Showing 12001 words to 15000 words out of 94443 words

Chapter 5 - HADARIN GABAS HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

160

tari ba ya magana sai dai ta idanu hakan ya zame masa jiki ga duk wanda ya san shi kuma ya san shi akan irin wannan halayyar. A ransa ya sake maimaita kalmar gantalallun yana jin b acin rai ya cije bakinsa a hankali ya furta you will explain clearly. Ya mik e yana goge hannunsa da hand towel bayan ya wanke hannun duk da ba da hannun ya ci abinci ba.


Kansa tsaye ya nufi d akin su. Yana jin duk hukuncin da zai yiwa Amani ba zai gamsar da shi ba idan ba mugun duka ya mata ba. Yarinyar tana da taurin kai da kunnen k ashi a wannan halayyar sun yi ban ban da y ar uwarta.


Imani na zaune saman sallaya ta idar da sallahr walaha kenan da Alk ur ani a hannunta.
Dahda ya tura k ofar d akin da k arar k ofar ya saka zuciyar Imani bugawa.
Amani kuwa ba abinda ya dameta irin mayataccen k amshin turarensa da yake tuna mata wancan yanayin na cikin mafarkinta. Fuskarsa a ha de ya shigo d akin idanunsa a kan Imani ya ce  fita Parlour Imani, and what ever da zaki ji ya faru don t try open this door&  Imani idanunta ya kawo ruwa ta yi raurau tana kallonsa zuciyarta na bugawa ta ce  Pleas& . Kallon da ya mata ne yasa ta ha diye guntuwar maganar da ta yi niyyar yi, jikinta na rawa ta fice da k ur aninta a hannunta idanunta na zubar da hawaye.

Ya k arasa bakin gadon inda Amani take zaune idanunta a k asa tana wasa da zoben hannunta.
K afarsa guda ya d ora a kan gadon ya dogara da ita. Cikin wata irin hargitsatstsiyar murya ya furta  Amani Imam Moddibo& . Hakan da ya furta yasa zuciyarta wani irin tsalle ba shiri ta d ago tana kallonsa. Fuskarsa a ha de take kamar ba shi ya yi furucin ba. Ita
Kuwa sunan da ya kirata da shi ba abinda ya tuna mata sai wani ru dadden mafarkinta da ya yi amfani da hakan wajen kiranta. Kallonta yake yana noticing reaction d inta kafin ta ji ya jata da k arfin gaske ya matse fuskarta  Raininki yazo kai na? Ni mahaifinki kika yiwa abinda kika yi d azu? Kin san ba zan d auka ba ko? Banda ina tausayin maraicinku wallahi sai na aurar da ke a satinnan. Na gaji Amani na gaji da halayenki haka kika ga y ar uwarki na yi? Mommy ba uwa bace wajenki da kika rainata? Turo bakinta ta yi cikin wani kalar k unk uni ta furta  Ni ba uwata ba ce, Allah ya kiyaye& . D al ya d alle bakinta kafin ta ji ya tsinka mata mari right and left. Amani ta rik e k uncinta duk da b acin ran da take ciki bata bari hawayen idanunta ya zuba ba. Abu guda da ya dameta kusancinta da shi da k amshin turarensa da ya
Bi ya kewaye mata hanci. Ya wancakalar da ita a saman gado  Ki tattara kayanki now now ki koma gidan Hajja Didi I can t tolerate this behaviour anymore. Ya fice daga d akin Amani madadin kuka lumshe ido ta yi komai ya kunce mata da zarar ta rufe idon Lips d in Dahdan take gani a lokacin ji take dama Dahdan ya sumbaceta kamar yarda ta saba faruwa a mafarki& Shigowar Imani ce da kiran sunanta da ta yi yasa ta bu de ido. Imani ta dinga kallonta tana mamakin yarda idanunta suka bayyana halin da take ciki.  Bai miki komai ba ne? Sai lokacin ta ji hawayen idanunta sun sauka ba na dukan da Dahdan ya mata ba ne na zallar takaicin halin da take ciki ne akan mahaifinta da k ananan shekarunta sha bakwai kawai.  Ya min Habibteey, ya mareni ya kuma
Koreni daga gidansa ya ce baya son gani na. Imani mahaifina mahaifina ke guduna saboda rashin uwa, maraici hauka ne? Imani hannunta tasa ta jata jikinta  Don t say this again, Dahda yana son mu kema abinda kika yi ne isn t good at all. Ko bakomai Dahda ya yi deserving respect a wajenki&   Yana son ki dai, ni ba ya wani sona ba tun yau na yi noticing haka ba.. ta Mik e a zafafe ta shiga ha da kayanta  Zan je na gayawa Didi zan kuma koma gidanta ita ka dai ke so na kowa ma laifi na yake gani, kun manta ba laifina bane haka Allah ya yi ni&  Ta shiga ha da kayanta a akwati Imani tana rok onta ta bari taje ta bawa Mommy da Dahda hak uri wani kallo ta mata tana furta  Na bawa wannan matar hak uri akan me? Over my dead body wallahi, ke dai da ta mayar sokuwa ki je ki yi ta biye mata&  ta ja akwatin da sauri ta fice daga d akin bata kula kiran da Imani take mata ba..


