Showing 72001 words to 75000 words out of 94443 words

Chapter 25 - HADARIN GABAS HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

170

min ba, Amani, me yasa? Me yasa kika b oye min? Amani ta runtse idonta tana fusgar leb enta ta furta  Nima ban sani ba sai yau, sai yau na San dukkan wannan halin da na shiga Dada ne sila, amfani yake da mutum mutumina yana having sex da ita, wallahi tana nan a d akin sirrin sa, irin d akin da ya hana mu shiga a gidansa, yau k addara tasa na shiga ashe Allah yaso Ya bayyana min gaskiya ne, yaso ya nuna min wanene Dahda&  ta runtse idonta kafin ta furta  Sai na gansu da ita, yana sex da ita, wallahi Iman kamar ni a zaune haka Toy D in take&  Imaan ta runtse ido kafin ta mik e a fusace ta yi hanyar waje tana fincikar hannun Amanin  Mu je, zo mu je mu gani. Wallahi idan haka ya tabbata da kaina zan tonawa Dada asiri, sai na gayawa Duniya waye shi? Amani bata ji wani shakka ba tabi bayanta. Suka fita zuwa parlorn. Sai dai ba alamar k ofar zata tab a bu duwa haka suka dinga buga k ofar Amma shiru. Jikinsu a sanyaye suka koma d akin su. Idonsa fal hawaye&



Juye-juye kawai yake a gadon. Yana jin yarda zuciyarsa take wani irin zafi& a hankali ya dinga Jin bugunsu ya tabbatar su ne, amma ba zai iya bu dewa ba. Yana jin kunya tabbas yana jin kunyar ya kalle su don ba zai iya yi musu bayani ba. To ya ce musu me? Ya runtse idonsa kawai kafin ya mik e hannayensa a aljihu ya fita daga bedroom D in. Tafiyar yake kamar Wanda ba damuwa a ransa da k arfinsa ya isa bedroom D in nasu. Ya ci sa a ya samu k ofar a bu de. Idonsu suka sauke a kansa suna masa kallon tuhuma, kallon da yake bayyana tarin tsanarsu gare shi. Hannayensa a aljihu ya isa wajensu. K ok ari yake sosai wajen son sarrafa zuciyarsa sai dai bashi da makamin da zai kare kansa. Don haka ya lumshe idonsa kawai. A karo na farko a gaban yaransa hawayensa ya d iga. Hawayen da yake bayyana ragwantakarsa a yau, duk da kasancewarsa jarimi mai k ok arin b oye damuwarsa Amma yau kam ya kasa, ya bayyana rauninsa a gaban yaransa. Jikinsu ya yi sanyi, zafinsa da suke ji ya fara narke wa zuwa tausayi, tausayin da basu San dalilinsa ba, basu San me yasa ba? Musamman Imani da ta dinga jin kamar taje ta rarrashe shi. Ya da de a haka yana hawayen suma suna nasu. Duk zafin da zuciyar Amani take yi sai ta neme shi ta rasa. Tsanarsa da take ji ta gudu, wata irin tarin k aunarsa ta sake ji a ranta soyayya mai zafin gaske da take jin zata iya aikata komai saboda taga ta kawar masa da damuwa. Ta dinga binsa da kallo tana lumshe idonta jin husky voice d insa yana furta  Am sorry Ama& . It wasn t my fault, zuciyata ce In sha Allah komai zai zama labari duk da na San Nine silar afkuwar halin da nake ciki, Soon zan maku bayani Amma kafin nan please keep this a secret& . Daga haka ya lumshe idonsa sai kuma ya fara tafiya da baya da baya. Amani ta dinga kallonsa tana jin kamar ta tashi ta rungumoshi ta lallashe shi. Tana kallo ya fice ya bar musu k amshin sa a cikin d akin. Sai kawai ta rungume pillow tana sake sakin kuka. A sannan take jin zuciyarta bata mata adalci ba& Imani bata lallasheta ba don itama kukan take kanta a saman bayan Amani ta furta  Sister, mu rufawa Dada asiri, a idonsa na hango ba laifinsa ba ne, da gaske yake ba laifinsa bane, ban san wace kalar k addara ba ce take bibiyar rayuwarku daga ke Har shi&  Bata mata magana ba, don ita abinda ya dameta ya dameta, bakomai ba ne sai wani irin k aunar Dahda soyayyarsa da k iyayyar sa da suka caku de mata a zuciya ta rasa a wani muhalli zata ajiye Dahda masoyi ko mak iyi, ko kuma Mahaifi? A daren ranar kam basu yi barci ba, sun tashi sun yi Sallah kowannensu Ya dinga gayawa Allah damuwarsa da son ya magance masa ita. Sai sannan suka ji sanyi, suka kuma samu sauk in abinda suke ji a zuciyarsu, bayan Asuba barci ya d auke su.



