Showing 30001 words to 33000 words out of 87802 words
ya fice daga cikin gidan ba sai daga baya, huci tayi mai tattare da bak'in cikin rayuwa tace"hmmmm Labaran ya rasa abinda zaiyimin sai gorin haihuwa! Tabbas baisan wa cece ni ba amma da sannu zan nuna masa ainahin kalata! ".Tana k'arasa maganarta ta mik'e tsaye zumbur ta shige cikin d'akinta domin ta kwanta ta huta.
**********************
Ashagonsu Safiya ne na hango zaune yayinda Nazifa ta aza hannunta saman fuskarta tayi tagumi cikin yanayin fargaba da zullumi, alokacin ne Safiya ta lura da yanayinta ya chanza cikin natsuwa tace"lafiya kikayi tagumi Nazifa miye matsalarki arayuwa?".
Nazifa tayi rau rau da idanu kwallar zallar takaici ne suka cicciko mata cikin idanunta tace"kedai bari ina cikin tsaka mai wuya Yaseer ya kusa dawowa".
Safiya ta yamutsa fuskarta cikin nuna halin ko inkula tace"to idan ya kusa dawowa saimi zai faru kedai akwaiki da sanyawa zuciya damuwa?".
Ganin Safiya bata fahimceta ba yasa ta saukar da numfashi tace"baki fahimci inda na dosa ba bari yanzu in fahimtar dake kina jina kinsan na kori Fauzeeya ta koma gidan kakarta shiyasa nake fargabar idan ya dawo yadda zamu kwashe dashi! ".
"ohhh na tuna haka ne fa abinda zakice masa kawai idan ya tambayi ina Fauzeeya take? Kice masa sata tayi miki shiyasa kika koreta ta koma gidan ubanta Labaran!".
Numfashi ta saukar mai tattare da yanayin damuwa tace"auuu k'awata kina tunanin zai yarda da wannan maganar kuwa!? ".
Safiya ta bintsire baki tace"idan bai yarda ba mana ki k'yaleshi yaje yayi duk abinda zaiyi! In yaso ya koreki gidansa akan kin kori Fauzeeya".
"yana ma fara korana akan wata banza wai ita Fauzeeya wannan maganar bazata tab'a faruwa ba! ".
Safiya ta gyad'a kanta alamar gamsuwa tace"kedai bari inda kike tsammanin cin amana da zaluncin namiji ya wuce nan, yanzu dai kisa mana lokaci muje har gidan kakarta muci gundunbulin buro ubanta! Saboda na lura idan baki tashi tsaye ba Fauzeeya ta shigo cikin gidan Yaseer zata iya fitar dake ko ta halin tsiya daga cikin gidansa! ".
Nazifa tayi saurin kallonta cikin fad'uwar gaba da yanayin firgici tace"haba ki daina yimin wannan muguwar fata mana ni kaina na rasa inda zan tsoma zuciyata inji sanyi, wallahi na tsani kishiya arayuwata akanta zan iya kashe rai gaba d'aya!".
"hak'uri zakiyi tunda babu mafita sai ya aureta".
"bazan tab'a hak'ura ba Safiya har sai naga abinda ya turewa buzu nad'i ko ni ko ita sai anga wadda zata russunawa 'yar uwarta".
Safiya ta dafa kafad'arta cikin matsananciyar damuwa tace"bakida damuwa matuk'ar muna tare kedai ki kwantar da hankalinki yanzu dai in tambayeki hajiyarki taje gidansu Yaseer da Fauzeeya ta ciwa iyayensu mutunci sannan yaushe ne ranar da zai dawo daga katsina? ".
Nazifa ta dafe goshinta tace"ohh na manta ban gaya miki ba Ummuna taje gidansu Yaseer da Fauzeeya ta ciwa iyayensu mutunci da tozartasu kedai abin babu dad'in ji ko saurare saura kwana uku Yaseer ya dawo shiyasa kikaga zuciyata ta tsinke gabana yana dukan uku uku".