A babban parlourn ta gansu a zaune Mommyn ranta fes ta kalleta da akwatin ta a ranta tana furta  Kin tafi kenan yarinya in dai ina gidan nan ba zaki tab a zaman lafiya da ubanki ba, har y ar Uwar taki sai na yi silar da zaku koma gidan jarababbiyar tsohuwar nan&  Dahda dai ko kallonta bai yi ba yana ji ta bu de k ofa ta fice Iman zata bi ta yasa baki ya kirata  Koma ciki.. Turus ta yi tana kallon Dahdan ta furta  Dahda titi ta fita fa, bata jira driver ba..  And so what? Ai ta girma she can do what ever suits her& . Ya cigaba da kallon T.V d insa kamar ba abinda ya dameshi sai dai a k asan ransa haushin d abi un Amani ne yasa yake gallaza mata ba don baya sonta ba, ya lura idan ba haka yake mata ba she never change her habits.. Imani jikinta a salub e ta shige d akinsu tana kallon yarda Mommy fuskarta ta kasa b oye murnar da take ciki sai girgiza k afa take kafin ta ji muryarta tana furta  Ka burge ni Imaam, idan ba haka ake wa Amani ba ba zata saitu ba yarinyar kamar mai iblisai&  A fusace ya zuba mata wani kallo  Don t repeat&  ya danne ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?sauran maganar bayan ya mik e a zafafe ya bar mata wajen. Mommy ta bi bayansa da harara tana tsaki k asa k asa bata san me yasa malamanta har yau sun kasa aiki akan gayen nan ya tsani y ay ansa ba. Ita kanta wani lokacin idan ya mur de mata sai taga kamar ba Imaam Moddibo ba.


Yana shiga d akinsa ya zauna gefen faffad an gadonsa da ya sha shimfi da mai taushin gaske. D an haki ya sauke kafin ya rik e kansa a hankali ya furta  Amani why? Sai kuma ya ja guntun tsaki yana mamakin yanayin tsiwar yarinyar da rashin tsoro ko na misk ala zarratin a tattare da ita. Shi da kansa wani lokacin yana shakkar matar tasa, don dai namijin gaske ne da
Baya d aukar raini ko ka dan, banda Amani da tun lokutan yarintarta bata raga mata ko ka dan. Ya girgiza kai a hankali yana furta  Allah ka shirya mana. Sau tari ya kan yi tunanin wani irin zaman aure Amani zata je ta yi a gidan Mijinta da wannan tsiwar baki kamar parrot. Wayarsa ya yi saurin janyowa ya fara kiran Idi driver don sai yanzu ya tuna gangancin da ya aikata Amani bata shiga motar haya me ya rufe idonsa ya turata gidan Didi ita ka dai? Tsoro ya shige shi a gaggauce ya yi dialling call d in Idi driver. Tana shiga ya d aga  Ka bi Amani maza hanya ka kaita gidan Didi. Ya fa da yana zare wayar a kunnensa ba tare da ya amsa gaisuwar Idi Drivern ba..




