Showing 36001 words to 39000 words out of 94443 words

Chapter 13 - HADARIN GABAS HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

179

ce  Kutma& . Sai kuma ta shanye zagin ta furta  Zan kai su Malam, don Allah ka fita ka tafi kada jirgin Ya cika. Murmushi kawai ya yi yana furta  Ta Yaya jirgi zai cika bayan kowa da wajen zamansa, ga ma Boarding pass an turo min. Hannunsa ta fincika suka fita waje. Sai da ta kai shi har Airport sannan ta juyo da motar bata wani koma gida ba ta isa wajen Malaminta ta sanar da shi. A d inke bakin Moddi duk abinda suka ce suna buk ata ya amsa kawai. Malamin kuwa ya d auko allon k arfensa ya shiga rubutu yana k onawa da wuta mai zafi. Ya d ago yana kallonta yana murmushi ya ce  An gama! Itama murmushin ta saki ta fice daga wajen zuciyarta fes tana ji a ranta kamar Moddi ya yi arziki ya gama.





&&

Babban Hotel aka masa masauki. Ya dinga bin ko ina da kallo a zuciyarsa yana furta arziki yana wajen masu shi. Tabbas su Alwan suna da arziki fiye da tunaninsa.Sai da suka ci abinci sannan Alwan ya ce  Ka san me yasa na kiraka? Imaam ya girgiza kai. Alwan ya saki murmushi yana furta  Kafin mu yarda da kai sai ka amince zaka shigo cikinmu akan shara din duk abinda muka saka ka za ka yi shi? Imam ya d an bu de ido yana so ya ce  Kamar me? sai dai bakinsa ya k i bashi ha din kai kawai sai ya samu kansa da furucin  Na amince.  Good For you. alwan ya fa da yana murmushi  Abu na farko da zamu buk ata daga wajenka shine mahaifar matarka, Ma ana ba zaku haihu da matarka ba. Imaam ya  dago yana kallonsa Ya ji kansa ya wani sar? masa, amma sam ya kasa masa musu& Alwan yana murmushi ya ce  Ka kirata ku yi shawara&  Ya fice ya bar masa wajen. Da sauri Imaam Ya kira Safna. Tana d agawa ta ce  Yaya? Imaam Allah yasa dai baka musu taurin kai ba? Ya saki huci ka dan ya furta  Ba zan iya abinda suke so ba& .  Zaka iya Imaam, ka yi koma me suke so? Yanzu fa ba abinda baa yi saboda ku di, ana ya Kai Kai, mutum yana kwanciyar da y ar cikinsa, da Uwar data haifeshi ma saboda ku di, ana luwa di da ma digo saboda ku di, ana bada Uwa ko y a Yaya ko k anwa, K ani ko wa? Duk saboda ku di, don haka ka yi ko me suke so Moddi Saboda ku di& bana son musu&  ta fa da tana zame kanta a duk sunayen da ta ambata, bata k i ya yi komai ba in dai zai samar musu da ku di, bata damu ta ji shara din da suka bashi ba. Imaam Ya saki ajiyar zuciya, sai ya ji ya samu k warin gwiwar bayar da mahaifarta tunda ita ta jawowa kanta ta ce ya yi komai saboda ku di. A zuciyarsa Ya dinga jin baya so, amma harshensa ya kasa amince masa ya furta baya so d in. Ya kalli Alwan da Ya shigo d akin idanunsa a kansa shima ya ce  Yaya Aboki? Ka yarda ko a a? Abu guda dana sani baka isa ka San sirrinmu sannan ka bijire mana ba& ..




JIKAR NASHE.=?O?HADARIN GABAS& ..=?L?

Page& 14.

NAZEEFAH SABO NASHE&
'?


08033748387.

(Book 1 free. Book 2&3 paid ne)


Ku saka ku dinku anan account d in don samun Shiga paid group. 500 =?L? (0000612945 TITAN TRUST BANK) mutanena Na Musamman cikin Gida Na Musamman 1k Dai Kacal as Usual. Jikar NASHE LOVES YOU ALL.)

_*=?%?BRIGHT PENS...=?%?*_
2nd batch
Zazzafar tafiya mai abin ban mamaki, tawayen jerin marubuta huWu a sabuwar tafiyar ta second batch.

*HADARIN GABAS*
Nazeefah Sabo Nashe

*?ARFE A WUTA*
Ayushercool

*ZAYTOON*
Zee kumurya

*MUTALLAB*
Nimcyluv Sarauta.



14.


