Showing 90001 words to 93000 words out of 94443 words

Chapter 31 - HADARIN GABAS HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

176

sai bin su take da ido cikin tashin hankali. Turo k ofar da aka yi ne ya saka su juyawa gaba  d aya. Ya shigo cikin d akin fuskarsa ba yabo ba fallasa. Sai zabga k amshi yake kasancewar garin sanyi ne, jikinsa sanye yake da riga da wandon jeans sai jibgegiyar rigar sanyi a jikinsa, hannayensa sanye cikin aljihun rigar. Umma T ta d auke kai daga kallonsa. Har cikin d akin ya shiga yana kallonsu da yanayin tambaya a idonsa sai dai ya kasa bu de baki ya yi tambayar. A zafafe Umma T ta ce  Hankalinka ya kwanta ko? Ka Yi ruining rayuwar Amani, ta tafi ta shiga duniya tunda hakan ka zab ar mata. Ya waro ido yana furta  What? Fateemah ta yi tsaki tana furta  Ai na San ka ji sarai abinda na ce, Amani ta tafi, ba irin kunnenka da ban ja ba Moddi amma sai da ka aikata abinda ka so, yanzu me gari ya waya? Me kake so muce da mutane? Shiru ya yi yana taune lips d insa, yana danna waya sai kuma kamar Wanda aka ce tashi, ya tashi da sauri ya nufi waje wayar a kunnensa&  Fateemah ta bi shi da kallo idanunta har yaji suke saboda hawayen da Moddibo yake saka ta. Didi ma binsa ta yi da kallon don ita yanzu ko magana bata iya yi ciwon hawan jini ya saka muryarta ta karye& Iman kuwa haushin Dada kamar ya kasheta abinda ta lura da shi kamar bai damu ba, kamar ba abinda ya dame shi da tafiyar Amanin, tunda burinsa ya cika..


Yana fita ya shiga motarsa, tsabar turirin da zuciyarsa take masa ne yasa ya kasa driving d in ya zubawa wayarsa ido. Still numberr Alwan ta k i shiga. Taune lips d insa kawai yake yana Jin kamar ya rufe ido ya gan shi a Abuja. Kamar wasa a karo na barkatai wayar ta shiga sai dai instead of Alwan d in ya yi picking sai bai yi ba, ya turo masa text message  Ka daina kira na, don ba zan amsa ba, ka gama mana aikin mu bamu da wani sauran business da kai& yarinya kuma tana hannun mu. Moddibo ya waro ido yana sake kallon message  din mai hakan yake nufi? Alwan ya yaudare shi kenan? Har Abuja ya je Amma an sanar masa Alwan baya nan. Bai dawo daga wancan firgicin ba wani message  din ya shigo masa& .  Amani bata Nigeria Imam, kada ka yi wahalar nemanta zamu dawo da ita da zarar mun samu abinda muke so, Nima kuma ba zaka sake samu na ba& .. da k arfi Moddi ya ce  Don t Alwan, Don t ba haka muka yi da kai ba&  ya fa da a zafafe kamar Alwan  din yana gabansa. Ya tura masa message amma bai tafi ba, da alama da gaske Alwan ya daina aiki da layin. Me kenan ya aikata me ya shiga Kansa da ya aikata komai ba shaidu? Me zai ce da Didi wani bayani zai yi musu? Dole ne ya yi shiru kawai da bakinsa& ya dinga cijen leb ensa yana Jin kwanyar Kansa kamar ta tarwatse& ba kowa ya jawo masa wannan matsalar ba sai Safna& ta ina zai fara? Kiran numberr Alwan yake amma still wayar bata shiga. Ya kifa kansa kawai a saman sitiyarin motar yana sakin huci a hankali. A haka ne yake pretending kamar bakomai, kamar ba ya Jin komai a zuciyarsa Amma shi ya San abinda yake zuciyar tasa& kamar an tsikare shi, ya sake fincikar motar da mugun speed. Allah ne ya kiyaye, Allah ne kuma ya kai shi gida lafiya& ko motar bai rufe ba ya fito ya nufi cikin gidan& . A bedroom  dinta ya dinga jiyo hirarsu da dariyarsu basu San da zuwansa ba shi yasa suka cigaba da hirar cikin  daga murya. Boss lady ta ce  Kice dai gida ya zama naki, kai Safna kin iya tsiya, ya aka yi wai aikin ya ci har haka? Ba za ki gane ba Na ima, bafa k aramar tsanar yarinyar nan na yi ba, duk wani aiki da na yi a kanta baya tafiya min successfully. Ba k aramin asarar ku di take saka ni ba, yarinya sai ka ce aljanna. Alwan shine tsani na na cikar buri na, da abinda ya bani na yi amfani, na saka mata a furar da na san tana sha duk dare, na san Didi bata Shan sugar don haka mazubin da ake zuba mata daban ne, a cikin na Didin na saka maganin barci, shi kuma Imaam a kettle  din shayinsa da yake sha duk dare kamar ibada anan na zuba maganin da na karb o wajen bokan, Wanda ya tabbatar min in dai suka sha a tare sai sun kusanci juna, koda ba a cikin hayyacinsu ba ne, na kirkirarwa kaina ciwon k arya don kawai na cika buri na& sai gashi komai successfully, ai ina ta jira ki dawo daga South Africa ki sha labari. Zancen da nake miki suna can har tsohuwar zube a asibiti sakamakon bayyanuwar ciki a jikin yarinyar, cikin da na tabbatar koda tsiya koda tsiya tsiya sai na zubar da shi& . Da sauri Dada ya ja baya, yana k ok arin controlling zuciyarsa& Ashe Safna ce da wannan mugun aikin, yaransa suke zargin shi ya saka musu magani suka kusanci juna. Ya dinga jin jiri a Kansa fisgar leb ensa kawai yake, yana k ok arin danne b acin ransa, bai kamata ya nunawa Safna ya ji komai ba, zai yi maganinta a lokacin da bata tsammani ba, shi yanzu burinsa ganin inda Amani take. Don haka ya shige part  d insa hankalinsa a tashe, duk wani layin Alwan da na Boss  d insa ba Wanda bai kira ba sun k i shiga&



