Showing 78001 words to 81000 words out of 87802 words

Chapter 27 - SAKACI BY MUGIRAT MUSA

05 Jul 2024

4253

sharri da k'azafi kike yimin iri iri daban daban waike miyasa komai naki babu gaskiya da tsoron Allah acikinsa?".

"eh bana tsoron Allah bakai kana tsoronsa ba".

"kinga alama ai".

Nazifa taja k'afafunta ta shige cikin d'akinta domin batason ta cigaba da sauraren irin kalaman dake fitowa daga cikin bakin Yaseer, ganin ta wuce yasa Yaseer ya jingina bayansa acushion yace"wannan matar tanason sakani cikin matuk'ar damuwa da b'acin rai".Ta dafe kansa da hannayensa biyu cikin matuk'ar takaici.

Fauzeeya ta jaye hannunsa cikin matuk'ar lallashi da tausayin mijinta tace"nace maka ka daina biyeta mijina wannan ba girmanka bane".

"hmmm my Fauzee naji zan daina kulata amma kinsan kwata kwata halayyarta bata yi domin batada rayuwar k'warai".

"hak'uri zaka cigaba dayi akodayaushe wata rana sai labari".

"haka ne".Kawai yace yaja bakinsa ya tsuke yana sak'a da warwara acikin zuciyarsa.

**********************
*BAYAN WATA D'AYA*
Fauzeeya tana cikin room d'inta tana gyara tufafinta dake cikin wardrobe duba d'aya zakayi mata ka gane tanada shigar ciki, yayinda Yaseer tun safe ya fita bai dawo ba tana zaune saman gado tayi ashe ashe saiga sallamar k'awarta Adama ta shigo tsakiyar d'akin da sallama abakinta ta amsa mata da murmushi k'unshe afuskarta tace"oyoyo oyoyo k'awateey ashe kin iso tun jiya da kika sanardani zaki zo".

Adama ta k'araso wurinta ta zauna gab da ita tana murmushi tace"amarsu ta ango bak'ya laifi".

Fauzeeya ta harareta tace"kece amarya Adama aini na tsufa da aure nasan komai na rayuwa".

Adama tace"Fauzeeya kenan ai nasan kinsan komai tunda gashi kin kwashi cikin Yaseer kinyi k'iba".

"nifa ba haka nake nufi ba Adama karkiyimin wata fassarar daban sannan wa cece take d'auke da ciki?".

"ke mana dibi yadda fatarki ta chanza kika k'ara haske da k'yawo".

Fauzeeya ta dubi jikinta da fuskarta ta cikin dressing mirror tace"ni banga wani chanzawa da jikina yayi ba kindai fad'a ne domin kiji dad'in bakinki ".

Adama ta gyara zamanta tace"k'arya nayi miki yanzu dai abinda ya kawoni domin in gayamiki aurena saura sati biyu ".Ta sanya hannunta cikin handbag ta d'auko katin gayyata ta mik'a mata ta amsa.
Fauzeeya tana kammala karanta abinda katin gayyatar ta k'unsa ta d'ago idanunta cikin murna da annashuwa tace"ai kuwa katin yayi k'yau Aminiyata ubangiji ya sanya alkhairi".

"Amin ya rabbi k'awata".

Firar tsare tsaren da zasuyi abikin Adama sukeyi yayinda Fauzeeya ta kawo musu abinci saman tire da lemun gora suna ci suna k'yak'yatawa, ji sukeyi kamar su tabbata ahaka domin sun aminta da shak'uwa da juna .
*********************
*BAYAN SATI BIYU*

Aranar Lahadi misalin k'arfe sha d'aya na safe ababban masallacin dake cikin unguwarsu Iya Kulu mai tsamiya dubban mutane suka shaida d'aurin aurensu Zakawanu Isa da amaryarsa Adama Daheeru,su Fauzeeya sune manyan k'awayen amarya suketa hidima dakai da kawo duk wad'anda sukazo bikin sunci sun sha .