 Na amince&  Shine abinda ya ce yana jin kansa yana wani irin sarawa. Alwan ya d ago yana murmushi kafin ya zare glass d in fuskarsa ya furta  Ka kyautawa kan ka, wannan ya zama sirri a tsakanin mu, Zan baka maganin da zaka mata amfani da shi a lemo komai zai tafi yarda muke fata successfully. Sannan Daga haka zaka samu duk abinda kake buk ata zamu ajiye ka a companyn da zaka dinga samun ku di ba k akkautawa kafin wata buk atar ta bijiro& Congratulations Mr. Imaam Moddibo and welcome to the Family&  sakin ajiyar zuciya ya yi yana furzar da huci ka dan gani yake kamar ya yi gaggawar amincewa da buk atar da suka zo maka da shi. Idanunsa a lumshe Alwan ya mik a masa ruwa mai sanyi. D an bu de lumsassun idanun nasa ya yi yana kallon Alwan d in da yake kallonsa fuskarsa cike da murmushi ya d aga masa kai  Sha&  Bai yi musu ba ya karb a ya saka a bakinsa ya shanye tas. Sai ya ji kamar an tafi da tsoron da yake zuciyarsa wata nutsuwa ta shige shi. Alwan ya mik a masa wani dogon file me d auke da takardu a ciki  Ka yi signing. Ka kuma cike form d in company. Hannunsa har rawa yake ya aikata abinda aka ce masa.


A ranar Alwan ya kai shi masauki sannan ya saka aka kawo masa abinci mai rai da motsi bai bar hotel  din ba sai da Imaam ya ji alert d in 50million a account d insa. Yana ware ido yake kallonsa da neman k arin bayani.  Na siyan kayan sawa, waya da duk abinda kake buk ata. Ai kana da y ay a ko? D aga kai kawai Imam ya yi don ba shi da karsashin amsawa.  To ka musu hidima ka ajiye musu duk abin buk ata zamu yi wata tafiya da kai zamu yi 2weeks don zan nuna maka yanayin business d in da zaka dinga mana. Zan sake jaddada maka bama son surutu, ka gane ko? Imaam ya d aga kansa yana kallon Alwan  din ya fice da sauri saboda kiran wayarsa da ake ta yi.

Sai sannan Imaam ya saki ajiyar zuciya yana rik e kansa da ya ji yana sara masa ka dan. A ransa yake jinjina girman wautar sa na amsar tayin kasuwancin da bai san menene ba? Ga bayar da mahaifar matarsa da ya yi. Anya bai yi kuskure ba duk da wata zuciyar na tunasar da shi Ku di Imam! Ku di zaka yi yaranka zasu huta Hajja su Huta da Yayyenka& matarka Kuma ai ita ta janyo koma me ya faru& wayarsa da take k ara ce ta dawo da shi cikin hankalinsa idanu ya kai kan wayar ganin numberr wife sai da ya ji gabansa ya fa di da ya tuna abinda ya aikata mata.. bari dai ya gaya mata idan ta yarda shikkenan idan kuma bata yarda ba kawai sai ya hak ura&

Yana saka wayar a kunnensa ta furta  Hope dai kun gama kuma ka amince da dukkan shara dansu? Shiru ya yi yana jan ajiyar numfashi  Moddi baka ji na ne? Ya furzar da iska ya furta  Ina jin ki.. sun zo min da abinda nake tunanin ba mai yiwuwa ba ne& .  Ba wani abu da ba mai yiwuwa bane Moddi a duniyar nan Moddi ka amince da komai suka ce maka. Duk duniyar haka ta riki de ta koma yanzu kowa ka gan shi ka k yaleshi kawai da guntun kashinsa a gindinsa& don haka in dai ni zan baka shawara kawai ka aikata abinda suke so yanzu ake yankan kai ma don a samu ku di& . Imam ya d an waro ido  Yankan kai fa?  Eeh yankan kai kai in gaya maka mai k ank at mutum yana sadaukar da Uwarsa ko y arsa ko y aruwa don ya yi ku di& . ta cire mata don koda wasa ba zata so Moddi ya bada ita a yi tsafi don ya samu ku di ba, amma bata k i ya bada Hajja ko Y ay ansa ko Yayyensa ba. Moddi ya ji wani abu ya daki k irjinsa ya ce  Haba dai? Allah ya kiyaye.  Ameen, ai ina gaya maka ne ka amince da duk me za su ce maka, har luwa di ake da mutum don ya samu ku di&  Wannan karan sai da Moddi y runtse idonsa ya ji gabansa yana wani irin bugawa. Ajiyar zuciya ya yi ya furta  Shikkenan, bari na kwanta. Ya latse wayar yana sakin murmushi sai ya ji zuciyarsa ta daina nauyin da take masa ya ji ya amince da sallama mahaifarta tunda ita ta jawowa kanta. Wato tana tunanin ya bada uwarsa da y ay ansa amma bata tunanin ya bada ko farcenta? Ya tab e bakinsa kawai yana kurb ar lemonsa mai sanyin gaske& .




