Showing 1 words to 3000 words out of 89400 words
asmeetah writer ✍️
*MY ENEMY _*
🫦 مقىينا 🫦
Mallakin
أسماء محمد أولا 🥳
Asmeetah (giaɗe writer)
STEP TWO
1 and 2
ƘASAR JIDDER✈️🌎
Razhdeen shi da Roshan ne suke zaune a babban falon masarauta, sun jeru akan wani tsararren sopa mai uku, gwanin burgewa.
Mai martaba ne ya zuba musu ido sai faman sakin murmushi yake yana daga kan kujerarsa, yayi matuƙar yin farin cikin ganin su Razhdeen, fuska ɗauke da murmushi yake faɗin "a gaskiya naji daɗin zuwanku tin a lokacin da Mahaifinku ya sanar mun cewa kuna hanya, amma nayi mamaki sosai da naji labarin dawowarku Nigeria tsawon wata biyu amma baku tako ƙafarku kun zo ba sai yanzu, yanzun ma saboda bikinku ne yasa....."
Murmushi Roshan ya yi tareda faɗin "Uncle kayi haƙuri wallahi abubuwan ne suka cakuɗe mana..."
Mai martaba yace "daman nasan abinda zaku ce kenam ai, toh gaskiya ku gyara domin zumunci yanada kyau...."
Roshan kai a sunkuye yace "Insha ALLAHU Uncle, a mana afuwa..."
Mai martaba yace "shikenam ba damuwa, ALLAH ya muku albarka"
ya kuma cewa "yaushe ne bikin nakun?..."
Ɗan ɗago da kansa Roshan ya yi daga bisani yace "am sauran kwana biyar yanzu, amma Ni kaɗai ne mai yin Auren banda twins..."
Mai martaba kallon yanda Uncle Deen yake yayi tareda faɗin "why? Razhdeen!..."
Ɗagowa Uncle Deen yayi shima idonsa akan mai martaba ya ce "Uncle!..."
Mai martaba yace "baka magana ne?..."
Daƙer yake motsin da lips ɗinsa yace "ina yi..." ataƙaice.
Mai martaba yace "naga tinda na fara magana baka ce komai ba, kai meye zai hanaka yin Auren?..."
Kafin mai martaba ya iddasa maganarsa sai ji sukayi Hajiya Maamie ta tari yawunsa da cewa "ya zaka tambaye shi alhalin ku kuka hanashi...."
Duk ɗagowa sukayi suna kallon ta cike da mamaki ko sallama batayi musu ba, kuma da alamun laɓe tayi tana jin duk maganganunsu.
Mai martaba yace "haba baiwar ALLAH ai ko sallama zakiyi Koh..."
wani irin harara ta wurga masa cike da takaici take faɗin "ai ba buƙatar yin sallama tinda ana shirin watsa mun ƙasa a ido,
fisabilillah mai martaba saboda rashin gaskiya irin taka mun gama tsaida magana akan cewa ku haɗa Razhdeen da Ramlat in yaso ayi bikin rana ɗaya duk gaba ɗaya, amma shine yanzu kake tambayarsa wai meye zai hanashi Aure? toh wa kuke tunanin zai Aura kenam?...."
Mai martaba girgiza kai yayi sannan yace "Maamie kenam! shin kin tsaya Kinga ƙarshen wasan ne?
ki tsaya kiga gudun ruwana mana, Nima abinda nake shirin yi kenam, nima so nake a haɗa bikinsu gaba ɗaya..."
Hajiya Maamie ɗaga kafaɗa tayi tareda cewa "gwara kam in har anason ganin farin ciki na, zanje na turo Ramlat tazo su gana da juna..."
tana kaiwa nan tayi ficewarta.
Mai martaba sunkuyar da kai yayi ƙasa yana jinjina irin ƙarfin hali na Maamie.