Kwana biyu Fauzeeya tayi agidansu wurin mahaifinta Labaran saboda tuni ya sake aure bayan ya saki Inna Munari ya auri Daraja bazawara mai hankali da tarbiya, ganin baba Labaran ya saki Inna Munari yasa Iya Kulu ta tarkato duka kayayyakinta ta komo gidan d'anta Labaran ta cigaba da rayuwa anan, Fauzeeya anan d'akin kakarta tayi kwana biyu tanata tarairayarta da tsantsar shagwab'ata abin sai ya baka sha'awa da burgewa, kwana biyun da tayi anan ji takeyi kamar ta tabbata gidansu domin yadda take samun kulawa daga wurin Iya Kulu har baba Labaran da matarsa ba baya wurin nuna mata so.
Dak'yar Yaseer ya daure yabar Fauzeeya tayi kwana biyu agidansu domin ya riga ya saba da ita daidai da rana d'aya basu tab'a yin nisa da junansu domin sun shak'u da juna, ji yayi kwana biyun tamkar shekara biyu awurinsa tana gama cinye kwanakinta Yaseer yazo ya d'auketa suka koma gidansu, ganin yadda yake nan nan da ita yasa ta fahimci cewa mijinta yana buk'atarta akowane lokaci bashi muradin zuciyarsa tayi ya samu natsuwa, fad'awa sukayi cikin bathroom sukayi wankan tsarki da wankan sabulu sannan suka fito manne da juna dak'yar suka rabu Fauzeeya taja hannunsa ta zaunar dashi saman gado d'auko lotion tayi suka shafe jikinsu dashi ta ciro masa jalabiya milk colour ya zura ajikinsa, itama ta sanya riga da guntun sicket ta yadda zatafi jin dad'in shan iska da walwala arayuwarta kusa garesa tazo ta kwanta saman k'afafunsa shi kuma yana shafar lallausan gashinta mai k'amshin mayukan kitso................

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 46*



Suna kallon fuskar juna cikin marari da shauk'in soyayya wani irin sinadarin k'auna ne ke huda sassan jikinsu da zuk'antansu, sai kwaranya yakeyi cikin jini da magudanar jijiyoyi Yaseer yayi ajiyar numfashi tareda kallon fuskar Fauzeeya yace"my Fauzee dak'yar na daure har kikayi kwana biyu agidanku amma ji nakeyi tamkar na d'auki tsawon shekaru batare dake ba, alal hak'ik'a so babbar cuta ne matuk'ar ya kama zuciyar mutum yana sakashi zaucewa tareda sanyashi cikin matsanancin hali".
Fauzeeya tace"yayana nima hak'uri kawai nayi na rashinka akusa dani saboda bikin na babbar aminiyata ce wadda muka taso tare shiyasa naje domin itama ta taka rawar gani abikina".

Lumshe fararen idanunsa yayi ya bud'esu yace"gaskiya ne abinda kika fad'a ki sani bazan sake juriyar rashinki ba duk hidimar data k'ara tasowa saidai in baki gudunmuwa ki basu amma ganinki kam sai anyanka ticket ".

Kallonsa tayi tace"kana farashi ma".

"OK zan iya farashi ba nine mijinki ba mai iko dake".

Ajiyar zuciya tayi tace"to sarkin iko da gadara".

"nine kuwa wlh naji dad'in wannan sunan sosai".

Murmushi ta saki ta k'ara shigewa cikin k'afafunsa shi kuma sai wani tarairayarta yakeyi, yana furta mata tattausan lafazi mai dad'i da sanyaya zuciyar masoya.

**********************

Yaseer ya shigo cikin d'akin Nazifa sanye da kayan barci ya isketa tana shan madarar gora mai sanyi sallama yayi ko kallonsa batayi ba, ya k'araso wurinta yayi tsaye yana k'are mata kallo hannunsa rungume ak'irjinsa, shanye madarar tayi ta aje gora gefen gadonta ta gyara kwanciyarta saman gado babu alamun zatayi masa magana duk dayake taji k'amshin turarensa ya bugi hancinta.
Ganin yayi batada niyar yi masa magana yace"Nazifa inason magana dake".

Maida fuskarta tayi b'angare daban batace masa ci kanka ba saboda wani irin zafi da rad'ad'in kishinsa yake taso mata a k'irji,gyaran murya yayi cikin matuk'ar mamakin halin ko inkula data nuna masa sake cewa yayi"kinaji fa inayi miki magana amma kin k'yaleni wai mi yake damunki?".

Batare data juyo ba tace"kaga nifa gaskiyar zance ka takurawa rayuwata ka barni inji da damuwata banason wani k'arin bak'in ciki Yaseer".

"miye takurawa aciki Nazifa bayan ba hak'k'ina kike bani tun kafin inyi aure kika fita batuna to yaya kikeson inyi da rayuwata? Duk abinda nayi kece silar faruwar hakan".

"ai haka zakace bayan babu irin walak'anci da bak'in cikin da baka k'unsamin saboda kayi aure kaji dad'inta".

Yaseer ya rausayar da kansa yace"ki daina cewa ina k'unsa miki bak'in ciki da damuwa azuciyarki ni nasan babu abinda nakeyi miki na walak'anci gwargwado ina kwatanta adalci atsakaninku".

