Showing 15001 words to 18000 words out of 94443 words

Chapter 6 - HADARIN GABAS HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

162

amma ta yi abin da tayi lokacin yarinta shi yasa nake cewa Moddi ya k yaleki kema zaki daina duk da har yanzu idan Dijatu ta tubure sai kowa ya ji a jikinsa& Sallamar Dahda ce ta katse musu hirar. Didi ta amsa a k asan mak oshi Amani kuwa ido ta zuba masa tana hango yarda ya gimtse fuskarsa kamar bai tab a dariya ba.  Tashi Magajiya ki samo masa bulala don a fuskarsa na hango so yake da ni da ke ya rufe mu da duka, idan banda haka meye na shigowa fuskarsa a turb une kamar dai an sanar da shi na mutu&  Moddi d an murmushi ya yi ya zauna a gefenta yana kama hannayenta ya furta  Allah ya rufa min asiri ba dake nake ha da rai ba, ni ba zan dakeki ba amma idan aka cigaba da tafiya a haka Magajiayr taki tana daf da fara dukan mu ni da matata&  Didi ta ware ido tana furta  Allahumma ajirni! Mugun fatan da kake mata kenan, to ba zan ga wannan ba, d a dai kiwonsa Allah yake bawa Bawa, idan ka k i kula da shi Allah kai zai kama, kuma gida ba zata bar shi ba tunda gidan Ubanta ne ba na Uban buzuwa ba, don haka ka d auketa ku tafi a yi ta mata addu a kurwar Yayarka Dijatu ne a tare da ita&  Moddi ya wara ido jin abinda ta ce ya furta  Wallahi Didi ki bar maganar nan anan Kada Adda Dija ta ji ki&   Ba zan bari ba Dijan Uwata ce? Ai ba k arya na fa da ba, ba ta inda ta baro kaf halayenta, sawunka a likkafa ka d auketa ka bar min gida& idan ta gagareka ka kaiwa Dija ita nima ba zan iya ciwon kai ba..
Amani ta zuba mata ido tana turo baki ta furta  Ni nake saki ciwon kai kenan? Kuma wallahi sai na gayawa Umma Dee abinda kika ce mata. Didi ta sake ha de fuska duk da a ranta ta ji d an fargabar a gayawa Dijatun abinda ta ce sai dai bata nuna ba, ta furta  Ki gaya mata d in tsoronta nake? Uwata ce
Ko Ubana ko kuma ita d in ta maye gurbin Uban Moddibo ne?
Shi dai Dahda a k asan ransa yake murumushi a bayyane kuwa harara ya zubawa Amanin yana cije leb ensa. Amanin ta d an turo baki tana kallon Didi ta furta  Allah ya kai mu asabar zaki amsa da bakin ki&  (Asabar itace ranar da duk ahalin Didin suke bayyana a gidanta da yaransu da jikokinsu. Sak Jikin Didin ta yi kafin ta furta  Magajiya fitina dai barci take Allah kuma ya tsinewa mai tayar da ita& . Ta
D auke kai tana furta  Oho ashe ba kya son na gaya mata sai a bayan idonta ki yi ta zaginta
Kina ce mata mai bak in hali amma a gaban idonta ba abinda kike iya yi sai abinda ta zartar kamar dai Umma Dee d in Uwarki ce? Dahda ya waro ido kafin ya furta  Amani zagin Didin zaki yi?  Ah to yau Kai ka fara jin ta zageni, ai ba sabon abu bane wajen Magajiya kai kanka Ubanta ma idan ba ka nan ce maka take Mallakak& . Wata irin sufa Amani ta yi ta dira a gabanta tana toshe mata baki  Allah ki ka gaya masa sai na fa dawa Umma Dee maganar rannan da kika gaya min&  Tsaf Dada ta shanye zancen. Dada dai lumshe idonsa ya yi kafin ya
Mik e yana wurga mata harara don yana da wajen zuwa da yamma ba zai iya da Didi da Magajiyatta ba  To Didi bari mu wuce..  Allah ya yi maka albarka, Yauwa Moddi ya maganar mu ta kwanaki ne? Baka samu matar auren ba ne har yanzu? Ko sai na tara maka y an uwanka, wace irin masifa ce ta sameka ace kana zaune da mace ba haihuwa ta hanaka aure balle ka samu magaji, ka san dai y ay a mata ba naka bane gidan wasu zasu ko? Moddi ya koma ya zauna ya rik e kansa kafin ya d ago yana kallon Didi ya furta  please Didi ki bar maganar nan, kin san dai sau uku ina neman aure bai yiwu ba to ba mamaki k addara ta ce a haka? Ba wata k addararka a haka, ni na samo maka mata yarinyar arziki shekaranjiya suka zo da Kakarta k awata Bintalo, ina ganin yarinyar na ji na maka sha awarta don haka in dai ba so kake na ha daka da Dijatu ba ka yi azamar zuwa ku daidaita da yarinyar nan&  Yarinya kuma Didi ni zan auri yarinya k arama ina da wa dannan y an matan a gabana na auro sa arsu ai abin kunya ne.. Didi ta saki baki tana kallonsa kafin ta ce  Mhmn! To sannu Moddibo ina fatan ba kai ka yankewa k asa cibiya ba? Ce maka na yi sa arsu ce? To nauyin aure ta yi don na san a k alla zata yi shekaru ashirin da shidda idan ma bata fi ba, a haihuwar tumaki ai ta haifi yaran naka. Dahda dai ya yi shiru ba don yana jin zai iya ba. Ya mik e yana furta  Ke wuce mu tafi, kina zaune idanunki k uri a bakunan mutane suna magana. Ta mik e tana k unshe dariyarta don ta san yau Didi ta kunno Dahda idan da abinda ya tsana bai wuce a masa zancen aure ba. Ta bi bayansa bayan ta yiwa Didi sallama ta d auke mata wani kwalin Biscuit da Didin take ji da shi don tana cinsa sosai  Zo ki bani abu na
Ja ira Mamuda ne ya kawo min.. Ta tsaya cak da biscuit d in a hannunta jin abinda Didin tace don bata son Mahmoud shine kuma ya mak ale har da zuwa kawowa Didi Biscuit Mahmoud d an Umma Dee ne Yayar Dahda ta farko. Mayar da biscuit d in tayi ta ajiye a gefen Didi  Ga abinki nan&  Didi ta saki baki tana kallonta  saboda nace mak iyinki ne ya kawo? Ai kuwa ko kin k i Allah sai kin auri Mamuda&  Bata wa Didin magana ba ta fice da sauri ta bi bayan Dahda da yake ta zabga mata horn&



