Showing 72001 words to 75000 words out of 87802 words
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 42*
Tun daga lokacin da hajiya Ramlat ta haifi Nazifa ta d'auki soyayyar duniya ta d'ora akanta batason ko k'uda ya tabata adalilin k'aunar da takeyi mata, shidai uban yana sonta amma hakan baisa ya bayyana mata k'arara ba domin gudun tab'arb'arewar tarbiyarta, alokacin data fara tasawa ta fahimci uwar duk abinda takeso shi takeyi mata sannan taga tayi wani abu ba daidai ba bata iya kwab'arta saboda son Nazifa ya riga ya rufe mata idanu.
Haka ta taso asangarce shagwab'ab'b'iya bata iya komai ba dangane da ayyukan gida ko sarrafa abinci saidai taci ta kwanta tayi barci harda minshari 😁,wannan dalilin ne yasa Alhaji Mu'azu yayiwa hajiya Ramlat magana akan ta rage nunawa Nazifa so amma tayi biris da maganarsa, cikin haka ne ta zamo bata ganin kan kowa da gashi saboda alfahari da tutiyan ita d'in d'iyar mai kud'i ce ta sanya irin suturar da takeso ta shiga irin motar da take ra'ayi komai tsadarta.
Haka dai rayuwar gidan ta cigaba da gudana har Yaseer yakai minzalin aure farat d'aya yaji babu wadda yakeso da k'auna sai Nazifa, baiyi nauyin baki ba ya samu mahaifinsa ya gaya masa abinda ake ciki hak'ik'a Alhaji Taheer yayi matuk'ar farin ciki da jin kalamansa, nan ya gayawa hajiya Sadiya yaronta yanason Nazifa da aure har azuciyarta bata wani ji dad'i ba saboda Nazifa ba wani cikakkiyar tarbiya ne da ita ba amma gudun kada ta rushe farin cikin d'anta yasa ta nuna murnarta azahiri, daga nan Alhaji Taheer bai zarce ko'ina ba sai gidan amininsa Alhaji Mu'azu yana isowa tsakiyar parlourn Alhaji Mu'azu ya taso ya tarbeshi suka rungume junansu daga baya ya jaye jikinsa anashi yasa hannunsa sukayi masauki saman cushion, saida suka gaggaisa sannan Abin Yaseer ya koro masa bayanin duk abinda ya kawosa alal hakika Alhaji Mu'azu yayi matuk'ar farin ciki da wannan maganar nan da nan ya amince masa suka yanke shawarar ranar d'aurin aure saboda basu son aja dogon lokaci ba'ayi ba.
Anan Alhaji Taheer ya yini sannan daga k'arshe ya koma gidansa yana ficewa mahaifin Nazifa yaje room d'in hajiya Ramlat, ya gaya mata duk abinda ake ciki duk da maganar tayi mata dad'i sosai azuciyarta amma bata nuna afuskarta ba saina wani yatsine yatsine takeyi tana b'ata fuska, ganin batace komai ba yasa Alhaji ya mik'e tsaye ya fice daga cikin d'akinta.
Tun daga lokacin da aka saka ranar aurensu soyayya da tsantsar shakuwa mai k'arfi ta shiga atsakaninsu, akowane lokaci suna manne da waya suna jin muryar junansu domin kowanensu ji yakeyi bazai tab'a iya rayuwa ba saida d'ayan, cikin haka ne aka d'aura aurensu tamkar su lashe juna akan madarar k'auna da sukayi auren ma basu fasa bawa junansu kulawa da tarairaya ba saboda wani lokaci Yaseer har kasa fita yakeyi majalisarsu fira domin yasan yanada mai faranta masa akodayaushe.
