Showing 21001 words to 24000 words out of 94443 words

Chapter 8 - HADARIN GABAS HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

165

bari na gaya masa halin da kike ciki ba?  Saboda abin kunya ne a gareni a ce ina son mahaifina so irin na aure& . Ta furta tana zuk ar tea d in da lumshe ido.  Ki tashi ki shiga wanka mu je kiga doctor.. Ta mik e ba don tana son Ganin Doctorn ba sai don a rayuwarta ba abinda yake faranta mata irin su fita da Dada a mota guda tana shak ar k amshin turarensa. Wani irin moment ne da baya gogewa a k wak walwarta.


Tsaf ta shirya cikin wasu shegun Riga da siket masu colour d in baby pink da touch?s d in maroum a jiki, hakan yasa ta yana mayafinta maroum ta yi kyau sosai kamar ka saceta har Imani ta dinga kallonta da mamaki ta furta  We are going to hospital fa Malama, ba gidan biki ba.. murmushi ta saki tana watsa hannunta ta ce  Me kika ga na yi? Bata sake mata magana ba ta cigaba da shirin ta tana gamawa ta saka dogon hijabinta har k asa ta mik awa Amanin nata. Amani ta waro ido a ranta tana furta Tab di Allah ba zan saka Hijab ba& A fili kuwa amsa ta yi ta ajiye tana furta  Attak wa Hahuna Ustaza& ba sai ka saka Hijab bane zaka amsa sunan mai tsoron Allah&  Daga haka ta ja y ar ficilar jakarta da ta cilla wayarta a ciki ta fice parlour cikin annashuwa da tarin farin ciki. Iman ta bita da kallo sai kuma ta fita ta bi bayanta tana d an tab e baki a fili ta furta  Rabbi Yahdiki ya Ukhteey& 


Amani na zuwa parlorn ta tarar da Dada a zaune da cup d in coffee a hannunsa sai zuba k amshi tea d in yake yana turiri amma a haka yake zuk arsa ko zafinsa ba ya ji idanunsa akan laptop yana pressing da tattausan hannunsa cikin nutsuwa. Zama ta yi a kujerar da take kallon tasa ya d an d ago yana kallonta kafin ya cigaba da abinda yake idanunsa akan laptop d in ya furta  Good Morning Amani? Kunya ce ta kamata tunawa da ta yi bata gaisheshi ba yau gaba d aya. Ta fara fidgeting yatsunta tana furta  Am sorry Dahda ina kwana&  Bai amsa ba ya cigaba da abinda yake kafin Imani ta shigo a gefensa ta durk usa tana furta  Dahda ina kwana? Ya d ago yana kallonta cike da murmushi ya furta  Good girl, lafiya lau. Idanunsa akan Amani da ta cigaba da fidgeting yatsunta tana murmushi k asa-k asa. Girgiza kansa kawai ya yi yana ajiye tea cup d in ya mik e bayan ya d au mukullin motarsa ya kallesu yana furta  Let s go.. duk da naga kamar ma ta ji sauk i& . Amani ta d an langwab ar da kai ya girgiza kai kawai yana d an murmushi ya furta  Stubborn child ke kuma son zuwa asibitin kike? Ba kuka kuwa idan yace allura zai miki agree? Ta girgiza kai don ta san bata da wannan juriyar.