Shirun da Didi ta ji basu fito ba, yasa ta gaji da jira ta kalli Fateemah ta ce taje ta taso su. Time D in k arfe 10:00 na safe. Da k yar Amani ta bu de nauyayyen idanunta da suka kumbura fiye da na Imani, ta zube su a cikin na Umma Teey da take kallonsu cikin matuk ar fa duwar gaba. A kasalance ta ce  Me ya same ku? Me ye haka? Me ya faru? Lumshe ido Amani ta yi tana kokawa da hawayen da ya kasa tsayawa daga idonta. Hakan yasa fargabar Umma teey ta sake yawaita ta zauna gabanta na fa duwa sai dudduba jikinsu take.  Ku gaya min mana. Imani ce ta sauke ajiyar zuciya kafin ta kama hannun Umma Teey D in. Tana sakin ajiyar zuciya da k ok arin kawar da damuwarta ta furta  Bakomai fa, waccan matsalar ce dai ta Amani har yau bata daina ba. Umma Teey tausayin yaran ya sake kamata sai kawai ta jijjiga kai tana furta  Soon, zata daina In sha Allah, ina nan ina addu a, lamarin ne akwai sark ak iya. Ina so dai ku cigaba da rufawa mahaifinku asiri Har muga abinda hali zai yi, kun ji? D aga kansu suka yi. Suna furzar da huci kusan a tare. Umma T,ta ce ku tashi maza ku shirya Didi na can hankalinta yana nan, duk ta damu, kuma daga yau ina son ku koma sashenta da kwana gwara kuna kusa da ita, Ya fi wannan zaman naku anan da hankalina sam bai kwanta da shi ba. Basu musa mata ba, suka yarda da abinda ta ce, don kam zamansu anan su da kansu sun san bai kamace su ba.



****
A daidai lokacin Safna na tsaye gaban Ramin data aikata komai, cikin tashin hankali take bin Ramin da kallo tana cije yatsa.  Kan Uba! Ta furta tana kallon yarda aka tone komai. Tashin hankalinta yana hauhawa bata manta garga din bak in bokan ba,  Kada ki bari kowa ya san kin birne abin nan, idan har wani ya gani tabbas kina cikin matsala. Zufa ta dinga zubo mata, ganin ko alamar kayan sihiran nata,  Akwai Matsala Safna, duk wani sihirinki ya warware asirinki Ya kusa tonuwa! Ta dinga jin muryar bokan a kunnenta& jikinta na rawa ta zube a wajen. Zuwa ta yi dama a lokacin ta zuba rubutun da ya sanar mata idan safiya ta yi taje ta zuba a kai. Sai dai taga wannan tashin hankalin. An tone Ramin an kuma kwashe tarkacen Sihirin. Zafi zuciyarta take yi irin zafin da take jin da zata ga Wanda ya mata hakan, sai ta kashe shi Har lahira& Idonta ne ya sauka akan hular Amani da zobenta& da sauri ta saka hannu ta  dauke su cikin zafin nama kamar wacce ake wa Gangi ta juya a zafafe ta nufi cikin gidan. Kai tsaye d akinsu Amani ta nufa ta tura k ofar da dukkan k arfinta. Idonta ya sauka a kansu suna yafa mayafi da alama Sun shirya zasu fita daga d akin. Ta watsa musu kayan a gabansu tana furta  Na Uban waye a cikin ku? Imani da sauri ta kalli Amani don ta San nata ne, hularta ce ta jiya data kwanta barci da ita& ta waro ido ganin Amanin ta mik e cikin taku mai nuna isa da rashin kunya zalla ta isa gaban Safnan tana mata wani irin fisgaggen kallo, mai bayyana wulak ancinta zalla& a gabanta ta tsaya tana sakin wani murmushi ta nuna kanta tana furta  Na Amani Imaam Moddibo ne& . Safna ta k ank ance idonta cikin na Amani, tsanar yarinyar na sake girmama cikin zuciyatta ta dinga jin tamkar ta shak ota ta mutu, amma idanun yarinyar a yau Sun razanata Sun kuma firgita ta. A idanun Amanin ta dinga hango rashin kunya zalla da wani irin kwarjini da ba shakka idan ta cigaba da tata masifar Amanin zata iya tona mata asiri. Zata iya fallasa sirrinta ta sanar da zuri ar Lami do wacece ita? Sai kawai ta cije baki, k walla tana shirin zubo mata. Ba k wallar komai ba ce sai ta rashin sanin madafa, da rashin sanin abinda zata aikata& cikin k unar zuciya ta furta  Kin cuce ni Amani, kuma wallahi ba zan barki ba sai kin biya abinda kika aikata min, sai na saka ki bak i ciki fiye da Wanda kika sa min a cikin kwanakin nan zan mayar da rayuwarki miserable&  daga haka ta juya ta fice cikin mutuwar jiki. Imani ta dinga kallon Amani a firgice ganin wata irin da Amanin take hankalinta kwance kafin ta furta  Before ta yi making life d ina miserable ni na mayar da tata, matsafaciya kawai& . Juyota Iman ta yi a fusace tana furta  Ba zaki daina shiga sabgar matar nan ba ko? Ba zaki fita hanyarta ba ko? Sai ta cutar da rayuwarki? Amani ta dafa hannunta tana murmushi ta furta  Wait and See, ba abinda zai faru sai alheri, In sha Allah sai naga bayan matar nan& .na tsaneta Imani, kuma ko yanzu na San burina daf yake da cika.

