Showing 57001 words to 60000 words out of 94443 words

Chapter 20 - HADARIN GABAS HAUSA NOVEL

16 Sep 2025

184

sai dai hakan bai yi tasirin rusa soyayyar da suke yiwa yaransu mata ba. A basu da shi  din suka d auki d awainiyar karatunsu tun daga primary har zuwa secondary. Malam Lami do Uban Moddibo Sam kasancewarsa mutumin da, da yazo daga Rugar fulani bai saka zuciyarsa ta jahilce shi wajen bawa yaransa ilimi daidai gwargwado ba na addini da na boko. Dijatu ce babba sai Fateemah, Sa adatu, Maryam, Kareemah da Jameela. Kafin su samu cikin Moddibo a lokacin Dijatu da Fateemah sun zama matasan y an mata masu kyau don duk yaran Didi sai Allah ya taimaketa ya bata su kyawawan gaske. Sai dai bayan Haihuwar Moddibo da ya yi Kama kwabo da kwabo da Fateemah sai aka ga Ashe ba wani kyau suke da shi ba, kyau kam mai suna kyau sai Moddin Didi. Samuwar cikinsa Malam Lami do Ya kwanta jinyar da ko tafiya baya iya yi, a haka Didi ta dinga jinyarsa tana kuma kula da laulayin cikin da yazo mata da masifaffen laulayin da bata tab a ciki irinsa ba. A Daren da ta haifi Moddibo wani irin zallar farin ciki ta dinga gani a fuskar Lami do Wanda bai tab a yi ba a duk sauran haihuwarta. Yasa a ka d ora masa shi a saman cinyarsa yana binsa da kallo murmushi d auke a fuskarsa Ya furta Allah ya raya min Kai rayuwa mai albarka, Ubangiji yasa ka zama sanyin idaniya a wajen mahaifiyarka da y an uwanka, ni dai kam na San bana raye zaka tashi, da na nuna maka kulawa da gata sosai Amma a hakan ma Alhamdulillah na San zaka Maye gurbina wajen kula da k annenka da mahaifiyarka, ina fata ubangiji ya baka managarciyar mace da zaka yi alfahari da aurenta& . Bayan gama masa addu a ya sunkuya ka dan ya masa hu duba da Muhammad Moddibo.


A ranar Sunan Muhammad Moddibo a ranar Malam Lami do Ya bar duniya. Tashin hankalin zuriyarsa kam ba a magana musamman Didi. Sun yi kukan rashinsa kamar ba gobe don duk da bai kasance mutum mai wadata ba Amma yana daga cikin maza masu kula da ci da Shan iyali da suttura daidai gwargwado. Sanda ya Mutu bai bar musu komai ba sai gidan da suke ciki. Tashin hankalin da Didi take ciki ya ninka na yaranta ba don komai ba sai don tana tunanin ta inda zata fara. Duk da tana y ar sana arta ta siye da siyarwa sai dai sana'ar ba inda zata Kai ta don sana ar ma bata farata ba sai bayan da Uban Moddi Ya kwanta ciwon ajali. Wannan tashin hankali da take ciki sai ya shafi har kula da Moddibo dole kulawarsa ta koma wajen Fateemah ita ke masa komai idan har yaje wajen Didi to kuwa shayar da shi zata yi. Hakan ya sanya wata irin shak uwa a tsakaninsu kullum yana manne da jikin Fateemah da sunanta ya fara bu de baki zaka ga yana d aga hannu yana kiran T T T. Hakan har yasa kowa ya koma cewa Fateemahn T. Dijatu ma bai iya ba sai dai D D sai kawai duk sunan y an uwansa Ya koma farkon sunan sa. Kulawar Didi gaba d aya ta koma kan Moddibo wannan Ya d arsa jin haushinsa a zuciyar Dijatu idan har yaje kusa da ita sai ta yakice shi musamman ganin yarda ya tashi a sangar ce, ga rashin tsoro da taurin kai. Idan za su yi masa fa da Didi ta hana. Abu guda da yasa yake sake shiga ran y an uwansa tun bayan tasowarsa sai ya tashi da tsananin y an Uwarsa da Didi. Burinsa duk abinda ya je ya samo ya k arar da su akan y an uwansa. Idan Didi ta ga haka sai ta yi murmushi ta ce  Allah yasa ka d ore Har girman ka Moddi, Allah yasa ba zaka auri matar da zata kawar da hankalinka daga wajenmu, Ubangiji yasa ka auri matar da zata taya ka so na da y an uwanka baki d aya. Tun bai San dalilin Didi na fa dar haka ba sai ya turo baki ya ce  Ai Didi ba a yi macen da zata raba ni da ku ba, balle ma ni ba zan yi aure ba ina tare da ke, idan ma na yi ta ce zata raba mu wallahi sakinta zan yi, bayan ina kallon irin wahalar da muke sha tare. Didi Shafa kansa take a lokacin ta ce  Allah yasa Moddi, na San Addu ar Uban Moddi ba zata tafi a banza ba& .