A guje Idi yake driving har ya samu ya cimmata a gefen titin sai fama take da akwati kici kici, don sam Amani sai tsiwar amma bata da k arfi ko ka dan to ina ma ta ci abincin arziki balle ta samu k arfin. Kuka take son yi musamman ganin inda duk ta wuce idanu a kanta masu motoci sai tsayawa suke don su rage mata hanya, ta ha de ranta tsam kamar bata tab a dariya ba. Zata iya cewa bata tab a shiga motar haya zuwa ko ina ita ka dai ba don haka ta rasa ma ya zata yi. Hawaye kawai ta ji ya fara zubo mata tana sake tsinewa Mommy a ranta. Jin horn da ake bai saka ta ta juya ba, don a zatonta mutanen da suke ta tsayawa don su rage mata hanya ne. Har sai da ta ji Muryar Driver yana furta  Hajja k arama, ki shigo in ji Alhaji na kai ki gidan Hajja Babba&  ta d ago ranta a b ace kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta turo bakinta ta furta  Just go Baba, zan tafi da kaina.. ta cigaba da tafiya ba yarda Drivern bai yi ba akan ta shiga ta k i har ya gaji ya kira Moddi. Jin abinda ya ce Moddi ya saki k aramin tsaki ya furta  Give her the phone, bata wayar. Kamar ba zata karb a ba sai dai ta saka hannu ta karb i wayar ta kai kunnenta  Ki shiga motar nan before I knock your head. Haka ya furta cikin Murya mai tsaurin gaske..  Da& .  I said Enter the car.. Ya katseta ba tare da ya bari ta k arasa maganar ba. Idanunta ne ya kawo ruwa ta shiga motar da zafin nama ranta a b ace. Idi ya shiga ya tayar da motar yana furta  Sai hak uri Hajja K arama, in dai aka ce yaro maraya ne yana rayuwa a koma ina ne sai ya yi hak uri Allah yaji k an mahaifiyarku mutuniyar kirki.  Ameen ta furta tana lumshe idonta ta jingina da jikin kujera. Haka kowa yake ce mata amma ita ta kasa yarda, ba yarda za a yi don uwarta bata raye a dinga takata
A gidan Ubanta ta hak ura ina wallahi ba a yi mata ba. Hawayen da ya fara zubo mata ta saka tissue ta goge don ma kar a cigaba da ganin gazawarta..




A k ofar gidan Didin ya tsaya babban gida ne irin ginin zamanin da don Didin sam ta k i yarda a yi renovating d insa daga waje. Babu gate a gidan sai maka makan zaure. Daga wajen gidan kuma akwai bishiyoyi guda biyu na guava da na mangwaro. Sai garejin ajiye mota guda d aya.


Zaure uku zaka wuce kafin ka isa faffa dan tsakargidan da ya ji malalan suminti mai santsin gaske tun na zamanin Da don shima Didi ta k i yarda a zamanantar da shi ta ce ba za a canja mata fasalin gida daga inda Uban Moddibo ya bar shi ba, ba za a kawar mata da tunaninsa ba a goge memory d insa. Bishiyu ne a tsakar gidan guda uku maka-maka, daga gefe can kitchen ne irin dai namu na gargajiya.


Parlourn Didin jibgegene d auke yake da wani carpet mai taushin gaske a saman carpet d in kuma Dadduma ce ta manyan
Mutane sai tun-tun da aka zagaye parlorn da su ba kujera a parlourn. A jikin bango kuwa T.V ce plasma babbar gaske ita ka dai ta yarda a sabunta mata da ta Zamani don Didi akwai son kallo. Amma daga gefe ga ta Uban Moddibo nan da ya bar
Mata gado. Da radio irin ta da babba.


A zauren da zai sadaka da cikin gidan Amani ta ja tunga da akwatin ta ta tsaya ta daddage ta rusa ihu..  Na shiga Uku Didi na, Dada da Safna suna shirin kasheni don an ga bani da Uwa wayyo Allah na& .


Hajja Didi da tada sallahr azahar d inta kenan ta yi saurin sallame sallahr ta fito a guje tana furta  Wa nake ji haka kamar muryar magajiya Uban waye zai kashe kin?  Buzuwa da Mijin Buzuwa&  Amani ta amsa mata da irin sunan da take kiran Moddibo da matar tasa.. Didi ta ce  Jar uba, to shigo magajiya in dai ina raye ba mai tab a ki ya kwana lafiya mik o min Salula ta ki kira min Mijin Buzuwar na ji dalili& .



JIKAR NASHE
'?s?HADARIN GABAS& .=?L?

NAZEEFAH SABO NASHE.&
'?


5ة?5ض?5???/!/!5ػ?5ض?5ؽ? 5ة?5ض?5???5ؽ?/!
'?


08033748387.

&&&&& 5ث?5ض?
!/!6??




  -
Salular ta mik a mata sai kuma Hajja Didin ta wurga mata harara tana furta  Duba kiga zaki ga k wallo guda shidda itace lambar Uban naki.. Amani ta kuwa duba sai ta ga an yi saving da hotunan ball guda shidda murmushi ta saki wato ta inda Hajja Didi take gane numberr yaranta kenan. Dahda shine d a na shidda a wajen Didi ya biyo bayan mata biyar cur! Ta danna numberr kafin ta saka a handsfree don ta san a haka Didin take waya. A duk sanda zata duba wayar sai Didi ta canja wani abin da yake banbanta mata yaranta. A da tambarin hula ce alamar da take gane Dada, yanzu kuma ta
Mayar da shi 6Balls.


