Showing 6001 words to 9000 words out of 87802 words
kin kasa jawo ra'ayinsa ya soki wannan ai rashin dabara ne?".
"bazaki gane ba Adama Yaseer yanada tsattsauran ra'ayi ba kowace mace bace ke burgesa kedai ki bani shawarar yadda zanyi in sace zuciyarsa ya soni".
Adama ta saukar da numfashi tace"kina abu kamar ba wayayya ba kinsan matarsa bata yawan zama gidan mijinta, kamata yayi ki dinga yawan kwalliya da shisshige masa ajiki ta haka ne zai soki Fauzeeya,amma idan kikasa wasa har abada bazai tab'a sonki ba kindaiji na gaya miki!".
Fauzeeya ta rausayar da kanta cikin sanyin jiki tace"naji zan gwada shawarar da kika bani Adama".
Adama tace"ya kamata kam ki tashi tsaye idan ba haka kina ji kina gani ki rasa Yaseer har abada!".
"ki daina yimin mugun fata Adama domin idan na rasa Yaseer rayuwata zata iya tarwatsewa in lalace! Bakisan yadda nakeji ba azuciyata ba soyayyarsa tayimin mugun kamu cikin rayuwata".
Adama ta dafa kafad'arta cikin tausayawa k'awarta tace"kibi komai asannu Fauzeeya sannan ki rage sakawa zuciyarki damuwa duk abinda ubangiji ya k'addaro ga bawa babu makawa saiya sameshi".
Cikin mutuwar jiki da tsantsar damuwa dayake shimfid'e afuskarta Fauzeeya tace"haka ne Adama nizan wuce gida yanzu na baro yaransa su kad'ai".
Adama yace"to yayi ki gaida uwargidanki Nazifa".
"hmmmmmm naji amma bazan iya gaya mata ba saboda matar nan sai ahankali".
"to Fauzeeya ki cigaba da hak'uri ubangiji yana tareda masu hak'uri".
"a'a babu damuwa sai wata rana".
"sai wata rana d'in".
Adama ta rakata har bakin k'ofar gida sukayi tsaye suna firarsu cikin jin dad'i,bada jimawa ba saiga mai keke napep ya gifto ta gabansu Adama tayi saurin tsayar dashi ya parker napep d'insa, Fauzeeya tayiwa Adama sallama ta shige cikin napep d'in ta zauna mai keke napep ya tambayeta inda zai kaita tayi masa kwatance unguwar da gidan Yaseer yake, tadda napep d'in yayi suka fice daga cikin unguwar yayinda Adama ta juya ta koma cikin gidansu.
Sunyi tafiya mai nisa har suka iso bakin get d'in gidan Yaseer ya ajeta kud'i ta ciro daga cikin k'aramar handbag d'inta ta biyasa, ya amshi kud'insa ya k'ara gaba Fauzeeya ta shige cikin gidan murmushi k'unshe afuskarta.
Tana isa tsakiyar parlourn ta iskosu Sameer kwance saman carpet suna minshari Fauzeeya ta k'araso wurinsu ta zauna tareda gyara musu kwanciya,can dai ta mike tsaye ta fad'a cikin d'akinta domin ta watsa ruwa taji sanyi ajikinta ta dad'e tana wanka sannan ta fito daga cikin bathroom d'in tana goge jikinta da k'aramin towel, direct wurin mirror ta nufa ta shafa mayuka masu k'amshi atamfarta ta ciro ta sanya d'inkin doguwar riga ta sanya ajikinta yayi mata d'ass kamar tare aka haliccesu, turare ta fesa sannan ta dawo wurin gadonta ta fara barci tana lumshe idanu cikin sanyin jiki.
**********************
Yaseer ya tashi tsaye ya shiga cikin bathroom yayi wanka tareda d'auro alwala, yana fitowa daga cikin toilet ya shafa manshafi mai k'amshi shaddarsa ya ciro light blue taji aiki ya sanya ajikinsa, turarensa masu shegen k'amshi ya feshe jikinsa dashi ya saka hula da agogo ya jawo k'ofar d'akinsa ya fito.
Yaseer ya iso tsakiyar parlourn zai wuce kenan idanunsa suka hango 'ya'yansa kwance saman carpet suna barci, wani irin d'aci da zogi zuciyarsa keyi ga bak'in ciki k'unshe cikin ransa asanadiyyar rashin dace da mace ta gari, wani irin abu ke yawan taso masa a k'irji yana damunsa, dak'yar ya kauda kansa daga barin kallon fuskar 'ya'yansa ya juya ya fice daga cikin gidan direct parking lot ya nufa, isarsa parking lot keda wuya ya bud'e k'ofar motarsa ya shiga ya zauna danna horn yayi da k'arfi maigadi y wangale masa get ya fice daga cikin gidan da sauri.
