Showing 81001 words to 84000 words out of 87802 words

Chapter 28 - SAKACI BY MUGIRAT MUSA

05 Jul 2024

4251

ceceni zai kasheni zai ketamin rigar mutunci!".
Dundu yayi mata abaya yace"nasan abinda zanyi miki yanzu sai kinci na jaki zaki bani had'in kai".

Tsaye ya tsaye cikin matuk'ar bak'ar zuciya da gushewar hankali zai bata kashi kenan yaji an banko k'ofar d'akin da k'arfi! Zuciyarsa ta girgiza gabansa ya fad'i hankalinsa ya d'unguma juyawar da zaiyi ya hango polices sun kama yaransa sun sa musu ankwa har Nazifa 'yan sandar sun kamata! Yaseer ne ya gani agabansa fuskarsa ta rikid'a zuwa b'acin rai idanunsa sunyi jajir akan tsantsar takaici da bak'in ciki arayuwa, ganinsa yasa Fauzeeya ta k'ara volume d'in kukanta cikin matuk'ar farin ciki tace"yayana ka ceceni wlh shine yaso lalata dani ban amince ba!".

"bayan aikin gama ya gama na gama shan zumar........... ".Kafin ya k'arasa maganarsa Yaseer ya kasheshi da rikitaccin maruka biyu masu k'yau wanda asanadiyyar haka saida yayi taga taga zai fad'i Yaseer ya kamosa tareda shak'e masa yunwa idanunsa jajir jijiyoyin kansa suka tashi rud'u rud'u akan tsantsar bak'in ciki da suyar zuciya tace"ni zaka kalli tsabar idanuna kacemin kasha zumar matata wallahi saina kasheka inga wanda ya d'aure maka gindi! ".Mutsul-mutsil Baura ya dingayi numfashinsa yana batun d'aukewa domin ya shak'u iya shak'uwa! Polices d'in dake taredashi ganin zaiyi kisan kai yasa suka iso da sauri suna k'ok'arin b'anb'aresa ahannun Yaseer suka kasa domin ba k'aramar shak'a yayi masa ba, dak'yar da wahala suka b'anb'are Baura ahannun Yaseer shi kuma sai zaburowa yakeyi yana cewa"ku k'yaleni in kashe shege d'an iska! ".

Polices biyu suka sanya Baura tsakiya tareda sanya masa ankwa yayinda suka bada umurnin awuce dasu can police station, ogansu kawai ya dubi fuskar Yaseer cikin lallashi da lafazi mai dad'i yace"ka daure kayi hak'uri Yaseer ai abin ma yazo da sauk'i tunda basu cutar maka da mata ba".Girgiza kansa yayi cikin wani irin yanayi yace"naji amma ka sani abin ne da ciwo arayuwa ace matata Nazifa keson ganin bayan amaryata! ".

Police ya dafa kafad'arsa yace"ai kaga dayake baka ci amanarta ba sai gashi *K'AIK'AYI* ya koma kan mashek'iya! Saboda haka kabi komai ahankali zamusan matakin daya dace mu d'auka nizan wuce police station sai kazo za'ayi case".Yana kammala maganarsa yaja k'afafunsa ya fice daga cikin gidan ya shige cikin motarsa.

Fauzeeya dake d'ad'd'aure saman gado sai rusar kukanta takeyi kamar zata shid'e jikinta har rawa yakeyi adalilin batasan ko Yaseer ya amince da cewa Baura baiyi iskanci da ita ba, zuciyarta sai luguden fargaba da tsantsar zullumi takeyi ta rasa abinda yakeyi mata dad'i aduniya ashe Nazifa zata iya saka ayi iskanci da ita saboda Yaseer ya saketa tabar mata gida ita kad'ai, tabbas mutanen duniya abin tsoro ne ke kina zaune da mutum da zuciya d'aya ita kuma sai bibiyarki da sharri takeyi. Yaseer dake zaune hawayen bak'in ciki sai gangarowa sukeyi afuskarsa yayinda sinadarin takaici yayi masa k'abe k'abe a k'irji ji yakeyi da wannan abin kunyar gwara mutuwarsa jin abar sonshi tana kuka yasa hankalinsa yayi k'ololuwar tashi cikin sanyin jiki ya nufi wurinta zuciyarsa cunkushe take da tsagwaron takaicin rayuwa, yana isa wurinta yasa hannunsa ya banye mata igiyar da suka d'ad'd'aure Fauzeeya da ita yana kammala kwance mata igiyar yasa hannu ya rungumeta ajikinsa ita kuka shi kuka babu mai lallashin wani daga cikinsu .

