Showing 78001 words to 81000 words out of 94443 words

Chapter 27 - HADARIN GABAS HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

174

ba. Imaan  din ta dinga amsa mata a  darare don tsoron Safnan take ji kamar yarda take tsoron ranta. Ban da Allah ya kiyaye tana dagewa da addu a da tuni ta sakata a mummunar hanya bata San me yasa a yanzu ma Safnan ta janye makaman yak inta ba.



K arfe shidd ta k irk iri ciwon cikin k arya bayan da ta tabbatar ta aikata abinda take so successfully& Ba wanda ya kawo komai Didi ta ce su tafi asibiti da Imaan. Suna zuwa asibiti Doctor ya tabbatar musu sai an yi admitting Safnan. Iman taso guduwa gida Amma Safnan ta rik e hannunta tana furta  Why? Idan kika tafi wa zai zauna da ni, ki bari drip  din ya k are mu tafi tare. Haka Imaan ta hak ura ta zauna ba don ranta yaso ba.



Suna zaune a parlorn Didin Amani ne da Didin kawai. MODDI ya shigo sai  daukan ido yake fuskarsa cike da walwala ya zauna a kujerar da take gefen Didi. Yana kallon Amani da take zaune tana kallonsa cike da fa duwar gaba. Wani irin take ji a duk sanda suka kusanci juna. Didi da farin ciki ta furta  Alhamdulilah Ya ka baro amaryar? Ya cire hularsa yana jingina da kujera idonsa a lumshe murmushin fuskarsa ya kasa d aukewa Ya furta  Tana gaishe ki, da kowa ma. Amani taji zuciyarta kamar ta tarwatse don haka ta mik e kawai zata wuce Moddin ya ce  Ama&  ta juyo jin ya ambaci sunanta ledar hannunsa ya mik a mata sai kuma ya mik awa Didi tata. Daga haka ya mik e ta gefen Amanin yazo zai shige ya furta  Koma ki zauna, Dodon naki ya tafi. Duka jikinta ta ji wani irin yarrr jin yanayin sound  din muryarsa. Ta rik e ledar a hannunta kafin ta zauna cikin mutuwar jiki. Didi tana kallonta ta furta  Alhamdulillah yau buri na ya cika Moddi Ya auri kamilar mace wallahi. Baki ganta ba. Amani ta  d an cije leb e kawai. Didi ta saki tsaki  Wai Uban me aka miki ne yau nake ganinki sukuku, ina lura koda aka sha ruwa ba wani abin kirki kika sha ba, wuce ki je kitchen akwai fura a fridge dana dama Miki don na San ke gwanarta ce ki  d auko ki sha a gaba na. Amani ba don tana so ba, sai don tana son Didin ta daina mata hayaniya a kai ta samu kuma ta barta ta huta yasa ta shiga kitchen  din ta  d auko furar ta kawowa Didin. Didi ta zuba a cup ta mik a mata tana janyo ledar da Dadan Ya bawa Amanin taga nama ne mai zafi sai Icecream a ciki da fresh milk. Ta furta  To maza ki zauna ki sha komai, haba yarinya duk kin bi kin fige&  Dole Amani ta dinga turawa a cikinta, komai ciki take yi cikin rashin kwanciyar hankali. Didin ma ta ja nata tana ci kaza ce da yoghurt. Amani dai bata San ta kusa shanyewa fresh milk D in ba ko don da gaske tana jin yunwa ne. Ta ajiye tana kallon Didi ta mik e  Zan je na yi freshen up na kwanta. Didi ta fara kallonta da dishi-dishin idonta da take jin wani irin masifaffen barci ta  daga mata kai. Tun kafin Amani ta kai  d aki Didi ta mik e ta shige nata d akin tsabar barcin da yake idonta. Amanin wanka ta yi ta kwanta rigingine tana jin yanayin da take ciki yana sake k arfi. Ta runtse idonta da k arfin gaske tana hango Dada tana kuma jin muryarsa a kunnenta kamar yarda ya saba zuwa mata a barci. Abu fa Ya fara zafi ga wani irin yanayi da take ciki kamar mai maye, ta runtse idonta tana imagining abin wani irin feeling Mara misali take ji, a yanayin mayen ta mik e daga ita sai b ingilar rigar barcin da take jikinta ta fice daga sashen Didin zuwa sashen Dada, ta  d an walkway  din da yake hanyar da zata sadaka da sashen Moddin& . Cikin mayen ta tura k ofar parlornsa tana tafiya cikin wani yanayi kamar ba ita ba ta shiga bedroom  d insa. Jin ta take kamar a mafarki ba abinda take so irin jinta a jikin Moddi yana aikata mata abinda take imagining bata cikin hayyacinta kamar yarda bata San sanda ta kai kanta gadon ba ta kuma shige jikin Moddin& & .