&&

A karo na biyu ta sake Jin motsi a bakin k ofar d akin& da sauri ta gyara zamanta don wannan karan kam ta shirya fita daga gidan koda hakan yana nufin sai ta sumar da mai kawo mata abincin ne. A lissafin ta kwananta biyu a gidan ko wanka bata yi ba, ba kuma ta damu ta yi ba duk da nacin matar da take kula da ita. Ta d auki k ullin yajin data b oye a hannunta ta tsaya da shirin ko ta kwana. Ana bu de k ofar ta nufi kan Wanda ya bu de k ofar da niyyar ba da masa yajin sai dai da sauri ta ja baya tana Ware ido ha de da nuna Wanda yake tsaye a bakin k ofar murya a sark afe ta furta  You?




JIKAR NASHE
'



34.



NAZEEFAH SABO NASHE&
'?


08033748387.


BRIGHT PENS SECOND BATCH.



Lumshe ido Alwan ya yi yana d aga mata Kai ya furta  Yes Me&  Sai ta zauna jikinta na rawa ta furta  Uncle kai ka kawo ni nan? Ya  d aga mata kai yana cigaba da fa din  To save your life from danger ba. Sai ya zauna idanunsa a kanta yana kewayeta da wani irin kallo da ta kasa fassara shi.  Akwai dalili babba na kawo ki nan, dole zan nesantaki da jama a gudun idon mutane a kanki, zaki haihu anan ba tare da kowa ya san abinda ya faru ba, Boss zata karb i Babyn ta rik e ke kuma sai a samar miki admission ki tafi karatu bayan kin je kin yi sallama da su Didi. Abu guda da zan gaya Miki ki aikata duk abinda aka umarceki bana son musu, idan ba haka ba komai zai iya faruwa, bana son tsiwa bana son rashin kunya kin ji ko? Da k yar ta tattaro nutsuwa ta saka a fuskarta tana Jin yawun bakinta na son d aukewa. Ta furta  Ni dai Uncle ka mayar da ni, na San Didi da Imaan suna can hankalinsu a tashe&   Da kuma Dada ba. Ya furta yana kallon cikin k wayar idonsa with a smile kwance a fuskarsa. Ta turo bakinta tana Jin wani b acin rai a zuciyarta bata son zancen Dada da duk abinda ya dangance shi.  Ni Ban ce maka Dada ba.. ya sake fad ada dariyarsa murya a k asa y a furta  But Why? Dada kuma ya damu dake fiye da zaton ki, banda ma damuwar da yayi da ke  din da tuni wani zancen ake ba wannan ba& . Tun jiya yake kirana don ma na yi blocking line d insa, amma me Dadan ya Miki ba kya son zancensa? Ta lumshe idonta tana Jin zuciyarta na sake nauyi da k yar take fusgar numfashinta ta furta  I hate him&  sai ta danne lips D in kalar yarda Dadan yake yi.
Alwan ya tuntsire da dariya yana furta  Like daughter like father, so duk kin  debe wannan halin cije leb en nasa&  Ta sake turo Baki tana furta  Ni bana Kama da shi&   Ni ban ce kina Kama da shi ba&  ya fa da yana kwaikwayon muryarta with happiness in his voice. Sai ya kalli kwanonin abincin ya  d ago kuma yana kallonta  Me yasa ba kya son cin abinci? Idan kina son fa kina son kullum na dinga zuwa,



