Showing 6001 words to 9000 words out of 87750 words

Chapter 3 - GUDU DA WAIWAYE bilyn abdull

29 Jun 2024

13335

haskenta gwargwadon iko, sannan Samina ?ya?y?yawace babu laifi.
?ananun burikan Samina sun fara faWaWa, dan yanzu kowane biki saita san yanda ta ?walkwali Ahmad kuWin ankonsa. Ada bata kula kowane saurayi sai Ahmad, amma zuwa yanzu kam ai samari babu iyaka take kulawa, dataga kazo da ?ar kalar manyan mutane babu wani jan aji take mi?a kanta.
Tun Ahmad na zuba mata idanu akan ?ananun sabbin Wabi'unta harya kasa ha?uri ya tuhumeta akan bilicin data fara, ya tabbatar masa shi bama ya ra'ayin farar mace, yafisonta da kalar fatarta choco color, alokaci ha?uri tabasa, ta shirya masa ?aryar ba bilicin baneba, kayan gyaran jikine irin namu na gida take amfani dashi.
Cayay kosu Winne tabar amfani dasu sai sunyi aure ya yarda da ingancinsu.
Ta amsa masa da to, amma tana bama su Nafy labari sai suka zugata akan ai ba aurenta yakeba, taci gaba da abinta, gashinan harta fara zama big girl shine zata wani biye masa, inharfa bazata cire tsoron Ahmad a rantaba to bazata taSa wayewaba ta zama cikakkiyar ?ar jami'a balle shima ta maidoshi kan hanya su shi??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nfiWa ?ya?y?yawan rayuwa irinta jaruman littafi>?&? @&.............
'







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=?-?=?O?



*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*=?O?
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*(3)*

...........Da waWannan shawarwarin dukkan ginin Ahmad ya fara rushewa ga tarbiyyar Samina, ta fara biyema ruWin su Nafy, idonta ya fara buWewa da rayuwa ta manyan yara masu aji, duk wani dandalin wayewa suna wajen matsayin manyan ba?i masu lokaci, wannan damar samarin jami'a ?an ?walisa da lectures suka samu wajen shiga jikin su Samina, sai ga ?a?an manya masu abin magana a aljihu sun fara kutso kai cikin rayuwarsu.
Tunanin Samina ya fara bata cewar lallai Ahmad bazai zama dai-dai da burinta na rayuwar Jaruman novels ba, saboda har lokacin dai ana nan jiya iyau, buga-bugar sana'a ce dai kawai a samu na yau na gobe sai an fita nemansa, suturar kirki wannan ta shiga taro Ahmad bashi da ita, gaba Waya kayan nasa duk yadin (Tashi sama sallau) ne, idan ?ananun kaya ka gansa dasu ma dai na gwanjone ba sabbi ba, ?yawune kawai Ahmad Win zai iya mata burga dashi.
A samarinta kuma na yanzuma akwai waWanda zasu iya linkashi ?yawun, ga kuWi na gaske suna mata wasa dasu, wanda suka fara lulluSe zuciyarta dana mahaifiyarta wajen mance alkairin Ahmad a garesu.
Duk tsiyar da Samina ke aikatawa mama gaje ta sani sarai, kwaWayin abinda Samina ke kawo musu na ciye-ciye ne ya lulluSe idanunta ruf.
Idan cikin samarin Samina wani yace zaizo bata kawoshi gidansu, sai dai ta kaisa can gidan kakanninta da suka haifi mama gaje.
Hakan yasa Ahmad baisan mi Samina ke aikatawa ba, dan bai taSa kawoma ransa zata kula wani saurayi bayan shiba, musamman da yasan akwai al?awarin aure a kansu da ?aunar juna mai ?arfin gaske.


_________________________

A yanzu haka Saminar na gidan kakarsu, taima Ahmad ?arya Inna mari bata da lafiya dan kawai tasamu taje wani bikin ?awarta da za'ayi.
Sai dai tsoron kar wani yakai masa gulma yasata kiransa a waya ta sanar masa cewar zataje wajen kamun bikin ?awarta.
Bai musa mataba ya barta, amma yace ta jirasa yazo da mashin Win Sufyan zai kaita.
Hakan ba ?aramin haushi ya bataba, amma yaya ta iya dashi.