Nazifa tace"k'arya nakeyi maka bakayimin komai ba sanardani abinda ya kawoka d'akina ?".

Yaseer ya numfasa yace"ki juyo mu fuskanci juna muyi maganar data dace".

"bazan tashi zaune ba duk abinda zaka fad'a ka fad'a ina jinka ai kunne keji k'wak'walwa ke aiki".

"bazan iya magana dake ahaka ba".

"to ka tabbata haka Yaseer".

"tunda bazaki tashi muyi magana ba nizan wuce".

"OK ka rufemin k'ofa".

Yaseer ya juya ya fice daga cikin d'akin tareda jawo k'ofar ya rufe cikin matuk'ar b'acin rai da damuwa cunkushe cikin bak'in ciki, d'aki Yaseer ya shiga ciki ya kwanta saman gadonsa yana tunanin rayuwarsa ta baya rayuwar daya taso cikin matuk'ar k'auna da soyayyar iyayensa.

********************
Washegari da safe misalin k'arfe goma sha d'aya Yaseer ya fad'a cikin bathroom yayi wanka d'aure da towel ya fito, direct wurin dressing mirror ya nufa yayi tsaye yana taje sumar kansa k'aramin towel d'in ya goge jikinsa dashi sannan ya shafa lotion ajikinsa, ya d'auko dakakkiyar shaddarsa ya zura ajikinsa ya kawo turarurka masu k'amshi maida turaren yayi cikin kwali ya aza kan mirror, hularsa ya sanya ya jawo k'ofar d'akin ya fice daga cikin gidan da sauri.

Bayan fitarsa Fauzeeya ta dinga yamutsa fuskarta domin yanayin jikinta batajin dad'insa, zaune take saman kujera tana shan tea kad'an kad'an kamar bataso kallo d'aya zakayi mata ka gane batajin dad'in yanayin jikinta tana gama shan tea ahankali ta mik'e tsaye ta nufi cikin d'akinta, tana shiga room d'in kawai taji zuciyarta tana tashi kayan cikinta sun hautsine da sauri ta fad'a bathroom ta dinga kwara amai kamar d'iyan hanjinta zasu fito, amai ta dingayi kamar numfashinta zai d'auke ta kwarara amai mai yawa dak'yar ta samu aman ya tsagaita ta kwarara ruwa anan amai yabi ruwan, wanke bakinta tayi da brush tana sauke numfashi ahankali ahankali ta fito daga cikin toilet ta kwanta saman gado tana numfashi da nishin wahala cikeda matuk'ar galabaita, jiri ne take gani cikin k'wayar idanunta wani irin yanayi ne wanda batasan ma'anarsa takeji cikin gangar jikinta.

Nazifa tana shafa mayukan gashi akanta tana fuskantar madubi phone d'inta aje saman kan mirror kitso takeson zuwa amma bata tambayi izinin Yaseer ba, can wayarta ta fara ruri tana neman agaji receiving call tayi ta kara wayar akunnenta tace"Ummu barka da yau".

"k'alau baby ya kike ya yara?".

"Alhamdulillahi".

"mijinki ya fita ne?".Inji hajiya Ramlat.

"eh yanzun nan ya fita ko akwai wata magana ne?".

"akwai magana baby su Baura suna nan tafe sai kiyi dabarar da zasu shigo cikin gidan batare da kowa ya gani ba, bayan sun shiga cikin gidan ki kaisu har d'akin Fauzeeya akwai abinda zasuyi mata wanda zai zamo silar mutuwar aurenta inyaso shegiyar ta k'ara gaba tabar miki mijinki! ".

Nazifa ta k'yalk'yale da dariyar murna harda tsalle adalilin farin ciki tace"kice k'aryarta ta kusa k'arewa Ummuna wlh ban tab'a jin dad'i irin yau ba".

hajiya Ramlat ta musk'uta tace"aina gaya miki muddin ina raye babu ke babu kukan takaici aduniya kedai ki iya takonki domin banason asamu matsala asirinmu ya tonu! ".

"kwantar da hankalinki Ummu da yardar Allah asirinmu bazai tab'a yiyuwa ba saboda nasan yadda zan tafiyar da komai cikin tsari da salon dabara".

"shikenan duk yadda ake ciki ki kirani ki gayamin sai anjima".