Haka Ya taso namijin gaske da burinsa ya mayar da taro sisi. Burinsa ya fita ya samu ko ka dan ne ya kawowa Didi don yana jin haushin wahalar da jikinta da take wajen yin abincin siyarwa Kunu da k osai da safe. Da rana kuma shinkafa da wake. Da daddare ma ba zata huta ba zasu  d ora kaskon wainar filawa duk da wannan su Fatima ne suke yi a tsakargida Amma Allah ya sakawa neman su albarka duk sana ar da suka saka hannu a kai sai ka ga ta yi albarka. Shi kuwa Moddi duk ba ya son yaga suna wannan abin, burinsa ya yi ku di ya tallafi rayuwarsu don haka ya dage da Sana a da karatun boko da na addini gaba d aya.


Sanda Fateemah da Dijatu suka samu Miji duka dangin Ubansu sai suka guje su suka juyawa Didi baya Wanda a bayyana take ba don komai suka aikata haka ba, sai don basa son ta jingina musu wahalar yaranta. Don k iri da muzu suka kalleta suka furta  Ai sai ki aurar da y ay an naki, sanda Ubansu ya Mutu ba nuna mana kika yi ba zamu rik e su ba, sai yanzu da aure ya zo zaki neme mu ashe muna da rana? Didi ta ha diye wani yawu mai zafi tana tuna Uban Moddibo da dukkan alherinsa ga y an uwansa, burinsa kyautata musu koda last kobo da ya rage a aljihunsa ne idan Har zata yi magana sai ya ce Maryama kenan? Idan baka taimaki y an uwanka ba wa zaka taimaka? Sam bani da burin samun ku din da wani na waje ma ba zai ci ba, balle jini na. Didi sai ta ce  Mhmhn, Malam kenan, Allah yasa bayan ba kai su rama maka abinda ka musu&   ba zasu rama ba, har abada kuma bana neman ramuwarsu don Allah na yi kuma gareshi nake neman sakamako. Sai ta ja bakinta ta yi shiru. Haka suka dinga fafutuka Har Allah ya fitar da su kunya don dai Fateemah Mijin marainiya ta aura take ya ce baya buk atar a kaita da komai sai zallar Fateemansa ita yake so da halayenta ba kayan d aki ba da zasu zo su Mutu ko mu da de ko mu jima. Ingancin tarbiyyyarta da nagartar halayenta ya fiye masa tilin kayan d aki. Didi taso ta turje amma sai iyayen Ahmad suka nuna dattako suka ce basa buk ata kuma har abada ba gori tsakaninsu da Fateema sun yaba da halayenta da tsatson da ta fito. Don haka duk wani shiri na Didi sai ya koma kan Dijatu aka siya mata kayan d aki da duk wani abu da zata buk ata. Haka aka yi biki aka k are cikin kwanciyar hankali. Zo kaga abin tausayi ranar rabuwar Fateemah da Kiddonta. Wunin ranar zama ya yi kamar marar lafiya, haka zai shige d aki ya saka kuka don baya son a ga kukansa Didi na hankalce da shi murmushi kawai take saki don itama ji take kamar ta fashe da kukan, tabbas ka ga auran y ay anka babbar ni ima ce, amma fa rabuwa da su akwai ra da di mai zafin gaske. Musamman yarda ta taso da y ay anta kamar k awayenta, haka dai ta daure tana ji tana gani aka rabata da su zuwa gidan aure. Kiddo dai bai raka Dijatu ba, don ita murna yake da tafiyar ta Adda T kawai zan raka ya furta kansa tsaye yana kallon Dijatun. Ta kuwa zabga masa harara har da rank washi ta furta  Sai me idan baka raka ni ba? Kuma koda wasa kada naga k afarka a gidana ka zo kwa dayin kaza. Ya janye jikinsa kafin ya furta  Ke ma ki samu kazar tukun, wannan k ulumin ne zai siya Miki kaza? Ta bi shi da duka sai dai kafin ta cim masa ya fece da gudu, kamar lokutan baya da suka Saba. K wafa Dijatu ta yi kafin ta sake rushewa da kuka tana furta Ai Didi tana Jin abinda ya ce mata Amma ta k i yi masa magana saboda ita ba a sonta shine d an so& ..


