Showing 75001 words to 78000 words out of 87802 words
suka bi hanyar da zata sadasu da gidan Iya Kulu mai tsamiya, shan corner Yaseer yayi ya iso bakin k'ofar gidan Iya Kulu ya parker motarsa yaja ya tsaya yana kallon yadda jikin Fauzeeya ke rawa akan tsantsar murna dake shimfid'e afuskarta, kallonta yakeyi yarintarta yana burgesa zata bud'e k'ofar mota kenan ya rik'e mata hannu ta juyo da sauri tana kallonsa tace"ya zan fita ka wani rik'emin hannu?".
Nannauyar ajiyar zuciya yayi yace"naga jikinki yana mararin zuwa wurin Iyarmu amma ai k'ya bari muyi sallama da juna ko?".
Logayewa tayi tana zumb'ura baki tace"mi kake nufi bazaka shiga ciki ka gaisa da kakata ba? ".
"idan na dawo d'aukarki zan shiga cikin gida na gaidasu kinji kada ki manta ki bud'e bayan mota ki d'auki ledodin kikai musu".
"ba komai to zan jiraka har ka dawo".
"OK babyna".
Fauzeeya ta fito daga cikin motar sannu ahankali taje ta bud'e boot ta d'auki ledodin ta shige cikin tsakiyar gidan,saida yaga ta shige cikin gida sannan ya juya akalar motarsa yabar unguwar gaba d'aya.
Fauzeeya tana isa tsakar gida ta isko Iya Kulu zaune saman tabarma tana lissafin kud'in kayan miyan da take sayarwa k'amshin turaren Fauzee ne yayi mata iso ta d'ago idanunta suka fad'a cikin nata, ai kuwa nan da nan Iya Kulu ta washe hak'ora tace"a'aaaa amarya ce agidanmu yau sannu da zuwa".
Fauzeeya ta cire takalminta ta zauna kusa gareta tana murmushi tace"nice Iya yauwa".Ta aje ledodin agabanta.
Iya Kulu taja gwauron numfashi cikeda matuk'ar farin ciki tace"ya mijinki da kishiyarki ina fatar kuna zaune lafiya babu wata matsala? "."Lafiya k'alau muke Iya shima ya kawoni domin in ganku yace yana gaidake ssannan shine yace in kawo miki wannan ".(ta nuna mata ledodin). Iya Kulu taji dad'i tace"madallah ubangiji yayi albarka ya kuma k'ara yalwar arzik'i gaskiya Fauzeeya kinyi sa'ar dacen miji nagari ".Fauzeeya tace"ai Iya don ma baki zauna dashi ba yaya Yaseer bayada matsala yanada hak'uri da kawaici shiyasa ba kasafai rayuwarsa take b'aci ba"."Eh lallai kece mijin nawa baida matsala tabbas nayi dace ".Fauzeeya ta zumb'ura baki tace"mijinki ko nawa Iya kinyi masa tsufa da yawa?".😂..............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 44*
Iya Kulu ta murgud'a mata baki tace"aganinki nayi masa tsufa amma awurin Yaseer garas yake ganina tamkar yau aka haifeni".Yadda ta murgud'a mata baki ta fashe da dariya tace"kayyyy Iya kin iya wasar kwaikwayo zakiyi k'yawo da shirin hausa film".Iya Kulu ta katse mata hanzari da sauri tace"bakinki ya sari d'anyen kashi tsofai tsofai dani mizai kaini shirin film saidai ire irenku sabon jini sunfi buk'atarku".Fauzeeya ta sassauta murya tana had'iye dariyarta tace"haka ne fa Iyata agaskiya ina sonki fiyeda zatonki saboda tun tasowata dake na saba rayuwa dake na shak'u kece matsayin mahaifiya agareni".Jikin Iya Kulu yayi matuk'ar sanyi cikin tausayinta tace"ayyah Fauzeeya ki sani banda tamkarki aduniya ko Labaran dana haifa sonki ya zarce nasa fiyeda tunaninki saboda ke d'in jinina ce".Fauzeeya ta jingina jikinta ana Iya Kulu tana yamutsa fuskarta tace"Iya akwai sauran furar da kika ajiye inje insha".Iya Kulu ta tsura mata idanu tana mata kallon k'walelecewa dubin yadda yanayinta ya chanza gaba d'aya nisawa tayi tace"akwai furar Fauzeeya muga tafin hannunki".Fauzeeya ta nuna mata tafin hannu Iya Kulu ta sanya hannunta ta bud'e k'wayar idanunta tana nazari can tace"ciki ne dake Fauzeeya".