Bayan watanni uku da aurensu Nazifa ta samu ciki zo kuga murna da annashuwa afuskokin wad'annan bayin Allah, domin daga ita har Yaseer ba'asan wanda yafi wani d'okin cikin ba sannan ga iyayensu da sukeyi mata aike akowane lokaci, babu irin abinda bataci data samu cikin nan hakan ne yasa hajiya Ramlat ta kawo mata wadda zata dingayi mata ayyukan gida tana zaune tana kulawa da cikinta, cikinta ya dinga girma Nazifa ta k'ara kumbura yanayinta gaba d'aya ya chanza ta shiga cikin watan haihuwarta ta haifi sankacecen d'anta yaci suna Sameer "yan uwa da abokan arziki sukayita tururuwa ganin jariri kammaninsa sak mahaifiyarsa babu inda ya d'auko kammanin Yaseer sai wurin farar fata.
Nazifa ta cigaba da rainon d'anta cikin k'auna da so har ya isa yaye ta yayesa ta kaiwa hajiya Ramlat domin ya cigaba da zama wurinta, hajiya Ramlat ta dinga kulawa dashi har yakai shekara biyu cifcif sannan ta mayardashi wurin mahaifiyarsa alokacin tana d'auke da cikin Sameera, Sameer yana dawowa gidansu da watanni biyar Nazifa ta haifi d'iyarta taci suna Sameera itace ta biyo kammanin mahaifinta kamar yayi kaki ya tofar, haka akaci biki lafiya taro ya watse Nazifa ta cigaba da kulawa da rainon d'iyarta Sameera tayi bulbul zad sha'awa itama mai jefo tayi haske da k'iba fatarta tayi luwai luwai tana k'yallin jefo, bayan haihuwar Sameera da watanni uku hajiya Ramlat taje ta d'auko Fauzeeya ta dawo gidan Yaseer da zama ya sakata aschool itada Sameer ta 'ya'yan masu kud'i.
Duk da haihuwar nan da tayi baisa ta daina kulawa da mijinta tareda bashi hak'k'insa dake rataye awuyanta ba saboda ta tsani taga b'acin ransa ko kad'an arayuwarta, domin so d'aya takeyiwa Yaseer saboda ya riga yayi kane kane aranta batada wani abunda takeso fiyedashi kullum soyayyarsa k'ara kwaranya takeyi ajininta shiyasa take masifar kishin mijinta bata fatar ya auri wata mace bayan ita, shima azuciyarsa yana masifar sonta kuma bai tab'a tsammanin zai iyayin rayuwar aure da wata mace bayan ita.
Wata rana ne bayan Nazifa takai ziyara gidansu hajiya Ramlat ta bata mak'udan kud'i domin ta fara yin business, da farko Nazifa kin amincewa tayi saida hajiya Ramlat ta zageta tass tareda balbaleta da masifa sannan ta amince ta amshi kud'in bata jima ba ta koma gida ta gayawa mijinta duk abinda ake ciki, saboda bayason ta samu sab'ani da mahaifiyarta yasa dole ya amince mata ta fara business ta bud'e fankacecen shago, alokacin data fara business bata chanza ba saida ta had'u da k'awarta Safiya duk ta chanza mata tsarin rayuwa tareda barkata mata lissafi, ta dinga zugata tana d'orata akan muguwar hanya har ya zamo sanadiyyar tab'arb'arewar farin cikin gidan Yaseer domin kwata kwata Nazifa chanza masa tayi cikin k'ank'anin lokaci ta dagula masa lissafi tareda hargitsa masa tunani, har takai ta kawo ko hak'k'insa dake rataye awuyanta bata bashi ta dinga musgunawa rayuwarsa tareda shuka masa rashin mutunci, amma Safiyar dake zugata ita biyayya da tsantsar kulawa takeyiwa mijinta Haidar yayinda dama ba soyayyar gaskiya take mata ba, hassada da kushe takeyi mata saboda ganin ta ko'ina Nazifa tayi mata fintinkau, amma dayake k'wak'walwar kifi gareta bata fahimci cewa ba son tsakani da Allah takeyi mata so take ta kashe aurenta ta zamo k'aramar bazawara.