Haka rayuwa ta cigaba da gangara musu, da da di ba da di suna cikin godiyar Ubangiji don shi ke bayarwa ya kuma hana a sanda ya so ya kuma ga dama. Moddibo na girma kyansa da wani irin kwarjini yana sake bayyana tattare da shi. Shekara 19 idan ka gan shi sai ka zata wani babban saurayi ne, saboda son gayu da Allah ya bashi. Bai k i ba ko last kobo ne a jikinsa ya saka ya siyi riga da turare duk don ya je makaranta ya yi burga ya shiga cikin gayu kuma yafi kowa. Sau tari idan ka ganshi zata zaka yi wani shegen d an mai ku din ne, duk da bai d au girman Kai ya  dorawa Kansa ba Amma yanayin suturunsa da fatar jikinsa da ta bayyana tsananin Hutu duk da naturally haka take, wannan zai saka ka yi zaton Uban Moddibo attajiri ne, haka Didi take furtawa a duk sanda taso ta tsokane shi. Murmushi yake saki ya ce  Didi ki yi shiru fa, nan gaba baki san me Moddi zai zama ba, idan bai zama D an Attajiri ba zai iya zama attajirin da kansa& . Didi ta kan ce  Allah ya bada masu albarka, amma a rage dogon buri, rayuwar ma nawa take gaba d ayanta Moddi? Duk arzikin da zaka yi wani ya yi fiye da shi tun kan a san asalinka, don haka ka yi fatan masu albarka kuma na Halak. Idan kuwa Dijatu na kusa harara take zuba masa ta ce  Da charging wayar za ka yi arziki? Ko da siyar da raken? Idan Moddi ya juyo da birkitattun idanunsa Didi ce kawai take rusunar da su ta hana ya Kai mata duka, sai ko idan Fateemah tana nan.



Sanda Moddi ya shiga Jami a yana shekaru Ashirin cif, a sannan za su ce k addararsa ta fara daga ranar da suka ha du da Safna daga ranar basu sake gane kan Moddi ba, har bayan auren da aka masa da y ar riga da mutuwarta& .. Didi ta saki ajiyar zuciya Jin hannuwan Moddibo a kafa darta ta d ago tana kallon idanunsa da yake binta da natkakken kallo, mai nuni da yana son sanin menene a ranta me take tunani? Duk da bai furta ba, hakanan ta sanar masa murmushi tana Shafa gefen fuskarsa ta furta  Ina tunanin Moddi ne, ina tuna Uban Moddi da duk wata rayuwar mu ta baya mai cike da k alubale, ina tuna wancan Moddin masoyin Didinsa, wancan Moddin Wanda ya zama majinginar y an uwansa, ba wannan ba da gaba d aya ka canja a idanunka nake hango rashin gaskiya Moddi, tun bayan ha duwar ka da Safna ban sake farin ciki ba Moddi, na yarda ha duwarka da Safna shine silar rugujewar farin cikin zuri ar Lami do Uban Moddibo& . Moddibo ya runtse idonsa yana Jin wani irin zafi a zuciyarsa, haka nan idanunsa wani irin ra da di suke, da alama so yake kawai ya zubar da hawaye. Hannu ya cusa aljihu yana cizon gefen leb ensa, shi da kansa ya San Safna itace silar rushewar farin cikin ahalin Lami do. Zufa ce kawai take zubo masa ya runtse ido yana tuna ranar da k addara ta caku de zuciyarsa da ta Safna wace guda, daga ranar ya canja daga Moddibonsa ya koma wani mutum daban& ..


Da sauri ya dinga shiri saboda murna da zakwa din shigar sa Jami a. Jami ar da da yasan Safna zata zamo k addararsa a ciki da koda wasa bai je ta ba. Wanka ya fesa sosai ya kuma k ure Adaka cikin wani rantsatstsen jeans black da Jar shirt da ta yiwa fatar jikinsa masifar kyau. Ya kawo P.Cap black ya saka a kwantacciyar sumar sa ta asalin fulani. Sannan ya saka Black shade a idonsa. Idan ka gan shi wallahi ba zaka zata haihuwar Nigeria ba ne cikin garin Kano a unguwar Yola, saboda tsananin kyan da ya yi. Kamar yarda ya Saba a duk sanda zai fita daga gida sai ya isa wajen Didi ya zube a gabanta ita kuma sai ta sunkuya saman Kansa ta karanto masa addu oin tsari. Wannan karan saboda azarb ab i yana shiga Jameelah ta ce masa Didi tana wanka. Ba zai iya jira ba don haka ya ce idan ta fito ki ce mata na wuce saboda abokaina suna jira na. Jameela ta bi shi da kallo kafin ta furta  Addu ar fa? Yau ka yafe? Sai ga Didi ta fito da d an hanzari tana furta  Tsaya Moddi, bana son fitar ka gida ba addu a, duk saurin da kake ka dinga tsayawa ina maka addu a saboda ido da bakin al umma, don na lura Kai Sam addini da addu a basu wani zauna a ranka ba, kullum kuma fa dan hakan nake maka. Ya  dan turo baki yana furta  To ki yi sauri Didi, bana son na ja layi da yawa. Ta fa da yana mik a mata kansa bayan ya rusuna ka dan. Addu ar ta masa sai kuma ta tofa tana furta  Allah ya tsare sharrin mutum da Aljannu Allah ya kareka. Ya amsa da Ameen yana ficewa daga gida. Mamaki yake me yasa har yanzu Didi take mayar da shi yaro. Ya saki murmushi shi ka dai bayan ya d ane bayan machine D in abokinsa da ya fara tsokanarsa  D an Autan Didi, wallahi ka ji da dinka, ka samu Uwa mai kula da dukkan lamarinka, inama duka iyaye haka suke? Murmushi kawai ya saki shi Kansa yana alfahari da Uwa kamar Didi.