Shiri take da sauri-sauri gudun kar Ahmad yazo ya sameta a gidan...... Dan tafison su tafi tare dasu Nafy, kiran da taji Iya kishiyar kakarta Inna mari na ?wala mata daga waje yasa gabanta faWuwa, tasan dai yanzu haka Ahmad ne yazo.

 Samina!, Samina!!, Wai Samina ba?ya jinane kokuwa lalatar takice ta motsa ne? .
Ta sake jiyo muryar iya daga tsakar gida.
Cikin cuno baki ta fito daga Wakin dake can cikin wani lungu tana gyara Waurin Wankwalinta ture kaga tsiya tana kumbura fuska.
 Kai Iya, irin wannan kira haka saikace na mafarauta, Wan kwalifa nake Waurawa saboda su Nafy zasuzo yanzu mu wuce, mi kuma zan miki? .
Baki iya dake tsaye bakin murhu tana ?okarin hura wuta ta ri?e,  Samina anya wannan rayuwar ta dace dake kuwa? Ba?ya ganin kinason wuce gona da iri? Yanzu nan kodan yaron nan Ahmad ai ?yaWan sassauta wani abun, wlhy kibar biyema lalatattun yarancan su Nafisa karsu kaiki su baro .
Baki Samina ta Wan taSe tana gyara zaman gyalen kafaWarta,  Iya nifa wlhy banajin daWin irin maganganun nan naki, ni mi nakeyi mara ?yau a rayuwata dan ALLAH? .
 Ba nace kina wani abu mara ?yau bane ba Samina, Inason dai ki tsaya matsayinki kodan Yaronnan da ya gama wahalar duniya a kanki, karsuje su hure miki kunne akan Wabi'u mara amfani .
 A'a Atine, anface ka fadi alkairi ko kai shiru, dan Ahmadu yaymata wahala sai akace bazata mori ?uruciyarta ba? Naga ba aure aka Waura musu ba al?awarin auren ne kawai ko? .
Wata dattijuwar tsohuwa mace dake fitowa daga bandaki ta faWa tana ?okarin ajiye butar hannunta.
Su duka kallonta sukayi.
Iya tace,  Amma dai Mari ai kowa yasan dama ALLAH shine yake yanda yaso ga mutum, amma kinsan ta yaro ?yau take bata ?arko, tunda har da al?awarin auren, wataranama Waurawa za'ayi kamar yanda muke fata
 Uhm Atine, mubar wannan batunma dan ALLAH, dan yanzu ba lokacin yinsa bane, ni dai abinda nasani kawai shine bazamuyima yarinya auren doleba, idan tace Ahmad takeso zamu bata, idanko ta kawo waninsa shima zamu bata .
 Hakane Mari .
Iya ta faWa tana Wauke kanta daga garesu ta koma ?o?arin hura wutar data fara.
Daga Samina har inna Mari kakarta harar Iya dake duke sukayi.
Samina ta maida kallonta ga kakar tata tana murmushi,  inna mari bara naje karsu Nafy suyita jirana, kinsan za'a fara kamun ?arfe uku na yammane .
 To Samina ALLAH ya tsare, a dai dunga kula saboda ?an saka ido, kana rayuwarka baka damu da kowaba saikiga anata ?okarin taWo ?afarka da harshe, bayan ko MANZON ALLAH ma yace mu kiyayi harsunanmu .
 Humm Inna ai mutanen duniya ba'a iya musu, sunfi son kullum su ganka jiya iyau, kuma idan arzi?in kayi sune zasu fara zakalkalewar kai nasune .
 Maganarki na kan hanya wlhy ?ar albarka, kedai jeki karki makara .
 Okey my sweet kakus bye .
 Duk da ban iya turancinba Samina, nima bye .
Ficewa Samina tayi tana dariyar zancen kakar tata.
Itama inna mari ta shige Wakinta tana ?yalkyata dariyar sake ?ular da kishiyarta iya Atine.
Murmushi kawai Iya tayi, tasan duk ita akema habaicin, ta girgiza kanta tana nemawa abokiyar zaman nata da jikarta shiriyar ALLAH, tare da fatan ganewa kafin guri ya ?ure musu.