**********************
Nazifa bata dawo cikin gidan ba sai kusan sallar magarib alokacin har Fauzeeya ta kammala girka abincin dare tuntuni,Nazifa ta shige cikin d'akinta ta watsa ruwa tareda d'auro alwala tana fitowa daga cikin toilet d'in, ta shimfid'a sallaya ta fara ramakon sallolin da ake binta harta kammala.
Tana zaune saman sallaya tana addu'o'i saiga Yaseer ya shigo cikin d'akinta sanye da jalabiya black colour, wurinta ya k'araso ya zauna yana jiran ta shafa addu'ar afuskarta tana shafawa ta juyo ta kallesa batare data ce uffan ba, Yaseer ya dubeta cikin rashin walwala yace"Nazifa".
"na'am"Ta fad'a batare data dubeshi ba.
Yaseer yayi huci mai k'unshe da takaici da bak'in cikin rayuwa kallo d'aya zakayi masa ka gano baya cikin kwanciyar hankali yace"yanzu irin wannan rayuwar da kika d'aurawa kanki kina ganin haka yafi dacewa awurinki miyasa bazaki bani dama ba mu shimfid'a tsabtatacciyar rayuwar aurenmu? ".
Cikin haushin kalamansa Nazifa ta b'ata fuskarta tace"yanzu kuma mi nayi maka Yaseer waikai har yanzu ka kasa fahimtata?".
"kece kika kasa fahimtata Nazifa saboda bak'ya son gaskiya duk abinda nake nufi kinfi kowa sani!".Yace ahasale.
Nazifa ta daga masa hannu cikin rashin girmamawa tace"ya isa Yaseer! Yawan complain d'inka ya fara isata saikace gareka aka fara auren mace 'yar business, idan banyi business ba kallonka kakeson in zauna inyi bafa zaka tab'a samun yadda kakeso ba har abada kaji dai na gaya maka gaskiyar zance! ".
Yaseer yaji matuk'ar zafin kalamanta har cikin jini da tsoka cikin zugi da tafasar zuciya yace"lallai na tabbatar da bakida tarbiya Nazifa hmmm hak'ik'a nayi nadamar aurenki arayuwata saboda kwata kwata wannan rayuwar da kika sawa gaba bamai b'ullewa bace ".Nazifa tayi masa kallo mai tattare da raini tace"nima nayi nadamar aurenka Yaseer domin ka cika yawan damuwa! ".
Yaseer ya jijjiga kansa cikin dacin rai yace"zaki gane bakida wayo da sannu zaki fahimci abinda kikeyi bayada k'yawo sannan duk abinda kikeyi ki cigaba duniya ce ta ishi kowa riga da wando! ".Yana rufe bakinsa yaja k'afafunsa yabar d'akin Nazifa zuciyarsa sai tururin zafi da k'una takeyi.
Yana ficewa daga cikin d'akin Nazifa tayi tagumi cikin zafin rai da rad'ad'i azuciya can ta nisa tace ohhh ni Nazifa naga ta kaina wannan auren ya fara isata rayuwar Yaseer tanada matsala mutum sai kace mai zuciyar kafirai ".
Tana rufe bakinta ta d'auko wayarta tayi dialling nombar Safiya ta shiga tana ringing d'id'id'id'i, tana shiga Safiya tayi receiving call d'inta tace"hello Nazifa lafiya zaki kirani cikin dare ?".
"hmmm ina fa lafiya Safiya Yaseer duk ya takurawa rayuwata ya hanamin rawa gaban hantsi nifa na fara gajiya da halayyarsa! ".
Safiya tayi doguwar ajiyar zuciya cikin lallashi da tattausan lafazi tace"ki daina cewa kin gaji da halinsa Nazifa rayuwar aure da kike ganinta sai hak'uri nima fa Haidar yana yimin irin abubuwan da mijinki yakeyi miki, hak'uri kawai nakeyi ina b'oye wasu abubuwa cikin zuciyata saboda haka ki share da maganarsa ki cigaba da sha'anin gabanki".
"to shikenan zan sharesa d'in".
"hakan ya kamata sai da safe".
"OK good night ".Tana k'arasa maganarta ta katse phone d'in tareda ajeta saman kan gado blanket ta jawo ta lullub'e jikinta dashi ta lumshe idanunta saboda tayi saurin tashi da safe zuwa wurin business.
