauna kallonta kawai yakeyi da murmushi, ganin ya shiga yasa ta d'an russuna cikin ladabi ta mik'a masa briefcase ya amsa, kallonsa tayi cikin sanyin jiki da tsantsar shagwab'a tace"yayana ubangiji ya kiyaye hanya ya baka abinda kaje nema".
Cikin jin dad'in addu'arta ya lumshe idanunsa cikin wani irin yanayi yace"Amin my life mi kike buk'ata in siyo miki".
"bana buk'atar komai burina shine ka dawo cikin k'oshin lafiya".
"ubangiji ya k'addara matata".
"Amin dear".
Yaseer ya numfasa yace"zan wuce ko kinada wata magana?".Fauzeeya tayi tunani na mintuna kadan ta dubesa tace"eh dama dama....... ".Ya katse mata hanzari yana tsura mata fararen idanunsa masu narkar da zuciyarta yace"dama mi? Nifa mijinki babu abinda zaki b'oyemin nima babu abinda zan b'oye miki saboda haka ki fad'amin abinda yake zuciyarki ".
Yakune fuskarta tayi tace"yaya batun komawa school nakeson in tunatar maka".
Murmushin da iyakarsa a leb'en bakinsa yayi yace"ba mantawa nayi ba karki damu idan lokacin rubuta waec da neco yayi zansa arubuta miki amma batun zuwa makaranta gaba babushi".
"saboda mi yaya? ".
"saboda bana ra'ayin zuwanki gaba kuma ina matuk'ar tsoron kije ki had'u da k'awayen banza su hure miki kunne! "."Kana nufi kenan ita Aunty Nazifa k'awayen banza ne masu horewa mace kunne akan kada tabi umurnin mijinta sune suka hure mata kunne? "."Babu shakka haka nake zato wannan bashida ance idan baki taka-tsan-tsan da k'awayen zamani ba zasu iya kaiki su baro abanza! Yanzu dai ki bari idan na dawo zamu tattauna cikin natsuwa"."Shikenan saika dawo ".Tana kammala maganarta ta rufe masa k'ofar motarsa ta juya ta koma parlour, k'arar ficewarsa taji alamar ya fice daga cikin gidan.
Ayadda tabar Nazifa hakan tazo ta sameta zuciyarta kamar zata buga akan zafi da bak'in ciki ta gabanta ta gifto zata wuce kenan! Nazifa ta mik'e tsaye zumbur ta chapko gashin kanta Fauzeeya taji wani irin rikitaccen zafi ya ziyarceta alokaci d'aya wutsil wutsil takeyi tana neman kufcewa amma ina ta kasa saboda k'arfi ba guda ba, marairaice fuskarta tayi ta fara yi mata magiya tana rok'onta akan tayi hak'uri cikin matuk'ar rad'ad'in ciwo tace"kiyimin rai Aunty ki sakarmin gashi!".
Asuk'e da tsantsar hasala sosai tace"yimin shiru munafuka saikin gayamin irin makirci da k'ulle k'ullen da kikeyimin awurin mijinta tunda ya aureki ban huta domin ya tsaneni asanadiyyarki, kinzo kin haddasa fitina da rashin jituwa atsakanina dashi ko ki gayamin munafurce munafurcen da kikeyi dashi idan yana d'akinki ko yanzu in halakaki! ".
"sakarmin gashi zan gaya miki ".Tace yayinda ruwan hawayen wuya ke shatata afuskarta.
"idan baki gayamin ba bazan tab'a sakinki ba saidai mu tabbata ahaka yak'i zamu gwazawa nida ke! ".
"to d'an sassautamin ta yadda zanji dad'in sanar miki".Nazifa dolenta ta sassauta rik'e mata gashi da tayi domin tanason ta fahimci itace ta gaya masa koba itace ba.
Fauzeeya ta furta cewa"maganar gaskiya bansan ko waye ya gaya masa yadai ga fatata tayi jajir da kwancin bulala ajikina shine ya tambayeni ta yaya hakan ya faru nace masa chanjin yanayi ne......... .".Ta bata labarin duk irin tattaunawarsu daga farko har k'arshe babu abinda ta b'oye mata Nazifa tsura mata idanu tayi domin ta gano gaskiyar abinda ta fad'a ta hango komai cikin k'wayar idanunta.................