Kallonta tayi da sauri tace"ciki fa kikace Iya yaushe yaushe akayi aurenmu?".
Harararta Iya Kulu tayi tace"amma dai akwaiki da shirme yarinyar nan to ai ko satin d'aya kikayi aure zaki iya samun ciki balantana ke da kikayi wata uku cikin na hudu".
"ganin nayi kamar nayi k'ank'anta da d'aukar ciki Iya duka duka shekaruna goma sha shida fa".
"hmmmmmm ai yanzu ana dad'ewa kafin ayiwa yaran zamaninku aure amma azamaninmu tun yarinya bata balaga ba bata fara ganin haila ba akeyi mata aure, ayanzu ma ana barin budurwa ta dad'e gidansu batada aure domin kai ya riga ya waye ilimi ya ratsa birni da k'auye".
"zancenki gaskiya ne bari inje in d'auko furar insha".
"to sarkin son ciye ciye kinyi babu dalili bale da dalili".
Fauzeeya ta shafi mararta cikin tsokanar Iya Kulu tace"gaskiya idan har inada cikin Yaseer zanyi farin ciki da hakan domin nima na kusa samun mai yimin addu'a".
"to naji sarkin fitsara shiga ki d'auko furar kisha banason salon iyayi".
Dariya ta saki ta shige cikin d'akin Iya Kulu ta d'auko robar furar zaunawa tayi ta kafa kanta zama guda ta zuk'e furar dake ciki ta d'ago fuskarta tana murmushi, Iya Kulu ta karkace baki tace"shafta kenan zama guda ki zuk'e furar wannan ciki naki da shegen ci yake".
Fauzeeya ta goge bakinta inda furar ta tab'a tace"matsalata dake Iya kwakwazo yanzu dai bari inje gidansu Adama mu gaisa da gidan babana".
Iya Kulu tace"ba damuwa ki d'auki leda d'aya ki ciri wani abu kiba Adama sauran ki kaiwa babanki".
Rau rau da idanu Fauzeeya tayi tace"kibar kayanki Iya Adama kud'i zan bata hakama babana".
"haka zakije musu babu komai ahannu gaskiya ki d'auki leda d'aya ki kaiwa mahaifinki".
"nifa ba mahaifina nake jin haushin bashi k'yauta ba bak'in ciki nakeji in kaiwa wadda tayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyata taci arzik'ina ki diba ki gani idan da babu ke bansan yadda rayuwata zata kasance ba, saboda Inna Munari so tayi ta kasheni inbar duniya baki d'aya taya kike tunanin zan iya manta sharri da makircinta alokaci guda?".
"haba d'iyar albarka miyasa bakida mantuwa arayuwa ai duk wanda ya bika da sharri ka bishi da alkhairi duk sharri daya nufeka dashi sai ubangiji ya mayar masa da abinsa, yanzu da kikayi hak'uri da tawakkali gashinan ubangiji ya baki mijin nunawa sa'a aiko wannan ya isheki ishara ".
Fauzeeya ta girgiza kanta cikin mutuwar jiki tace"shikenan Iya na gamsu da maganarki ubangiji ya kiyaye gaba".