Bubbuga bayanta yakeyi alamar lallashi da tsantsar tausayinta tabbas bai tab'a zaton Nazifa zata iyayi masa haka ba arayuwa, domin ya dauka ta hak'ura tuntuni da k'addara ashe abin ba haka bane akwai makirci da mugun sharrin da take k'ullawa! Yanzu ma hawayenta dayake gani suna shatata suke k'ara tayar masa da hankali tareda raunana zuciyarsa dak'yar ya bud'i baki tareda had'iyar abu mai matuk'ar d'aci mak'wat a mak'oshinsa idanunsa suka kad'a sukayi jajir akan tsantsar b'acin rai yace"calm down my Fauzee ki daina kuka kinji domin zubar da hawayenki yana tayarmin da hankali kuma ba k'aramar hasara ce awurina ba".

Saboda ta k'ara gasgatawa da tabbatar da abinda yake fad'a har cikin zuciyarsa haka yake tace"bakaji abinda ya fad'a bane yayana cewa yayi ya kwanta dani fa taya kake tunanin bazanji zafin abinda yayi mini ba".

Yaseer yayi murmushin da baikai zuci ba yace"ki share da maganarsa ni kwata kwata batayi tasiri azuciyata ba saboda na yarda dake nasan bazaki tab'a cin amanata ba".

"da gaske ka yarda bazan tab'a cin amanarka ba? ".

Yaseer yace"tabbas na yarda dake d'ari bisa d'ari my Fauzee ".
Nan taji ta samu natsuwar zuciyarta ta fad'ad'a fuskarta da fara'a tace"ina godiya mijina waye ya gaya maka gaskiyar abinda yake faruwa har kazo ka ceceni? ".

Yaseer ya lakaci kumatunta cikin matuk'ar k'auna yace"Tasallah ce ta kirani awaya d'azu take gayamini irin abinda taji Nazifa na fad'a sannan kuma gaya miki kawai ne banyi ba itace ta gayamin sune sukazo da k'awarta Safiya har gida sukayi miki mugun duka, kin tab'a gayawa baba maigadi dalilin dayasa kika gudu ranar da kika gifto ta cikin unguwar nan ina dawowa ya kwashe kaf abinda kika gaya masa ya sanarmini, alokacin ko naso in d'auki kwakkwaran mataki akanta banida wata hujja ko dalili mai k'arfi amma dayake komai yanada lokaci gashi yanzu na kama ta cikin ruwan sanyi ".Murmushi ta sakar masa tace"kayyy yaya ka iya tako da maida mutane sakarai ashe kasan komai".Yaseer ya k'ara mannata a k'irjinsa yace"nasan komai ai kallon kitse akewa rogo yanzu abinda za'ayi ki tashi kiyi wanka mu wuce zuwa police station akammala case d'in nan zan kirasu Abi da Abbu mu had'u can domin susan abinda ake ciki kada suce nayiwa Nazifa sharri da k'azafi ".Fauzeeya ta mik'e tsaye ta jaye jikinta anasa tace"haka ya kamata kayi tun farko yah Yaseer ".