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 38*
Alokacin ne Nazifa ta sakar mata gashi atake cikin matuk'ar gamsuwa da kalamanta domin tasan bata iya k'arya ko kad'an arayuwarta ba tun tana k'arama har zuwa girmanta, kallonta tayi tace"na yarda da maganarki amma wannan ba shine zai baki damar da zakiyimin abinda kika gadama ba nasan bak'in munafikin daya gaya masa zanyi maganinsa".Fauzeeya ta sunkuyar da kanta k'asa domin ba k'aramin tsoronta takeji ba tace"ba matsala Aunty bazaki tab'a samuna inayi miki munafurci ba".Tana k'arashe maganarta taja k'afafunta ta nufi wurin dinning table ta zauna tana breakfast zuciyarta cunkushe da rashin dad'in zuciya da gushewar farin ciki.
Itama Nazifa mik'ewa tayi ta fad'a cikin d'akinta ta shirya cikin suturarta mai tsada dayake tayi wankanta da safe, handbag ta rataya a kafad'arta sannan ta kawo turare mai k'amshi ta feshe jikinta dashi ta fito daga ciki tareda rufe k'ofar d'akin ta nufi parking lot.
*********************
Hajiya Ramlat ce k'awarta ta kawo mata ziyarar bazata suna maganarsu cikin yarda da amintaka, k'awarta mai suna hajiya Kaltume ta dubeta tace"ke kuwa hajiya ina labarin k'awarki hajiya Sadiya naga kwata kwata kin daina yimin zancenta?".
Bintsire baki tayi zuciyarta cunkushe da d'acin rai tace"keee Kaltume munyi fad'a kaca-kaca nida ita".
Firfito da idanunta awaje tayi tace"keee Ramlat miye ya had'aku fad'a haka wanda zai zamo sanadiyyar tarwatsewar k'awancenku?".
"asanadiyyar shegen d'anta mana data sagartashi baya ganin mutuncin kowa sai ita taya zai samu Nazifa yayi mata mugun duka tamkar ya samu jakar gidansu kinsan wannan abin bayada dad'i adinga dukar maka yarinya gata ita kad'ai ubangiji ya bani".
Hajiya Kaltume ta girgiza kanta alamar gamsuwa tace"eh gaskiya babu dad'i amma hak'uri zakuyi kuna kai zuciyarku nesa domin idan har aka fara tara iyali aure sai anyi hak'uri da juriya sannan yake k'arko".
Ba haka taso Kaltume ta fad'a so tayi ta shiga cikinta suyita tsinewa Yaseer amma gudun kada ta fahimci wani abu yasa tace"haka ne shiyasa kullum nake mata nasihar da ta dinga hak'uri rayuwar duniyar guda nawa take?".
"lallai kin kyauta Ramlat ki cigaba da lallashinta da tank'warata ta zamo mace mai matuk'ar hak'uri da k'yautatawa mijinta, nizan wuce zuwa gida mutane suna can suna jirana".
"da yardar Allah zanyi yadda kikace tun yanzu bazaki bari agama abinci ba".
Hajiya Kaltume ta tashi tsaye tace"a'a Alhmdulillahi na k'oshi".
"shikenan k'awata".
Itama tsaye ta mik'e tsaye domin ta rakata har bakin k'ofar get atare suka jera suna firarsu cikin fara'a da kwanciyar hankali har suka bakin get, hajiya Ramlat taja tayi tsaye tace"ubangiji ya kiyaye hanya sai wata rana"."Amin".Hajiya Kaltume zata wuce kenan sukayi kicib'is da Nazifa abakin get ta russuna ta gaidata amsa mata tayi cikin sakin fuska sannan ta shige cikin motarta ta k'ara gaba.
Dayake hajiya Ramlat taga Nazifa shiyasa ta tsaya harta iso wurinta suka rankaya suka nufi cikin parlour suka zazzauna, hajiya Ramlat sai kallonta takeyi cikin nazari tace"baby ya akayi ne ko wata matsalar ne ta sake kunno kai?".
