Showing 87001 words to 90000 words out of 94443 words

Chapter 30 - HADARIN GABAS HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

177

musa. Sai dai ko  d aga kansa bai yi ba. Kan nasa yana sunkuye a haka yake kallon kowa.  Tashi mu je ka bu de min d akin Moddibo, idan baka naso yau na maka abinda baka tab a zata ba&  Runtse idonsa Ya yi yana girgiza kai.  Ki yi hak uri Didi, shigar ki d akin bashi da wata fa ida, don Allah ki yi hak uri. Zubewa kawai ta yi akan kujera wannan karan sam ta kasa togace hawayen da suke zubo mata& ta saki kuka sosai tana furta Ya Allah! Safna ta mik e tana sakin murmushi tana kallon Fateemah da ta zama kamar statue. Sai ta kai wayarta daidai fuskarta ta furta  Ke kin san komai, kin san Moddi ya cusawa y arsa k aunarsa da sha awarsa ta hanyar tsafi, kin ga abinda kika gani a wayarta, sannan ga vedio, idan baku saka ya saketa ba a Yanxun nan zan saki vedion nan a tiktok wallahi& .. Ta fa da tana kunna vedion sannan ta shiga Tiktok. Da sauri Fateemah ta rik e hannunta tana furta  Moddibo saki Jameela saketa, Safna ta shirya tona mana asiri, ta shirya lalata mana sunan family&  Moddibo ya kalli Fateemah. Ta ce  Ka saketa na ce. Fateemah ta furta a tsawace. Moddi ya lumshe idonsa yana furta  Na saketa&  Fateemah ta saki hannun Safnan tana sakin ajiyar zuciya. Idonta na cigaba da zubar hawaye. Safna ta tuntsire da dariya tana furta  Ko yanzu nice da riba, na gaya muku na zame muku k arfen k afa. Ta fice tana cigaba da dariyarta, daga jinta ka san tana cikin farin ciki. Shiru duka  dakin ya  d auka baka jin komai sai sautin ajiyar zuciyoyinsu da suke yi a jere a jere. Didi ce ta fara magana  Hankalinka Ya kwanta Moddi, ka saki matar da na aura maka, Duk abinda kake b oyewa kuma Ubangiji Allah ya tona maka asiri kwana kurkusa, idan kuwa na sameka a matsayin matsafi Wanda Ya yi ku di ta hanyar tsafi wallahil azeem ba ni ba kai, Fateemah ki zama shaida&  Fateemah ta lumshe ido bayan jin sautin bugun k irjinta Ya tsananta. A idanun Didi ta dinga ganin duk abinda ta fa da gaskiya ne Har k asan ranta. Don haka ta mik e zuwa gabanta ta durk ushe murya a k asa ta furta  Ki yi hak uri Didi. Wani kallo ta mata da yasa Fateemahn ta ja baki ta tsuke tana matsa yatsun hannunta.  Kada ki ce min komai Fateemah, duk abinda Ya faru ace kin b oye min? Kin san abubuwa da dama amma kika rufe min? Kina tunanin gata kika yiwa Moddibo, y ar cikinsa fa? Da kin gaya min tuntuni da abin bai kai haka ba ai, baki kyauta min ba Fateemah kuma ina fushi da ke. Fatima ta saka kuka tana kama hannun Didin ta furta  Ki yi hak uri Didi, Ban gaya Miki bane saboda bana son ranki ya b aci, kuma sai da na ja kunnen Moddibo na ce kada Ya aikata Amma sai da ya aikata, ni kaina yanzu ina jin zafin Moddibo fiye da tunaninki, komai shi ya jawo Amma ta hanyar gudumowar Mace Mara imani, wacce take son Ya yi ku di ko ta wace hanya&  Didi ta mik e tana furta  Ai ga ku din nan ya samu, sai ta ci ku din shi kuma ta cigaba da walagigi da rayuwarsa&  ta shige toilet wannan ne Ya bawa Moddi damar mik ewa zai fice Fateemah ta bi bayansa da sauri. Jin motsin ta yasa ya juyo ta ja hannunsa  Mu je d akinka, ka nuna min abinda kake b oyewa a d akin sirrinka idan ba haka ba ba ni ba kai Moddi&  Ya ja ya tsaya, ba tare da ya cigaba da tafiya ba, fuskarsa a tamk e ya furta  Amma kin san ni ba yaro ba ne ko? 38 yrs ya wuce wasa na San ciwon kai na, na San abinda zan aikata mai kyau ko mara kyau ko? Fateemah ta dinga kallonsa cike da mamakin furucinsa ya cije bakinsa yana furta  Tunda Ban bu dewa Didi d akin can ba, bana jin zan iya bu dewa wani don haka leave me alone& . Turus ta tsaya tana
Kallonsa. Eeh lallai da gaskiyar Safna da ta ce koma meye a cikin d akin ba na alkhairi ba ne, tunda har Moddi ya iya kallon k wayar idonta ya gaya mata haka. Idanunta suka kawo ruwa tana ji Moddi ya rab a ta gefenta ya wuce. Sai kawai ta zame ta zauna a walk way d in don bata jin k afafunta za su iya d aukarta.