Dahda da yake tsaye kan Imani da take wani irin kuka ya kai dubansa kan wayar hannunsa yana d an tsaki  Ba zaki min shiru ba ne? Ta yi k asa da kanta kawai ba don ta daina kukan ba still idanunta na zubar da hawaye. Yana ganin numberr First Love kamar yarda ya yiwa Didin saving ya d an saki guntun murmushi don ya san yau kam tunda ya tab a Magajiyar Didi ba zaman lafiya. Wayar ya kara a kunnensa yana k asa da muryarsa kamar yarda ya saba  Hajja Didi& .  Tsaya Moddi ban buk aci gaisuwarka ba, Uban me Magajiya ta yi ka koreta daga gidanka? Ya d an fesar da hucin numfashi yana murza goshinsa abinda ya zame masa al ada, sannan cikin wata murya da bata fiye fita sosai ba ya furta  Bata gaya miki irin rashin kirkin da take a gidan ba? ta fitini kowa ita shikkenan ba zata zauna lafiya ba?  Bata gaya min ba, ba kuma na buk aci a gaya min d in ba, yo Ai yarinta ce kuma kowane yaro da irin yarinyartarsa abu guda da zan gaya maka ana iya canza mata banda d a balle kai da sukkenan k walli biyu Jalla ya baka, a haka ya kamata ka kula da su? To kazo yanzu ka d auketa Ai na sha gaya maka ba ta yarda za a yi kana raye ace y ay anka ba zasu zauna a gidan ka ba saboda son zuciya irin na matarka to bata isa ba gida dai gidan Ubansu ne sai dai ita Buzuwa ta fice fit daga gidan. Mintuna ashirin na baka kazo ka d au Magajiya Ka mayar da ita gida& .. Zan kuma zo har gidan na ja kunnen buzuwa.. Daga haka ta zame wayar a kunnenta ba tare da ta kasheba don yana jin ta ta ce  Yi shiru kin ji Magajiya yanzu zai zo ya
Mayar da ke, ba a yi matar da zata hanaki zama gidan Ubanki ba..  Ni gaskiya ki daina ce min Magajiya, Ni wallahi Dahda ya cuceni da ya saka min sunanki&   Ai inye ni kike gayawa haka? Bayan na gama kwatar miki y ancinki yanzu.. Dahda da yake jin komai ta cikin wayar ya saki murmushi a zuciyarsa ya ce da din abin kema bata kyaleki ba. Wannan yarinyar lamarinta sai addu a sai kace Mai jinnu. Ya saka wayar a aljihunsa yana kallon Imani ya ce  Sai ki rufe min baki yanzu zan je na d aukota ke kanki wahalar da ke take amma koda yaushe kin fi son ki
Ganki a tare da ita. Ya saki tsaki yana furta ranar da aure zai rabaku zan ga ya zaku yi? Iman dai murmushi take sai a lokacin hankalinta ya kwanta jin zaa d auko mata Amanin. Ta bi bayan Dahdan da kallo da ya fice cikin shigar black
Jallabiya da ta masa kyau sam ba zaka ce Dahdan ya diresu ba wani irin murjajjen jiki ne da
Shi mai kyan gaske da kullum baya tsufa ko don abin ya ha du da arziki ana kuma cin mai kyau& Ta shige kitchen don k arasa abinda take ranta ta furta  Saura Inna Talatu In sha Allah itama sai ta dawo a yau.



 Ta kori Inna Talatu ma ta ce a yau ta bar mata gidanta. Didi ta ware ido tana furta  Ita buzuwar? Eeh to lallai lamarin nata azimin ne, ban san sanda da na haifi Moddibo nace mata na bar mata shi ba? Irin wannan iko haka da k afafa sai kace ita ta min wahalar Moddibon? To Bari yazo na ji ko shine ya sahhale mata ta dinga ikon da ta ga dama a gidan. Talatu kam ko bayan raina ba zata bar gidan Moddibo ba, matar da tun daga k uruciyarta take wahala da ni sai kawai don Moddibo ya yi arziki ya auro Hurul aini sai ta koreta bari yazo na ji dalili? Amani ta saki murmushi don ta sake kunna Didi ta furta  Didi wai wacece Uwargida ne da Mamanmu da Buzuwa? Didi ta saki tsaki don ko zancen bata so ta furta  Allah dai ya gafartawa Uwarku mace ta gari salihar baiwa. Ita mai sunanta Ai kwafinta ce kwabo da kwabo Ke kuwa ba wanda kika gado sai Dijatu itace na sha wahala da ita tana yarinya kai Allah dai ya yafewa Dijatu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login