"yauwa ko kefa d'auki kikai musu ai albarkacin kaza k'adangare ke samu wurin shiga Munari taci albarkacin mahaifinki".
Fauzeeya ta sunkuya k'asa tana dudduba ledodin can ta d'auki d'aya ta fice daga cikin gidan, Iya Kulu tabi bayanta da kallo cikeda tsananin tausayi da k'aunarta shiru tayi tanata tunanin abubuwan duniya mai k'unshe da takaici da tsantsar bak'in cikin rayuwa.
*********************
Fauzeeya gidan mahaifinta ta fara shiga iske Inna Munari tayi d'aure da d'aurin k'irji zanenta cuwul cuwul da daud'a, idan mutum ya isa gab da ita wani irin fitinannen wari keyi masa iso da sallama adalilin tsabar k'azanta da yadda duniya ta juya mata baya, Fauzeeya ta isowa wurinta ta duk'a har k'asa ta gaidata Inna Munari tayita yi mata kallon rashin sani cikin fargaba tace"bak'uwa daga ina wa kike nema?".
Murmusawa kawai Fauzeeya tayi tace"baki ganeni bane Inna?".Inna Munari taji muryarta ta soma kamada ta Fauzeeya amma kanta ya k'ulle tunaninta ya rikice tace"ban ganeki ba baiwar Allah".
Fauzeeya ta isa wurin tabarmar data shimfid'a ta zauna tace"nice Fauzeeya".
Dummmm gaban Inna Munari ya buga zuciyarta ta tsinke! Cikin rikicewa k'arara afuskarta tace"wace Fauzeeyar kuma anyah ba b'atan hanya kikayi ba?".
Ta musk'uta tace"Fauzeeyar da kika sani dai d'iya tak aduniya ga Labaran da matarsa marigayiya Latifa! ".
Inna Munari ta kame wuri d'aya ta kasa kwakkwaran motsi domin ta shiga cikin wani irin mugun yanayi mai wuyar fassaruwa, ta fice cikin hayyacinta mamaki da tsantsar zullumi ne ya bayyana k'arara afuskarta! Tana tsaye saiga sallamar baba Labaran ya dawo daga kasuwa Fauzeeya ta amsa masa tareda yi masa sannu da zuwa amsa mata yayi fuskarsa asake cikin k'aunarta da murna ya k'araso wurinta yace"'yar baba ce yaushe kikazo?".
Fauzeeya tace"yanzun nan nazo baba".
"ya mijinki da abokiyar zamanki ina fatar kuna zaune lafiya?".
"lafiya k'alau muke baba".
Baba Labaran ya washe baki cikin farin ciki da murna yace"masha Allahu ubangiji yayi miki albarka".
Saurin kallonsa tayi baba Labaran ya kauda kansa gefe cikin kunyar d'iyarsa domin yasan kallon da takeyi masa baya rasa nasaba akan ya sanya mata albarka, saboda tunda ta taso arayuwarta bata tab'a jin ya saka mata albarka ba.
Cikin murna tace"amin baba ga wannan kuyi amfani dasu".Saka hannunta tayi cikin handbag ta zaro bandir na naira dubu dubu ta mik'awa baba Labaran hannunsa yana rawa ya amsa a k'ark'ashin zuciyarsa sai nadama da bak'in cikin walak'antasu da yayi itada mahaifiyarta yakeyi kwalla ce ta cicciko cikin k'wayar idanunsa wani irin abu yakejin yana yawo cikin jinin jikinsa yace"ubangiji yayi miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya Fauzeeya tabbas kin cika d'iyar halat mai saka alkhairi akan sharri ".
"amin ya rabbi baba".
Inna Munari mutuwar tsaye tayi tana mamakin ina Fauzeeya ta samu kud'i haka sana'ar mi takeyi domin ita duk azatonta Fauzeeya talaka take aure ba mai kud'i ba, wani irin zogi da k'una zuciyarta keyi saboda idanunta sun gasgata mata abinda take kwankwanto wato kenan shahararren mai kud'i ne.
