Showing 42001 words to 45000 words out of 87802 words
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 25*
Acikin gidan Iya Kulu Baura sai zagayar filin gidan yakeyi yana kai da komo cikin matsananciyar damuwa da bak'in cikin rashin samun nasarar da baiyi ba akan Fauzeeya, zuciyarsa sai zogi da k'una takeyi masa ya rasa abinda yakeyi masa dad'i aduniya domin ya riga ya kwallafa ransa akanta ya kuma yi alk'awarin ko waye zata aura saiya biya buk'atarsa akanta tareda kauda duk wani kwad'ayi da yakeyi akanta.
Yana tsaye ya kasa zama saiga yaransa sun dawo cuwul -cuwul agalabaice, duba d'aya zakayi musu ka gane sun wahala da shan matuk'ar wuya ganinsu yasa ya k'ara hasala domin yaga basu kamo ko mutum dayarsu ba yace"har kun dawo wawayun banza!".
"afuwan Oga sai hakuri duk sun gudu ko mai kamadasu bamu gani ba".
Baura yaja tsoki mtsssssss cikin zafin rai yace"kunyi *SAKACI* har sun gudu tareda sanyamu hasarar mak'udan kud'i awurin hajiya Ramlat".
"auuu Oga gaya mata gaskiya zakayi kace mata sun gudu ne kawai kace mata mun cika umurninta?".
"bakuda hankali halan ance muku anan gaba kad'an bazata gano gaskiyar al'amarin ba, ku wuce mu tafi zuwa inda muka saba had'uwa da ita hajiyar in kirata in sanar mata abinda ake ciki".
"to shikenan Oga duk yadda kayi daidai ne".Suka fad'a.
Yayinda Oga Baura ya shiga gabansu suna biye abayansa suna take masa baya kamar sarki da fadawansa, tafiya sukeyi sannu ahankali har suka fita daga cikin gari suka nufi hanyar kusurgumin daji wanda yakeda d'an nisa daga cikin gari zuwa nan, suna isowa wurin da suke rayuwa sai naga babbar rumfa da kujeru cikinta agefenta ga wani gida nan kusa garesu wanda suke rayuwa cikinsa.
Kujera suka d'aukowa Ogansu da sauri suka kawo masa ya zauna yayinda suka sakashi tsakiya yar k'aramar phone d'insa ya lalabo cikin aljihunsa yayi dialling nombar hajiya Ramlat, nombar ta shiga d'id'id'id'id'i alamar kira ya shigo hajiya Ramlat dake d'aure da towel ajikinta ta isa wurin wayarta da sauri tayi receiving call d'insa tace"hello Baura ya akayi ne ina fatar kun cika umurnina?".
Baura ya sassauta murya cikin tattausan lafazi yace"an samu akasi hajiya!".
Rasssss gabanta ya fad'i amma saita tattaro dauriya tace"an samu akasi fa kace ta yaya hakan ta kasance Baura?".
"wato hajiya da muka je gidan mu samu sa'arsu munyi musu shegen matsiyacin duka amma ban samu damar aiwatar da umurninki ba na cewa in ketawa Fauzeeya haddi, saboda haka saidai kiyi hak'uri zuwa wani lokaci zanyi miki yadda kikeso".
Hak'ik'a hajiya Ramlat bataji dad'in yadda Baura bai lalatawa Fauzeeya rayuwa ba amma ya ta iya tunda sun gudu dak'yar ta bud'i bakinta tace"shikenan ba damuwa Baura amma kuyi k'ok'ari karo na biyu ku samu nasara akansu".
"karki damu hajiya da girman kujerarki".
K'it hajiya Ramlat ta katse wayar ta shafa lotion tareda saka tufafi tsadaddi ajikinta turare mai k'amshi ta kawo ta sanya ajikinta.
Baura yana kammala waya ya dubesu yace"baku k'yautawa hajiya ba hak'uri kawai ne tayi amma ba domin taji matuk'ar dad'i ba".
"kayi hak'uri Oga ba za'a koma samun kuskure ba".
"hmmm Allah yasa".
"amin amin Oga Baura".
*********************
Su Fauzeeya suna guduwa suka nufi hanyar gidan baba Labaran da masifaffen gudu har na tashin hankali!suna shiga cikin tsakiyar filin gidan sukayi rududududu suka fad'a cikin d'akin Inna Munari afirgice saida suka tsorata su baba Labaran jikinsa yana kad'uwa yace"kai kai kai! Lafiya miye ya koroku haka!?".Yayi tambayar cikin zullumi da fargaba.