Daga lokacin gidan bai sake zama lafiya ba. Safna ce take zuba mulkin ta son ranta, Didi bata bar gidan ba don zuciyarta ta kasa amince mata ta yi nesa da Moddi. Addu a take masa sosai kuma tana sawa a yi masa. Yaran gidan suka daina walwala haka jama ar da suke cikin gidan. Kullum Amani na  d aki bata ma fitowa balle ta ga Dada Wanda kallonsa yake k ara wutar tsanarsa a zuciyarta. Sanda aka yi sati biyu da abin sannan Umma T wani tunani yazo mata da sauri ta mik e jin abin yazo mata a bazata.  Idan Amani ta samu ciki fa? Sai ta ji fa duwar gabanta ta tsananta ta fice da sauri ta shiga motarta. Chemist ta je ta samu maganin da ta tabbatar zai yi flurshing marar Amanin. Wanda ba zai mata illa ba.
Daga nan gidan Moddi ta je, duk da bata son shiga gidan don yanayin Didi baya mata da di. Su kansu Amanin da Iman basa cikin hayyacinsu. Duk da Didi ta matsa da maganar aurensu. Mahmud D in Umma Dee dai shi za a bawa saboda har yanzu su basu San abinda Ya faru ba. Kuma wata hu du kacal aka saka. Ba tare da Moddi ya sani ba don ko sako shi a zancen yaran Didi bata yi. Kamar ko yaushe Didi da Iman kawai ta samu a parlorn. Ta zauna tana gaishe da Didi. Ta amsa mata cikin yanayin da ta Saba. Tana nuna mata wasu kayan kitchen da ta fara siyawa su Amanin. Ta gani ta kuma yaba. Sai ta kalli Iman tana furta  Ina Amani? Iman ta mik e sai Fateemahn ta ce mata ta dawo ta zauna zan je na ganta da kai na.


A zube a saman gadon ta ganta. Idonta a lumshe gaba d aya ta fita daga hayyacinta kamar ba Amani y ar gayu ba. Ta saki ajiyar zuciya ta zauna tana saka hannunta kan gashin Amanin ta mayar da shi baya don ya rufe mata fuska. Duk gashin a cukurku de yake ba ya samun gyara. Amani ta bu de lumsassun idanunta ta zube su a kan Umma T  D in. Sai ta mik e a hankali don jikin duk ba k wari ba wani abincin kirki take iya ci ba. Gaishe da Umma T D in ta yi data zuba mata ido cike da tausayi take dubanta.  Ama.. ba zaki cire damuwa daga ranki ba ko? Sai wani ciwon ya same ki ko? Dubi yarda fa kika zama? Amani lumshe idonta ta yi kawai tana jin dama wani ciwon zai sameta har ya zama ajalinta da tafi kowa son haka. Hannu Umma T d in ta saka a bakinta, hakan yasa ta bu de ido tana kallon tafin hannun Umma T D in. Tablets ta gani. Umma T ta ce  Bu de ki sha, yanzu abin yazo min kada mu je ko kin samu ciki mu shiga uku, gwara tun wuri a koro duk abinda yake cikin mahaifar. Zuciyar Amani ta dinga wani bugu. Ta dinga jin a zuciyarta tabbas da zata samu ciki ba abinda zai hana ta bar s??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????hi ba don komai ba sai don ta tonawa Dada asiri, don ita Har a lokacin ba wai ta hak ura ba ne, tana dai kallonsu suna budirinsu da son rufawa Dada asiri, amma a zuciyarta tana jin ba afuwa tsakaninta Dada tilas Ya girbi abinda ya shuka. Ba zata so ta samu ciki ba balle ta sake b atawa kanta suna duk da a wautar ta hakan shine abinda ya kamata.  Ki sha Fateemah ta furta tana tura mata tablets  din. Sai ta sha  din zuciyarta tana addu ar Allah yasa bata samu cikin ba.  Ba zai miki illa ba, amma nan da 1 hour na San za ki fara bleeding Wanda zai
Zama period d inki na San shikkenan mahaifarki ta wanku. Amani ta lumshe ido kawai tana d aga kai. Umma T ta zauna tana mata nasiha game da Dada sai ta ji zuciyarta ta  d an samu sauk i. Sai kuwa ga mararta tana mur dawa ka dan. Kamar wasa sai bleeding. Umma T, ta ce  To Alhamdulilah hankalina ya kwanta. Sai maganar karatunku na gayawa Mahmud dole zaki fara karatu da zarar an fara next session a Sky Line. D aga kai kawai Amani ta yi tana mayar da kanta saman pillow don ita yanzu bata jin tana da wani buri a duniya. Sai da marar ta lafa mata sannan Umma T ta tafi gida.