"ki daina damar da kanki akan Yaseer ya kusa dawowa domin gudun kada wani mugun ciwo ya kamaki abanza, kedai ki zuba masa idanu kiyi kallo babu boka babu malami amma ko don tsabar makirci da tuggu sai tabar gidansa da k'afafunta dole ba domin son ranta ba".
Nazifa ta k'yalk'yale da dariyar murna tace"kayyy Aminiyata har kinsa damuwar dake cikin zuciyata ta gushe saboda yadda kika sanyani cikin farin ciki".
"bakima fara farin ciki ba sai nan gaba idan matsiyaciyar yarinyar nan ta shigo saita tozarta da walak'anta a idanun duniya! ".
"haba dai k'awata banda cika baki ba fa".
Safiya tayi murmushinta mai k'yau tace"bana cika baki Nazifa lokaci yana nan tafe zan koya miki tuggu da makirci iri iri wanda zaiyi sanadiyyar tarwatsewar farin cikinta da sanyata cikin uk'ubar rayuwa".
"shiyasa nake k'ara sonki Safiya saboda rayuwarki tayi batada matsala".
"nima ina sonki Nazifa saboda kin nunamin tsantsar soyayyar gaskiya da kulawa".
"zaman tare ne kinfi k'arfin komai awajena".
**********************
*BAYAN KWANA UKU*
Da safe misalin k'arfe goma daidai Yaseer ya dawo daga katsina yana dawowa ya iske babu kowa, sabodasu Sameer sun tafi school yayinda Nazifa ta nufi shagonsu.
Yaseer ya kishingid'a saman cushion yana lumshe fararen idanunsa cikin matuk'ar gajiyar hanya, jikinsa gaba d'aya ciwo yakeyi masa numfashi kawai yake fitarwa akan tsantsar galabaita, ya dad'e zaune can ya mik'e tsaye yana waige waige ko zai hango inda Fauzeeya take amma ina shiru bakajin motsin kowa tsit kamar sansanin yak'i,direct room d'in dayake mallakin Fauzeeya ya nufa saboda da k'aunarta yake kwana yake tashi aduk inda yaje aduniya, yana iza k'ofar d'akin yaga wayam babu kowa d'akin kuma duk yayi datti da k'ura alamun an daina shararsa da mopping d'in floor, tsantsar mamaki da fargaba ne ya bayyana k'arara afuskar Yaseer cikin sauri ya shiga cikin tsakiyar filin room d'in, kaya ne ya gani ayamutse gasunan birjik ako'ina haka kawai yaji tsantsar tsoro da d'imaucewa ya ziyarci zuciyarsa!.
Cikin mutuwar jiki ya isa wurin gadon ya zauna jugum yana mamakin ina Fauzeeya taje ne data bari har d'akin yayi datti haka, anya babu abinda yake faruwa cikin gidan nan bayan wucewata kardai ace wani mugun abu ya samu ya sameta? Dako na shiga uku ni Yaseer idan har Nazifa ta koremin budurwa!.
Haka dai ya cigaba da sak'a da warwara cikin zuciyarsa daga k'arshe ya mik'e tsaye ya jawo k'ofar d'akin ya nufi hanyar room d'insa, zazzafan k'aunar Fauzeeya sai nuk'urk'usar zuciyarsa takeyi soyayyarta sai k'ara kwaranya yakeyi cikin jini da gangar jikinsa, direct ya cire tufafinsa ya d'aura towel ajiki ko zaiji sanyi azuciyarsa.
Wanka yakeyi yana tunanin duk wasu movement nasu shida Fauzeeyarsa alokacin da suke rayuwar farin cikinsu tareda nunawa junansu so da tsantsar soyayyar gaskiya, ya jima yana gurje ko'ina ajikinsa sannan daga k'arshe ya fito d'aure da towel ajikinsa wurin wardrobe ya nufa ya d'auko lotion ya fara shafawa, zuciyarsa cunkushe da tunanin Fauzeeya dak'yar ya samu ya kauda tunani aransa ya shirya cikin shadda ash colour turare ya feshe jikinsa dashi, ya d'auki key d'in motarsa ya fice daga cikin room d'in ya nufi parking lot.