Jikinsu Iya Kulu sai mazari da rawar tsoro yakeyi kallo d'aya zakayi musu ka gane arikice suke suna cikin tsananin fargaba da tsoro, baba Labaran ganin basu bashi amsar tambayarsa ba yasa hankalinsa ya k'ara d'unguma Inna Munari kallonsu kawai takeyi awalak'ance babu wani tsoro da firgici afuskarta, dak'yar Iya Kulu ta musk'uta tareda tattaro natsuwa ta sanya azuciyarta cikin sanyin jiki tace"Labaran maciji ne ya koromu! ".
Fauzeeya da Adama sunyi mamakin yadda Iya Kulu bata gaya masa gaskiyar al'amari ba amma idan sukayi la'akari da duba da cewar akwai abinda take b'oyewa, shiyasa kwata kwata basu zargeta da komai ba sai alkhairi.
Baba Labaran ya d'an samu natsuwar zuciya yace"hmmm ubangiji ya k'ara kiyayewa ku zauna inji gari in samo masu kashe maciji su kashesa!".
Inna Munari tayi charap cikin rashin mutunci da tausayi tace"su zauna ina akan maciji zasu shigo mana cikin gida?To wallahi bazata sab'u ba saidai su tattara su koma inda suka fito yanzu saboda ni bazan iya zama da shaggun mutane ba! ".
Baba Labaran ya dubeta cikin matuk'ar mamakin maganarta zuciyarsa tayi masa wani irin soka acan ciki cikin hasala yace mata"Munari banason hauka fa yanzu mahaifiyata kike kira da mutuniyar banza! Bari kiji babu inda zasuje saboda ba gidanki bane nawa ne nikeda iko da abina idan zamansu zai iya tare miki wani abu ki koma gidanku! ".
Inna Munari ta girgiza kanta cikin masifa tace"zama daram Labaran babu inda zanje na riga na zamar maka mutu ka raba takalmin kaza! Saidai su tarkata su koma inda suka fi auki ".
"baki isa Munari kinyi kad'an kice mahaifiyata da d'iyata bazasu zauna cikin gidan nan saidai ke kibar gidan tunda ba naki bane".
"yimin shiru tijararren wawa gida gareka ko kango! Gidan da babu tsari babu kama shi kake tink'aho da gadara akansa! ".
"ko yaya yake dai yafi gidan ubanki mai kwasar bola!".
"ubanka dai wanda bai mutu ba saida ya tsine maka albarka! ".
Ganin abin nasu yak'i karewa yasa Iya Kulu ta dakawa baba Labaran tsawa tace"ya isa Labaran ka k'yaleta ita mace ce tanada k'arancin tunani".
"Iya ki barni da ita saita gayamin lokacin da mahaifina ya tsine mini albarka kafin ya rasu idan ba haka ba zamu kwashi 'yan kallo nida ita ".
"bakajin maganata ko ?".Inji Iya Kulu cikin rashin son fitina.
"bawai bana jin maganarki ba Iya raini da walak'ancin da matar takeyimin shekara da shekaru ya isheni! Saboda haka yau saina k'arshen hauka da rainin mutuncinta".
Iya Kulu ta juya ta kallisu Fauzeeya tace"tunda bayajin magana ku tashi mu koma d'ayan d'aki".Tana kammala yin maganarta suka d'unguma suka fice daga cikin d'akin.
Inna Munari tana ganin su Iya Kulu sunyi ficewarsu hankalinta ya tashi hanjin cikinta ya hautsine zuciyarta ta tsinke gabanta sai dukan uku uku yakeyi, amma saboda ta nuna masa bata tsoronsa tace"dallah gafara can bani wuri in wuce inada aikin yi ".
"kije ina? Ai babu inda zakije sai kin gayamin ranar da mahaifina ya tsinemin!".
"kai Labaran banason d'ibar albarka ka bani hanya wuce ko yanzu inci mutuncinka ".
"bazan baki hanya ba idan kinada k'arfi kizo ki wuce".
"sai ko na wuce".Inna Munari tana k'arasa maganarta ta dinga dube dube ko zaki zata hango wani makami ta buga masa, shidai tsaye yayi yana kallonta yaga abinda zatayi can idanunta ya sauka akan muciyyar tuwo ta isa wurin mucciyar ta sanya hannunta ta d'auko ta tunkari baba Labaran gadan gadan da mucciyar ahannunta, tsaye yayi k'yam yana k'are mata kallo ko kiftawa baya yi.