A kwana a tashi zuciyarta ta fara sanyi, Har ta koma walwalarta kamar da, suka cigaba da soyayyarsu da Mahmud, kan dole ta cusawa kanta son sa, don ko bakomai tana jin auren shine rufin asirinta. Duk da bata San me zata cewa Mahmud a sanda zai kusanceta ya jita ba budurwa ba. Wani kallo zai mata shine abinda yake  d aga mata hankali. Dada tun bayan faruwar abin bai fiye zama a k asar ba, ga wani arzikinsa da yake sake bunk asa kullum yana jirgi daga can k asar zuwa can. Don haka sam bai San abinda ake shiryawa na auren su da Mahmud ba, Didi bata gaya masa ba kamar yarda ta ja kunnen y ay anta akan kada kowa ya gaya masa. Da Umma D, ta tambayi dalili sai ta ce mata saboda Moddi ba ya son a yi auren nan kusa, ya fi son yaransa su yi karatu. Da wannan ta kashe bakin Umma D, don itama yanzu ba abinda take buri irin auren Mahmudu da Amani ba don komai ba sai don ku din Moddi da take gani, Moddi ba shi da magaji idan har Mahmud ya auri Amani ta San sune da riba. Haka Safna ma bata San me suke shiryawa ba. Ita yanzu hankalinta a kwance yake tana samun ku di irin ku din da take so. Burinta ya cika Muhammad Alwan ya cikata da naira. Ga Moddi ma yana sakar mata ku di duk da bashi da lokacinta don ya yi keeping kansa busy.



Ranar da Amani ta san tana da ciki a ranar saura sati biyu auren su, kuma a ranar Didi ta sanar da Moddi zata aurar da su Amani. Runtse idonsa kawai ya yi yana mamakin abinda Didin ta ce sai dai bai furta komai ba, don ba a ba shi damar furtawar ba. Yana kallo ta mik e ta fice daga parlorn sa. Sai kawai ya cusa hannunsa cikin sumar kansa yana fisga ka dan ka dan&



Wannan shine abinda ya faru& .



&&&&

An dawo labari&



Cikin dare Amanin ta dinga jin motsi a  dakin da take kwance a asibitin. Ba barci take ba hakan yasa ta bu de ido tana kallon mutanen da suka shigo cikin d akin jikinsu sanye da black wears& fuskarsu a sink e cikin face mask. Tana kallo suka gudawa duka mutanen d akin wata powder. Tana shirin ihu itama suka busa mata& daga nan bata San me Ya faru ba. Sai bu de idonta ta yi ta ganta a wani irin d aki& &





JIKAR NASHE
'


Saura 2 pages a gama book 1. Shine kuma free. Don samun cigaba ki tura 500 ko 1k don shiga aji na musamman ta wannan account D in. 2118666253 UBA.




HADARIN GABAS YANZU AKA FARA!HADARIN GABAS& ..=?L?



33.


NAZEEFAH SABO NASHE.&
'?

08033748387.


