Showing 33001 words to 36000 words out of 94443 words

Chapter 12 - HADARIN GABAS HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

171

ni ba ne? Girgiza kai Imaam ya yi kafin ya tsiyayi lemon mai sanyin gaske ya kai bakinsa. Idanunsa akan Alwan da yake sakin murmushi.  Nagode da ka sha, da baka sha ba akwai matsala& . Ya furta yana saka glass d insa da ya kasance bak i wuluk.  Matsala kuma? Alwan ba wani damuwa a fuskarsa ya d aga kai yana furta  Babba ma kuwa&  ya d an ja fasali sai kuma
Ya furta  Ka san mu larabawa bama son mu yiwa mutum kyauta ya k i amsa, sai mu ji ba da di a zuciyarmu. Ya sake fa da yana d an sakin murmushi. dafa shi ya yi ya furta  Rashin shan da zaka yi zai saka na ji a zuciyata baka amince da ni ba. Sai sannan Imam ya saki ajiyar zuciya, amma sai ya samu kansa da jin wani irin nauyi a kansa take ya d an lumshe ido yana sakin ajiyar zuciya bai kawo komai a ransa ba sai tunanin ko don yana cikin b acin ran Safna ne.

 Ka tashi mu je. Ya furta yana dafa kafa darsa Imaam ya mik e a hankali ya bi bayansa.

Motarsa ya ce su shiga ya ajiye machine d in nasa. Hakan kuwa aka yi. Direct cikin abinda bai fi mintuna ba Imaam ya gan su a cikin Government House. Da mamaki yake kallon Alwan d in. D aga masa kai kawai ya yi ya furta  Mu je, zan ga Governor na kai masa sak o. Jikin Imaam a sanyaye ya fito ya bi bayansa yana mamakin wai yau shine zai ga Governor lallai ha duwarsa da Alwan alheri ne.


A babban parlorn gwamnati aka saukesu inda gwamna yake gaisawa da manyan bak insa. Mamaki bai gama cika zuciyar Imaam ba, sai da Gwamna ya shigo madadin yaga Alwan ya mik e ya kai gaisuwa sai yaga ma Gwamnan ne yake daraja Alwan d in.  Barka da sauka Doctor Alwan&  Murmushi Alwan ya sakar masa yana firta  Nice to meet you excellency&  Gwamna ya d aga kai yana sake sakin murmushi sai kuma ya kai dubansa kan Imaam yana masa kallon rashin sani ko kafin ya yi magana Alwan ya yi gyaran murya ya furta  A best friend of mine&  Gwamna ya saki murmushi yana mik awa Imaam hannu. Imaam ya d an ji wani banbarakwai sai kuma ya dake ya mik a masa nasa hannun shima.


Zai Mik e ya fita ganin kamar tattaunawar tasu ta sirri ce Alwan ya saka baki ya kira shi.  Just sit, ba sai ka fita ba. Ya koma ya zauna. Yana kallon wani kallo da Gwamna ya masa sai kuma ya d auke kai ya cigaba da kallon Alwan da yake mik o masa papers.  Zaka yi signing anan kamar yarda na fa da maka, mun kuma amince da buk atarka ta ka sanya hannun jari a companyn da zamu bu de anan, mun yarda zamu bu de babban companyn don cigaban arewa&  Murmushi da ya bayyana tsananin murnarsa gwamna ya saki yana furta  Alhamdulillah& Nagode sosai ka mik a min godiyata wajen Boss&  murmushi Alwan ya saki yana furta  No problem Excellency.. ya mik e yana mik a masa hannu suka gaisa da tafawa sannan ya fice a hanzarce bayan ya kalli Imaam da duk yabi ya zama kamr wani gunki a wajen. Murmushi ya saki ka dan. Ya dafa shi yana furta  Shall we? Imaam ya d Aga kai ya mik e shima ya bi bayansa da d an hanzari.