Daidai lokacin Mommy ta fito tana kallonsu cikin mamaki ta furta  Sai ina kuma Moddi?  Hospital ya furta kansa tsaye yana d an gimtse fuska don ya tsani halayyar ta ta rashin tashi da wuri sai dai ta barwa yara aiki tana kwance ita hakima shi yasa ga shi nan tana ta k iba banda yana da babban dalili na rashin ha da mata biyu da tuni an wuce wajen to ya san bai isa ba a yanzu dai kam idan ba so yake komai ya dawo baya ba&  Asibiti? Waye ba lafiya?  Ama&  ya furta kai tsaye don sau tari haka yake gajarce sunan mutane, Mommy ta ware idonta tana kallon yarinyar da aka ce ba lafiyar bata ga komai a tare da ita ba banda ma wani shegen kyau da ta k ara.. sai dai ta san bata isa ta furta komai ba a yanayin da Moddibo yake na tsareta da ido yaga action d inta. Ta d an tab e baki tana furta  Allah ya bata lafiya, amma kuma idan Imani zata bi ku waye zai zauna ya taya ni preparing breakfast? Abin ma haushi ya ba shi wato ita in dai ba yaran nan ba zata iya komai na gidan ba, banda baya son tashin hankali da tafiya zai yi da su duka to sam baya son mita don haka ya kalli Imani ya furta  Ki zauna ki tayata ke&  Imani data ji wani irin bugu da zuciyarta ta yi da k arfi na tsoron fitar Dahda da Amani ita ka dai sai da ta d an waro ido har Dadan ya kalleta ya furta  What? Ta girgiza kai tana furta  Nothing I should stay& .. sai kun dawo. Dada ya girgiza kai ya fita Amani ta bi bayansa cikin matuk ar farin ciki da ta rasa dalilinsa. Front seat ta shiga wata irin ni ima na fusgarta musamman jin k amshin Dadan da ya zauna ra dam a cikin motar har sai da ta lumshe idonta. Addu a ya d an yi a hankali ta hawa abin hawa sannan ya ja motar ya fita daga gate d in. Shiru cikin motar ba mai magana ita ta lula duniyar tunani shi kuma yana bin sautul k ur an a hankali cikin suratul bak ara. Har suka isa asibitin idanunta a lumshe suke kamar mai barci sai dai kawai kallon Dadan take ta cikin lumsassun idanunta tana mamakin yarda Dadan yake da masifar kyau da kyan jiki kamar shi ya halicci kansa, bata ga aibun Mommy ba da take matuk ar kishinsa& tana ji ya yi parking sai dai bata motsa ba so take sai ya yi mata magana ta ji husky voice d insa kusa da ita. Ai kuwa ta samu abinda take so don sai da ya juyo ya kafeta da ido kafin ya saki ajiyar zuciya ya furta  Mun zo&  Ta motsa ka dan tana bu de idonta da suka yi wani kalar juyewa da k yar ta d aga lab b anta ta furta  Okay& . Dadan ya fara fita kafin tabi bayansa tana jan Hasbunallah a ranta don lamarin nema yake yafi k arfinta.


Cikin takun girma kamar wani sarki yake tafiya tana bayansa duk inda yabi idanun mutane a kansa musamman idan aka juyo masifaffen k amshin turarensa, mata da dama har sake juyawa suke su kallesu, Amani kuwa duk wacce ta ha da ido da ita sai ta zabga mata harara. Suna zuwa daf da wata budurwa da ta kasa d auke ido a kansa Amani ta furta  Auzu bikalimatil lahi tammmat maye ya ci kansa&  Murmushi budurwar ta yi ta furta  Ai fa sai kin yi hak uri y an mata tunda kika auri kyakykyawa kuma ingarmar namiji Ai dole a kalleshi& . Amani ta waro ido tana watsa mata wani kallo  Uban wa yace miki Mijina ne? To mahaifina ne& . Ji ta yi kawai Dada ya cafki hannunta ya runtse cikin nasa tattausan hannun don ya san yanzu ta tara masa jama a. Zata sake magana ya furta  Shshhhhh bana son magana&  Bai saketa ba sai da suka isa ga office d in likitan sannan ya zame hannunsa ya kuma tsare gira sosai ya zauna kafin ya dubeta ya furta  Zauna&  Zaman ta yi fuskarta a cukurku de don wani irin haushin mutanen da suka kalli Dadan take& Likitan ya bi su da kallo bayan ya gaishe da Dahdan ya furta  Me ya samu Ama Ta sanya Dada fitar sassafe? Ajiyar zuciya ta saki ta furta  Zuciyata ce take bugu da k arfin gaske ban san me yasa ba? Ido Doctorn ya zuba mata kafin ya furta  What time take miki haka? Ko any time haka kike jin ta? D agowa ta yi tana kallon Dada ta rasa amsar da zata bawa likitan da shima ya kafeta da ido yana nazarinta  Ki gaya masa mana, kike kallo na& .  Idan na ga Dahdah ko na ji muryarsa ko naji k amshin turarensa a mafarki ko a zahiri& 



5إ?5ؾ?5???5ض?5??? 5ة?5ض?5???5ؽ?/!& .
'?HADARIN GABAS& & =?L?


NAZEEFAH SABO NASHE.&
'?




5ة?5ض?5???/!/!5ػ?5ض?5ؽ? 5ة?5ض?5???5ؽ?/!&
'?


08033748387.

&&&&& 9??






&&&&


Abinda ya kamata ta fa da kenan, sai dai ita da kanta ta san fa dar hakan ba zai yiwu a wajen ta ba. Da kunya da kunya matuk a da gaske ta furta hakan kai tsaye. Dahda kuwa bai bar kallonta ba balle likitan da ya kasa cire k wayar idanunsa a kanta.