B'angaren Yaseer yana komawa cikin room d'insa zazzafan hawaye suka dinga sintiri saman fuskarsa yayinda zuciyarsa sai zogi da k'una takeyi masa akan yalwataccen gadonsa yayi masauki ya kwanta, alal hak'ik'a da yasan haka Nazifa zatayi masa dabai aureta ba tabbas baiyi dace da mace ta gari ba.............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 5*
Dak'yar Yaseer ya samu b'arawon barci yayi awon gaba dashi zuciyarsa cunkushe da tarin damuwa da bak'in ciki mara misaltuwa, harda mafarkin ya auri Fauzeeya yayi yana auratayya da ita ta haifa masa k'yak'k'yawan yara, cikin tsakar dare ya farka afirgice jikinsa sai tsiyayar zufa yakeyi yana karanto addu'o'i cikin ransa domin ya kad'u da firgita akan mafarkin da yayi! Ya jima zaune yana kwararo addu'o'in neman tsari daga shaid'an, sannan ya shafe addu'ar ajikinsa ya kwanta cikeda damuwa da rashin dad'in zuciya, haka ya dinga juye juye ya kasa barci har aka sallar asuba ya mik'e zumbur ya fad'a cikin bathroom ya watsa ruwa ajikinsa tareda d'auro alwala, yana fitowa ya zura jalabiyarsa ya nufi hanyar zuwa masallacin dake cikin unguwar.
A room d'in Nazifa itama ta tashi daga barci ta d'auro alwala tareda kabbarta sallah, haka room d'in dasu Fauzeeya suke barci itama ta falka daga barci ta d'auro alwala ta fito daga cikin toilet, shimfid'a sallaya ta kabbarta sallah raka'a biyu tana sallame sallah ta zauna tana kwararo addu'o'i, bayan ta shafa addu'ar afuskarta ta mike tsaye tareda linke sallaya ta adanata saman drower, cire hijabinta tayi ta aza saman gadon direct ta nufi cikin kitchen ta had'a musu breakfast ruwan zafi ta juye aplask ta rufe, sannan ta kwashi kayayyakin ta nufi wurin dinning table ta jajjerasu samansa zad sha'awa da tsari.
Tana gama jerawa ta koma cikin d'akinta domin tayiwasu Sameer wanka tana wurinsu ta sungumi baby Sameera tayi cikin toilet da ita, ta jima tana wanke mata jiki lungu da sak'o sannan ta d'auraye mata jiki da ruwan k'warai ta rungumota ajikinta tayo cikin d'aki da ita, tana isowa cikin d'akin ta kwantar da ita saman gado tareda rufe mata jiki da bargo, Sameer taja hannunsa ta shiga cikin toilet dashi tayi masa wanka fess ta fito dashi daga cikin toilet.
Suna isa tsakiyar room d'in ta zauna gefen gado tareda shafawa Sameer manshafi sai b'ata fuska yakeyi, Fauzeeya dai bata ce masa k'ala ba ta cigaba da abinda takeyi tana kammala shafe masa jiki ta ciro tufafinsa 'yan kanti masu k'yau ta sanya masa, sannan ta d'auko Sameera ta rungumeta saman k'afafunta tana shafa mata manshafi ita kuma sai shagwab'a takeyi mata Fauzeeya tana biye mata, kayan kwalliya ta jawo tayi mata had'ad'd'iyar kwalliya mai masifar k'yawo sannan ta ciro mata riga da sicket masu shegen k'yawo da tsada ta sanya mata.
K'aramin madubi Fauzeeya ta d'auko ta saita adaidai saitin fuskar Sameera tana murmushinta mai k'yawo tace"kin gani ko kinyi k'yawo babyna".
Sameera ta kalli fuskarta dake cikin madubi ta fashe da dariyar murna tace"gaskiya Aunty Fauzee kin iya kwalliya na gani nayi k'yawo sosai"..
Fauzeeya tayi dariyar dake bayyana hak'ora tace"da gaske na iya kwalliya babyna?".
Sameera ta sake washe k'ananan hak'oranta masu haske da k'yawo tace"eh mana kin iya sosai Aunty".Tana rufe bakinta sukaji Sameer yaja tsoki mtssss ya zumb'ura baki yace"Aunty ji yadda kike wani kod'ata kina k'arawa kanta zama k'atoto ina Sameera taga wani k'yawo idan ma ba fari dasai bola!".