**********************
Hajiya Sadiya tana zaune saman cushion yayinda 'yar aikinta Bara'atu ke yanke mata akaifar hannu da k'afa tana gyarawa, hajiya sai lumshe fararen idanunta takeyi tana gyangyad'i alamar gyaran akaifar yana yi mata dad'i sosai, Bara'atu sai kallonta takeyi tana dariya tace"hajiya barci kikeyi kuma".
"barni in d'an runtsa Bara'atu wallahi yau ji nakeyi jikina kamar ba nawa ba akan yadda k'afafuna sukeyimin ciwo".
"ayyah hajiya ubangiji ya sawwak'a amma ina maganin da yah Yaseer yake siyo miki ki dinga shafawa?".
"kedai jiya jiya ya k'are zuwa anjima idan zaki tafi gida ki tunamin in baki kud'i ki siyomin".
"to babu damuwa kwalin maganin yana kusa dai?".
"eh yana kusa ai idan na kammala shan magani bana saurin yassuwa kwalin maganin".
"bakida matsala hajiya anji......... ".Sallamar Yaseer ne ya dakatar da ita wurin k'arasa maganarta hajiya Sadiya ta amsawa tilon d'anta cikin tsantsar farin cikin dawowarsa lafiya gida, yana k'arasowa wurin mahaifiyarsa ya russuna k'asa ya gaidata ta amsa masa cikin tsananin murna da k'aunar yaronta.
Yaseer ya tashi tsaye ya zauna gab da mahaifiyarsa yayinda Bara'atu ta gaisheshi ya amsa mata cikin fara'a sannan hajiya Sadiya ta bata kud'in da zata siyo mata magani tareda umurtarta da taje saman kan gado ta d'auko kwalin maganin, Bara'atu ta girgiza kanta alamar to ta fad'a cikin d'akin hajiya Sadiya.
Murmushi ta sakar masa tace"ya hanya ina fatar anje cikin nasara? ".
Yaseer ya noce kansa k'asa yace"komai yana tafiya cikin nasara da sa'a Ummi".
"Masha Allah haka akeson ji ubangiji ya k'ara d'aukaka da taimakawa arayuwa".
"amin amin Ummi".Cewar Yaseer.
Shiru ne ya biyo baya na wani lokaci Yaseer yana son ya tambayi mahaifiyarsa ina Fauzeeya amma bakinsa yayi masa nauyi yana jin kunyar tambayarta, ita kuma tuni ta harbo jirginsa akwai maganar da yakeson yi mata ganin ya kasa cewa uffan yasa hajiya Sadiya ta musk'uta tace"ya naga bakinka yana motsi kamar kanason furta wata magana amma kayi shiru? ".
Yaseer ya sosa k'eyarsa cikin kunya yace"dama inason in tambayeki ne ina Fauzeeya taje ne na dawo cikin gidan nan ban taras da kowa ba".
Hajiya Sadiya tayi murmushin mai tattare da bak'in ciki aranta tace"kana nufin Fauzeeyar bata gidanka baka ganta da idanunka ba!? ".
"Allah Ummi bata nan ban ganeta ba".
Hajiya Sadiya ta jijjiga kanta alamar gamsuwa tace"to ka bari har ayi kwana biyu mu gani idan bata dawo gidan ba kenan tunanin da nakeyi ya tabbata ".
Yaseer ya waigo da sauri ya kalli fuskar hajiya Sadiya cikin matuk'ar mamakin zancenta yace"kamar ya kenan Ummi?".
"ka daina gaggawa zan gaya maka abinda ya faru bayan tafiyarka idan hasashena ya tabbata".
"shikenan Ummi Allah yasa inji maganar alkhairi".
"amin ya rabbi".Inji hajiya Sadiya cikin tunani.