Razhdeen gaba ɗaya bai gama fahimtar abinda suke nufi ba, juyowa yayi ya kalli Roshan, cikin sa'a kuwa shima Roshan Uncle Deen ɗin yake kallo, haka suke kallon juna cikin rashin fahimta abinda ake nufi da haɗa Razhdeen da Ramlat,
Ganin basu fahimci ina aka dosa ba yasa duk suka maida kallonsu kan Mai martaba wanda kansa har zuwa yanzu yake durƙushe,
Roshan ne ya buɗi baki yace "Uncle me yake faruwa ne kam? naga kana cikin damuwa..."
Mai martaba ya ɗago a hankali yana binsu da kallo yace "shin Razhdeen yanada wacce yake so?..."
ya tambayi Roshan ne saboda yana ganin shi zaifi bashi amsa akan lokaci,
Roshan yace "gaskiya Uncle banida masaniya akan haka amma ka tambaye shi mana gashi nan, nidai a sanina dashi bai taɓa yin budurwa ba kuma har zuwa yanzu babu wata..."
Kafin ya ƙarasa mai martaba ya dakatar dashi da cewa "ya isa haka Roshan, kowa yasan halin Razhdeen ba kula mata yake ba,
Razhdeen abinda nake so dakai shine za'a haɗa bikinku gaba ɗaya ayi kai da Roshan, tin ba yau ba na rigada na maka matar da zaka Aura tinda kai bazaka iya zaɓo ba...."
ya ƙarasa maganar idonsa akan Razhdeen wanda shima mai martaba yake kallo fuska a murtuƙe ba bu Annuri..
"Who is her?.."
yayi tambayar a taƙaice.
Mai martaba yace "ƙanwar matata Maamie wato Ramlat, tana zaune anan gurin mu..."
girgiza kai Razhdeen yayi zaiyi magana saiga Ramlat ta shugo da sallama a bakinta tana ɗauke da tray ɗin kulolin abinci, ta ajiye akan glass table dake tsakiyar falon, ba jumawa kuwa saiga kuyange su uku sun shugo ko wacce tana ɗauke da tray ɗin kayayyakin abinci aciki,
suna ajiye wa suka fice, Ramlat ce ta zauna a ƙasin carpet tana gaishesu, Roshan ne kawai ya amsa shi kuwa Razhdeen ko kallon yanda take beyi ba, tasha ƙwalliya sosai sai fidda ƙamshin turare take tana satar kallon Roshan,
ita har cikin zuciyarta tafi son Roshan saboda ya kasance mutum mai faram-faram babu ruwansa kuma ko wanne acikin su da kalar tsarin kyan da ALLAH yayi masa, babu wanda yafi wani kyau, sanin dai-dai sai ALLAH.
Mai martaba idonsa akan Razhdeen wanda kansa akan wayar hannunsa yanata pressing ko ɗagowa baiyi ba,
Mai martaba yayi ƙarfin halin cewa "Razhdeen ganan Ramlat wacce ake son haɗa ku, dan Allah ka dubeta da kyau kar ka watsa mana ƙasa a ido, Ni na zaɓa maka ita, ban taɓa neman alfarma a waranka ba sai yau...."
Gira a haɗe Razhdeen ya ɗago cikin ɓacin rai yake kallon Mai martaba murya ciki-ciki yace "Uncle alfarmar mai kake so nayi maka?..."
Mai martaba yace "akan Auran wannan yarinyar..." ya ƙarasa maganar yana nuna Ramlat da yatsa, sannan ya kuma cewa
"Na rigada nayi magana da Abbanku kuma ya amince mun akan wannan batun, mun rigada mun tsayar da maganar rana yata yau Insha ALLAHU za'a ɗaura muku Aure gaba ɗaya, sannan itama Ramlat zata biku can Nigeria ta zauna har zuwa ranar bikin..."