Fauzeeya ta k'yalk'yale da dariyar mugunta domin zancen Sameer ya matuk'ar sanyata dariya can ta tsagaita tace"kai Sameer miye abin kishi saboda nace baby Sameera tayi k'yawo?".
Sameera tayi charap tace"dallah rabudashi Aunty duk bak'in ciki ne da jiyewa".
Sameer ya hasala yana huci kamar zaki yace"rufemin bakinki ko yanzu inyi miki shegen duka mara jin magana kawai ".
Fauzeeya ta jawo hannunsa alamar lallashinsa tace"a'a kada ka kuskura ka dukarmin yarinya idan ba haka ba zamuyi fad'a ni dakai".
Sameera ta lahe ajikin Fauzeeya kamar mage tace"barshi Aunty saina had'ashi da mom in gaya mata zai dukeni".
"ya isa dai yanzu dai na shiryaku muje parlour muyi breakfast kowa ya tsaya ga kansa".
"to Auntynmu".Suka fad'a kusan atare da juna.
Jan hannunsu tayi suka nufi cikin parlourn.
Yayinda acan dinning table tun d'azu Yaseer ya fito shida Nazeefa suna breakfast babu wanda yayiwa wani magana, kowanensu zuciyarsa k'unshe take da haushin abokin zamansa musamman Yaseer dayake ganin tana tauye masa hak'k'insa,ita kuma anata wautar so yake ya takurawa rayuwarta ya hana mata neman na kanta, sun jima zaune suna kintsa cikinsu suna sak'e sak'e cikin zuciyarsu daga k'arshe Yaseer ne ya fara tashi saboda idan ya cigaba da kallonta zai iya haifar masa da babbar matsala domin ba k'aramin haushinta yakeji ba, direct parking lot ya nufa ya shiga cikin motarsa maigadi ya wangale masa get ya fice daga cikin gidan.
Nazifa tana jin k'arar motarsa alamar ya fice daga cikin gidan tayi k'yafci tace"aikin banza ji yadda yake wani d'auremin fuska yana b'ata rai ni ina ruwana idan ma domin nice ka tabbata cikin b'acin rai ".K'arasa maganarta keda wuya ta mik'e tsaye ta shige cikin d'akinta ta shirya sharp sharp cikin shaddarta ash colour, handbag d'inta ta rataya a kafad'arta hannunta rike da key d'in motarta ta nufi parking lot, kodasu Fauzeeya suka iso dinning table suka zazzauna basu isko kowa ba serving dinsu tayi itama ta d'ebi nata tana ci kad'an kad'an ayangace dayake Fauzeeya akwaita da son yanga da kuri,ci sukeyi cikin natsuwa har suka kammala ta kwashe kayayyakin da suka b'ata ta wankesu tasss ta adanasu awurin daya kamata.
Fitowa tayi daga kitchen d'in ta iskosu Sameer har sun dawo cikin parlourn suna buga game murmushi ta sakar musu ta samu wuri ta zauna saman cushion, su kuwa game d'insu suka cigaba da bugawa suna k'yalk'yalar dariyar farin ciki kallo d'aya zakayi musu ka gane suna cikin kwanciyar hankali da natsuwa itadai sai kallonsu takeyi tana murmushinta mai k'ayatar da fuskarta.
____________________
Yaseer ne na hango cikin wani irin katafaren office had'ad'd'e zaune saman kujera gabansa teburi ne babba cikeda takardu da computer, laptop, shiru yayi cikin matsananciyar damuwa tun d'azu daya shigo cikin office d'in ya kasa yin aikin k'warai, haushi da tsagwaron takaici ne shimfid'e saman fuskarsa kallo d'aya zakayi masa ka gane kwata kwata baya cikin hayyacinsa, tagumi yayi biro ne rik'e ahannunsa idanunsa sun kad'a sunyi jajir akan tsantsar damuwa, ya fad'a duniyar tunani saiga sallamar Abduljalal ya bud'e k'ofar ya shigo yana isowa wurinsa yaja kujera ya zauna, ya jima yana nazarin abokinsa sannan ya tab'ashi yayi firgigit ya dawo cikin hayyacinsa, kallon tausayawa Abduljalal yayi masa yace"haba Yaseer ka rage yawan sanyawa kanka damuwa idan ba haka ba wani ciwo zai iya kamaka akan mace zaka zauna kana neman kashe kanka abanza, ai wannan rashin tunani ne ya kamata kayi abinda ya dace!".