 Allah ya baki lafiya, amma dai ko meye a ranki ya kamata ki ciresa don ingancin lafiyar ki. Likitan ya fa da yana sake gwada b.p d inta. Magunguna ya rubuta mata da description d insu kafin ya mayar da kallonsa kan Dahda da sam hankalinsa ba ya kan su yana ta danna waya. Mik a masa takardun da yake ne yasa Dahdan d agowa a fusge yana kallonsa yasa hannu ya amshi takardar. Murya a k asa ya furta  Thanks Doctor&  Likitan ya d aga kai yana furta  A Kula da shan magungunan don Allah In sha Allah every thing will be alright&  Dahda ya sake d aga kansa yana d an sakin murmushi ya furta  In sha Allah Sannan ya yi gaba Amani ta bi bayansa tana taku cikin sanyin jiki.


Massenger ya mik awa takardar maganin kasancewar suna da file a asibitin ba buk atar ya basa ku di. Bai tsaya a wajen ba ya nufi hanyar waje yana d an tsaki ganin yarda idanun mutanen wajen suke zube a kansu. Amani kuwa zaginsu take a ranta tana mamakin dalilin wannan Uban kallo.



Madadin su nufi gida sai ta gan su a k ofar gidan Umma tee, don idonta a rufe yake bata san inda suke zuwa ba sai da ta bu de ido. Ta d an juyo tana kallon Dahda bata yi mamaki ba don ta san a kaf Yayyensa gidan Umma Tee kawai yake zuwa itace tasu tafi zuwa d aya yana son Umma Tee kuma kowa ya shaida a kaf zur iar Hajja D.

Bai mata magana ba ya fita daga motar hakan yasa itama ta fita ta bi bayansa tana jin d an farin ciki a ranta don ita kanta tana sonUmma tee don macece simple da bata d au rayuwa da zafi ba sab anin sauran y an uwanta.



Filin gida ne babban gaske da yake k unshe da wasu irin bishiyu da suka sake k awata filin wajen. Daga gefe can garden ne da carport mai kyan gaske. Daga shigarka gidan Umma teey zaka san suna da rufin asiri koda baka saka su a layin masu ku di can can ba. Za kuma ka shaida tsafta ta zauna gwargwadon iko a gidan.

Masu hidimar guda biyu suka dinga zubewa gaban dahda suna kai gaisuwa, don sun tabbatar da ganin Moddibo a gidan alheri ne, don kyauta yake musu kamar baya so.

Yanzun ma hannu ya saka a aljihu ya ciro ku din da bai san ko nawa bane ya dunk ule hannunsa ya tura musu a nasu hannun. Sannan ya shige yana amsa addu ar da suke masa a zuciyarsa don shi kansa ya san a wannan yanayin da yake ciki na sark ak iyar addu ar ce abinda ya fi buk ata.

Yana cikin wani hali da shi ka dai ya sani sai kuma Uban gidansa da ya zama musabbabin komai. Fatansa Allah ya d ora shi akan Uban gidansa da buk atarsa da ya bijiro masa wanda baya jin ko sama da k asa zata ha de zai aiwatar da muradin Muhammad Alwan& .