Daga haka ta saka kai ta fice daga d akin. Tana jin zuciyatta fresh kamar ba wata tarin matsala a tare da ita.


Babban Parlorn Didin taf yake da mutane. Wa danda suka zo taya ta murna. Yau bakin Didi Sam ya k i rufuwa don a yau ne zata saka a kai ku din auren Moddi. Auren da take ji idan ya yi shi dukkan matsalolinsa da nasu za su kau. Tana kallon k aninta Kawu Jauro ta furta  Duka a kai har ku din har lefen idan ta kama a basu Har sadakin bana son auren nan ya wuce sati biyu Jauro, ka gaya musu bama buk atar komai sai matar kawai. Jauro ya  d aga kai cike da gamsuwa. Amani kuwa gabanta ne kawai yake fa duwa haka kawai jin wai auren Dada za a je nema. A da kam ta fi kowa son Dada ya yi auren Amma yau sai taji wani abu ya dunk ule mata a k irji jin abinda Didi take cewa. Hakan yasa ta sulale daga cikin mutane ta shige d akinsu na sashen Didin tana shiga ta danno k ofa. Zuciyarta na bugawa ta lumshe ido tana jan Innalillahi a ranta don idan har ba mafarki take ba, ji take kamar kishin Dadan take, kishi mai zafin gaske mai dagargaza zuciya da saka zafi a cikin zuciyar& . Ta runtse idonta tana furta  Ya Allah! Me yasa ne? Ta fa da tana kwanciya saman gadon.


Iman kuwa farin ciki ne ya sakata neman idanuwan Amanin don su yi farin cikin tare ko ta hanyar kallon juna ne, sai dai bata ga Amanin ba. Don haka ta mik e zuwa cikin gida don neman Amanin a daidai Sitroom da Dahda yake zama da bak i. Ta fara juyo sautin muryarsa kamar waya yake, kamar kuma magana yake da wani a kusa da shi&  Wannan karan fa na shirya da gaske nake zan aikata abinda kuke so, zan cika muku burinku zan kusanceta& &  Nimfashin Iman ne ya kusa d aukewa tsabar tashin hankali bata San sanda ta yi baya ba, don idan Har zuciyarta ta fassara abin daidai Furucin Dada yana nufin zai kusanci Amani don cikar wani burinsa, Wanda ta tabbatar bakomai ba ne, sai SON DUNIYA& & .

(wannan littafin book one ne free, book 2 and 3 paid ne. A biya 500 cikin wannan asusun 2118666253 UBA. Don cigaba da jin labarin Moddin Didi, da Amanin da Dahda. Wa ke da nasara tsakanin Amani da Safna. Book 1 daf yake da k arewa.)


JIKAR NASHE&
'?HADARIN GABAS& & =?L?



28.



NAZEEFAH SABO NASHE&
'?


08033748387.