Yaseer ya mik'e tsaye cikin mutuwar jiki ya nufi hanyar dazai fita gab dazai fice daga cikin d'akin ya juyo yace mata "idan kin shirya ki sameni a room d'ina"."OK dear husband ".Yaseer ya fice daga cikin d'akin yayinda Fauzeeya ta fad'a cikin bathroom domin tayi wanka ta chanza tufafinta saboda wad'anda ke jikinta duk sun jik'e sharkaf da zufa.
Yaseer yana shiga cikin room d'insa yayi dialling nombar Alhaji Taheer mahaifinsa saida suka gaggaisa sannan yace masa su had'u police station shida mahaifiyarsa, da Alhaji ya tambayesa dalili sai yace masa idan suka had'u acan idanunsa zasu ganar masa abinda yake faruwa cewa yayi to ya katse wayar, bayan ya gama magana da mahaifinsa ya kira Alhaji Mu'azu ya gaya masa irin abinda ya sanarwa mahaifinsa shima ya yarda zaizo shida mahaifiyar Nazifa hajiya Ramlat. Kammala wayarsa keda wuya ya fad'a cikin bathroom ya sakarwa kansa shower ko rad'ad'i da zafin da yakeji zai ragu azuciyarsa bai wani jima ba ya fito d'aure da towel ajikinsa, sharp sharp ya shafa lotion d'insa ya kawo dakakkiyar shaddarsa ya zura turare ya feshe jikinsa dasu sannan ya koma parlour yana jiran fitowarta yana danne dannen wayarsa, bababu dad'ewa saiga Fauzeeya ta shirya cikin atamfarta riga da zane ta kawo hijabinta ta sanya kalar kayanta tsab, aparlour ta ganshi zaune ta iso wurinsa k'amshin turarenta ya bugi hancinsa ya lumshe fararen idanunsa ya mik'e tsaye suka rankaya zuwa parking lot suna isa ya bud'e mata k'ofar motar ta shiga ta zauna, sannan ya zagayo ya zauna mazaunin driver danna horn yayi maigadi ya wangale masa get ya fice daga cikin gidan ya nufi hanyar zuwa police station..............

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍
💍💍
💍

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
{Onward together}


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*Dedicated to*
*Sa'adatu Basheer Aliyu*.

_Special gift to Haruna Umar._

*PAGE 48*


Acan police station d'in su Alhaji Mu'azu da Alhaji Taheer suka iskosu Yaseer zaune anayin case d'insu Baura da Nazifa, samun benci sukayi suka zazzauna cikin matuk'ar tashin hankali da fargaba domin kuwa sun fahimci case d'in ya shafi Nazifa, hajiya Ramlat ganin asirinsu ya tonu yasa gabanta yake luguden tsoro da fargaba zuciyarta ta tsinke hankalinta yayi k'ololuwar tashi! Ji takeyi kamar k'yat ta zura da gudu.
Saida kowa yayi bayaninsa sannan aka kullesu Nazifa cikin cell kallo d'aya zakayiwa fuskar Alhaji Mu'azu ka hango b'acin rai domin maganar tayi masa ciwo tareda tunzura zuciyarsa, Alhaji Taheer ne ya dinga alfarmar abashi belin Nazifa saboda abin kunya ne agaresu ace 'yarsu ta kwana police station, da rok'o dak'yar suka basa belinta amma da sharad'in ya mayarda ita gobe tunda safe anan Alhaji Taheer ya amince da haka yayinda Nazifa keta risgar kukan takaici da nadamar rayuwa tabbas da tasan asirinta zai tonu da bata aikata hakan ba! D'unguma sukayi gaba d'ayansu suka koma gidajensu.

Suna komawa gida Alhaji Mu'azu ya fad'a cikin d'akinsa ahasale zuciyarsa tanayi masa suya da k'una, can ya fito ya iske hajiya Ramlat saman cushion tayi tagumi cikin fargaba da matsananciyar damuwa harara ya wurga mata yace"Ramlat kinga abinda son zuciyarki ya jawa d'iyarki ko ai nasan duk irin chakwakiyar dake faruwa agidan Yaseer dasa hannunki, ke inbanda toshewar basira taya zaku kira k'attin banza su shigar masa tareda basu umurnin suyi amfani da matarsa wannan ai tsabar hauka ne da *BAK'IN KISHI* ne!".