Dayake Inna Munari hankali bai isheta ba tana isowa gab da wurinsa ta d'aga mucciyar sama zata buga masa kenan, baba Labaran cikin zafin nama ya chapki hannunta ya murde tareda kwasheta da mari biyar masu zafi da hargitsa tunani! Ai kuwa nan da nan Inna Munari ta saki razananniyar kuwwa da k'ara mai rikita k'wak'walwar d'an Adam jinta da ganinta suka d'auke cak na wucin gadi.
Cikin suk'uwa da tafasar zuciya yace"gobe ki sake d'auko makami da niyar buga mini kiga irin hukuncin da zanyi miki sai yafi wannan muni!".Rufe bakinsa keda wuya yaja k'afafunsa ya nufi hanyar kasuwa domin ya siyowa su Iya Kulu abinci saboda yasan ko Inna Munari ta girka ba basu zatayi ba domin batada rayuwar k'warai.
Anan yabar Inna Munari tanata kukan bak'in ciki da tsantsar takaicin rayuwa domin arayuwarta baba Labaran bai tab'a d'aga hannu ya mareta ba sai yanzu, sannan gwargwado duk abinda tace tana so shi yakeyi mata saboda yana masifar sonta amma yanzu ta lura ko kashi ya fita daraja awurinsa.
**********************
Baba Labaran yana fita bada jimawa ba ya aiko yaro ya kawo musu abinci suka ci, sannan sukayi alwala suka kabbarta sallah suna kammala suka sake bud'e sabon shafin fira.
Suna zaune saiga Inna Munari ta shigo cikin d'akin amasifance suna ganinta suka ja bakinsu sukayi shiru, Iya Kulu ce ta dubeta tace"Munari lafiya mi kike nema?".
Inna Munari tace atsiwace "Kulu tsohuwar argunguma nake nema!".
Da sauri suka kalleta cikin k'unar zuciya Adama tayi charap tace saboda ita arayuwarta ta tsani walak'anci da rainin wayo "kece argunguma bak'ar makirar mace! ".Inna Munari ta bugi k'irji da k'arfi tace"ni kike kira da makira!? "."Ance miki makira abinda yafi hakan ma zan iya ce miki ".Inji Adama Iya Kulu tayi mata alamar ta daina tanka mata amma ina idanun Adama sun riga sun rufe zuciyarta ta kawo awuya, Inna Munari ta nunata da yatsa tace"tabbas zakisan kin zageni yarinya ahaife na haifeki".Adama ta wurga mata harara taja tsoki mtssss tace"banga alamar kin haifeni ba saboda banga 'ya'ya agabanki ba! ".
Hak'ik'a maganarta ta soki k'ahon zuciyarta tareda sanya k'una da rad'ad'in ciwo azuciyarta hucin takaici tayi tace"ni kikewa gorin haihuwa kuma? ".
"nayi miki idan fitsari banza ne kaza tayi mu gani! ".Cewar Adama cikin son tashin hankali da fitina!.
"zakiyi dana sanin yin sa'insa dani arayuwarki! ".
"kema zakiyi nadamar sa'insa dani Munari saina nuna miki ke k'aramar shed'aniya ce! ".Inji Adama Inna Munari tayi tsaye tana mamakin yadda Adama ke mayar mata magana babu tsoro ko shakku cikin k'wayar idanunta, ganin haka ne yasa Inna Munari bata sake magana ba taja k'afafunta fuuuuu ahasale tabar d'akin tana ficewarta, Iya Kulu ta murmusa tace"Adama bakida tsoro tun d'azu nakeyi miki siginal da ido akan ki k'yaleta amma saida kika biyeta mata ".Fauzeeya tayi saurin cewa "gara da taci mata mutunci Iya saboda matar nan batada natsuwa da hankali atsarin rayuwarta ".Adama ta sake gyara zamanta tareda bintsire baki tace"wato Iya na fahimci idan banci mata mutunci ba raini da iskancinta saiya fi haka sannan taya za'ayi ta iskomu har cikin d'aki da nufi ta ci mana mutunci tareda tozartamu wannan ai kinsan walak'ancin yayi yawa, duk yadda ka raina mutum karka fara iskeshi har inda yake da sunan tozartawa! "...........
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 26*
Fauzeeya ta nisa cikin zafin rai da nadamar amincewa da auren Yaseer domin ayanzu ta matuk'ar tsorata da k'ara tsinkewa gameda Nazifa, ta tabbatar ayanzu babu abinda suke muradi sai sunga bayanta ma'ana farautar rayuwarta sukeyi akowane lokaci!.