Gaba ɗaya ran Razhdeen ya gama ɓaci har eyes ɗinsa sun kaɗa sunyi jawur, cikin ɗaga murya yace "Umarni ake bani ko kuma Zaɓi?..."
shi kansa Mai martaba sai da ya ɗan tsorita ganin yanda yanayin Razhdeen ya chanza lokaci ƙanƙani,
Roshan ne yayi saurin dafa kafaɗarsa yana ɗan bubbuga shi kaɗan alamar rarrashi domin yasan halin ɗan uwan nashin muddin ransa yakai maƙura toh zai iya yin rashin kunya a kowa ma, kuma gashi suna matuƙar girmama mai martaba,
Razhdeen jin anyi shuru ba'a bashi amsa ba ya kuma cewa "ina tambayarku Umarni kuke bani ko kuma zaɓi?..."
Ramlat dake zaune itama ta gama tsurewa, ƙirjinta ne yake bugu da ƙarfi-ƙarfi domin tana matuƙar tsoron Razhdeen, shiyasa jininsu bai haɗu ba,
Mai martaba shima daƙer ya iya buɗe baki yace "umarni muke baka Razhdeen..."
A ɗan zabure yakai eyes ɗinsa kan Mai martaba tareda faɗin "whattt!? kuna nufin kuce Auren dole?..."
cike da mamaki yake girgiza kai yana cewa "impossible...." ya ƙarasa maganar tareda miƙewa tsare ya nufi hanyar fita,
shima Roshan da sauri ya miƙe yabi bayansa,
shi kam mai martaba ido kawai yabi su dashi, shima har cikin zuciyarsa bason haɗin nan yake ba, zaiyi ne saboda matarsa Maamie amma yasan Razhdeen in har ya bijirewa abu baya taɓa jin ƙira.
kallon Ramlat yayi sannan yace "toh Kinga a gaban ki abinda ya faru, da haka zaki zauna dashi?..."
Ramlat tana kuka tace "Abul wallahi Aunty Maamie ce take son haɗin nan Ni Yaya Roshan nake so, daman nasan Uncle Deen bazai taɓa sona ba..."
Jinjina kai Mai martaba yayi sannan yace "Roshan kuma kinga da matar da zai Aura..."
"Dan ALLAH Abul wallahi inason Yaya Roshan mezai hana ku Aura masa mata biyu Ni da wacce yake son Aura, wallahi zan zauna dashi a haka..."
Mai martaba yace "shikenam kije sai nayi shawara..."
ta tashi jiki ba ƙwari tayi ficewarta,
Shi kuwa Razhdeen niyarsa shine yabar ƙasar gaba ɗaya, daƙer Roshan yake rarrashinsa yana so ya shawo kansa amma fur Razhdeen yaƙi,
sai cewa yake "Please inason komawa Nigeria daga nan zan wuce U.S,
saboda an raina mun wayo Ni za'ayi wa Auren dole? hakan ma wannan kucakar yarinya marar class, a gabana Auntynta take wulaƙanta Uncle amma a haka zan Aure ta? Impossible..."
Roshan riƙe hannayensa yayi yana bashi haƙuri game da cewa "My Man ka kwantar da hankalinka, Insha ALLAHU wannan haɗin bazaiyu ba, saboda Nima kaina yarinyar bata mun ba, sannan ga ɗabi'un Yayarta marasa kyau amma inaso komai ka bishi a hankali, ka dubi darajar Uncle shima kamar mahaifi yake a wurin mu, Uncle ba kamar Abbah bane yanada sauƙin kai, muje ka same shi muyi magana ta fahimta sannan ka nuna masa cewa kanada wacce kake so kaima..."
Daƙer Razhdeen ya haƙura suka koma cikin masarautar, kai tsaye part ɗin da aka tanadar musu suka wuce domin a halin yanzu Razhdeen baya buƙatar yin wata magana ta fahimta...