A tsaye Umma tee take tana zuba turaren wuta a burner da take hannunta ta tsinkayi sallamarsa. Cak ta tsaya tana amsa sallamar fuskarta a washe don rabonta da Moddibon ya tako gidanta tsawon wata uku kenan..  Muryar wa nake ji kamar ta Kiddo, Moddin Didi. Ya d an watso mata kallo yana mata nuni da Amani.  Wannan sunan ba zai bar bakin ki ba at my 40 ages kike kira na Kiddo s. Harararsa ta yi tana k arasawa inda yake ta furta  Har yanzu kallon da nake maka kenan Moddi, baka wuce Kiddo ba a wajena ya gida yau an tuna da mu kenan? Sosa kai ya yi yana zama ya saki ajiyar zuciya yana furta  Dama ban manta da Tee ba kina zuciyata kawai komai ne ya caku de min&   Zancen kenan, kulllum da an yi magana kace wani kana busy ban tab a ganin ma aikacin gwamnati da zama busy irinka ba, kamar wani mai company& .. Ya d an ji bugun zuciya ka dan ya same shi ya runtse ido don an zo wajen da yake fa dar masa da gaba wajen da zai zo ya tari y an uwansa ya sanar da su tarin arzikin da yake da shi. Abinda yake ba shi tsoro amsar da zai basu a duk sanda suka bijiro masa da tambayar a ina ya samu ku din? Shi yasa har yanzu ya kasa gaya masa waye MODDIBO A BADINI, don ya tabbata ZAHRIN MODDIBO kawai suka sani& . Bai farka daga tunanin da yake ba sai da ya ji muryar Fateeman a sama tana furta  Ama ki shiga Haulat na ciki. Sannan ya dawo da hankalinsa kanta. Ya tarar ta kafa masa idanunta da ya san duk sanda ta masa wannan kallon kamar tana karantar har cikin zuciyarsa ne&  Kiddo me kake b oyewa a cikin zuciyarka wanda baka so mu sani? Ta fa da tana nutsa manyan magananta cikin nasa idanun da ya lumshe su ba shiri, yana kuma matse hannunsa da d an k arfi. Tsoro ne ya kamata bata san sanda hankalinta a tashe ta mik e ta isa inda yake zaune ba, sai ji ya yi ta kama tattausan hannunsa a cikin nata yarda take masa kenan yana yaro idan tana son taji damuwarsa.  Bu de idonka ka kalleni Moddi&  Kasa musu ya mata sai da ya ware idonsa tarrr a kanta yana sakin huci ka dan tare da taune leb ensa wata zufa ka dan tana zubo masa. Fateema ta lumshe ido tana furta  Oya tell me exactly what is happening? Kada kace min bakomai don na san tabbas there is& . Ya girgiza kai yana furta  Ba wani matsala ba ne fa Tee, amma dai ku taya ni da addu a akwai business da na shiga na samu ku di sosai kuma a business d in sai dai a k arshe inaga kamar business d in zai zame min mara amfani& .  Ya sake sakin ajiyar zuciya  Mu ajiye wannan a side, don na san ba lallai ki fahimceni ba, ba mamaki ki fassara ni da abubuwa da dama a zuciyarki. Yanzu abinda nake so ki min ki yi duk yarda zaki yi Hajja Dee ta dawo gidan da na gina nake so na tare da ita a railway& . Fateema ta waro ido ta furta  Kai ka ka san ba ni da wannan damar, amma ni ba wannan bane a gaba na wani business ka je ka jefa kanka? Alhali ni dai na san kai government worker ne ajiye aikin gwamnatin ka yi a ina ka samu ku din da har ka Gina gida a railway? Unguwar da na ji ana fa dar sai Wanda ya ci ya tada kai. Ya d aga kai  Na da de da barin aikin gwamnati na fa da business ban gaya muku ba ne don na san zaku iya hanawa yanzu haka ina da company a Abuja ina da shi a kano zan bu de next week a kuma ranar nake so na tare a sabon gida na, Ending month kuma zan yi lunching sabon jirgina da zai fara jigilar passengers zuwa k asashen waje da suka danganci& & &  sai sannan ya lura da shock d in da Umma tee ta shiga, ta dinga kallonsa baki sake idanunta ko motsi basa yi. Har sai da ya yi clapping hannunsa a fuskarta sannan ta saki wani gwauran numfashi tana nuna shi da yatsa ta mik e tsaye tana ja da baya. Firgicin da Moddibo ya shiga yafi nata da sauri ya mik e ya bi bayanta sai dai ko kafin ya cimmata ta shige d akin da yake bayanta da sauri ta rufo da key. Don tabbas tana buk atar nazari. Moddi ya tsaya a bakin k ofar yana buga mata k ofa da rok on ta bu de amma ta masa shiru a cikin d akin sai furzar da huci take Me Moddi ya d auke su mak iyansa ko me? Da wannan gagarumin cigaba zai same shi amma ya kasa bu dar baki ya gayawa ko mahaifiyarsa, Saboda matarsa ya d auka mutum, matarsa tafi su mahimmanci& . Ba ma wannan ba wace Sana a yake da ta Samar masa ku di masu yawa haka? Shine abinda ya fi razana ta.
Bugun da yake mata ne ya isheta don haka a zafafe ta ce  Imaaaam live me alone pls! Ka fice min a gida kafin na aikata maka komai, me zaka ce mana? Saboda ka auri matar da bata san mutuncin mu ba, matar da bata daraja mahaifiyarka shi yasa ka kasa gayawa Hajja abin alherin da ya sameka, ka tafi ka yi rayuwarka da matarka da y ay anka bana buk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login