Yaseer ya d'ago fuskarsa ya kallesa cikin damuwa yace"bazaka tab'a gane irin yadda nakeji ba Abduljalal ina buk'atar mace wallahi nakai mak'ura wurin buk'atuwa saboda kwata kwata rabon da Nazifa ta bani hak'k'ina na auratayya harna manta kullum sai jamin rai takeyi".
Abduljalal yayi matuk'ar kad'uwa da razana akan maganarsa cikin matuk'ar mamaki yace"abinda ka fad'a gaskiya ne Yaseer?".
"kana mamakin maganata ne ka daina mamakin zancena domin Nazifa ta wuce tunaninka".
Abduljalal yayi shiru na tsawon lokaci can yace"lallai kana cikin tsaka mai wuya Yaseer amma gaskiya ya kamata ka d'auki kwakkwaran mataki akan Nazifa idan ba haka zata sakaka cikin wani irin mugun yanayi".
"nina rasa wani irin mataki ya kamata in d'auka akanta saboda ta riga tayi nisan kiwo batajin kira".
"kadaiyi tunanin irin matakin daya kamata ka d'auka abokina nizan koma office d'ina na barka lafiya".
"OK ba damuwa friend".
Abduljalal ya fice daga cikin office d'in ya nufi nasa yayinda yabar Yaseer zaune yana zullumi da tunanin mafitar daya kamata ya d'auka,dak'yar ya tattaro dauriya ya sanya azuciyarsa ya fara wasu ayyukan domin kada suyi masa yawa.
**********************
Nazifa da Safiya na hango zaune cikin hamshak'in shagonsu suna siye da sayarwa zaune suke saman kujerar roba, mutane sai sintirin zuwa sukeyi sayayya ashagon yayinda sunada yaro mai suna Anwar shike kula da duka shagon da abinda yake cikinsa.
Suna zaune suna firarsu cikin fara'a da kwanciyar hankali Nazifa ta dubi fuskar Safiya tace"hmmm lamarin Yaseer sai ahankali yanzu haka fushi yakeyi dani baya yimin magana ".Safiya ta yamutsa fuskarta tareda karkace baki tace"aikin banza yiwa karen mak'wabta wanka ki k'yaleshi kada ki kula dashi idan ya gaji dayin fushin da kansa zai sauko yayi miki magana".
Nazifa ta yamutsa fuskarta tace"ai bana kulasa Safiya saboda abin nasa yayi nisa nidai iyakata idanu dashi".
"gara da kika fita batunsa saboda bak'in ciki yakeson yayi miki domin kada ki samu kud'i ".
"ai tuni na harbo jirginsa besty na fahimci hassada da bak'in ciki yakeson yimin saboda bayason cigabana".
Safiya ta rik'e baki tace"mazan yanzu da kike gani sai abarsu saboda babu abinda suka iya sai yiwa matansu hassada da kushe saboda basuson matansu su zamo wani abu arayuwata, shiyasa kikaga ko Haidar yayimin fad'a da guna guni nake fita batunsa domin ni arayuwata na tsani namijin da bayason cigaban matarsa".
Nazifa tayi ajiyar zuciya cikin damuwa tace"Yaseer kam yana daga cikin irin wad'annan mazan shiyasa bana bashi fuska domin kada ya kawomin raini da ikon banza"."Ai yanzu mu mata saimun tashi tsaye mu k'waci 'yancin kanmu idan ba haka ba kina ji kina gani zaki zama baiwar k'aton banza! "."Abin dai ba'a cewa komai ubangiji ya karemu daga sharrin mazaje 'yan bak'in ciki"."Amin amin aminiyata mukam yin business yanzu muka fara saidai zuciyar mutum ta buga ya mutu bamuda hasara sai riba! "..............
💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}
*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*
*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.
_Special gift to Haruna Umar._
*PAGE 6*
Nazifa tayi murmushi tace"kayyy Safiya bakida sauk'i cikin lamarinki muddin zaki samu kud'i gaskiyar magana rayuwarki tana burgeni".Safiya ta musk'uta cikin yanayin murna tace"hmmmm bana wasa muddin haraka idan ta kud'i ce saboda yanzu zamani ya riga ya waye namiji da mace kowa na kansa yake nema"."Wannan maganar taki haka yake k'awata".
Cigaba firarsu sukeyi cikin kwanciyar hankali da natsuwa har zuwa wani lokaci mai tsawo, can da suka fara jin yunwa suka kira yaronsu Anwar suka bashi kud'i domin yayi musu take away na abinci, yana ficewa daga shagon yahau mashin d'insa