Showing 87001 words to 87802 words out of 87802 words

Chapter 30 - SAKACI BY MUGIRAT MUSA

05 Jul 2024

4254

sai kallon Fauzeeya takeyi da cikinta ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe.

Ahaka suka cigaba da gudanar rayuwar gidansu cikin mutunci da girmama junansu domin yanzu Nazifar da kuka sani ada mara mutunci ta chanza halayyarta, wani irin k'auna da tarairayar Fauzeeya takeyi domin ta fahimci yanzu babu abinda Yaseer yakeso da k'auna fiyeda Fauzeeya, duk dayake yana k'okari wurin ganin baya nuna bambanci atsakaninsu tareda daidai adalci atsakaninsu domin bayason asamu wata b'araka ta fito daga wurinsa, haka suke tafiyar da aurensu cikin so, yarda, tausayi, juriya, kawaici, soyayyar gaskiya, in tak'aice muku komai tare sukeyi na ayyukan gida saboda yanzu Fauzeeya ta koya mata girke girke da duk abinda bata iya ba, ganin kansu ahad'e yake yasa yah Yaseer ya sallami Tasallah da k'yautar kud'i da kayayyaki ta koma gidan ubanta domin ta samu kud'in siyen kayan d'aki.

**********************
*BAYAN SHEKARA BIYAR*

Cikin wad'annan shekaru biyar abubuwa da dama sun faru na farin ciki dana bak'in ciki, Fauzeeya ta haifi 'ya'yanta maza 'yan tagwaye Salman da Sadik bayansu ta haifi santaleliyar d'iyarta k'yak'k'yawar gaske Sadiya ana mata lak'abi da Amrah yanzu tana nan d'auke da jaririn ciki, itama Nazifa ta sake haihuwar Muslim da Ramlat suna kiranta da mama.
Zamantakewar rayuwar gidansu sukeyi cikin zaman lafiya da k'aunar juna kan ya'yansu ahad'e yake komai tare akeyi musu, shiyasa Yaseer yake alfahari da shiriyar Nazifa saboda yanzu ta aje batun business Anwar tabarwa amana yana kulawa dashi, sai ya zamo tana koyi da k'yak'k'yawar halayyar Fauzeeya .

Su Nazifa ne na hango cikin kitchen atare suna kichaniyar dafa abincin rana yayinda Nazifa ke dafa farar shinkafa Fauzeeya tana k'ok'arin had'a miya, k'amshin girkinsu duk ya gauraye cikin parlourn da gidan gaba d'aya domin dukansu sun k'ware wurin sarrafa abinci kala kala.
Nazifa ta dubi fuskar Fauzeeya cikin kulawa tace"k'anwata k'amshin miyarki duk ya gauraye ciki da lungun gidan nan daga gani girkin zaiyi dad'i ".Fauzeeya tayi murmushin daya bayyana fararen hak'oranta tace"hmm Aunty ina wani dad'i anan kawai kuyi maneje har in sauka lafiya kinsan wata rana ciki yakan haifar da kasala ".Nazifa ta musk'uta cikin yanayin farin ciki tace"kina iyakar bakin k'ok'arinki k'anwata burinmu shine ubangiji yasaukeki lafiya ".

Fauzeeya taji matuk'ar dad'in kalamanta murmushi k'unshe afuskarta tace"amin Auntyna".Tana kammala maganarta saiga Amrah ta shek'o da gudu ta shigo cikin kitchen yayinda Muslim ke biye da ita yana huci kamar zaki, tana isowa wurinsu ta fad'a ajikin Nazifa tana zumbura baki cikin shagwab'a kammaninta sak Fauzeeya tace"Mommy ga yah Muslim nan zai dokeni".Nazifa ta k'ank'ameta cikin matuk'ar k'auna tace"mi kikayi masa ne Amrah? "."Banyi masa komai ba".Cewar baby Amrah, Fauzeeya ta harareta tace"k'arya kikeyi Amrah".Ta bushe da dariya tace"da gaske nakeyi ".Alokacin ne Muslim ya iso azuciye zai bugi Amrah mommy Nazifa ta chapkesa tace""kai kai dakata aiko mutuwa tana kunyar idon mahaifi".

Muslim ya b'ata fuska cikin sagarci yace"zagina takeyi mommy tana yimin gwalo saboda haka saina bata kashi".Fauzeeya tace"karka yarda ka bata iya ka bata kashi sai tayi fitsari awando ai baifi d'a ba".Nazifa ta kalleta da harara tace"kaga Muslim kyale maminku zan siya maka biskit idan baka bugeta ba".Muslim yace"bazan bugeta ba mommy ".Amrah tayi charap tace"nima ina cin biskit"."OK zan siya miki ".Inji Nazifa can babu dad'ewa suka kamala dahuwar abincin tareda sakawa cikin kuloli direct dinning table sukaje jajjara samansa.
Haidar mijin Safiya daya samu labarin itace silar mutuwar auren Nazifa nan take yayi mata saki uku ta koma gidansu da zaman zawarci, yaransa ya amshe daga hannunta hak'ik'a awannan lokaci Safiya tayi kukan takaici da nadamar rayuwa daga k'arshe taje har wurin Nazifa ta rok'eta gafara dak'yar ta yafe mata, cikin haka ne ta samu mijin aure warin babanta ya aureta idan ta tuna irin abubuwan data aikata arayuwarta sai tayita zubar da kwallar zallar nadama, rayuwa kenan wata rana sai labari ka aikata alkhairi shine yafi dacewa ka guji aikata sharri wato anan kun fahimci cewa *K'AIK'AYI* ne ya koma akan mashek'iya......
Su Baura kuwa gidan yari aka kaisu aka kulle shida yaransa suna yin aiki mai wahala da tsanani na tsawon shekaru.......

*ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN.*
_Hmmmmmm laifin dad'i k'arewa duka duka anan na kawo k'arshen wannan littafi nawa mai suna *SAKACI* ina rok'on ubangijina Allah ya yafe mini kuskuren da nayi cikin wannan novel nawa, abinda na fad'a daidai ubangiji yayi mini sakamakon Alkhairi ina fatar makaranta littafina zasu d'auki darasin dake cikin wannan labari su watsar da abinda ba daidai ba._

_Ku cigaba da kasancewa dani akowane lokaci masoyana ku sani ni Mugirat Musa ina alfahari da masoyana aduk inda kuke aduniya banda kamarku, saboda ni daku nake gadara kuma arayuwata inason mai mai sona harma da mak'iyana ku tuntub'eni da wad'annan nombobi domin samun littafaina documents ko pages gasu:08163650557 or 08035370039._

~Sai kun jini a sabon novel d'ina mai suna *B'ARAUNIYA*~.



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login