sai kin dinga yarda ana miki duk abinda ake so, ki dinga musu biyayya idan ba haka ba& . Sai ya girgiza kansa. Da sauri Amani ta ce  Idan ba haka ba me? Ya ja hancinta yana furta  Idan ba haka Boss zata yi fushi, kuma fushinta means a lot.. don haka ki kiyaye, bana son wani Abu ya samu Babyn Dada, nafi son yarda muka d auko ki mu mayar da ke, ba tare da ko kwarzane ya same ki ba, Boss Babyn jikinki take so kawai sai a sallame ki, kin ga ba Wanda zai San kin haihu ko? Ta wani irin waro ido, tana kallonsa ta furta  Me zata yi da shi? Ya bu de hannunsa ya wara su alamar he don t know. Sai ta turo bakinta tana furta  You meant zan yi five months anan kenan? Ya  daga mata Kai yana furta  Sure, after kin haifi Babyn za a mayar da ke wajen Dadan ki&  Sai ta saki kuka da k arfin gaske. Alwan ya yi saurin kallonta yana furta  Oh sorry, Ban sani ba Nima ban sani ba, idan kika yi musu biyayya zasu bari ki tafi, kin San ina nan ko? Zan dinga zuwa kuma, ba zan bari a cutar da ke ba&  ta ji wani relief a ranta. Ta San Alwan kam yana son su, Don idan suka yi tafiya da shi ba abinda ba ya siyar musu, yana kula da su sosai.  Anan ka ke? Ya d aga mata kai  Aiki nake ma Boss&   Wai wacece Boss  din nan? Alwan ya yi dariya yana furta Zaki ganta as soon ta dawo daga tafiyar da ta yi& kina so ki ganta ne? Amani ta  daga Kai tana amsar plate  din da ya cika mata da abinci. Sai ta samu kanta da cin abincin sosai ko don yana ta janta da hira ne. At last ta saka hannu zata  debi abincin sai taji wayam. Ta yi saurin kallon plate  din tana waro ido. Shima Alwan waro idon ya yi ya ce  Duka kika cinye? Kunya ta kamata ta yi saurin sunkuyar da kai. Alwan ya yi dariya yana janyo leda ya tura mata a gabanta. Chocolates ne da Ice cream masu mugun tsada. Farin ciki ya bayyana a fuskarta sosai don ta yi missing  dinsu. Da sauri ta ja robar Icecream  din mai flavor  din chocolate ta fara sha. Tana furta  Thank you Uncle&  Alwan ya saki ajiyar zuciya yana mayar da fuskarsa serious face ya furta  Kina so na cigaba da zuwa? Ta d aga Kai.  To ki dinga yin duk abinda aka saki, kin ji? Bana son musu kuma ko me aka baki ki ci, a yanzu dai ba zasu cutar da ke ba, don ba su d auko ki don haka ba, but idan kika musu taurin Kai zasu iya cutar da ke. Hawaye ne yazo idonta ta yi saurin Kama hannunsa tana girgiza kai. Don t live here Uncle, ka zauna please&  ya duba watch d in hannunsa yana girgiza kai  I have a meeting, but bari na kunna Miki kallo akwai Korean movies da Indian movies ki kalla zasu dinga d auke miki kewa&  ta bi babbar Wall Tv  din da kallo ita ta manta ma da wani zancen kallo saboda tashin hankalin da take ciki. Sai ta ji wani relief ganin Uncle Alwan yasa ta ji ta samu nutsuwa sosai, a yarda ta  d auke shi kuma a inda yake mu amalantar su sai taga kamar ba zai cutar da ita ba. Ya kunna mata kallon sannan ya fita bayan ya ce mata ta yi wanka. Bata yi musu ba kuwa yana fita ta mik e ta shiga wankan, don ita da kanta ta san tana buk atar wankan a yanayin yarda take Jin jikinta. Wanka ta yi sosai a ha dadden toilet  din. Kuma ta samu Skin routine masu kyau sosai. Ta wanke gashin kanta. A mirror ta tsaya tana kallon cikinta da ya fara tasawa ka dan. Sai ta dinga Jin tausayin cikin tana mamakin dalilin da yasa Alwan ya ce cikin kawai suke so, amma ta San ya yi haka ne don ya taimaketa, don da kansa ya furta shi yasa aka  d auko ta don baya son a San ta haihu. Hankalinta ya kwanta ta ji bata da wata damuwa tabbas hakan shine rufin asirinta& ..