A mota kasa shiru Imaam ya yi sai da ya kalli Alwan ya furta  Dama ka tab a zuwa Nigeria? Murmushi kawai Alwan ya sakar masa kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya saki ajiyar zuciya ya furta  Rabin rayuwa ta na yi ne a Nigeria Abuja, shi yasa zaka ji na iya Hausa sosai, amma all my family suna Turkey, ni na zauna anan ne saboda issue na business&  Imaam ya girgiza kai.  Ka san Turkish companies da suke cikin k asar nan? Imaam ya yi saurin d aga kai  Shi kuwa ya san Turkish group of companies duk wanda yake K asar nan Ai ba zai ce bai san wa dannan companies d in da k asar nan take alfahari da su ba. Kamfaninnika ne da suke sarrafa kayan masarufi iri iri na abubuwan amfani da furniture s masu kyau da tsadar gaske,?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? a kwanan nan suke shirin bu de companyn ha da motoci.  Na familyn mu ne&  Ya ji muryar Alwan a sama  Ni nake monitoring na Nigeria. Da sauri Imaam ya juya yana kallonsa idan kuwa har ta tabbata da gaske ne tabbas Alwan ba shi da girman kai kuma ya tsinci dami a kala.  Kana son ka yi business da mu? Imaam ya d aga kai da sauri don ba zai bar kansa ya k ulle ba. Murmushi Alwan ya saki a zuciyarsa ya furta  Nice, hakan ya yi&  a fili kuwa cewa ya yi  Akwai shara di& idan ka amince sai nace maka ka godewa Allah ka kusa shiga sahun billionaires na Arewa&  Imaam ya ha diye yawu yana d aga kai  Sharad in me? Sai da Alwan ya juyo kamar ba driving yake ba sai kuma ya juya yana cigaba da tuk in ya furta  I will tell you, but not now.


A wurin siyar da motoci ya yi parking yana kallon Imaam ya furta  Mu je ka min rakiya, Allah yasa ka iya mota ka ja min ita. Imaam ya d aga kai yana furta  Na iya.. ya jijjiga kai yana murmushi suka isa wajen wata Honda accord mai masifar kyau bak a wuluk. Ya yi ciniki ya biya ku din ya mik awa Imaam key d in. Imaam yana kallonsa ya furta na menene?  Na taimako na da ka yi, kuma kada ka ce min ba zaka amsa ba ka san hukuncin hakan islamically.. Imaam ya saki ajiyar zuciya ya kuma kasa yi masa musu yana kallo ya fita ya bar shi a wajen yana furta  Zan kiraka anjima zan je Abuja but zan dawo morning. Ya lakace hancin Imaam ya fita daga wajen yana murmushi ko bakomai burinsa ya cika. Imaam kasa motsa wa ya yi daga wajen ya dinga kallon Motar da aka ce tasa ce ya lumshe ido yana mamakin Alwan da dukkan alherensa daga ha duwa jiya kawai? Ko da yake a arziki irin na danginsu ya san wannan bakomai ba ne. Don haka sai ya ji ya samu nutsuwar zuciya ya shiga motar cikin matuk ar farin ciki ya ja zuwa gidan Hajja don ita ya kamata ya fara sanarwa& .




&&
'?


Safna kuwa tun bayan fitar ta gida hankalinta tashe bata tsaya ko ina ba sai a gaban Malaminta. Yanayinta da ya gani ya tabbatar masa ba lafiya ba. Ya san Safna ba tun yau ba ta amince da cewa shi ke samar Mata da duk wani farin ciki.


Sun gaisa hankalinta a tashe ta sanar da shi dalilin zuwanta. Idanu ya zuba mata bayan duk ya gama jin abinda ta ce ya furta  Akwai matsala Safna, dole ki tashi tsaye akan Mijinki don idan baki wasa ba kina ji kina gani zai fi k arfinki&  Tashin hankali ya bayyana k arara akan fuskarta idan da abinda ta tsana a sanar mata da Imaam zai rabu da ita. Ta yarda da aikin Malamin nan tun farkon ha duwarsu da Imaam shi ya mallake mata zuciyarsa da tunaninsa.  Akwai alheri ma da yake matso shi nan kusa, sai dai idan ba ki yi da gaske ba zai ture Alherin akan wani dalili&  Ta waro ido  Malam hakane wallahi, don jiya ya ha du da wani mutum mai ku di sai dai da dukkan alamu baya son tarayyarsu da mutumin Malam ina son ka kulle bakinsa ya zama duk abinda mutumin ya umarceshi kawai ya aikata ba musu, ni in dai Imaam zai yi ku di kawai koma ta wani hali ne ya yi, ko na huta da gorin dangina na auri wanda ba shi da ku di&  Malam ya saki murmushi  An gama Safna, arziki kam Mijinki zai yi shi, amma a k arshe fa naga wani duhu& ..  In dai a k arshe ne Malam duk daga baya ne, kawai a min aikin da zai yi abinda suke so ko baya so. Sannan ka rufe min bakinsa tsaf kada ya dinga gayawa kowa sirrinsa sai ni ka dai don kada ya je ya gayawa Hajja ta hana shi ta cucemu. Ta fa da ba tare da ta bari bokan ya gaya mata duhun me ya gani ba.Malam ya jijjiga kai ya cigaba da dube duben k asarsa ya d ago yana kallonta ya furta  Zaki iya birne bunsuru da rai?  Ba abinda ba zan iya ba Malam kai kanka shaida ne don na yi wanda ya fi wannan in dai akan Moddibo ne& . Tabbas kin yi Safna ni kaina ina jinjinawa jarumtarki da rashin tsoro, don ma dai mijin naki tsohuwar sa a tsaye take a kansa da wallahi sai yarda kika yi da shi tsabar Mallaka& amma yanzu ma ki sha kuruminki za mu yi masa aikin da ba zai gaya musu komai ba daga cigaban da ya sameshi gudun kada su hana ruwa gudu& . Ta saki ajiyar zuciya ta fara kallon Malam tana godiya. Ya ha da mata duk abinda ya dace saura kuma ya ce ta dawo kashegari.  Yanzu Malam idan na aikata haka d in, ba zai min maganar abinda ya faru da safe ba?  Ko zancen ba zai d aga ba, ki je kuma zaki bani labari. Bata ji ko d ar a ranta ba don ta yarda da Aikin Malamin. Ta zura takalminta jikinta na rawa ta fice direct gida ta koma hankalinta kwance ta fara aiwatar da surkullenta da k ulle k ullenta& Tana yi tana sakin murmushi a ranta tana k addara cin zalin yaran da bata son ganinsu ko ka dan yanzu ta fara& .