JIKAR NASHE&
'?HADARIN GABAS& & .=?L?



NAZEEFAH SABO NASHE&
'?



08033748387.



BRIGHT PENS SECOND BATCH



30.



Cikin wani irin hali da shi kansa ya kasa controlling kansa gangar jikinsa da zuciyarsa. Ruhinsa gaba d aya baya tare da shi, kamar a maye yake kamar kuma a buge yake a haka komai ya kasance, k addarar kusantar junansu a daren ta afku, cikin wani irin hali da su kansu basu sani ba, idonsa ya rufe burin juna kawai suke& . Sai da ta ji shigarta jikinsa ya bu de kuma abinda kowace budurwa ke alfahari da shi, Sannan ta sake fita daga hayyacinta. Wani irin barci mai nauyin gaske barcin da su kansu basu San yaushe ya  d auke su ba&



A gadon asibitin wani irin fa duwar gaba ne ya samu Safna. Ta dafe k irjinta tana karanta addu oin da ita kanta ta san da wuya Allah ya amsa mata. Tana tare da tarin manyan laifukanta. Ta sani mai afkuwa ta afku, ta cika burin Alwan gefe d aya tana tunanin nata burin ya cika. Burin mallakar Imaam Moddibo, ruhinsa dukiyarsa. Zata juya shi son ranta sannan zata yi amfani da wannan damar wajen threatening danginsa. Ta lumshe idonta tana jin zafi a k asan ranta Wanda ba na komai ba ne sai na tsananin kishi. Yau Imam ya kusanci budurwa Ya ji d and anon budurwa zai gane tarin banbancin da yake tsakanin budurwa da bazawara. Sai ta dinga jin wani d aci a ranta. A zafafe ta fisge ledar drip  din da yake hannunta sannna ta mik e, idanunta akan Imaan da take zaune itama duk ta rasa nutsuwar, wani irin firgici take ji a ranta. Ta kira wayar Amani yafi a k irga ba ta  daga ba, ta kira Didi itama shiru. Ta kira Umma Talatu ta tabbatar mata komai da kowa lafiya, kuma Didi Sun kulle sashensu balle ta kai mata. Sai ta mayar da kiranta kan Dada shima still bai  d auka ba. Haka ta gaji ta zubawa wayar ido tana jin fa duwar gabanta na sake k arfi.  Tashi mu tafin da Safna ta furta shi ya dawo da ita cikin hayyacinta ta Ware idonta kafin ta mik e a hanzarce, don tafiyar ita tafi buk ata, wannan yanayin da take ciki ba zai zama bakomai ba, dole akwai abinda yake faruwa Wanda ba ta fata mummunan mafarkin da ta yi ya zama gaskiya. Idan kuwa hakan ta faru bata jin zata yafewa Dada da Amanin kanta. Jiki a sanyaye take bin Safna da take tafiya da k arfinta kamar ba patient ba da kallo. Sai ta samu kanta da k aryata ciwon Safnan& zuciyarta ta tsananta bugu tana fatan ba wata kitimirmira Safnan ta shirya ba. A motar Safnan da aka bari a asibitin suka nufi gida. Cikin wani irin rough driving Allah ne ya kai su lafiya. Horn ta dinga zabgawa mai gadin irin Wanda ta tabbatar zai gigita shi. Ai kuwa ya gigitashin don da sauri ya fito a mugun gudu. Ya danna remote gate D in ya zuge ta shiga da motar da wani irin gudu kamar zata take ma aikatan gidan. Da sauri suka koma gefe suna mamakin mai yasa ta wannan gudun. Ko jakarta bata d auka ba ta fita a fusace sai Iman ce ta rufe k ofar motar. Tana taku kamar tana tafiya ne da zuciyar ta, don yanayin takunta yanayin bugun zuciyarta. Ta San komai ya faru kuma recorded kamar yarda ta mak ala mitsitsiyar camera a  d akin. Hannunta na rawa ta saka zata bu de part   d in Imam  din sai ta juya ta kalli Iman da ta biyo bayanta. Wani irin fusataccen kallo ta watsa mata, Wanda ko bata fa da ba Iman  din ta San garga di ne take mata, na kada ta sake ta kusanto k ofar. Iman ta yi baya ta koma part  din Didi.