BRIGHT PENS SECOND BATCH&

A gigice ta ja da baya da sauri, don bata son Dahdan ya ganta. Sai dai aikin gama ya riga Ya gama, don tuni idanunsu suka ha de da juna. Ta Ware ido tana toshe bakinta da k ok arin ha diye kukan da yake son taho mata. Sai dai ina bata da juriyar rik e wannan kukan tuni hawayen ya kufce ya dinga zuba daga idanunta& Mik ewa Dahdan ya yi don isa wajenta da son ya yi mata bayani, sai dai ko kafin ya kai k ofa ta fice da sauri, bata son ganinsa ba kuma ta son jin ko wane kalami daga bakinsa. Ta ji komai ta kuma amince Dadan matsafi ne, da gaske tsafi yake yi shi yasa duka abubuwan suke faruwa. Ashe hauka take da take d orawa Mommy Alhajin komai. Dahdan ne mai laifi shi ya yi silar afkawar Amani cikin wannan halin. Ta mayar da k ofar ta rufe Har da murza key sannan ta jingina da k ofar wani irin kuka da bata tab a irinsa ba a rayuwarta ta shiga yi. Da dukkan k arfinta take buga k ofar da kanta tana furzar da wani irin huci mai zafi. Daga k asan ranta take jin wani irin zafi zuciyarta kuwa kamar ana tafasa ta da ruwan zafi. Gangar jikinta idan banda tsiyayar da gumi ba abinda take yi. Duk da tarin sanyin A.cn da yake d akin jin ta take kamar tana cikin Oven, tsabar zafin da take ji na tashin hankalin da take ciki. Ta zube a gado idanunta akan hoton mahaifiyarsu, kallon hoton ta yi kafin ta fisgo shi da k arfinta ta shiga magana da shi kamar wacce take cikin hoton tana jinta.  Me yasa? Me yasa Mahmeey kika Mutu kika bar mu? Me yasa baki tafi da mu ba, kika barmu a wannan duniyar mai cike da maciya Amana da burin duniya? Mun fuskanci k alubale da dama kafin mu tashi mu kai yanzu, sai gashi a yanzu muna fuskantar k alubalen da yafi Wanda muke ciki, mahaifinmu Mahmeey, Dahdah yana shirin kusantar Amani y ar cikinsa don Son Duniya&  Sai ta sak? fashewa da kuka da k arfin gaske, ta rungume hoton y ar riga a jikinta. Ta da de zube a wajen cikin fitar hayyaci kamar wacce ta zare, burinta mutuwa a loakcin burinta ha duwa da mahmeey a can inda ba zata sake ganin Dahda ba, ba zata sake ha duwa da duk wani k alubale mai shirin tarwatsa mata zuciya ba. Tana so ta Mutu sosai kamar yarda Amani take burin mutuwar itama. Bugun k ofar da ake yi ne yasa ta dawo cikin hayyacinta, sai kuma tabi k ofar da kallo tana tunanin waye sai ta ji muryar Amani tana kiran sunanta. A kasalance ta mik e ta bu de mata k ofar. Idanu suka zubawa juna gaba d ayansu kowa yana jin wani irin ciwo a ransa, ganin halin da d an uwansa yake ciki. Iman ta finciko Amanin ta mayar da k ofar ta rufe ta rungume ta da k arfin gaske, a tare suka saki kuka sautin bugun zuciyarsu yana k aruwa. Jikin Amanin zafi zau da alama mugun zazzab i ne ya kamata. Iman ta ja hannunta zuwa bakin gadon ta zaunar da ita kafin ta mik e cikin First aid box da yake gefen gadonsu ta bu de ta Ciro pain reliever ta d auko table water ta dawo inda Amanin take. A baki ta zuba mata maganin Amanin tana b ata fuska ta sha maganin. Kafin ta zube a saman?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? gado. Iman D in ma kwanciya ta yi daf da ita tana sakin ajiyar zuciya ta furta  Matsalar mu daga yau In sha Allah ta kau Ama. Amanin ta  d ago tana kallonta da neman k arin bayani. Iman ta d aga mata kai  Dole zamu bar gidan nan a daren yau& . Amanin ta zaro ido kafin ta lumshe su sai kuma ta ciji leb enta bata ce komai ba.  Zamu wuce wajen dangin Mahmeey, Har sai komai ya lafa, ina tsoron afkuwar wani abu da naji shi da kunne na yau, da wani ne ya gaya min ba zan tab a yarda ba&  Amanin bata bu de idonta ba. Zuciyarta ce kawai take bugawa da wata irin k aunar Dahda mai zafin gaske& tana kallo Iman ta shiga ha da musu abinda zasu buk ata. Har ta gama bata ce komai ba, tana jin abinda Iman  D in ta yanke shine mai kyau&



Dahda kuwa tun bayan fitar Imani sai kawai ya lumshe ido Ya jingina da kujera yana jin kansa yana matsa da wani irin ciwo. A hankali yake taune lips d insa. Daidai lokacin Amanin ta shigo kamar an jehota a firgice duk ta yi wani irin. Kallonta yake da mamakin yanayin da take kamar wata Mara lafiya. Zama ta yi a gefen kujerar da yake kawai sai ta samu kanta da saka kuka. Bai ce mata komai ba har ta gama kukan da ya tabbatar shine zai saka ta samu sauk in ra da din da take ji a zuciyarta. Ta  d ago a fisge ta sauke ganinta a kansa kafin ta furta  Dahdah da gaske kai ka haife ni? Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai dai bai janye idonsa daga kanta ba, ya furta  Kina tantama ne? Ta cije leb enta da k arfin gaske kafin a fusace ta ce  Ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login