Ta bu de front seat ta shiga Dahda ya d an kalleta ganin yarda fuskarta ta nuna b acin ranta. Ya cigaba da tuk insa
Hankalinsa a kwance kafin wayarsa ta yi ringing. Ya d aga kiran bayan ya saka wayar a bluetooth ta yarda yake Jin maganar mai wayar a cikin radion motar.  Mun kawo paint D in yallab ai, masu kitchen ma duk sun gama na part ukun ko zaka shigo ka gani? Moddibo ya d an Saci kallon Amani da take ta murmushi Jin abinda aka ce a cikin wayar. Ya furta  Okay zan shigo, ka bani 30minutes zan yi dropping yarinyata, are you sure sun gama da kitchen D in?  Definitely sure. Aka ce a cikin wayar. Sai ya kashe wayar yana juyawa don cigaba da driving Amani ta furta  DADA sabon gida kake ginawa? Are we going to live our House? Ya d auke Kai yana ha de girar sama da k asa ya furta  Bana son surutu, me yasa ko me ake kunnenki na kai? Ta d an turo bakinta idanunta na kawo ruwa, wani sabon yanayi yana bak untar ta kamar yarda ta Saba sometimes idan suna tare da Dadan. Ta d an runtse idonta har hawaye na son zubo mata. Moddi ya d an zuba mata ido. Ya saki murmushi kawai yana furta  Barbie, open your eyes. Ta turo bakinta tana bu de idonta da suka fara canja launi.  Why are you crying? Ta yi saurin d auke kanta rasa me zata ce masa ta yi. Da kunya ta ce masa ina kuka ne because na rasa yarda zan yi da sha awarka. Sai ta kawar da zancen ta hanyar cewa  Am crying, Saboda ka k i kai ni sabon gida. Kallonta Ya yi kawai ya saki murmushi sai taga Ya juya kan motar sun nufi wata ha daddiyar unguwa da ake kira Rail way a kano. Suna shiga babban gate D in gidan Amani ta ware ido ganin kyau da tsarin gidan a cikin motar ta buga tsalle tana furta  Wow! Dada wannan gidan fa? Bai amsa mata ba ya fita kawai yana murmushi. Hakan yasa ta bi bayansa da sauri tana furta  It looks great Dada. Allah yasa namu ne. Har cikin gidan suka shiga tana k auyanci ganin yarda gidan yake d auke da duk abubuwan da take so. Swimming pool. Ga garden ga komai ma da yake cikin mafarkin Amani. Irin gidan da ta sha zanawa a takarda tana gayawa Imani duk wanda zata aura zata gaya masa irin gidan take so. Bata San ta isa wajen Dada ba har ta kama hannunsa wani irin farin ciki ne Ya saka fuskarta Blushing take tama kasa rufe bakin. A haka suka shiga cikin gidan hannunta rik e da na Dada. Suka gama zagaye gidan da yake part Uku Har Da part D in Didi. A d ayan part D in ne ta kalleshi tana murmushi ta furta  Dada Are you going to get married? Dada ya waro ido yana kallonta kafin ya ja bakinta Ya furta  To whom? Sai ta yi dariya tana shigewa gaba. Zuciyarta na wani irin bugu. Inama dai Mafarkinta Ya tabbata& .. sai dai ta San Har abada shirme ne kawai irin na zuciya. Ta Yaya Y a zata auri Ubanta? Ta fita daga gidan haka kawai ta ji k walla na son zubo mata.