Duk inda tashin hankali yake to Familyn Lami do suna cikinsa. Ba inda basu duba Amani ba sai dai ba ita ba labarinta. Didi kam ciwo ya sake rikicewa, ga Umma D data saka su a gaba da tijara iri iri, tana furta  Ashe citata aka so a yi, shi yasa aka dinga cusawa  dana ita, to yanzu kam Asiri ya tonu, ai na San za a kai ga haka, wannan dukiya ta Moddi ai abin a binciki hanyar da ya samu ne, ga abinda sangarcin da kuka masa ya janyo, sannan ake tunanin na rufa masa asiri bayan Allah ya tona masa& . Didi ta dinga kallonta tana tuno sanda ta haifeta da kanta a cikin d aki, bada haka da sai ta ce canja mata Dijatu aka yi. Hawaye take fitarwa cikin karyayyen harshenta ta furta  Dijatu, kika furta labarin nan ga kowa Allah ya isa ban yafe Miki ba, d anki dai Amani ba zata aure shi ba, ba shikkenan ba&   Bas kuwa. Fateemah ta furta zuciyatta cike da jin haushin y ar uwarta. Dijatu ta watsa mata wani kallo ta furta  Eh Mahmud ba zai aureta ba, ke ki aura mata wani cikin y ay anki, kinibabbiya kawai. Fateemah ta sauke wani murmushi tana furta  In dai ni na haifi yara na kuwa kuma na isa da su zaki sha mamaki&  fa da fa ya kaure a tsakanin su. Moddi yana ji ya lumshe idonsa kawai ya yi shiru. Sai yamutsa sumar kansa yake zuciyarsa na fitar da wani irin hucin turiri. Idan har ya ce zai bu de bakinsa ya yi magana abinda zai fa da ba zai zama mai sauk i ba, zai kuma iya yiwa Dijatu mugun duka idan ya bu de idonsa ya ganta. Shi yasa ya rufe idon ruf. Shi duk ba wannan ne a gabansa ba ina Amani ta shiga shine tambayar da yake wa kansa. Ina Alwan ya kai ta. Furucin Didi shi ya togace Dijatu daga yama di di da zancen, sai dai an ce zancen duniya baya b uya don labari sai ya fara baza gari da ka dan ka dan.



&&&&


Ita ka dai take juyi a saman gadon. Bayan shigar Dada toilet ya kuma gaya mata ta shirya zasu Paris.  Duniya sabuwa! Ta furta cikin wata irin murya mai nuna zallar farin cikin da take ciki. Komai yazo mata a sauk i burinta ya cika. Amani ta bi duniya. Dama yarinyar ce take togace ta da komai. Don ba k aramin shakkar yarinyar take ba.  Y ar banza mai kafaffar zuciya, yau kema kin bi Uwarki&  ta furta tana sakin dariya. Imaam kuma shi da aure har abada. Sai ta sake jin wani relief a zuciyarta. Fitowar Moddi ce yasa ta ta yi shiru ta dawo cikin hankalinta ta dinga binsa da kallo tana son furta abinda ke k asan ranta, ta wani gefen tana shakkarsa. Mik ewa ta yi ta isa wajensa tana karb ar lotion  din da yake shafawa cikin yaudara ta dinga Shafa masa. Murya a k asa ta furta  Amma idan mun je, this time zaka
Amince naga Doctor Akan maganar rashin haihuwar nan&  D auke kansa ya yi kafin ya furta  No need&  da sauri ta kalleshi cikin harzik a ta furta  Wai me yasa Moddi? Me yasa duk sanda na maka magana akan matsalar rashin haihuwarta sai ka ce wani No need? So kake sai na wuce haihuwar? Ya  d ago ya kalli cikin idanunta. Sai Ya saki murmushi yana furta  Ba zaki tab a haihuwa ba&  Da sauri ta saki lotion  din a k asa jikinta na rawa ta furta  Saboda me? Ya lumshe idonsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login