Baba Labaran ya dubeta cikin sanyin jiki yace"Fauzeeya kiyafemin duk abinda nayi na musgunawa arayuwa nasan na cutar dake tareda k'untatawa rayuwarki tabbas gashinan tun ba'a je ko'ina ba ubangiji ya nunamin ishara ya d'aukaki da darajaki alokaci d'aya, alal hak'ik'a d'iyan da ake nunawa tsamgwama da tsantsar *RASHIN SO* aduniya sunfi zama mutanen k'warai masu daraja aduniya domin sunsha wahala da k'yara arayuwarsu shiyasa ubangiji yake d'aukakasu domin ya zamo wa'azi da ishara ga mutane! ".
Fauzeeya ta natsu tana sauraren kalamansa yayinda duk jikinta ya game da sanyi dak'yar ta daure cikin tausayawa mahaifinta tace"ka daina bani hak'uri babana duk abinda ya faru ga bawa muk'addari ne daga Allah kuma na d'auki duk k'unci da bak'in cikin dana shiga *K'ADDARA CE* !Saboda haka ka daina tunamin da abinda ya riga ya wuce domin duk d'an Adam ajizi ne mai aikata kuskure ne ".Baba Labaran ya share kwallar zallar takaicin data zubo masa afuskarsa yace"nagode da kika fahimceni Fauzeeya Allah ubangiji ya baki zuri'a d'ayyiba ya kuma k'ara d'aukaka rayuwarki".
Tace"amin baba".
Sai alokacin nan ne baba Labaran yaga Inna Munari dake tsaye murmushi k'unshe afuskarsa yace"kinyi tsaye baki iso ba k'araso kiga abin alkhairin da d'iyata ta kawomin kayyyy haihuwa mai rana hak'ik'a komai yanada lokaci ".Inna Munari ta k'araso jikinta asab'ule zuciyarta cunkushe da tsantsar tarin damuwa da hassadar Fauzeeya domin yanzu ta gama fahimtar ubangiji yabata miji mai kud'i.
Fauzeeya tayi mata magana Inna Munari ta dinga amsawa ciki ciki zuciyarta cunkushe take da tsagwaron k'iyayyar Fauzeeya da bak'in cikin rayuwa, saida ta d'an jima gidan babanta sannan tayi musu bankwana baba Labaran yayi mata rakiya har bakin k'ofar gidan, saida yaga shigewarta gidansu Adama sannan ya juyo ya dawo cikin gidan ya iske Inna Munari ayadda ya barta tana ganinsa ta rufeshi da fad'a ta inda take shiga ba tanan take fita harda ce masa tayi bak'in munafuki! Baba Labaran ganin rainin wayonta yayi yawa yasa ya bata mugun kashi yyayi mata saki d'aya tareda korata gidan iyayenta.
**********************
Fauzeeya ta shiga cikin tsakiyar gidan da sallama abakinta tareda hango Inna Amo mahaifiyar Adama tanata aikin kwasar kashin awaki, tana isowa wurinta ta gaidata Inna Amo ta amsa mata fuskarta ayalwace tace"ya maigidanki? ".Fauzeeya tace"lafiya k'alau Inna".Inna Amo tayi murmushin farin ciki tace"to madallah haka akeson ji ayita hak'uri aure d'an juriya da hak'uri ne kinji Fauzeeya ".Fauzeeya ta gyad'a kanta alamar gamsuwa da maganarta cikin kunya .