Zumb'ura baki tayi ta b'ata fuska cikin matuk'ar damuwa tace"Ummu ya dace kiyi wani abu idan ba haka Yaseer yana gab da sakina!".
Zuciyarta ta girgiza hankalinta ya d'unguma tace"akan wane dalili zai sakeki baby ko kuna fad'a cikin gidan ne keda shegiyar yarinyar nan?".
Nazifa ta k'ak'aro hawayen k'arya da makirci har wani irin logayewa takeyi tana b'ata fuska tace"haka kawai ina zaune cikin d'akina ina barci akan tsantsar rashin mutunci irin nasa saida yazo ya tayardani abarci ya balbaleni da masifa babu zato ko tsammani Ummu, na gaji kullum k'unsamin bak'in ciki da d'acin rai kawai yakeyi akan ya samu sabuwar jini yana cinta yadda yakeso, ki diba ki gani ko kallon arziki bayayimin bale insa ran maganar kirki zata had'amu idan baso kike ya kasheni ba ya dace ayiwa Fauzeeya mai k'ank'at tabarmin gidan mijina".
Hajiya Ramlat hankalinta ya k'ara tashi tsagwaron takaici da zullumi ne ya bayyana k'arara afuskarta cikin mutuwar jiki da lallashi tace"yi hak'uri bari zanyiwa Baura magana wannan karon kam ina tabbatar miki saitabar miki gidan mijinki tunda ba tare aka haifesu ba! ".
"kenan in kwantar da hankalina Ummi?".
"Eh dama ki sanyawa zuciyarki dangana zakiga irin abubuwan da zasu biyo baya".
Nazifa ta tashi zaune tace"naji amma please kada abin ya d'auki tsawon lokaci".
"ungo nan baby kin cika gaggawa fa shiyasa ban cikason ingaya miki zan saka ayi miki abu ba".
"sorry Ummu na daina".
"OK zaki iya tafiya shago ubangiji ya bada kasuwa".
"Amin".Gama maganarta keda wuya taja k'afafunta tabar cikin gidan ta nufi hanyar zuwa shago.
**********************
Agidan Haidar Safiya ce na hango zaune tana yiwa mijinta wankin tufafinsa masu datti yayinda shi kuma yake zaune gab da ita yana jifarta da kallon soyayya, 'ya'yansu suna zaune suna wasar k'asa duk sunyi burum burum adalilin wasa da k'asa shiyasa take sauri ta gama ta sakeyi musu wanka.
Haidar yana shan tea ahankali yace"my yau baza kije shago bane?".
Waigowa tayi tace"mi ka gani sweet husband?".
"saboda naga sai wanki kikeyi gashi lokaci yana tafiya".
Cikin salo ta fad'ad'a fuskarta da murmushi tace"zuwa shago bazai tab'a hana in k'yautata maka mijina domin aljannata nake nema a k'ark'ashinka".
"da yardar Allah zaki samu aljanna my Sofeeya idan namiji ke d'agewa mace k'afa ta shiga aljanna ni tawa k'afar a d'age take".
Murmusawa tayi cikin farin ciki tace"ina godiya Abbansu Idris".
Shitttt kawai yayi mata alamar tayi shiru cigaba da wanke tufafin tayi harta gama ta shanya akan igiyar wanki, anan waje tayiwasu Idris wanka ta shafe musu jiki da manshafi kayansu ta d'auko ta sanya musu itama ta shiga cikin bathroom tayi wanka, ahanzarce ta zura tufafinta powder kawai ta shafa afuskarta saboda tayi late sosai handbag d'inta ta rataya a kafad'arta sannan ta iso wurin Haidar tayi masa kiss agoshi tace"zan wuce maigidana".
"fatar Alkhairi ubangiji ya kaiki lafiya".
"amin".Wucewarta tayi daga cikin gidan ta shige motarta ta kama hanyar zuwa shago.
**********************
Bayan Yaseer ya fita Fauzeeya ta sake shek'a wankanta ta kawo matsattsun tufafinta ta saka wad'anda suka bayyana surar jikinta, kusan boob's d'inta manya manya gasunan awaje ana