_Mu kiyaye ba kowace 'k'awa ce ake bawa yarda da amana ba saboda haka mata ku lura da k'yau duk wadda tayi SAKACI za'a yi mata sakiya._
_Dawowa cikin ainahin labarin._
Fauzeeya ce rungume a faffad'an k'irjin Yaseer yana bata abinci a spoon shima yana ci sai wani narkewa takeyi tana masa shagwab'a,shi kuma sai lallashinta yakeyi cikin so da tsantsar soyayyar gaskiya haka suka cigaba da cin abincinsu atsanake harsuka gama,Yaseer ya ciko kofi da ruwa ya bata tasha ya shanye sauran ruwan data rage yace"Alhamdulillahi baby kin k'oshi ko? ".
Fauzeeya tayi narai narai da idanunta ta lahe ajikinsa tace"eh na k'oshi yaya dama inason neman alfarmarka ".
Yaseer yaja numfashi yace"my Fauzee wace irin alfarma kike nema awurina?".
Zumb'ura baki tayi tace"gidanmu nakeson zuwa ziyara kaga nayi watanni biyu banje ko'ina ba gashi ina matuk'ar buk'atar ganin Iyata".
Yaseer ya shafi mararta yana murmushi yace"keda fita sai kinyi watanni takwas ko kinyi haihuwar farko saboda ina tsananin kishinki banason maza su kallemin k'yak'yak'k'yawar fuskarki mai d'aukeda hasken an nuri".Ya fad'a azolaye murmushi k'unshe afuskarsa wani irin sanyi ke kwaranya cikin k'ofofin jikinsa da k'wak'walwarsa.
Fauzeeya tayi saurin kallonsa afirgice tace"haba yaya karkayimin haka please yanzu idan kace saina haihu yanzu yaushe nasan zan haihu kabarni inkai musu ziyara su ganni in gansu muji sanyi azuk'atanmu".
"kika sani ko kinada cikina na tsawon watanni biyar kinga kenan sauranki wata hud'u kije musu ziyara ".
"wannan kuma sanin gaibu sai Allah abu ne aduhu".
Yaseer ya kauda kansa gefe yace"bazan yarda da wayonki ba my Fauzee sai kin bani cin hanci".
"fad'i abinda zan baka cin hanci mijina yanzun nan inbaka koma miye".
"haka kika fad'a idan na gaya miki banason wani complain fa? ".
Fauzeeya ta girgiza kanta alamar eh mana babu damuwa sannan tace"ka fad'a aini nace ka fad'amin babu abinda zai biyo baya sai Alkhairi ".
Yaseer ya sauke gwauron numfashi cikeda matuk'ar buk'ata yace"kanki zaki bani har saina gamsu dake".Fauzeeya ta murmusa tace"ai nasan gatanar gizo bata wuce k'ok'i ba komai na yarda".Yaseer ya ciza labb'ansa cikin matuk'ar k'auna yace"to shikenan tunda kin amince babu matsala zamu fara daga yau idan naga bakiyimin ragganci ba da kaina zan kaiki gidanku :".Fauzeeya ta langwab'e kanta cikin sagarci tace"kayyyy yah Yaseer ka cika wayo da yawa".