Hakan ne yasa tace"gaskiyar zancenki Adama abin ba dad'i wato Inna Munari tun asalin rayuwarta kawo yanzu batada mutunci bata ganin kowa da gashi akai sai kanta".Iya Kulu ta musk'uta cikin yanayin damuwa tace"hak'uri zakuyi ku daina biye mata har sai anyi bikinki lafiya zan koma can gidan saboda yanzu idan har muka kuskura muka koma babu shakka sai sun lalata miki rayuwa Fauzeeya wanda ko amafarki bana fatar haka! ".Adama jikinta yayi lak'was cikin matsananciyar damuwa da bak'in ciki tace"wannan maganar taki gaskiya ce Iya saidai mu dingayi kaffa kaffa da taka tsan-tsan akodayaushe Fauzeeya saboda mutanen nan basuda imani da tausayi azuciyarsu ".
Fauzeeya tayi rau rau da idanu kwallar zallar tsoro da fargaba ne suka taru cikin k'wayar idanunta wani irin d'aci da zogi zuciyarta keyi dakyar tace"ni wallahi duk na tsorace da auren Yaseer arayuwata mutum ace babu halin yace zaije wani wuri kenan batare da wad'annan mutanen sun biyoni ba wayyo Allah naga ta kaina ni Fauzeeya, ubangiji Allah ina rok'onka kayimin katangar k'arfe daga fad'awa sharrinsu".
Adam ta dafa kafad'arta cikin tausayi da tsantsar k'aunar Fauzeeya tace"ki daure ki cire komai azuciyarki da yardar Allah bazasu samun damar cutar dake ba kedai ki dage da yawan addu'ar ubangiji ya karemu daga sharri da kaidinsu".
Iya Kulu cikin jimamin abinda yake faruwa dasu tace"amin ya rabbi lamarin sai ahankali kana kwana anayi maka minshari amma na k'ara tabbatarwa ayau hajiya Ramlat da d'iyarta Nazifa basuda d'igon imani da tausayi ko kad'an azuciyarsu".
"haka ne gaskiyar maganarki Iya Kulu".
Tattaunawarsu suka cigaba dayi domin su samu mafita amma ina basu hango komai ba, kowaccesu sak'a da warwara ta dingayi azuciyarta.
*********************
Da maraice muna zaune cikin d'aki nida Adama muna shan furar da Iya Kulu ta aika aka siyo ta dama, saiga sallamar yaro ya shigo har cikin tsakiyar d'akin ya kallesu yace"barkanku da yini".
"barka dai".Inji Adama".
Yaro ya sake cewa"wai ana sallama da Aunty Fauzeeya awaje".
Adama ta dubesa da sauri ta jefo masa tambaya tace"waye yake sallama da ita?".
"yana nan waje da mota bak'a wulik".Inji Yaron.
Fauzeeya ta murmusa cikin sanyin jiki tace"yi tafiyarka kace masa ina zuwa".
"to Aunty".Cewar yaron tareda juyawa ya fice daga cikin gidan da sassarfa.
Adama tace"kin gane ko waye da zaki ce ya tafi ne Fauzeeya?".
"hmmm babu mai zuwa wurina sai Yaseer saboda haka ina tsammanin shine yazo".
"OK ki tashi ki kintsa jikinki".
Fauzeeya tace"to k'awata".Ta mike tsaye dak'yar ta lalabo hijabinta ta sanya azuciyarta babu abinda takeyi mata dad'i saboda yadda taga ana farautar rayuwarta asanadiyyar zata auri Yaseer, bayan tasan ba haramun bane kuma bata ci amanar Nazifa ba domin itace tayi sake da rashin kulawa da mijinta.
Kallon Adama tayi da zata wuce tace"na tafi".
"to sai kin dawo".Inji Adama.
Fauzeeya ta nufi hanyar fita daga cikin gidan tana isa waje ta hango Yaseer tsaye ya jingina jikinsa ga motarsa yayinda abokinsa Abduljalal yake zaune cikin motar, tun daga nesa ya tsura mata idanunsa masu haske yana mata kallon so da k'urilla ita kuma sai sunne kanta takeyi domin batason su had'a ido, tafiya takeyi atsanake har ta k'araso wurin Yaseer wanda ya mace akan soyayyarta k'amshin turarensa ya bugi hancinta ta lumshe fararen idanunta, Yaseer yaja numfashi yace"barka da zuwa amaryata sarauniyar mata".
"barka dai an wuni lafiya?".
Yaseer ya dubeta yayinda kanta yake noce a k'asa yace"k'alau na wuni my Fauzee ina k'awarki Adama?".
"tana gida".
"OK bari ki gaisa da babban aminina Abduljalal domin kusan juna idan kun gama gaisawa sai kije kiyimin sallama da k'awarmu Adama".Ya fad'a azolaye.