Har k ofar gidan Hajjan ya je da motar, sai dai yana fitowa ya samu k aton kwa do a k ofar gidan. Rik e kansa ya yi kawai don bai ji da din rashin ganin Hajjan ba. Don haka ya sake komawa motar ya nufi gidansa duk da yaso zuwa gidan Fateema sai ya ji zuciyarsa ta kasa aminta gida kawai yake so ya je ya nunawa Safna.



Gidan fes ta saka su Mama Talatu sun share sai k amshin turaren wuta yake. Ita Kuma ta fece wanka da wani Ubansu Riga da wando ta yi kyau sosai don kam k irjinta a cike yake sosai har yana rinjayarta daga k asa ne dai bata da shape ko ka dan. Jikinta gaba d aya ta balbaleshi da turarukan sihirin Malam. Ta d au Layar ta saka a k asan harshenta idonta akwai sihirtaccen kwalli.

Tunda ya yi sallama ya ji kansa ya sara da k arfin gaske. Matsalar Moddibo kenan rashin addu a ya kama kan yana zama a saman kujera kafin ya yi aune Safna ta shiga jikinsa ta yi amfani da wannan damar wajen ribartasa ya kusanceta a take a wajen cikin fitar hayyaci saboda turarenn da yake jikinta ya sabbaba masa son kusantarta a k asanta kuwa dama ta shafa rubutun da Malam ya bata. Tuni Moddi ya manta da duk abinda ya faru. So da k aunar Safna sai sake ruruwa suke a ransa. Ya kama hannunta yana janta waje.  Zo mu je kiga kyautar da aka ba ni?


Cikin farin ciki ta dinga zagaye motar tana jifansa da wani kalar murmushi ta furta  Alwan d in ne ya baka? Ya  d aga mata kai yana murmushi. Cikin son sanin ko aikinta ya kama shi ta furta  To kada na ji kada na gani bana son ka gayawa kowa cigaban da zai sameka& &  Imaam Ya d aga mata kai, fuskarsa na bayyana da gaske ya bi umarninta. Ta d an saki murmushi tana lakace masa hanci ta furta duniya sabuwa!