Yarda hannunta ke rawa haka jikinta yake b ari sanda ta tura k ofar part  din Imam  din. Haske ne ka dan a  dakin, sai wani kalar azababben k amshin turare da ya shiga hancinta. Zuciyarta ta cigaba da bugu. Idonta a rufe ta danna Switch  din wutar  d akin. Idonta ya hango mata su, da gaske komai ya faru don ga Amani nan bisa k irjin Ubanta tana barci, shi kuma ya rungumeta sosai& Wani irin ihu Safna ta saka Ihun kuma bai saka Sun farka ba. A fusace ta bu de Fridge  din da yake d akin ta bu de ta  d auko ruwa mai shegen sanyi ta watsa musu. A gigice suka bu de ido a tare, kuma hankalinsu a take ya dawo abin ya dawo musu kamar flash. Da sauri Amani ta janye jikinta tana Ware ido sanin cewa wannan ba mafarkin da ta Saba bane, don da gaske take jin wani irin zafi a k asanta, zafin data tabbatar na rasa budurcinta ne& . Da sauri ta runtse ido jin Ihun da Safna ta sake yi, ihun da ta tabbatar Didi zata ji ta, don windown ventilation  din d akin Dadan yana fuskantar na Didi kuma duk a bu de suke. still a cikin maye take don ji take kamar ta fa di duk da a zaunen take, amma fa komai ya dawo mata daki-daki kamar majigi da sauri itama ta zabga nata ihun. Dahdan ma idonsa a runtse suke kawai. Amma dukan da Safna ta kaiwa Amani ya saka ya bu de idonsa. Da sauri ya rik e hannunta  Don t touch her&  ta fisge hannunta tana masa wani irin kallo daidai lokacin da Bugun k ofar Didi da Iman ya cika musu kunne& Safna ta tafi zata bu de da wani irin jarumta da fisgo muryar da yake tunanin Anya tasa ce ya furta  Idan kika bu de a bakin aurenki, idan maganar nan ta fita shima a bakin aurenki& . Da sauri ta juyo tana zuba masa wani irin kallo. A zafafe ta ce  Imaam, kana da courageous har kana iya kallo na ka gaya min haka, ni zaka yi threatening da wannan& . Cije bakinsa ya yi fuskarsa a d aure sosai ya zira rigar jallabiyarsa, wata irin kunya yake ji dannewa kawai yake. Ya isa gefenta a fisge yake wani kallonta  Am telling you the truth, ba laifin yarinya ba ne as we all know nima ba laifina bane, ke kika jawo komai ke kika amince na yi ku di ko ta wani hali, so ga hanyar da son ku dinki ya kai mu nan& . Ihu Amani ta sake saki tana jin zafi a ranta burinta ta iya mik ewa ta dak umi Dada ta shake shi shi da Safna su Mutu. Idan har lissafinta yana tafiya daidai sun yi amfani da ita ne don son duniya da son su yi ku di. Tafarfasa zuciyarta kawai take tana jin bugun k ofar Didi. Ba zata iya bu dewa ba don bata da lafiya, jikinta ciwo yake kamar yarda k asanta ya matsa mata da ra da di da zugi& tana jin Safna ta saki wata shigiyar dariya tana furta  Ni na jawo ko Imaam, to zan gayaw duniya waye kai zan nunawa duniya abinda ka aikata da y ar cikinka, zan fallasawa duniya wannan vedion Har Uwarka Didi wallahi sai na nuna mata sai dai hakan ya yi ajalinta! Imaam da yake tsaye ya dinga jifanta da wani irin kallo yana cije bakinsa, kafin ya furta  Bar  d akin nan Safna kafin ranki ya b aci, zan iya aikata miki komai I swear&  ya fa da yana cusa hannunsa cikin tarin sumar da take kansa cinkus. Safna ta share hawayenta tana furta  Za ka sani Imaam. Tana kallo ya fisgo hannun Amani ya bu de wata k ofa Ya tura ta ciki, ba zai so Didi ta ganta a haka ba. Don haka duk turjewar Amanin bai sake ta ba sai da ya saka ta a cikin d akin, bedroom ne babba da ya sha kayan alatu. Ya fito yana kallon Safna da still take tsaye kuma har lokacin Didi da Iman basu daina bugun da suke yi ba& hannu yasa ya  dau wayarsa ya danna kiran Umma T. Umma T jikinta na rawa ta amsa wayar  Ki zo yanzu please! Da sauri ta Ware idonta tana furta  Me ka aikata Kiddo? Shi yasa tun  d azu na kasa samun nutsuwa, me ka aikata na ce maka. Murya a can k asa ya furta  Bakomai, ki