"to yaya".Cewar Fauzeeya.
Yaseer yayi knocking d'in glass Abduljalal ya bud'e k'ofar motar da murmushi k'unshe afuskarsa yace"kai lafiya kake damuna dayin knocking?".
"matata nakeson ku gaisa kusan juna".Cewar Yaseer.
"OK ba damuwa".Inji Abduljalal bayan ya fito daga cikin motar ya isa wurin Fauzeeya dake tsaye yayi mata sallama ta amsa masa cikin sakin fuska, gaggaisawa sukayi cikin mutunci da karamci sannan Abduljalal ya k'ara da cewa"Fauzeeya ina fatar idan har ubangiji ya k'addari aurenku da abokina zaki rik'eshi amana tareda bashi kulawa da tsantsar *SOYAYYAR GASKIYA*,saboda maganar gaskiya kin sacewa abokina zuciya farat d'aya bayada kuzari da k'arfin jiki asanadiyyar tunaninki, hak'ik'a sonki ya riga mamaye zuciya da ruhinsa domin bayada *ABAR SO* da bege fiye dake saboda haka ki zamo mace kwantar da hankalin mijinki da share masa hawaye, kada ki bari mak'iyanku su ganku arana suji dad'i kada ki kuskura ki bari wata k'awarki ta zugaki akan ki sabawa umurnin mijinki sau da yawa mafi akasarin mata k'awaye ne ke zamo sanadiyyar mutuwar aurensu".
Kunya ce kwance afuskarta tace"karka damu da yardar Allah zan bashi kulawa na musamman idan har mukayi aure sannan ba za'a samu matsala daga wurina ba".
"naji dad'in kalamanki Fauzeeya ubangiji ya nuna mana lokacin aurenku".
"Amin amin nagode sosai da nasiha".
"ba komai ai yiwa kaine".K'arasa maganarsa keda wuya ya ciro kud'i daga cikin aljihunsa ya mik'a mata tak'i amsa tana girgiza kanta alamar a'a, Yaseer kallonsu kawai yakeyi yana murmushi k'unshe afuskarsa.
Abduljalal ya dubeta yace"ki amsa mana"."Da kabar kud'inka kawai nagode sosai".Inji Fauzeeya.
"ki daure ki amsa zasuyi miki amfani wurin hidimar biki".Cewar Abduljalal cikin lallashi da lalama.
Ganin ya matsa da nacewa yasa Fauzeeya ta amshi kud'in ahannunsa cikin kunya tace"nagode ubangiji ya k'ara bud'i na alkhairi".
Tabbas yaji matuk'ar dad'in addu'arta har cikin jijiyoyin jikinsa numfashi ya saukar mai tattare da farin ciki yace"amin ya rabbi".Yana kammala maganarsa ya nufi cikin motar ya zauna yana danne dannen phone d'insa.
Yaseer da yaga sun gama magana ya dubeta cikin k'auna da soyayyar gaskiya yace"kun gama gaisawa ko? ".
Ta gyad'a kanta tace"eh mun gama".
Ajiyar zuciya yayi yace"dama dalilin dayasa nazo shine domin in tambayeki ne yaya kikeson painting d'akinki ya kasance wace irin colour kikeso asanya?".
Fauzeeya ta b'ata fuska tareda zumb'ura baki tsantsar tsoro da fargaban aurensa ne kwance cikin k'wayar idanunta wani irin d'aci da zogi zuciyarta keyi dak'yar ta bud'i bakinta tace"yah Yaseer maganar gaskiya ina ganin abinda yafi kawai mu hak'ura da juna! Saboda kwata kwata hankalina bai kwanta da aurenka ba".
Dummmmm yaji saukar maganarta tamkar an soka masa kibiya azuciya cikin firgici da d'imauta ya kalli Fauzeeya mamaki da tsantsar al'ajabi ne kwance afuskarsa jikinsa duk yayi lak'was bayada wani kuzari cikin yanayin tsinkewar zuciya yace mata"mu hak'ura da juna kikace fa Fauzeeya wannan wace irin magana ce mara dad'in ji da saurare!? ".
Fauzeeya ta langwab'e kanta tareda marairaice fuskarta kamar zatayi kuka tace"ka fahimceni yah Yaseer banyi nufi yaudararka ba ko kadan arayuwata saboda soyayyar gaskiya nakeyi maka wadda tafi gaban kwatance ".
"shut up! Banason jin komai daga gareki Fauzeeya ta yaya zaki kalli tsabar idanuna kicemin