Kamar an saita Samina na fitowa daga ?ozajjen soron gidan kakanninta da Ahmad ta fara cin karo zaune bisa Wan dandamalin dakalin dake ?ofar gidan ma?wafcinsu.
Ta tsaya tsam tana ?arema kwalliyarsa kallo, tabbas Ahmad ?ya?ykyawane, shiyyasa duk rashin tsadar kaya sukan zauna masa a ?ya?y?yawar surarsa suyi Was.
Ba wani kayane mai tsada a jikinsaba, hularsa ?ube da ita kaWai ta iya saninsa dashi ta ?arshen gayunsa ya saka, ta zauna Was akansa, inda daga bayan ?eyarsa kwantacciyar sumarsa ta jinin fulanin rumawan asalin katsinawa ta bayyana, sai yadi mai ?arancin kuWi mai kama dana ?an makaranta kalar ruwan shanshan bale, takalmansa ?an sa?e suma masu ?arancin kuWi, sai agogon fatar da itace ta saya masashi naira Wari huWu Waure a hannunsa da zoben azurfa a yatsansa, kayan sun Wauki guga, dan haka suka kwanta luff tare da Soyewar tsufan da suka fara a idon mai kallonsa, ?amshin turarensa yake mai ?arancin kuWi, amma akwai daWi ga hancin mai sha?a.
Ganinta ya sakashi mi?ewa yana ?awata nutsatstsiyar fuskarsa da murmushi na musamman.
 Barka da fitowa tauraruwar mata ma'abociyar haske da walwali .
Samina ta kallesa a wani yatsine tana cuna baki gaba, ba tare data amsa masa kalmomin yabonsa ba ta maida murtani da faWin,  Kai yaya, dama zakazo Win amma kaki kirana ka sanarmin kuma? Gashi nacema su Nafy su jirani a gidansu saimu tafi tare .
Murmushi yaWanyi duk da yanda tai masan ya bashi mamaki,  Yi ha?uri Samie na, banzo danna hanaki ?yautata zaman tareba, nazone dama na kaiki basai kinsha wahalar jiran abin hawaba .
Yanzu kam sosai ta juyi ta kallesa, cikin waro masa manyan idanunta tace,  Ka kaini kuma yah Ahmad? Da wane motan? .
Huci yaWan fidda mai Waci, dan ta fara ?okarin janyo fusatarsa da wannan salon rainin wayon data Wakko, amma kasancewarsa sonta na Wawainiya dashi saiya sauke numfashi da ?okarin hadiye dukkan fusatar tasa ya saki murmushi a karo na babu adadi.
 Banda abunki Samina ina naga mota, wannanma mashin Win Sufiyanu ne na aro danna sau?a?a miki wahala .
 Tofa, to ALLAH yay mana maganinta ita wahalar, karka damu na hutar dakai, kaje kawai zamu tafine dasu Nafyn tunda kaga na musu al?awarin binsu dan ALLAH .
Wani irin bugawa yaji zuciyarsa tayi, sam baya ?aunar alakar Samina da su Nafyn gidan Wan-majillisa, amma ya kula yanzu dukkan hankalinta yana ga mu'amulantarsu. Ganin zata tafi yay saurin tsaidata ta hanyar faWin,
 Okey to babu damuwa tunda kin samu abokan tafiya, ga wannan kozaki bu?aci wani abu a wajen .
Har tayi niyyar wucewarta saita dawo baya jin ya ambaci kuWi, babu kunya tazo ta amshe kuWin dayake mi?omata canzazzu ?an hamsin-hamsin rabin bandir Waya.
Godiya tai masa cikin ladabi, ta tura kuWin a jakarta tare da sakar masa murmushi duk dan dai hankalinsa ya kwanta da barinta ta wuce ita kaWai.
Ta Waga masa yatsun hannunta guda biyu alamar bye cike da wani salo.