Daga ranar an d au tsawon sati biyu Alwan bai neme shi ba. Bai kawo komai a ransa ba don shi sam bai saka son duniya a gabansa kamar yarda Safna ta saka ba. Itace dai shiga d ari fita d ari idan zai yi, she will keep asking Alwan D in Ya kira ka? Idan ya girgiza mata kai. Sai ta yi kamar zata yi kuka ta furta  Kai kuma ba sai ka nemeshi ba, ni wallahi Ban tab a ganin Wanda arziki ke bi ba sai kai, ko da yake ba abin mamaki ba ne dama kun yi gadon talauci duk Wanda Ya Saba da arziki ai ba zai guje shi ba&  Ranar da ta fara fa da masa haka zuba mata ido ya yi ransa a b ace yana fitar da hucin numfashi Amma kuma ya kasa d aukan mataki. A kashegari kamar wasa sai ga kiran Muhammad Alwan nan wajen sha biyun dare& Da wani irin sauri Safna ta finciki wayar ta saka ta a handsfree tana masa nuni da Ya amsa& murya a hankali suka gaisa da Muhammad Alwan d in. Sai daga can Alwan D in Ya ce  Friend, sai ka ji ni shiru kuma? Amma baka nemeni ba, haka ake abota? Da sauri Safna ta ce  Eeeh wallahi, yana ta son kiranka to ba ya so ya damekane kana aiki, amma kana ransa wallahi&  ta furta tana hararar Imaam da ya yi shiru kawai ya kasa furta komai. Alwan daga can ya d an yi murmushi kawai kafin ya furta  Haba Aboki, ai an zama d aya you can call me at what ever time you want& yanzu forget wannan, abinda yasa na kiraka I want to meet with you at Abuja that s why na maka booking flight na 7:30 am zaka same ni gobe a can. Moddi ya d an waro ido. Safna ta zabga masa harara tana furta  Zai zo In sha Allah, ba abinda zai hana shi zuwa. Mun gode k warai. Muhammad Alwan Ya yi cutting kiran, yana mamakin hali irin na matar abokinsa da alama ko wata matsala ce ta taso nan gaba, ba zasu yi wahalar siye matar can ba. Ya saki murmushi kawai. Yana gyara zamansa idonsa akan Boss d insa data zuba masa ido. Hannunta d auke da wani glass cup mai shegen kyau tana kurb ar ruwan tattaccen inib?. Kayan jikinta masu masifar kyau. Ita kanta dattijuwar mai kyau ce jikinta duk ta sha adon gold wuya da hannu Har da sark ar k afa. Kanta ba d ankwali hakan ya bawa gashinta irin na larabawa damar zuba Har gadon bayanta. Muryarta very low kamar wacce bata son yin magana ta furta.  Aikinka yana kyau Bro& ya amince zai zo goben? Alwan ya d aga kai yana furta  Sure zai zo Hala. Kuma aikin ba zai mana wahala ba, don wannan matar tasa masoyiyar ku di ce. Matar da Ya kira da Hala ta d an saki murmushi tana lumshe idonta ta sake kai cup D in bakinta, ta yi sipping kamar bata so sai kuma ta furta  Make sure ka yi yarda na ce, bana son kuskure you know a komai nawa bana son shirme, ku di ba matsalata ba ce ka jik a su da Naira matuk ar zan samu cikar burina&  Alwan Ya jinjina kai. Yana furta  Ba wani kuskure fa In sha Allah Hala.  Good for you. Ta furta tana mik ewa cike da tafiyar rangaji ta shige d aki. Alwan Ya bi bayanta kafin ya mik e shima Ya fice tabbas gaba da gabanta ji yarda yake Boss a waje, amma anan Macece take da mulkin take kuma bashi umarni yarda take so. Ya saki murmushi kawai ya fita don cigaba da shirin tarar Moddi da zai zo a goben.




&&

Asubar fari Safna ta tashe shi, da mamaki ya dinga kallonta don baya tunanin ta yi barcin arziki. Matar da da sai ya yi da gske take tashi ta yi sallah k arfe bakwai amma yau itace ta tashi da wuri haka. Ya zuba mata ido da sauri ta ja hannunsa tana furta  Ka tashi mana Imaam, ka wani zuba min ido sai lokaci ya k ure? Kai komai sai ka saka shiririta. Ta zabga tsaki tana shigewa Toilet tana jansa kamar wani yaro. A toilet da k yar yake wankan haka kawai sai ya dinga jin gaba d aya ba ya jin da din zuciyarsa ga wani irin fa duwar gaba da bai San ko ta Mecece ba. Haka dai ya yi wankan ya fito. Kafin nan har Safna ta fito masa da kaya sabuwar shaddarsa ta Sallah, abinda da bata tab a yi ba. A hanzarce ta saka shi Ya shirya ranar har cikin bedroom ta kawo masa breakfast. Ya  dan kurb i ka dan ya ajiye yana yamutsa fuska ya ce  Safna, bafa son tafiyar nan nake ba, gaskiya a hak ura kawai&   Ai kuwa tafiya kamar ka je ka gama&  Ta fa da idonta a cikin nasa tana danne Layar bakinta. Ba shiri ya zura hularsa kamar Wanda ake kunnnawa da remote Har ya kai k ofa ya jiyo yana kallonta Ya ce  Su Ama fa? Wa zai kai su School yau? A zafafe Safna ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login