Yaseer ya d'an fuske fuskarsa domin kada taga damarsa yace"idan baki amince ba babu dole my Fauzee aiba ni kad'ai nakejin dad'i ba hardake saboda idan ina d'akinki munayi gunjin kukanki kakeji yana tashi domin harakar tanayi miki dad'i ".Fauzeeya ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta cikin tsananin kunya tace"kaima ai kanayi yaya ".Yaseer yayi murmushin dake bayyana hak'ora yace"ki daina jin kunyata inayin mi? ".Yakune fuska tayi tace"ka sani basai na fad'a ba"."Naji ai ".Daga nan bai sake yin wata magana ba ya fara aika mata zazzafan sak'onni tana maida masa martani ganin zasuyi abinda yafi k'arfin idanuna yasa na shek'a da gudu na fice daga cikin d'akin abakin k'ofar naci karo da Nazifa dake lab'e cikin kussuwar k'ofa tana lek'onsu tareda sauraren duk abinda suke tattaunawa hawayen bak'in ciki sai gangarowa sukeyi afuskarta wani irin tururin d'aci da tsantsar damuwa ne ya tokare mata a k'irji zafi da suya zuciyarta keyi,ji takeyi kamar ta shiga cikin d'akin ta rufesu da matsiyacin duka hawaye sai shatata sukeyi saman fuskarta yayinda a k'ark'ashin zuciyarta k'ololon bak'in ciki ya gauraye jinin jikinta da sassarfa tana jaye abakin k'ofar ta fad'a cikin d'akinta tana isowa tsakiyar room d'in ta fad'a da k'arfi saman gadon tanata rusar kukan zafi da k'unar zuciya hakika ayau tayi nadamar biyewa son zuciya da rudin shaid'an ta sabawa umurnin mijinta gashi yanzu tana kammayanzu ta ji tana gani Fauzeeya ta mallake zuciyar Yaseer sai juyashi takeyi ta rasa abinda yakeyi mata dad'i aduniya ji takeyi gwara ace ta mutu da wannan matsananciyar rayuwar da take ciki mai cikeda matuk'ar takaici da k'angin rayuwa.................
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 43*
Saida Nazifa taci kukanta ta k'oshi kamar hawayenta zasu k'are sannan ta sanya hannunta ta rarimo phone d'inta, nombar hajiya Ramlat tayi dialling ta shiga babu dad'ewa hajiya Ramlat tayi receiving call d'inta tace"baby ya ake ciki ne kina lafiya?".Hawaye sai sintiri sukeyi afuskarta taja numfashi mai tattare da bak'in ciki da rad'ad'in zuciya tace"babu lafiya Ummu wlh so suke su kasheni inbar duniya ji nakeyi kamar zuciyata zata fashe akan tarin damuwa! "."Kinga baby ki natsu ki gayamin abinda sukayi miki banason kina kuka da sanyawa zuciyarki bak'in ciki!".Ta fad'a hankalinta atashe domin ta tsani taga 'yarta ta shiga damuwa ko rikicin rayuwa babu yadda zatayi saboda abin yafi k'arfinta".Nazifa ta saukar da numfashi kad'an kad'an zuciyarta cunkushe da tsantsar tarin damuwa tace"Ummu Yaseer walak'antani kawai yakeyi yana k'unsamin takaici iri iri daban daban agidansa domin har agabana auratayya yakeyi da Fauzeeya, Allah yarinyar nan ta zamomin k'adangaren bakin tulu kak'i shiga kak'i fita na rasa yadda zan b'ullowa al'amarin! ".Hajiya Ramlat ta girgiza kanta alamar gamsuwa da maganarta cikin matsanancin hali tace"share hawayenki baby anyanka ta tashi dole Fauzeeya zata bar gidan nan! ".Tana kammala maganarta ta katse phone d'in tareda dialling nombar Baura tana shiga ya kara wayar akunnensa, sun jima suna tattaunawa batare da naji abinda suke fad'a ba daga k'arshe hajiya Ramlat ta katse wayar tanata kaida kawo cikin d'akinta zuciyarta adagule lissafinta ya tarwatse!.