Makarantar ta B.U.K dank am take da y an mata da samari, kasancewar a ranar duk aka fara registration. Shigowar sa filin wajen ba wacce bata kalle shi ba a jikinsa ya dinga Jin hakan. Tsaki ya d an ja yana kallon abokinsa ya furta  I hate kallo wallahi, su kuma matan yanzu basu da kunyar hakan. Salihi ya ce  Aa fa wallahi kada ka zargesu kana da duk abinda suke so ne yaro, ai dole su kalleka Ma sha Allah. Ha de ransa ya yi sosai kamar bai tab a dariya ba, yana Jin yarda y an matan wajen suke furta  Subhanallah, Allah ya yi halitta bala i. P.CAP d insa ya ja ya rufe fuskarsa yana kallon Salihu ya furta idan an zo Kai na please ka kira ni, ina k asan bishiyar can. Kafin Salihi ya amsa masa har ya wuce cikin wata kalar tafiyar sassarfa da ta sake jan hankalin y an matan wajen. Suka bi shi da kallo. Ya zauna a saman wata kujera yana jan tsaki duk sai ya ji ransa ya b aci Sam baya son mata marasa aji. Idonsa a rufe cikin P.Cap ya dinga Jin ana buga table D in gabansa ga wani masifaffen k amshi da baibaye wajen. Cikin kunnuwansa ya dinga Jin sound D in yarda take taunar chewingum& da wani irin masifa ya cire P.Cap D in daga fuskarsa idonsa ya fa da cikin nata data kafe shi da mayataccen kallo tana cizar leb enta& & &





Jikar Nashe&
'?HADARIN GABAS& .&
'?

23.

NAZEEFAH SABO NASHE&
'?



08033748387.

BRIGHT PENS SECOND BATCH


Takaici bak in ciki, da b acin rai ne suka dabaibaye zuciyarsa, a lokacin da ya kalli Safna, Ya dinga Jin wata irin tsanarta a ransa kamar ya saka hannu Ya bugeta. Wani irin rashin aji ne haka? Shi fa yana son Mace Ma aji wacce idan ka kalleta ma zata zuba maka harara ba irin wannan da take gabansa ba. Shi yasa ko aure zai yi zai sha wuya wajen neman matar aure don sai ya tantance sosai kada ya auro B ARAGURBI. Ya sake gintse fuskarsa Har girarsa tana alamar tattarewa gefe guda yana fin cikar leb ensa al amari ne da yake nuna kaiwa k ololuwa wajen b acin ransa. Madadin fushi daga Safna dariya ta saki ka dan irin dariyar shahararrun y an bariki ta kuma ja ta tsaya hannayenta a k irji ta furta  Dole ka yi, kai da kanka ka San ka ha du, nice to meet you sunana Safna addu a ta guda Allah yasa department D in mu d aya. Idan kai da baka wajen ka yi magana to Moddi ma ya yi magana, shiru ya yi bai amsa mata ba ya sake mayar da P.Cap d insa kawai zuciyarsa na gaya masa ya tashi ya falla mata mari. Sai dai kawai ya share yana k ananan tsaki ya furta  Bar nan wajen. Safna ta ware ido tana kallonsa ta ce  In ji ina? Ai ni nan naga wajen zama& . A zafafe ya mik e Har yana y ar da P.Cap d insa ya saka hannu don d auka hannunsu ya sauka tare da na Safna ya bi hannun da kallo da ya sha zak ala zak alan farce kamar ba y ar musulmai. Caraf ta rik e P.Cap d in Har da manna ta a k irjinta tana furta Alhamdulillah na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login