Bai bita ba har sai da Ya gama sallamar masu aiki sannan ya nufi wajen motar. Yarda ta yi zurfi cikin tunani ya tsaya yana kallonta kafin ya yi tapping hannunsa a fuskarta ta saki ajiyar zuciya tana dawowa cikin hayyacinta daga can wata duniya da ta fa da. Ido ya tsura mata yana noticing yanayinta. Sai dai ya yi shiru Ya tada motar ya juya a hankali yana furta  Bana son surutu, bana son ki gayawa kowa ina gina gida,I have a planned& . Ta turo bakinta a hankali tana furta  But why? Bai mata magana ba ya cigaba da driving d insa.


 Dahda don Allah ka aureta&  Da sauri ya juyo yana kallonta kafin cikin mamaki ya furta  Ita wa d in? Tana murmushi ta furta  Wacce Didin ta ce&   So duk abinda ake fa da kina ji ko? To wallahi idan kika fa da Safna ta ji sai na zaneki. Ta d an turo bakinta don ta tsani Mommy sosai bata sake magana ba har suka isa gidan ya sake juyawa yana kallonta ya furta  Kin dai ji me nace ko? Ta d aga kai  Kada ma ki ji, ki yi creating wani scene d in kiga abinda zan miki fita min a mota& . Ya fa da yana parking daidai parking space na cikin gidansa. ta fice da sauri ba tare da ta d au akwatinta ba& a hankali take kallon y ar k aramar harabar gidansu tana mamakin arzikin Dadan da za a iya kira na DARE DAYA& . Amma sana ar me yake yi da ta bashi ku di lokaci guda haka? Shine tambayar da ta kanainaye zuciyarta& haka ta shige gida da burin dole zata tambayi Dadan.


Tana shiga ta tarar da
Mommy zaune a parlorun ita da k awayenta, ta ji shigowar Amani da sauri ta d aga kai tana kallonta ta furta  Kan Uba! Uban waye ya dawo da ke cikin gidan nan? Amani ta mata wani kallo kamar ta ce  Ubanki ne sai dai ta gintse ta ce  Ubana, mai gidan shi ya dawo da ni, akwai wani abu ne? Shiru suka yi k awayen Safnan wasu hamshak an mata suka bu de baki suna bin bayan Amanin da kallo.  Cab amma lallai k awa kin yi sakaci, ji fa idanun yarinyar nan ba kunya take furta mana abinda ta so& . Safna ta yi k wafa  Ki bar Ibilishiya amma ba da ita zan yi ba, da shi da ya dawo da ita gidan zan yi& kafin na
Koma kanta, lokaci guda nake jira da zan yi ruining rayuwarta, sai ta gwammace bata zo duniya ba, ku jira ku ga.. Amani da ta ji komai ta dawo ta tsaya daga gefe ta bi su da kallon d aya bayan d aya. Kafin ta saki dariya ta furta  Before you ruin my life ki jira kwana ka dan za ki bar gidan nan, don Dada ya kusan yin aure muguwa kawai& &

A firgice suka bita da ido, ita kuwa ta shige bedroom zuciyarta fara k al. Ko bakomai ta kuntata mata kamar yarda itama ta mata.