*********************
*BAYAN SATI UKU*
Yaseer yace wa Fauzeeya ta shirya kafin ya dawo zaya kaita gidansu taga su Iya Kulu tsalle tayi ta rungumesa cikin matuk'ar farin ciki mara misaltuwa,tana murmushi k'unshe afuskarta Yaseer jayeta yayi ajikinsa yace"kiyi sauri kiyi wanka zanje super market in siyo kayayyakin da zakiyi musu tsaraba".Fauzeeya tayi fari da idanunta tana tura bakinta agaba tace"yaya zanyi saurin wanka shirina bayada wahala".Yaseer yayi mata kiss abaki yace"idan na dawo baki kammala shiri ba na fasa kaiki sai wata rana! ".Harararsa da wasa tayi ta b'ata fuska cikin yanga tace"dako nayi maka kuka".Yaseer ya lakaci kumatunta cikin shauk'in k'auna yace"a'a banason ganin hawayenki domin ke d'in wata ab'ace mai matuk'ar muhimmanci aduniyata".Murmushi ta sakar masa tace"ko acikin maza daban kake yayana domin ka iya sace zuciyar duk wata mace maiji da kanta ka sani har kaine *ABUNDA NAKE SO* ban tab'a riskar kaina akogin soyayya ba sai akanka muradin zuciyata ".Dad'in kalamanta yasa Yaseer kwallar zallar farin ciki da soyayyarta ta zubo afuskarsa yace"my Fauzee ina matuk'ar k'aunarki azuciyata saboda kin taimakeni alokacin da nake buk'atar taimako kin fitar dani acikin k'angin rayuwa kin mayardani arayuwa mai d'auke da sinadaran ni'ima ,kinyimin halaccin da har abada bazan tab'a mantawa dake atarihin rayuwata".Fauzeeya ta iso gab dashi suna jin numfashin juna sanya hannunta tayi ta share masa hawayensa tace"ka daina ya mijina matuk'ar ina numfashin adoron duniya babu kai babu kukan bak'in ciki saina farin ciki, nayi matuk'ar yi maka alk'awarin zan sakaka cikin farin ciki na har abada zan zamo garkuwa agareka domin soyayyar da nakeyi maka yasa banason ganin b'acin ranka".
Yaseer yaji ya samu natsuwar zuciya kallon k'wayar idanunta yayi yana hango soyayya da k'aunarsa kwance cikin idanunta, ahankali ya sake k'ank'ameta ajikinsa ayayinda yakejin wani irin abu yana fisgarsa zuwa gareta yace"naji dad'in yadda kike sona my Fauzee ubangiji ya bamu ikon hak'uri da juriya da junanmu har abadan da'iman".
Fauzeeya tayi ajiyar zuciya cikin ni'imtaccen farin ciki tace"amin ya rabbi k'albina".
Yaseer ya jayeta ajikinsa tareda d'aukar key d'in motarsa yace mata"na wuce".
Baki ta bud'a tace"ubangiji ina rok'onka ka karemin mijina aduk inda ya shiga fad'in duniyar nan".
"Amin".Yace a k'asan mak'oshinsa ya fice daga cikin d'akinta direct parking lot ya nufa ya shige cikin motarsa maigadi ya wangale masa get ya fice daga cikin gidan da sauri.
Ficewarsa keda wuya Fauzeeya ta fad'a cikin bathroom tayo wanka d'aure da towel ta fito lotion ta shafa ajikinta sannan ta tsantsara kwalliyarta mai masifar k'yawo, domin so take Iya Kulu ta ganta tsab -tsab kallo d'aya zakayi mata ka gane tana cikin jin dad'i da hutu saboda fatar jikinta tayi luwai luwai sai shek'i takeyi, daga gani babu tambaya kasan babu abinda ya nema ta rasa arayuwarta akwatinta ta bud'e ta ciro tsadadden lace d'inta wanda duba d'aya nayi masa saida numfashina ya kusa d'aukewa adalilin masifar kyawonsa.