Hajiya Ramlat ta kallesa jikinta amace tace"wai miyasa akodayaushe kakeson d'auramin laifi Alhaji kullum idan yarinyar nan tayi laifi nice kake cewa nike d'aure mata gindi ka daina banason mutum mai zargi! ".
"ai dole kice haka tunda gashinan kina neman kashewa 'yarki aure! ".

Nazifa dake zaune saman carpet sai kukan takaici da tausayin kanta takeyi saboda ayanzu ta gano ta tafka babban kuskure arayuwarta, ta aikata abinda har abada bazata tab'a daina nadamarsa domin ta riga tayi *SAKACI* arayuwarta!.

K'irjinta ta buga tace"ni nake neman kashe mata aure sharri zakayimin!? ".

Alhaji Mu'azu ya k'ara hasala cikin zafin rai yace"kece Ramlat saboda duk irin abubuwan da yarinyar nan keyi ke kike d'aure mata gindi saboda haka idan aurenta ya mutu asanadiyyar wannan abu kema naki zai mutu duk ku tarkata ku barmin gidana! ".

Jin ya ambaci kalmar saki yasa hankalin hajiya Ramlat ya d'unguma zuciyarta ta dinga dukan uku uku rau rau tayi da idanu tace"yanzu Alhaji ni zaka saka idan har auren Nazifa ya mutu tunda muke dakai baka tab'a yimin maganar saki ba sai yanzu!? ".

"ai dole inyi miki saboda kece silar tab'arb'arewar tarbiyar Nazifa".Yana rufe bakinsa saiga sallamar matashin saurayi ya shigo cikin tsakiyar parlourn rik'e da farar takarda ahannunta, yana isowa ya russuna ya gaida Alhaji Mu'azu ya amsa masa cikin sakin fuska saurayin ya mik'a masa farar takarda yace"gashi Alhaji akace inba Aunty Nazifa wannan takarda".

Alhaji Mu'azu yace"to shikenan inji wa?".Ya amshi takardar yana jujjuyawa cikeda matuk'ar mamaki da tsantsar al'ajabi k'unshe afuskarsa.

Matashin saurayin yace masa"Yaseer mijin Aunty Nazifa ne ya bani in bata".Yana k'arasa maganarsa yaja k'afafunsa ya fice daga cikin gidan.

Jin ya ambaci sunan Yaseer yasa hankalinsu hajiya Ramlat ya tashi zuciyarsu ta tsinke tsantsar tashin hankali da fargaba ne ya bayyana k'arara afuskokinsu! Cikin Nazifa ya dinga k'ugi k'uuuuuuu gabanta ya fad'i rasssss kasala da rashin kuzari ne ya ziyarci sassan jikinta da k'wak'walwarta gudun kada afahimci ta tsorata yasa ta tattaro dauriya da natsuwa ta sanya azuciyarta.
Alhaji Mu'azu ya musk'uta cikin yanayin damuwa yace"bari mu warware takardar inga abinda ta k'unsa ".Yana rufe bakinsa ya warware takardar ya fara karantawa da k'arfi ta yadda zasuji abinda ta k'unsa kamar haka!

_Assalamu Alaiki Nazifa_
_Alal hak'ik'a nayi matuk'ar mamakin irin abubuwan da kika dinga k'ullawa iri iri daban daban cikin makirci da tsantsar rashin tsoron Allah! Tabbas kinyimin abinda har abada bazan tab'a mantawa dake ba ace wai kice kikasa k'attin banza su shigo cikin gidana su aikata zina da matata akan gadona na sunnah, lamarinki ya bani tsoro saboda haka na sakeki saki d'aya karki kuskura ki dawomin cikin gida bana buk'atar ganinki._
_karki kuskura ki tako k'afarki gidana idan kunne yaji gangar jiki ta tsira!._

Alhaji Mu'azu yana kai k'arshen karantawa Nazifa ta rushe da rikitaccen kuka harda birgima k'asa kamar zautacciya! Wani irin zogi da k'una zuciyarta keyi aza hannunta saman kanta tayi tace"Abbu Ummu na shiga uku! Dan Allah ku kirashi kuce masa ya mayardani d'akina wlh bazan iya rayuwa idan babu 'ya'yana akusa dani ba ji nakeyi gwamma mutuwa da wannan rayuwar dana tsinci kaina acikinsa! ".