"OK zan kiraki Ummu sai anjima d'in".Tana k'arasa maganarta taji hajiya Ramlat ta katse wayar dif Nazifa ta jaye wayar akunnenta cikin matuk'ar farin ciki da murna mara misaltuwa, ji takeyi duk bak'in ciki da tsantsar damuwar da take ciki ya gushe saboda wani irin nishad'i takeji cikin zuciyarta fiyeda zato, ji takeyi tamkar anyi mata bushara da shiga aljanna domin ta k'agu da matsuwa akan Fauzeeya tabar mata gidan ita kad'ai ta rayu cikinsa saboda idan ka cire mutuwa babu abinda ta tsana kamar *KISHIYA*!.Duk abinda take fad'a sai akunnen Tasallah data gifto zata shiga cikin kitchen tayi goge goge sai taji Nazifa tanayin waya, zuciyarta ta umurceta data tsaya ta saurari abinda suke fad'a domin alokacin taji bata yarda da ita ba kuma gabanta yana yawan fad'uwa, komai taji hakan ne yasa zuciyarta ta tsinke hankalinta yayi k'ololuwar tashi fargaba da tsantsar tsoro ne ya bayyana k'arara afuskarta! Ta rasa yadda zata b'ullowa al'amarin ta rasa yadda zatayi ta taimakawa rayuwar Fauzeeya saboda ita har azuciya tana sonta saboda kirkinta da girmama mutane ko waye kai k'arya kakeyi kace ta munanawa rayuwarka.

Cikin rashin kuzari Tasallah ta juya ta koma cikin d'akinta arazane jikinta sai rawa da kad'uwa yakeyi kafkafkaf kamar mai jin sanyi, zaune tayi tana tunanin mafita da dabarar da zata fissheta domin tana ji tana gani bazata tab'a barin acutar da rayuwar baiwar Allah ba akunsa mata bak'in ciki rayuwarta ta lalace abanza!.

Fauzeeya baiwar Allah tana cikin d'akinta zazzab'i duk ya saka mata rashin k'arfin jiki da kuzari tayi kwance saman gado rigiggine fuskarta na fuskantar ceiling dake saman d'akin,tunanin mijinta kawai takeyi idan ta lumshe fararen idanunta dad'i takeji aranta adalilin da tayi dace da *MASOYIN GASKIYA* murmushi ne kwance cikin yalwatacciyar fuskarta mai d'auke da hasken annuri, can tunanin mahaifiyarta marigayiya Latifa ya fad'o mata arai ai kuwa hawaye suka dinga shatata afuskarta babu k'ak'k'autawa domin ta tuna mai k'aunarta jigon rayuwarta, saka hannu tayi ta share hawayenta tsab zuciyarta cunkushe da damuwa da zogin rashin mahaifiya.

_Allah sarki kukan da Fauzeeya takeyi ya sakani zubar da kwallar zallar tausayi 😢 ni Mugirat domin rashin mahaifiya babban rashi ne arayuwar 'ya'ya, saboda mahaifiyarki itace ke iya sadaukar da farin cikinta akan na yaronta itace ke k'ok'arin ganin ka zamo wani abu arayuwa, ubangiji ina rok'onka ka jik'an iyayenmu ka haskaka kabarinsu tareda basu aljanna firdausi._😭🤲🏻😭

Nazifa tana cikin d'akinta kiran waya ya shigo tayi receiving call tace"hello kuna waje? ".Ab'angaren daban naji ance"eh mana ke kad'ai muke jira autar hajiya ".Nazifa ta sanya takalminta tace"Ok gani nan zuwa kar kuje ko'ina "."Muna jiranki".Suna kammala maganar Nazifa ta katse wayar ta fito daga cikin d'akinta tana tafiya tana kalle kalle har ta iso tsakiyar compound d'in gidan direct d'akin baba maigadi ta lek'a taga yanata barci su Baura zaune cikin d'akin sunyi shiru, shiga room d'in tayi tana musu kallon mamaki afuskarta tace"mi kukayiwa wannan sakaran tsoho yaketa barci haka? ".
Cikin muryar 'yan duniya Baura yace"maganin barci muka saka mishi cikin ruwan shansa ".
Nazifa ta k'yalk'yale da dariyar mugunta can ta tsagaita tace"gaskiya kunyi dabara Baura lamarinku akwai tunani da iya tako".

"autar hajiya aikinmu babu wasa cikinsa".
Nazifa ta gyara tsayuwarta tace"ku taso muje ciki kuyi abinda zakuyi kada Yaseer ya dawo ya riskeku asirina ya tonu! ".Tana rufe bakinta su Baura suka mik'e tsaye suka fito daga cikin d'akin itace gaba suna biye da ita, har suka iso tsakiyar parlourn babu kowa tsit kakeji sai k'arar TV aparlour giftawa sukayi suka wuce direct room d'in Fauzeeya suka nufa.............