Rigarta ta fara zurawa ajikinta ta d'aura zanenta d'aurin d'an kwali ta nad'a akanta mai k'yawon dubi, turarurka ta feshe jikinta dasu ta ciro takalmi da mayafi farare ta yafa ajikinta handbag d'inta white colour ta rataya a kafad'arta ta zauna saman gado tana yin charting tana sakin murmushi, ta d'an jima zaune tana jiran dawowarsa k'amshin turarenta duk ya gauraye cikin d'akin da kewayen gidan gaba d'aya, ta aza k'afarta d'aya saman d'aya saiga sallamar Yaseer ya turo k'ofar d'akin ya shigo tsakiyar room d'in hannunsa rik'e da ledodi manya manya guda hudu, Fauzeeya ta mik'e tsaye ta iso wurinsa ta amshi ledodin dake hannunsa tace"welcome back honey".
Yaseer ya jefeta da murmushi yace"uhmmm my Fauzee kin shirya ko?".
"eh mana yayana".
"to karki zauna tashi mu tafi kada lokaci ya k'ure".
Ayyah na zata saika huta ne".
Yaseer ya firfito da idanunsa yace"ina ni ina hutawa yanzu".
Fauzeeya tayi tsaye rike da ledodin ahannunta ta yafa mayafinta handbag tana rataye a kafad'arta tace"muje to".
Yaseer ya amshi ledodi biyu ahannunta yace"bari in rage miki kaya kada ki zubarmin da cikina dake mak'ale mararki".
Fauzeeya ta bushe da dariya cikin nishad'i tace"kayyy waye ya gaya maka ina d'auke da cikinka?".
"auuu sai angayamin zuciyata ce ta sanarmin kina d'auke da d'ana ko d'iyata amararki".
Fauzeeya tayita murmushin dake bayyana tsantsar k'yawon fuskarta Yaseer yana gaba ita kuma tana biye bayansa har suka iso cikin parlourn suna isowa tsakiyar parlour, sukaga Nazifa tana shan hollandia akofi kad'an kad'an ganinsu yasa ta had'iye wani irin abu mai d'aci a mak'oshinta, kallonsu takeyi tana jijjiga kanta cikin matuk'ar b'acin rai da bak'in kishi tsoki mtsssssss taja tace"karuwancin banza bita zaizai ahaka zaku tabbata! ".
Yaseer dake gaba ya waigo da sauri yace mata"da wa kike!? ".
"da wanda duk tsargu dashi nake! ".Tace tareda kauda kanta daga barin kallonsu.
Yaseer ya musk'uta yace"kedai akeji duk bak'in cikinki saidai ki mutu! ".Yana soka mata magana suka fice daga cikin gidan suka iso parking lot Yaseer ya bud'e mata gefen driver ta shiga ta zauna, shi kuma ya zagaya ta b'angaren mazaunin driver ya shiga ya zauna tareda danna horn maigadi ya wangale musu get d'in suka fice daga cikin gidan suka nufi hanyar zuwa unguwarsu Iya Kulu.
*********************
Tafiya sukeyi ahankali saman kwalta firarsu kawai kakeji yana tashi cikin nishad'i da tsantsar soyayyar gaskiya,karatun qur'ani yah Yaseer ya sanya mana muna sauraro ni kaina na rasa irin tsantsar farin cikin da nake ciki adalilin na mallaki muradin zuciyata kallo d'aya zakayi mana ka gano mun dace da junanmu can Yaseer ya kalleni ta wutsiyar ido yace"my Fauzee kinada buk'atar wani abu ne in tsaya in siya miki?".
Fauzeeya ta kallesa tace"bana buk'atar komai yayana hidimarka gareni tayi yawa sosai".
Maida hankalinsa yayi saman kwalta yana tuki cikin matuk'ar k'warewa yace"hidima gareki wajibi ne akaina saboda kin kasance rayuwata abar alfaharinah".
Fauzeeya ta karkace kanta tareda jingina bayanta akan kujerar k'amshin turarensa take shak'a, cikin shauk'in k'auna tace"godiya nakeyi tauraron zuciyata".
"babu godiya atsakaninmu my Fauzee".
D'ayansu bai sake magana har suka gangaro daga saman kwalta