Alhaji Mu'azu taja tsoki mtsssssss cikin matuk'ar b'acin rai da tafasar zuciya yace"dallah yimin shiru da kika tashi k'ulle k'ulle da makircinki kin tab'a shawara dani ko fad'amin saboda haka bazan tab'a tilasta masa ba ya mayardake d'akinki inya gadama ya mayardake idan bai gama ba shikenan".

hajiya Ramlat ta marairaice fuskarta tace"haba Alhaji ka sanya bakinka cikin wannan al'amarin ya maidata d'akinta".

Alhaji Mu'azu ya d'aga mata hannu yace"yimin shiru Ramlat dama irin wannan ranar nake guje muku wato *RANAR NADAMA* !Kin kashewa d'iyarki aure kinji dad'i saboda haka dama na gaya miki duk aurenta ya mutu saina sakeki hmmm nima na sakeki saki d'aya! ".

hajiya Ramlat ta zabura afirgice cikin matuk'ar razana da kad'uwa akan zancensa ta mik'e tsaye tace"Alhaji ka sakeni kace fa?".

"eh na sakeki ki kwashi kayayyakinki kibarmin gidana keda 'yarki da kikayi sanadiyyar mutuwar aurenta! ".Inji Alhaji Mu'azu ya fice daga cikin parlourn direct ya fad'a cikin dakinsa.

hajiya Ramlat ta fashe da rikitaccen kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro Nazifa ta isa wurinta ta fad'a ajikinta tana zubar da kwallar zallar takaici, yayinda suka k'ank'ame junansu sunata kukan nadama da dana sani arayuwa! Kukansu kakeji duk ya gauraye cikin parlourn saida sukayi suka k'oshi dak'yar hajiya Ramlat ta tsagaita dayin kukanta tace"kiyi shiru Nazifa alal hak'ik'a na cuci rayuwarki tareda tarwatsa farin cikin aurenki kiyafemin 'yata nasan ban zamo uwa ta gari agareki ba".

Shasshekar Nazifa kawai kakeji tace"na yafe miki Ummuna duk abinda ya sameni idan akwai k'addara to akwai *SON ZUCIYA* da rud'in shaid'an aciki saboda haka ki daina bani hak'uri ".

"duk da haka nima da laifina cikin tab'arb'arewar tarbiyarki".

Nazifa ta musk'uta cikin yanayin damuwa tace"yi sauri Ummu mubar masa gidansa kafin ya riskemu! ".

"baby harna manta da cewa yace mubar masa gidansa bari in d'auko akwatina ".Tana rufe bakinta ta shiga cikin d'akinta ta jawo akwatin tufafinta ta fito suka fice daga cikin gidan amotar hajiya Ramlat suka nufi hanyar zuwa gidan yayar hajiya Ramlat mai suna hajiya Hamamatu.

**********************
Su Alhaji Taheer suna komawa gidansu sukayi masauki kan cushion aparlour yayinda Fauzeeya itada Yaseer ke zaune saman carpet kanta ad'uke cikeda kunyar surukanta, saida Alhaji Taheer yayi gyaran murya yace"godiya ta tabbata ga uubangijin talikkai mai kowa mai komai tsira da aminci sun tabbata ga manzonmu d'an Amina Annabi Muhammad (S. A. W), abinda yasa na taraku anan shine dama ita rayuwa da kuke gani sai anjarabi abubuwa iri iri daban daban domin agwada imaninsa ko zaiyi hak'uri ko bazaiyi ba, don haka Yaseer kaida Fauzeeya ina rok'onku da kuyi hak'uri ku yafewa Nazifa duk abinda ya faru ya riga ya faru, sannan ubangiji ya riga ya rubuta duk ire iren abubuwan da zasu sameku tun fil'azal saboda haka ku mance komai azuciyarku".