Inna Amo ta dubeta tace"ki shiga cikin d'aki Adama tana nan kwance batada lafiya ".Fauzeeya tace"ayyah ubangiji ya sawwak'a "."Amin Fauzeeya ".Tana rufe bakinta taja k'afafunta ta shige cikin d'akin ta iske Adama kwance saman gado lullub'e da mayafi ajikinta da sauri Fauzeeya ta isa wurinta tace"Adama ubangiji ya baki lafiya ".Idanunta alumshe ta bud'esu tarrrr sai afuskar Fauzeeya dak'yar cikin yanayin ciwo tace"naji sauk'i k'awata yaushe kikazo? ".Fauzeeya ta zauna gab da ita ta sanya hannunta cikin tafin hannun Adama tace"yanzu yanzun nan nazo na taras da bakida lafiya "."Eh dama na kwana biyu da zazzab'i ajikina".Fauzeeya ta dubeta cikin yanayin tausayi tace"rabbi ya kawo sauk'i ".Adama ta tashi zaune domin taji dad'in fira tace"amin aminiyata aurena ya matso kusa fa ".Ta firfito da idanunta waje cikin matuk'ar farin ciki tace"kee Adama kice kin kusa zama amarya ".Adama tayi murmushinta mai k'yau tace"insha Allahu kuwa ina kishiyarki Nazifa take ne? "...........
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 45*
Fauzeeya ta yamutsa fuskarta cikin tsananin kishi da tsagwaron takaicin Nazifa tace"tana can mun barota gida".Adama ta gyara zamanta tace"kice itace kika barwa fakon gida".Fauzeeya ta kalleta cikin fara'a tace"Aunty kam bata iya fakon gida maybe ma muna fita ta fito saboda inda kike ganinta ba baya ba wurin yawo kamar taci k'afar kare"."Saina gaya mata ince kince mata taci k'afar kare akan yawo lungu lungu sak'o sak'o".Adama ta fad'a tana k'yalk'yalar dariya.
Fauzeeya ta d'aga kafad'arta alamar ko ajikinta tace"tun yanzu kije ki gaya mata ga kud'in napep in baki kihau".Ta sanya hannunta cikin handbag ta zaro kud'i masu kauri ta mik'awa Adama tace"amsa ki shiga napep".Adama ta razana da ganin kud'i masu yawa haka ta girgiza kanta tace"Fauzeeya ina kika samu kud'i haka da zaki bani k'yauta?".Fauzeeya ta harareta tace"banason tambayar rainin hankali k'awata ai kinsan mijina yanada hali saboda haka ki daina mamakin inda na samu kud'i gudunmuwa ce na baki ki k'ara ki sayayyar kayan aure".Adama ta nisa tareda amsar kud'in tace"nagode sosai ubangiji yabar zaman tare ya k'ara bud'i".Fauzeeya ta bintsire baki tace"inason addu'arki nace amin amma godiyarki ki rik'e abarki bana so".Adama tace"na daina yi miki tunda bak'ya so"."Dakam yafi miki".Cewar Fauzeeya tana dariya anatse.
Cigaba da maganganunsu sukayi cikin natsuwa da walwala har daga baya Fauzeeya tayi mata sai anjima, Adama ta rakata har bakin k'ofar sukayi sallama da juna ta juyo ta dawo cikin gidansu tareda nunawa mahaifiyarta gudunmuwar da Fauzeeya ta bata hak'ik'a Inna Amo tayi farin ciki sosai sai sakawa Fauzee albarka takeyi dayi mata k'yak'k'yawar addu'a.
Fauzeeya tana komawa gidan ta taras da Yaseer har yazo sai fira yakeyi da Iya Kulu yana murmushi domin shi bai faye dariya ba, ganinta ne yasa Iya Kulu tace tazo su wuce tana zumb'ura baki tana komai sukayi mata sallama suka fita daga cikin gidan direct wurin motarsu suka nufa, yah Yaseer ya bud'e mata motar ta shiga ta zauna sannan ya zagaya gefen driver ya zauna ya tadda motarsa suka fice daga cikin unguwar suka d'auki hanyar zuwa gida.
**********************
Suna komawa gida suka fad'a cikin bathroom sukayi wanka suka fito d'aure da towel ajikinsu lotions suka shafawa juna, sannan suka zura tufafinsu mara nauyi Yaseer ya dubeta cikin so yace"palour zanje inyi kallon news idan zakije kizo mu tafi".