Firarsu suka cigaba dayi kamar zasu lashe juna akan tsantsar so da k'auna kunsan ance tsakanin uwa da d'a sai Allah, yah Yaseer anan gidan yaci abinci ya yini shine bai koma gidansa ba sai bayan sallar isha'i .
Yana komawa gida ya iske Nazifa tayi wanka har ta kwanta saman gadonta yayinda su Sameer suke kwance agefenta, Yaseer ya shigo cikin room d'in atsanake ya isa har wurinta jin takun tafiyar mutum yasa ta d'ago idanunta ta kallesa da murmushi k'unshe afuskarta tace"daddyn Sameer har ka dawo gida sannu da zuwa?".
K'asa k'asa ya amsa mata kamar bayaso yace"yauwa ina fatar mun iskeku lafiya".
"lafiya k'alau ka iskemu".
Tsaye yayi yana tsurawa fuskarta kallo na tsawon lokaci can yaja doguwar ajiyar zuciya cikin sanyin murya da lalama yace mata"Nazeefa".
Nazifa ta tashi zaune tace"na'am daddyn Sameer".
"ina Fauzeeya taje ne naji banji motsinta ba?".Yace cikin yanayin fara'a.
D'immmmm taji gabanta ya fad'i tsantsar tsoro da tashin hankali ne ya ziyarci sassan jikinta da k'wak'walwarta gudun kada ya fahimci batada gaskiya, dole yasa ta tattaro dauriya da natsuwa ta sanya azuciyarta cikin sakin fuska ta langwab'e kanta tace"ayyah daddyn Sameer ta tafi gidansu ne asanadiyyar kakarta batada lafiya saboda tayi jinyarta shiyasa ta koma gidan kakarta".Yaseer ba domin ya amince da maganarta ba yace"Allah ya bata lafiya "."Amin daddyn Sameer".Bai sake ce mata komai ba yaja k'afafunsa ya fice daga cikin d'akinta tareda ja mata k'ofar ya rufe..............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 19*
Yana fitowa daga cikin d'akin Nazifa taja mugun tsoki mtsssssss! Tace"aikin banza yiwa karen mak'wabta wanka ji yadda yake wani tambayata ina Fauzeeya saikace anyi auren nasu! Ya kamata ki d'auki kwakkwaran mataki akan Fauzeeya idan baso nake ta shigo ta fitar dani ko ta k'arfin tsiya agidan mijina ba".Tana rufe bakinta ta dinga sak'a da warwara azuciyarta domin ganin ta b'ullowa al'amarin cikin sauk'i amma ina ta kasa hango wata mafita cikin wannan sark'ark'iyar al'amari,kwantawa tayi ta rufe jikinta da blanket bata jima ba nannauyar barci ya kwasheta batare data ankara ba.
**********************
Fauzeeya ce duk'e tana sharar tsakar gida yayinda Iya Kulu ke zaune saman tabarma tana shan kunu da k'osai ,alokacin ne Iya Kulu ta dubi fuskar Fauzeeya tace"aje tsintsinyar kizo kisha kunu".
"gaskiya na k'oshi bana shan kunu".
Iya Kulu ta rike baki tace"ke jimin d'iyar zamani idan bak'ya shan kunu mi zakici so kike ki zauna da yunwa?".
Zumb'ura baki tayi cikin sagarci tace"maganar gaskiya nina gaji da shan kunu idan ke Iya bak'ya gajiya ni ina gajiya".
"to naji idan kin k'arasa sharar kizo ki amshi d'ari biyu ki siyo abinda zakiyi karin kumallo kinsan ko zama da yunwa babbar illah ne".
"to Iyata agaskiya kinyi bakida matsala".Alokacin ne ta k'arasa sharar ta tule wuri d'aya ta kwashe takai bola.
Murmushi Iya Kulu ta saki tace"kina cewa nayi ai yanzu wallahi ki kiyayi yunwa Fauzeeya so kike koda za'a kaiki gidan miji kin koma kamar k'warangwal akan rashin k'iba".