Fauzeeya kanta noce akasa tace"nidai komai ya wuce awurina".

Alhaji Taheer yaji matuk'ar dad'in kalamanta murmushi yayi yace"ubangiji yayi miki albarka ya saukeki lafiya".

Cikin kunya tayi murmushinta mai k'yau tace"amin ya rabbi Abi".

Alhaji Taheer ya juya b'angaren Yaseer ya kallesa yace"saura kai banji kace komai ba".

Yaseer ya sauke gwauron numfashi cikeda matuk'ar b'acin rai da zafin zuciya yace"nima komai ya wuce awurina saidai Abi na riga na yanke hukunci batare da nayi shawara daku ba".

"wani irin hukunci ne ka yanke batare da kayi shawara damu ba!? ".Cikin zullumi da fargaba.

hajiya Sadiya jugum tayi tana sauraren abinda suke fad'a batare da tace uffan ba, Yaseer ya numfasa cikin fargaba yace"na saketa ne bayan mun fito daga cikin police station na bayarda takardar saki aka bata".

Azauce suka d'ago fuskokinsu suka kalli Yaseer salati suka saka atare sukace "ina lillahi wa ina ilaihirraji'una! ".

hajiya Sadiya ta bugi gabanta tace"ka saketa fa kace Yaseer!?".

Alhaji Taheer yace masa"miyasa kayi saurin yanke wannan mummunan hukunci irin haka batare da saninmu ba? Gaskiya ka aikata babban kuskuren da banji dad'insa ba Yaseer "."Kayi hak'uri Abi rayuwata ce ta b'aci zuciyata cunkushe take da tsagwaron bak'in ciki da tsantsar takaicin rayuwa ".Inji Yaseer cikin mutuwar jiki.

"lallai na tabbatar da bakada hankali to bazata sab'u ba dole ka maida Nazifa d'akinta saboda bazan tab'a barin rayuwar jikokina ta tagayyara ba! ".Inji hajiya Sadiya cikin takaicin kalaman Yaseer.

Alhaji Taheer ya sassauta murya cikin tattausan lafazi yace"Yaseer".

"Na'am Abi".Cewar Yaseer cikin ladabi da tsantsar damuwa cunkushe azuciyarsa.
"zanyi maka wata tambaya uku rak ka bani amsarsu".
"insha Allahu zan baka amsa gwargwadon abinda na sani".
"OK nine mahaifinka? ".
"eh mana Abi aduniya banida wanda yafiku".
"inada iko dakai ko banidashi? ".
"kanada iko dani domin aljannata tana k'ark'ashin tafin k'afafunku saina yi muku biyayya zan shigeta ".
"zan iya baka umurni kabi?".
"tabbas zaka iya bani umurni inbi dole koda ace zuciyata bataso ".

Alhaji Taheer ya jinjina kansa alamar gamsuwa yace"idan har na isa dakai Yaseer to ina baka umurnin kayi gaggawar maida Nazifa d'akinta".

Yaseer yayi kalar tausayi yace"Abi zan mayarda Nazifa d'akinta amma don Allah kuyi mini lamuni tayi koda sati uku agidansu sannan in maidata d'akinta so nake ta fahimci cewa duniya makaranta ce mai d'auke da classes na d'aukar darasin rayuwa".

hajiya Sadiya tayi charap tace"nufinka kenan bazaka maidata d'akinta da wuri ba? ".Yaseer yace"zan maidata Ummi inason ta gane akowane lokaci rayuwa jujjuyawa takeyi".Alokacin ne Alhaji Taheer ya jijjiga kansa cikin jimamin abinda ya faru yace"shikenan na gamsu da maganarka ubangiji yayi mana jagora cikin lamarinmu".Sukace"Amin amin Abi"...............

💍💍💍💍💍💍
*SAKACI*
💍💍💍💍💍💍
💍💍💍💍💍
💍💍💍💍
💍💍💍

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login