INDO tana zaune kan sallaya da carbinta a hannu tana lazumi ta fara jin kururuwar Maamie daga Falo sai balbala masifa take,
Dasauri INDO ta tashi a tsorace ta fice domin ganowa abinda ke faruwa,
tana fita Falo ta tarar da mai martaba zaune akan sofa ita kuma tana tsaye a kansa baki ya gagara rufuwa, ga kuma Ramlat itama zaune a one seater ta ɗora hannu akan goshi, gaba ɗaya ta tsani ganin Maamie tana masifa a mai martaba wannan abun kunya,
INDO ce ta ƙaraso wurin tareda faɗin "lafiya kuwa?..."
a fusace Maamie ta kallo yanda take tsaye da zureren hijab ɗinta, ta ɗago yatsa tana nuna ta dashi tace "ki maida hankalinki bada ke nake ba, ina ruwanki da shiga shirgina, tin ba yau ba na gaya miki idan ina magana da mijina ki daina shiga...."
INDO tace "naji hayaniya ne shiyasa na fito naji meke faruwa..."
Maamie cikin tsawa tace "toh babu ruwanki, idan kinji abinda ke faruwan akwai abinda zakiyi ne?..."
INDO ta girgiza kai tareda cewa "a'ah kiyi haƙuri, naga bai dace ki tsaya a kansa kina ɗaga masa murya bane..."
Kafin ta ƙarasa maganar Maamie ta malmalo wata ashar ta maka mata tareda faɗin "kije kiji da wannan tsohon uban nakin da yake gab da mutuwa akan kujerar mulki ya gagara sauƙa saboda kwaɗayin abun duniya..."
INDO tace "kiyi haƙuri abun bai kai ga haka ba..."
Mai martaba ne ya buɗi baki yana cewa "kibi duniya a sannu Maamie..."
Harara ta watsa masa tareda faɗin "Duniya kam gani a cikinta ta ishi kowa ma bani kaɗai ba,
Kuma wallahi kusan yanda zakuyi ku Aura wa Razhdeen Ramlat tin kafin ajiyo kan mu, kana maganar wai tace Roshan take so yooo banda na ga, mai Roshan yake da shi, wanda ko rabin kamo ƙafar Razhdeen baiyi ba a arziƙi..."
Sai a yanzu Ramlat ta buɗi baki tace "nifah Maamie Yaya Roshan nake so...."
Maamie a fusace ta miƙar da hannu tana danƙwalonta tareda faɗin "ke kin ci ubanki, ina samar miki waran da zakiji daɗin rayuwa ki ƙwanta a dukiya ki tashi a dukiya amma ke kina Kai kanki wurin wahala, mai za'ayi da kishiya banda dole, ALLAH ya tsinewa wanda ya ƙirƙiri sunan kishiya babu daɗin ji,
Haka zamu ƙare rayuwar mu a zuwa kan kishiya?
lokacin da mai martaba zaiyi Auran farko mu biyu ya haɗa ya Aura lokaci guda Ni da Maimuna wacce ba'a san duniyar da take ba yanzu, kafin daga baya ya ƙara Auran wannan matsiyaciyar,
shine ke kikeso kema ayi miki irin nawa? kamar wasu marasa gata da farin jini,
toh bazaiyu ba Razhdeen ɗin zaki Aura..."
Mai martaba hannu yasa ya dafe saitin zuciyarsa jin an ambaci sunan da yake tada masa da hankali wato Maimunatu...
Ana cikin wannan halin saiga Razhdeen da Roshan sun shugo falon, duk maganganun da Maamie tayi suna jinta,
Roshan ne yazo har gaban Maamie ya tsaya yana mata kallon ƙurilla daga bisani ya cire glass ɗin kan dara-daran idanuwansa, ya soma magana cikin ɓacin rai yake faɗin
"Alhamdulillah tinda ALLAH ya hore mun abinda zan rufawa kaina asiri, dukiya inada su dai-dain gwargwado kuma fiye da yanda kike tunani, domin da za'a haɗa kanki dana danginku gaba ɗaya bazaiyi kwatan yawan