BRIGHT PENS SECOND BATCH

Ware idonta ta yi sosai tana duban babban bedroom d in, da ya sha Kayan more Rayuwa masu azababben kyau. D akin banda fitar da wani irin sassanyan k amshi ba abinda yake yi. Ta dinga bin d akin da kallo tana mamakin ina ne nan? Bata samu amsa ba kasancewar ba kowa a wajen. Ta mik e tana jin yarda kanta ya wani irin sar? mata kamar zai fa do, hakan yasa ta rik e kan nata tana cije bakinta ka dan. Ta koma ta zauna don ba zata iya tafiya ba, wani irin ciwon kai take ji ga mararta data matsa mata da ciwo. Tsawon mintuna tana zaune a gefen tattausan gadon ba tare da ta San abin yi ba. Sai ta dinga jin motsi alamar ana bu de k ofar d akin. Ido ta Ware ganin wacca ta shigo. Mace ce cikin kamilalliyar shiga sai kallonta take murmushi fal fuskarta ta furta  Kin tashi? Madadin Amanin ta amsa mata sai ta d auke kanta, zuciyarta na wani irin bugu ta furta  Ina ne nan? Wa ya d auko ni daga asibiti ya kawo ni nan? Girgiza kai matar ta yi tana furta  Sanin ba shi da wani amfani, don haka gwara ma ki daina tambaya ki fuskanci abinda yake gabanki, Uwargida ta ce a yi Miki duk abinda kike so, mu lallab aki tamkar sarauniya don haka yanzu zamu cigaba da bin Umarninki&   Uwargida? Amani ta furta cikin sigar tambaya. Matar ta sake sakin murmushi ta furta  K warai kuwa, na San baki Santa ba, amma nan gaba ka dan za ki Santa, ta ce tana gaisheki ki kuma kula da kanki da abinda ke cikin ki, don a yanzu bata da wani abu mafi soyuwa da ya zarce ke da  d an cikinki a duniyar nan& . Hannu Ama ta saka ta Shafa cikin, zuciyarta na wani irin wuntsilawa bata so ta gasgata abinda yake ranta, amma tabbas ko ta k i ko ta so dole ta yarda Dada ya siyar da ita, Ya kawo ta inda za a tsafaceta a tsaface d an cikinta& sai ta dinga jin wani irin takaici zuciyarta ta dinga zafi. A zafafe ta kalli matar ta ce  Idan burinku d an cikin, ku cire shi ku bar ni naje na yi rayuwata kamar yarda kuke so&   Ba hurumina bane wannan&  Matar ta fa da tana sakin dariya. Sai kuma ta jawo food warmers masu kyau ta shiga zuba lafiyayyen abinci a cikin plate ta tura gaban Amani. Kallon abincin ta yi kafin ta furzar da huci.  Ba zan ci ba, ki d auke daga gabana. Bata bi tata ba ta fice ta bar mata d akin. Amani ta yi saurin mik ewa zuwa bakin k ofar. Sai ta tarar k ofar irin mai thumbprint ce dole ba zata iya fita ba komai zata yi. Hawaye ya zubo mata, a hankali ta zube a saman tattausan carpet  din tana sakin kuka. K amshin abincin ya dinga rinjayar yunwar da take ji don haka bata San sanda ta ja plate D in ta fara ci ba. Ita kanta ta manta yaushe rabonta da abinci don haka ta zage ta ci abincin sosai. Ta kuma sha sassanyan kunun ayar da aka ajiye mata.




_______

Sai da gari ya yi haske sosai sannan Iman ta farka daga sumar da ita da aka yi a d akin asibitin, aka sakata barcin dole. Su Didi da Umma T, ta fara kalla kafin ta mik e tana jin kanta na wani irin sarawa. Bu de ido ta yi ganin agogo Ya nuna har k arfe 9:00 ta fara tunanin wani irin barci suka yi, don dai bata jin duka mutanen d akin sun yi sallahr asuba, idan kuma Sun yi me yasa ita basu tashe ta ta yi ba. Saman gadon Amani ta kalla sai ta ga wayam. Tunaninta tana toilet sai dai duk zaman jiran da ta yi, ba Amani ba labarinta. Da sauri ta mik e ta isa bakin toilet d in tana zabga kiran Amanin jin shiru yasa ta tura k ofar toilet D in taga wayam. Da sauri ta dawo  d akin idonta Ya hasko mata takarda. Ta isa da sauri ta fara karanta takardar tana jin bugun zuciyarta na k ara gudu ganin abinda yake cikin takardar.  Kada ku neme ni, ba zan dawo ba, na yi nisan da ba zaku tab a samu na ba, ba zan iya zama ba, ba zan iya cigaba da rayuwa da ku ba&  Ta dinga kallon rubutun tana son ta tantance na Amanin ne ko na wani daban. Idonta ya fara zubar da ruwa. Bata san sanda ta k walla ihu ba. A razane Umma T, ta farka kafin Didi ma ta farka. Suka furta  Lafiya Iman? Takardar hannunta ta nuna mata tana furta  Ama& Umma T, ta gudu ta tafi ta bar mu.
Umma T, ta zauna turus a saman gefen gadon dafe da k irjinta da ya matsanta mata da bugu.  Kira wayarta Imaan, kira mu ji idan Har wayar na yi zan saka a yi tracking d inta duk inda take. Iman ta yi saurin d aukar wayar ta fara kira sai dai me, wayar Amanin tana d akin tana ringing alamar bata tafi da ita ba. Umma T, ta runtse idonta tana jin tashin hankalinta na sake girmama, ina Amani zata tafi? Wace rayuwa zata je ta yi shine abinda ya tsaya mata a rai. Didi kuwa ba bakin magana don maganar ma ta d auke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login