Fauzeeya ta d'aga muryarta da k'arfi tace"bazan ma koma hakan ba Iya".Tana zubar da sharar ta dawo wurin Iya Kulu ta zauna tana shagwab'e fuskarta cikin b'atanci tace"gani Iya na gama".
"to sannunki d'iyar albarka".
"uhmmmm Iyata".
"shiga cikin d'aki ki d'aga k'ark'ashin filo kina ganin d'ari biyu ki d'auko ki sayi abinda kike bukata".
Fauzeeya ta mike tsaye ta shige cikin d'akin ta d'auko d'ari biyu d'in ta fito sanye da hijabinta tace"zan fita Iya".
"sai kin dawo Fauzeeya ya batun tufafinki dake gidan Yaseer yaushe zakije ki kwaso kayanki?".
Fauzeeya ta rausayar da kanta tana wuk'i wuk'i da idanunta kamar tsohuwar b'arauniya tsantsar fargaba da tsinkewar zuciya ne ya bayyana k'arara afuskarta cikin sanyin jiki tace"nifa bazan iya shiga cikin gidan nan ba har sai yah Yaseer ya dawo daga katsina in sanyashi ya kawomin tufafina da kansa, kinsan ko wancan karon dak'yar na tsira ahannunta da tuni ta nakkasani abanza ".
Iya Kulu ta musk'uta tace"haka ne gaskiya Fauzeeya ki dinga taka-tsan-tsan da kanki saboda wad'annan mutanen basa tsoron Allah".
Fauzeeya ta gyada kanta cikin yanayin damuwa tace"insha Allahu zan kiyaye".
"yayi k'yau".Inji Iya Kulu.
Yayinda Fauzeeya ta fice daga cikin gidan ta nufi hanyar zuwa shagon Alu tana tafiya gefen hanya sannu ahankali, wayarta tayi ruri alamar tana neman agaji receiving call d'in Yaseer tayi ta kara wayar akunnenta tace"Assalamu Alaikah".
"Wa'alaikis salam ya sanyin zuciyata".
Murmushi k'unshe afuskarta tace"yah Yaseer kana lafiya ya katsina".
"lafiya k'alau aina dawo daga katsina".
"haba dai yaushe ka dawo?".
"jiya na dawo da safe misalin k'arfe goma daidai".
Fauzeeya ta zumb'ura bakinta cikin sagarci kamar yana ganinta tace"shine baka sanarmin tun jiya ba sai yau gaskiya nayi fushi dakai".
"afuwan gimbiyata ayi mini hak'uri ya jikin Iya ina fatar taji sauk'i?".
Cikin mamakin kalamansa Fauzeeya ta firfito da idanunta awaje tace"kai yah Yaseer waye ya gaya maka Iya batada lafiya? To lafiyarta k'alau babu abinda ya sameta".
Yaseer yayi yake yace"babu wanda ya gayamin nayi zaton batada lafiya ne".
Numfashi ta sauke tace"a'a k'alau take".
"OK yaushe zaki dawo gidana inzo in d'aukeki?".
"a'a bazan dawo cikin gidanka ba har sai munyi aure abinda kawai nake buk'ata dakai shine ka kawomin tufafina dake cikin room d'ina".
"yaushe zan kawo miki?".
"duk ranar da kakeda lokaci yayana".
"to da yardar Allah gobe zanzo in kawo miki tunda bazaki dawo gidana ba ko akwai abinda Nazifa tayi miki ne mara dad'i?".
Tayi sauri tace"babu abinda tayimin ganin nayi na kusa shigowa cikin gidan amatsayin matarka shiyasa naga ya dace in d'auke k'afafuna har zuwa wani lokaci idan muka zamo miji da mata".
"kinyi tunani mai k'yau duk abinda kikayi daidai ne my Fauzee".
"ko?".
"eh mana".
"to sai anjima yanzu akwai inda zanje".