Wannan shine mafarin samuwar arzikinsa don daga lokacin da suka yi tafiya ya je yaga yanayin business d in, shikkenan Alwan ya sakar masa jan ragamar companynsa na turkey da yake Abuja. Bai fiye zuwa Kano ba. Ya kuma kasa sanarwa da Didi sana ar da yake ya dai ce mata companynsu sun koma Abuja an kuma yi masa k arfin girma. Fatan alheri ta masa tana furta  Ka dai kula Moddi, ka saka Allah a gabanka ka kuma kula da amanar da Allah ya baka ta yaranka bana jin da din yanayin yarda yarannan suke rayuwa a gidanka.. D aga kai shi kansa sau tari baya son irin rayuwar da suke sai dai ba yarda zai yi ne, idan ya yi nufin tsawatarwa sai Safna ta janye hankalinsa. Sau tari Didin na zuwa ta kwana musu biyu don ita da kanta ta ce su dawo hannunta Umma Dee ce ta hana tana furta  idan suka dawo Didi Ai makirar matarsa sai ta yi murna ta ci galaba akan mu, gidan Ubansu ne dole su zauna wallahi. Hakan ne yake togace Didi daga janye yaran zuwa gidanta. Don kam bata ja da duk abinda Dijatu ta ce.

Ranar da ya gama gininsa da yake ciki a yanxu, kasa gayawa Didin ya yi sai Gidan Umma Tee ya ya sanar mata ga shi a lokacin ma Safna ta riga ta matsa masa sun tare cikin murna da zakwa di tana ji dai da fankamar mijinta ya zama mai ku di.

Umma Tee kallonsa ta dinga yi tana mamakin abinda ya ce mata.  Ka gama gida Moddi? Har kun tare a ciki ba tare da Hajja ta je ta gani ta saka albarka ba? A hankali ya sunyar da kansa yana jin kansa da jikinsa sun masa wani irin nauyi tabbas ya san bai kyauta ba, amma baya sanin rashin kyautatawar tasa sai ya aikata abin rashin kyautatawar sannan yake dawowa cikin hankalinsa.  Abin ne yazo bagatatan ki rufa min asiri don Allah kawai ki je ki gaya mata&  Tsam ta yi da ranta tana nazarin idanunsa  Wai Anya kuwa Kido baa canjawa Didi kai ba? Ta fa da wata k walla na shirin zubo mata. Idanunta sun ka da sun yi jawur. Shima sai ya samu kansa da zubar k wallar  Ni kai na Tee ban san me ya same ni ba? Wasu irin abubuwa nake aikatawa da ban san ya aka yi tunani na yake gocewa ba sai na aikata na ji ina da na sani& . Hawayen ta share ta ce  Shikkenan akwai Allah, yanzu ka tashi mu je gidan Didin ka gaya mata da kanka ka kuma bara hak urin rashin sanar da ita da baka yi da wuri ba. Zaka iya cewa gudun kada ta maka fa da ne. Ya d aga kai yana amincewa da shawarar da ta ba shi. Suka tafi gidan Didin. Tun a mota ita kanta Fateeman ta dinga mamakin zundumemiyar Motar Moddin mai kyan gaske.  Kiddo sun k ara maka matsayi a wajen aikin ne? Ta furta don ta kasa shiru. D an murmushi ya yi yana d aga kai ya furta  Eeh, sun k ara min mantawa na yi ban sanar da ku ba&  Ta saki ajiyar zuciya kawai tana furta  Anya Kido kana dagewa da Azkar kuwa? Ya d an saci kallonta a idanunsa ta ga rashin gaskiya don ya kasa kallonta sai d an cije leb en da ya zame masa jiki yake yi.  A kula dai da addini da Azkar ba don komai ba sai don duniyar yanzu gaba d ayanta abar tsoro ce. Ya d aga kai kawai daidai lokacin suka zo gidan Didin.