Masifa k awayen nata suka shiga yi, suna furta Cab amma Safna kin yi sake, ai kuwa in dai kika bari aka miki kishiya ki tabbatar barin cikin group d in mu ya zama dole gareki. Kin san taken mu& BA MU BA KISHIYA& .



Shigowar Dahda ce yasa suka yi shiru da zancen illa Mommy da ta zuba masa ido tana masa kallon tuhuma. Tsare girarsa ya yi sosai yana amsa gaisuwar da k awar Mommyn take masa kafin ya shige part d insa don duk zancen da suke a cikin kunnuwansa, baya son raini amma ya lura Safnan kwana biyu nema take ta raina shi. Yana jin knocking d in k ofarta ya mata banza har ta gaji ta koma d akinta ranta yana sake fisga da halin ko in kulan da yake mata&



A bakin gado ta zauna tana kallon Imani da take kallonta duk da fuskarta ta kasa b oye murnar ganin y ar uwarta da ta yi hakan bai sa ta k i yi yin kicin-kicin da fuska ba ta k i kallon Amanin. Amanin murmushi ta saki tana zama daf da ita ha de da rungumota a jikinta  Kada dai kice fushi kike da ni Adda na. Ta kirata da sunan data son Imanin tafi so, don tana mugun son ta bata girma kamar ba tare aka haifesu ba&  Ba dole na yi fushi ba Amani, gaba d aya ni ban san wace irin zuciya ce da ke ba? Rashin kunya fa Amani? Yau rashin kunyar taki har ta kai kan Mahaifin da ya haife mu? Amanin turo bakinta ta yi ka dan kafin ta furta  Shi ya jama kansa, komai matar nan zata yi Dada baya gani wallahi wata rana idan bata yi wasa ba sai na mata tabo a fuska tabon Da Dadan zai ji ya tsani ko ganinta& . Imani ta saki baki tana kallonta kawai bata san sanda hawaye ya fara wanke fuskarta ba, Jikin Amani ya yi sanyi ta d an ware ido tana kallonta tana furta  To me nayi kuma? Ce miki aka yi yanzun zan mata illa? Bata fasa hawayen ba kamar yarda tsoron da take ji bai fasa bayyana akan idanunta ba&  Ba zaki daina irin wannan kalamin ba? Kina tunanin da Mami tana nan zata ji da din abinda kike yi? Ya zama dole ki amince da Mahmoud ki yi aure Wallahi ko wasu halayen naki zaki canja su shima Dada ya huta da saka shi magana da kike. Amani bata mata magana ba ta koma gadon ta kwanta idanunta a lumshe wani irin barci take ji sosai don da daddare ba barcin take samun yi sosai ba idan ba irin wannan lokacin ba saboda tsabar b acin rai ko abinci bata nema ba tun wanda ta tsakura da safe. Imani ta bita da addu ar shirya a ranta kafin ta mayar da kai itama ta kwanta idanunta akan hoton mahaifiyarsu da ta zuba mata ido kamar ta san a cikin kewar rashinta take wani abin da tana raye ta tabbata Amanin ba zata yi shi ba.




Sai Yamma can Dada ya fito daga d akinsa jikinsa sai baza k amshin turare yake. Idanunsa suka fa da kan na Mommy da take zaune ta fece wanka sai zabga k amshin turare take. Murmushi ta sakar masa tana furta  Sannu da fitowa Moddi Allah yasa dai ka bar fushin da kake yi a cikin d aki. Ya d an saki ajiyar zuciya yana zama a can gefe kansa ne yake d an sara masa. Mommy ta taso gefensa ta zauna tana saka jikinta ka dan a nasa ta shafa k irjinsa ta furta  Moddi ka yi hak uri please In sha Allah ba zaka sake samun b acin rai ta dalilina akan Amani zan rik eta kamar y ar cikina& . Ajiyar zuciya ya saki yana jin kaso casa in na cikin b acin ransa yana tafiya ya shafa kanta a hankali ya furta  Promise.. Ta saka hannunta cikin nasa a kunnensa ta ra da masa  Yes promised! Ya lumshe idonsa yana kai mata peck a lab banta  Allah ya baki iko&   Ameen ta furta tana ji a ranta wannan abinda ta yanke a zuciyarta shine abinda ya dace tuntuni&

Mommy mayaudariyar mace ce data san salo salo da take bi wajen mallakar Moddi, shi kuma a rayuwarsa baya son hayaniya don haka sam baya son maganar k ara aure, ya lura kuma shine abinda y

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login