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 47*



Suna tura k'ofar room d'in sukayi rududududu suka shige kwance saman gado suka isketa tanata sharar barcinta cikin kwanciyar hankali da natsuwa, kallon fuskarsu Nazifa tayi tace"kunga yanzu barci takeyi kuyi sauri ku aiwatar da nufinku kafin ta farka nizan koma cikin parlourn ina ganin mai shiga da fice saboda tsaro".Baura ya murtuk'e fuskarsa yace"karki damu za'ayi komai cikin sirri agama babu wanda zai ganmu".Nazifa ta murmusa tace"Ok ba damuwa idan kuka kammala duk abinda kukeyi ku sameni cikin parlour"."To autar hajiya".Nazifa tana gama maganarta taja k'afafunta ta fice daga cikin d'akin ta koma parlour da zama.
Ganin ta fita yasa Baura ya dubi yaransa biyu yana lasar baki domin kuwa ya fahimci alamar zaiji dad'i ajikinta cikin bada umurni da gadara yace"kuhau saman gadon ku d'auremin ita domin kada ta bani matsala".
Yaran suka hau saman gado suka d'ad'd'aure k'afafuwa da hannayenta ware mata k'afafunta sukayi cikin barci taji kamar ana tab'ata, ai kuwa nan take ta bud'e idanunta da suke rufe suka fad'a cikin nasu gabanta ya buga da k'arfi zuciyarta ta girgiza hankalinta yayi k'ololuwar tashi gabanta ya dinga luguden tsoro da fargaba! Jikinta karkarwa da makarkatar tsoro yakeyi d'iyan hanjinta suka hautsine tayi kalar tausayi tana kallon yadda suka d'ad'd'aureta tace"bayin Allah mi nayi muku? Kuyiwa girman Allah ku rufamin asiri ku kwanceni kada mijina ya dawo yayi zargin wani abu!".
Baura ya bushe da muguwar dariya can ya tsagaita yace"Fauzeeya kenan mu rufa miki asiri kikace fa ai babu wani tausayi atsakaninmu ayau ina tabbatar miki saina sha zumarki".

Marairaice fuskarta tayi ta fashe da kuka tace"na shiga uku! Kayi hak'uri karkayimin haka please na rokeka".

Daka mata rikitacciyar tsawa da hargowa yayi yace"keeeeee!Ki rufemin baki kafin in kasheki in binne gawarki anan".

"kayi... ha... ku....ri... karka.. za.. mo..silar mutuwar aurena...! ".

"nace ki rufemin bakinki ko yanzu lahira tayi manyan bak'i!".

Jikin Fauzeeya yana mazari da makarkatar fargaba Baura ya tunkarota gadan gadan Fauzeeya ta rasa yadda zatayi gata ad'aure babu halin guduwa, Baura ya iso wurinta yahau saman gadonta ya isa wurinta yana had'iyar miyau mak'wat a mak'oshinsa, da shaggun idanunsa yake k'arewa surar jikinta da kallo sanya hannunsa yayi yana shafar fuskarta yace"ki kwantar da hankalinki masoyiyata bazan cutar dake ba dad'inmu kawai xamuji inyi tafiyata".
Hawaye sai shatata sukeyi afuskarta ta girgiza kanta tace"karka cutar dani na rok'eka".
Aza hannu yayi saman bakinsa yace"shitttt kiyimin shiru kina cikamin dodon kunne da surutun banza".

Fauzeeya bata sake magana ba yayinda yaran Baura suka fita daga cikin d'akin suka koma bakin k'ofar room d'in suna jiransa ya aikata abinda yakeso da ita, Baura ne ya fara cire tufafinsa ya koma dagashi sai guntun wando da singlet yana kammala cire tufafinsa ya dawo wurinta, kissing d'inta yaje yi ta kauda fuskarta ya hasala sosai ya kasheta da gigitattun maruka biyu masu k'yau wanda asanadiyyar haka saida ta buga kuwwa da razananniyar kururuwa tana kuka nunata da yatsa daidai saitin fuskarta yayi yace"tunda na lura lalama batayi dake to sai nayi amfani dake ta k'arfin tsiya nama lura cikine dake ashe lusarin mijinki yana iya yiwa mace ciki na zata ya mutu tuntuni".

"mijina ba lusari bane!".

"tunda yana baki dad'i kina sha".K'arasa maganarsa keda wuya ya sanya hannunsa ya kaiwa na fulaninta chapka ta kauce da hanzari mangareta yayi har ya fashe mata baki jini ya dinga tsattsafowa yana tsiyaya, wani irin zogi da ciwo takeji awurin tana rusar kukan takaici tana cewa"wayyo Allah yayana kazo ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login