"ba damuwa mu jima lafiya".Yana kai k'arshen maganarsa ya katse wayar yayinda Fauzeeya ta dinga murmushin farin cikin dawowar masoyinta k'arasawa shagon Alu tayi ta siyo indomie guda biyu, sanya mata yayi cikin bak'ar leda ta amsa ta nufi hanyar zuwa gida.
*********************
Inna Munari ce naga tana guntsire tuwo guntu -guntu tana sanyawa cikin tire tana gama guncewa saiga sallamar baba Labaran ya dawo daga kasuwa ayunwace, ganinsa yasa ta juyo tana masa kallon wawa shi kuma yunwa sai nuk'urk'usar cikinsa takeyi jikinsa har mazari yakeyi cikin yanayin yunwa yace"Munari na shigo babu magana babu sannu da zuwa ina abincina yake?".
Inna Munari ta rik'e kwankwasonta cikin walak'antaccen kallo mai tattare da raini da fitsara tace"na d'auka bazaka dawo ba shiyasa na gunce tuwon na shanya arana saboda in samu k'anzon".
Baba Labaran ya kad'u da razana da jin kalamanta cikin matuk'ar b'acin rai da tafasar zuciya yace"kin gungunce tuwon Munari yanzu saboda Allah abincin nawa kika shanya arana saboda baki gaji tarbiya ba!? ".
"eh ban gaji tarbiya ba!".
Baba Labaran ya harzuk'a zuciyarsa ta kawo awuya kunsan ance mai jin yunwa yafi kowa saurin fushi, idanunsa har rufewa sukeyi akan tsabar masifar dake kwance cikinsu yace"wato na fahimci matar nan hankali bai isheki ba to yanzun nan zan nuna miki na fiki rashin mutunci! ".
"duk abinda zakayi kazo kayi ba tsoronka nak............".Bai bari ta k'arasa maganarta yasa k'afafunsa ya kwasheta ta fad'i rikcam k'asa kanta ya bugi dutsi kaji gwaffff! Tsantsar zafi da rad'ad'i ne ya ziyarci sassan jikinta da k'wak'walwarta ji takeyi kamar ba jikinta bane saboda ta fita cikin hayyacinta.
Ta jima kwance k'asa cikin matsanancin hali yayinda baba Labaran ya dubeta idanunsa jajir dasu yace"ki sake yimin rashin kunya kiga irin walak'anci da k'ask'ancin da zanyi miki cikin gidan nan da ba yanzu bane, ayanzu idan kikayimin rashin mutunci ina tabbatar miki ko kare saiya fiki daraja acikin gidan nan! ".Yana rufe bakinsa yaja k'afafunsa yabar cikin gidan domin yaje ya samu abincin dazai sakawa cikinsa kada yunwa ta kasheshi! ".
Yana wucewa dak'yar Inna Munari take motsa yatsunta hawaye ne suke kwaranya yab'e yab'e saman fuskarta yayinda wani irin sihirtaccen d'aci da bak'in ciki yake cunkushe cikin zuciyarta, dak'yar da sud'in goshi ta tashi zaune yayinda inda ta bugu adutsi ya d'an kumbura cikin yanayin bak'in ciki tace"asirina ya tonu ni Maimuna yanzu irin wannan cin mutunci Labaran ya fara yimin! Ina zan saka rayuwata tabbas idan banyi asannu ba wata rana sai yayimin shegen dukan da bana iya tashi! ".Tana rufe bakinta ta tashi tsaye dak'yar cikin rad'ad'i da zafin ciwo tana takawa sannu sannu har ta fad'a cikin d'akinta ta kwanta saman katifarta hawaye sai sintiri sukeyi afuskarta.
___________________
Washegari da safe Yaseer ya shiga cikin d'akin da kayan Fauzeeya suke ya fara sanyasu cikin akwati yana tsarasu, can Nazifa ta shigo cikin room d'in tana kallon yadda yake saka kayan cikin akwati, tsaye tayi k'yam tana k'are masa kallo tsab tareda mamakin k'arfin hali irin na Yaseer hannunta ta rungume a k'irjinta, Yaseer yaji motsin shigowarta cikin d'akin