Fauzeeya ta furta cewa"ok muje d'in".
Suka rankaya suka dawo cikin tsakiyar parlourn iske Nazifa sukayi zaune saman cushion sai cika takeyi tana batsewa, basu kulata ba Yaseer yaja hannun Fauzeeya suka zazzauna gab da gab da juna yayinda su Sameera sai guje guje sukeyi suna kuwwace kuwwace, ganin sun kasa natsuwa yasa Yaseer ya d'aga murya yace"kayyyyy ku natsu fa kun cika mana dodon kunne da kuwwace kuwwace".
Yaran sukayi tsaye turus tareda waigowa rau rau da idanu Sameer yayi yace"dad mun daina kayi hak'uri".
Sameera tayi charap tace"nima bazan k'ara ba".
Cikin k'auna da tsantsar soyayyar 'ya'yansa ya dubesu yace"oyahhh come and sit down".
Su Sameer suka iso cikin parlourn suka zazzauna saman carpet tareda lank'washe k'afafunsu, kallon news suka farayi kamar yadda su kaga iyayensu sunyi suka natsu cikin matuk'ar murna.
Ashe abinda Yaseer yayiwa 'ya'yansa yaci mata rai k'ara hasala sosai Nazifa tayi zuciyarta sai suya da tururin zafi takeyi mata, kallon banza ta wurga musu cikin b'acin rai tace"nifa Yaseer banason kana takurawa rayuwar 'ya'yana saboda na fahimci yanzu tunda kayi sabon aure ka daina sonsu tareda kulawa dasu".
Yaseer ya d'ago idanunsa da sauri suka fad'a cikin nata idanu cikin takaici da matuk'ar zafin k'azafi yace mata"kiji tsoron Allah Nazifa duk abinda zakiyi ki daina k'arya ki fad'i gaskiya na lura yadda kike bakida tarbiya haka kikeson yarana su kasance to ki sani har abada bazan tab'a d'aukar wannan sakarci da rainin wayo ba,ke yanzu har kinada bakin da zakice na daina kulawa da yarana alhalin ke baki maidani bakin komai ba sai shara bola!".
Nazifa ta yamutse fuskarta tace"duk da banida tarbiya ahaka ka gani ka nace kana sintirin zuwa gidanmu kuma kada ka k'ara cemin banida tarbiya domin baka fini ita ba".
"Nazifa Nazifa duk abinda kikeyi ina k'yaleki kada ya zamo silar da zaki rainani wlh zan d'auki kwakkwaran mataki akanki! ".
Nazifa tayi tab'i da hannunta tayi dariya tace"aikin banza babu abinda zaka iyayimin Yaseer na fahimci dai tun farko bak'in ciki da hassada kakeyimin saboda kaga ina samun kud'ad'e suna shigowa akowane lokaci ".
Fauzeeya da taga abin nasu baya k'arewa ta kalli mijinta tareda rausayar da kanta cikin rashin son fitina da tashin hankali tace"haba yah Yaseer dan Allah kayi hak'uri ka daina biye mata kuna sa'insa".
"barni da ita my Fauzee wannan matar da kike gani idan bana bud'a mata wuta ba iskancinta sai yafi haka! Tunda na aureta ban huta ba kullum kullum zuciyata cunkushe take da tsagwaron bak'in ciki da tsantsar takaicin rayuwa".
Nazifa ta tashi tsaye tana rik'e k'ugunta tace"wani bashi hak'uri kikeyi bak'ar makira bayan duk cin kashi da walak'ancin da yakeyimin asanadinki ne bak'ar kafirar yarinya! Kai kuma duk abinda kakeyimin kaida ubangiji Allah babu abinda ka iya sai nuna bambanci da cin amana".
"nine nake nuna miki bambanci da cin amanarki Nazifa