zo please akwai matsala.. daga haka ya yi cutting kiran Ya shige toilet daidai lokacin da Safnan ta bu dewa Didin k ofa. Didi tana kallonta cikin tashin hankali ta furta  Ina Amani? Safna ta rushe da kukan k arya tana nuna mata wajen da ba zaka tab a cewa d aki ba ne don ya saje da bangon wajen ba k ofa. Didi ta ce  Ban gane ba, ina take? Safna ta saka kuka tana furta  Ya b oye ta cikin d akin sirrinsa, d akin da yake ajiye tarkacen tsafinsa bayan ya mata fya de& . A tare Didi da Iman suka zube k asa da alama dogon suma suka yi. Moddibo da bai San abinda ake ba, ya fito jikinsa sanye da kayansa yana sake goge kansa. Ganin Iman da Didi a k asa yasa ya ware ido yana kallon Safna, ya yi kanta da sauri, yana furta  Me kika aikata musu? Ta fincike hannunsa a wuyanta tana furta  Na gaya musu abinda ka aikata, and so what? Wallahi ka sake ni sai na gayawa duniya abinda ka aikata, idan kaga ban gaya musu ba ka saki matar da aka aura&  Bai bi ta kanta ba ya dai cije bakinsa Ya isa kan su Didi yana shafa musu ruwa a fuska. Suka saki ajiyar zuciya a kusan tare. Didi ta kama hannunsa ta rik e sosai a hannunta tana furta  Ka gaya min Moddi, ka gaya min mummunan mafarkin da na Saba ne.. ya yi k asa da kansa hawayen idonsa yana zuba, Wanda shi kansa bai San dalilin zubar su ba, bai San a mizanin da zai ajiye su ba. Ya matsa hannunta a hankali ya girgiza mata kai. Shigowar Umma T, da sauri ne ya saka shi mik ewa ya matsa daga wajen da suke& a fisge ta ce  Ina Amani? Don burinta ganin Amanin ta kuma tabbatar da ba abinda ya sameta. Ya cije leb ensa kawai tunda Umma T taga haka ta tabbatar ya yi tsiyar Ya aikata. Sai kawai ta sulale a wajen itama ta zauna cikin tashin hankali. Da muryar kuka take furta  Why Moddi? Me yasa zaka saka mana ciwon da zamu kasa warke wa, Amani fa, Amani y arka da ka haifa& . Iman ma kukan take kawai. Shi kuma Uban gayyar ya yi k asa da kansa kawai, shi  din ma ba wai yana cikin sukunin zuciya ba ne, and bai san ta inda zai musu bayani su fahimce shi ba. Didi dai wani irin nishi kawai take, hakan ya ankarar da shi Ya  dau waya ya kira Doctor. Amma kafin zuwa Doctor Didi ta ce lallai sai an fitar da ita daga gidan Moddi ta daina ganinsa. Bata son ganinsa ta tsane shi. Umma T ce ta dinga bata hak uri ta saka aka mayar da ita  d akinta amma still hankalinta baya jikinta, bata cikin nutsuwarta hakan yasa Umma T ta sake shiga tashin hankali bata son Didin ta yiwa Moddinta baki. Suna shiga d akin ta rufo k ofar ta saka Didi a jikinta tana sake kwantar mata da hankali.  Ki yi hak uri Didi, Moddi a yanzu addu ar ki yake buk ata, amma k addarar auren Safna ne ta cilla shi cikin wannan halin. Nan Umma T ta shiga bata labarin abubuwan da da ita Didi bata sani ba. Didi ta dinga kallonta da wani irin shock ta furta  Fateemah, me yasa kika b oye min hakan? Me yasa a sanda na ce Miki me yasa su Magajiya zasu bar gidan nan me yasa kika min k aryar akan Moddi yafi son matarsa ne da su shi yasa zasu tafi sun gaji, sanda kika bijiro min da maganar aurensu da kin gaya min hakan ai da ba wani ja zan amince, me yasa Fateemah yanzu kin ga illar shirunki ko? Kinga halin da kika jefa mu a ciki ko? Burin Safna ya cika Moddi ya kusanci y ar cikinsa, ya b ata mata rayuwa da wani ido zan kalli jama a idan Safna ta tona asirin nan&   Ba zata tona ba Didi, ni na San Safna ba zata tona ba, abu guda ne dole a mata abinda take so dole Moddi ya fasa auren da ya yi dole ya amince su rabu da matar, shine na San burinta, to za a cika mata burinta, in dai akai haka ina tabbatar miki ba zata furta zancen nan ga kowa ba, zata zauna matsayin matar Moddi ita ka dai as she wish& 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login