A kunyace Ya shiga gidan Didin tana zaune a tsakargida tana gyara zogale. Gidan yana nan yarda yake ba abinda ya canja masa duk da tarin arzikin da Allah ya ba shi. A Ransa ya ji rashin kyautatawar sa ko ka dan ga matar da ta sadaukar da dukkan farin cikinta saboda su. Amma shi ya samu arziki bai damu da ita ba yana dai ajiye mata abinci da abubuwan da suka danganci kayan masarufi. Ya ja ajiyar zuciya yana zama a saman kujera ha de da kai idonsa kan Didin da fuskarta ta kasa b oye farin cikin da take ciki. Yaushe Rabon da taga Moddibo idan bata manta ba wata guda da rabi kenan cur sai dai ya kirata a waya shima sai ya bushi iska. Kullum addu a take masa amma lamarin k ara ta azzara yake. Ba b acin rai bakomai ta tare shi. Ya durk ushe a gabanta yana dafa cinyarta. Shafa gashin kansa ta yi ta furta  Yau Moddin Diddy ya tuna da ita? Saukar da idonsa ya yi k asa hawaye na zuba a idon ya furta  Diddy ki yafe min& .  kada kace komai Moddi ban rik eka da komai ba kuma kullum addu a nake maka Allah ya shige maka gaba a dukkan lamarinka, ya tsareka da dukkan abin k i. Fateema sai da ta saka gefen mayafinta ya share k wallar tausayin Diddy da Moddin da aka raba ta k arfi da yaji. Diddy ta shafa kansa  Rok ona d aya Moddi ka kula da amanar da Allah ya baka ta marayun yaranka. Ya d aga kai murya a sark afe ya furta  In sha Allah&  wani rauni yake ji a jikinsa tun daga k afarsa har tsakiyar kwanyarsa don tabbas yaran nasa ma ba wani kula yake da su sai ya shafi sati biyu ma bai gansu ba. Makaranta dai ya ajiye musu driver yana kai su ya d aukosu sai abincinsu da yake bawa Mama Tala da kansa sai dai abin haushin yana tafiya Safna take k wacewa ta cigaba da basu duk abinda taga dama.

 Diddy Moddinki fa ya miki laifi. Fateemah ta fa da tana k ok arin kawar da yanayin da zuciyatta take ciki akan fuskarta. Ta k ak alo fara ar dole ta aza fuskar. Diddy ta kalleta da son k arin bayani. Fateemah ta yi murmushi  Ya tare a sabon gida bai gaya miki ba, don yana gudun fa da. Shiru Diddy ta yi duk da lamarin ya daki zuciyarta sai bata nuna ba ta saki d an murmushin da yanayinta kawai zaka kalla ka san bai kai zuciyarta ba.  Allah ya sanya alheri Allah ya saka da dukiyar halak ka samar da shi, shine kawai fata na. Imaam wani abu ya ji ya masa yarrr a jikinsa ya lumshe idonsa kawai yana furta  Ameen Diddy. Hawayen da ya rasa dalilin zubarsu suna masa suntiri a fuska Diddy ta saka hannu ta share masa kwallar  Kukan na menene Moddi? Girgiza kai kawai ya yi yana futta  Didi ya kamata a rushe gidan nan a sabunta gininsa. Ta girgiza kai  Sam! Ban amince ba nafi son a bar min shi haka kamar yarda Uban Moddibo ya bar shi. Futawar da kai ma Allah ya maka albarka lokaci ka dan fa ya rage min a duniyar. To na me Zan zauna na mik e k afa na saka jin da din duniya a zuciyata bar ni a haka zan fi tuna lahirata Moddibo. Ba abinda ya rage min sai fatan cikawa da Imani. Ina kuma rok onka ka ci daga halak ka sha daga halak sutura daga halak ka nesanta kanka da duk wata dukiya da bata halak ba. Allah ya yi maka albarka.

Ranar kam sun da de a gidan Didin. Ba yarda ba su yi da ita ba ta je gidan Moddin ta girgiza kai  Ba zani ba, sai nan gaba in sha Allah. K arshen sati dai a dinga kawo min su Magajiya don Allah. A ranta kuwa sam zuwa gidan Moddi ya fita daga ranta ba don komai ba sai don Matarsa da bata ganin k imarta da mutuncinta shi yasa taga gwara ta ja girmanta ba zata zama irin surikar zamani ba mai ja ni in ja da surikarta ba.



&&&


A kuma wannan lokacin ne Muhammad Alwan ya bijiro masa da buk atar da ta tayar da hankalinsa ta kuma saka masa firgici da tsoro. Don idonsa Muhammad Alwan Ya kalla bayan dawowarsu daga tafiya. Suna zaune a Office. Moddi farin ciki ya isheshi musamman ganin wasu irin makafin ku di da yake samu na ribarsa kawai. Ga company mai girman gaske Muhammad Alwan d in Ya gina da sunansu MODDIBO CONSTRUCTION COMPANY.. shi kansa Moddibon bai San ana ginin ba. Ruwan tea mai zafi Muhammad Alwan D in Ya zuba musu. Sai da Moddibon Ya shanye idanun Alwan D in a kansa yana ta sakin murmushi murnar fuskarsa ta k i d aukewa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login