Da kallo kawai ya iya binta tamkar wani soko, ya sauke ?aramar ajiyar zuciya yana nufar roba-roba mashin Win dayazo dashi kalar jaa, hawa kawai yay ya zauna yana kallonta harta Sacema ganinsa, yanda take tafiyarta cikin yau?i da yanga sai sonta ya kuma nunkuwa a ransa, yanason Samina so irin mai tsanani Winnan, dankuwa dashi ya girma a zuciya tun baima gama sanin ma'anar SO Winba.
Ya Wauki kusan mintuna talatin a wajen kafin ya hau mashin Win yabar anguwar da tunanin ina ya dace ace yaje, dan shidai a yanzu ya koma majalisar abokansa dariya zasuyi masa, yanda ya fito yana Sare-Saren jiki zaije yakai Samina, sai gashi Samina ta watsa masa ?asa a ido, bayan kuma dama kullum abokansa na nuna masa yanzu Samina ta canja, ta fara fin ?arfinsa amma sam ya?i fahimtarsu balle ya yarda da batunsu.
Yawo yaytayi a gari, sai da ya fahimci man ciki yayi ?asa kafin ya koma gida.
Ya iske abokansa na hada-hadar shiga sallar magriba a massallaci, dan haka shima yay haramar yin alwala domin samun jam'i.
Bayan an idar duk suka fito Wai-Wai zuwa majalisarsu da suka kafa a ?ofar gidan su Yakubu abokinsu, saboda baranda dake wajen, shikuma yakubu yanada shagon littatafan hausane da yake bada rancin da saidawa.
Hannu suka shiga bama juna suna gaisuwa, Ahmad ya mi?ama Sufyanu key Win mashin Win yana faWin,  Broth nagode, ALLAH ya bada ladan zuminci .
Amin suka faWa a tare, yayinda Sufiyanu dake amsar key Win ke faWin Sharukhan Winmu nazata fa sai dare zamu ganka ALLAH, Amma kunyi saurin dawowa kaida gimbiyar taka .
Murmushin ya?e Ahmad yayi kawai, ya kishingiWa kusa da Musa yana bama Sufiyanu amsa da,  Ai ba yaune ainahin bikinba fa, kamu sukayi yau shiyyasa, sai jibinema Waurin auren, kasan mata da shegen son bidi'a, shiyyasa a kullum ake ?ara nisanta talaka da samun aure cikin sau?i .
Cikin damuwa Rabilu yace,  Maganarka gaskiyane wlhy Ahmad, ba gamunanba, acikinmu nan wanene bai isa aurenba, kuma duk munada ?ammata amma babu kuWin yin auren, to wai muma fa kenan dakeda sana'oi munkuma Wanyi karatun, inaga waWanda basuda sana'ar babu karatun kumafa .
Salisu daya zabga tagumi ya wani marairaice fuska yana harWe kafafunsa dake lilo a ?asan benci,  Abokai wlhy bidi'oin biki suna taka rawar gani wajen Wora mata a burin auren mai hannu da shuni, tana kuma jefa rayuwarsu a garari harma da ?ara yawaitar fyaWe, yanzu irina masu ?arfin sha'awa idan baka danne zuciyarkaba ai tuni zaka afkama ?ar wani ka jefa kanka a halaka da ?an uwanka a damuwa ko .
Lumshe idanu Ahmad yayi a hankali, dan maganar Salisu ta sosa masa inda ke masa ?aikayi, yace  Uhumm kawai ba tare da ya ?ara komaiba.
Hakane ya saka Sufiyanu da Yakubu dake kusa dashi kallonsa.
 Sharukhan yaya dai? .
Ameenu da tun Wazun baice komaiba ya faWa yana kallon Ahmad Win shima.
BuWe ido Ahmad yay da suka canja launi zuwa jaa, yay murmushi kawai yana girgiza kansa.
Hakanne yasaka su cigaba da hirarsu akan matsalolin aure da burikan da mazan da ?ammata ke dorawa saboda son gasa da masu kuWi keyi lokacin bikinsu.

Sallar isha'ice ta tadasu a majalissar, dukansu suka dunguma zuwa massalaci, akabar waWanda zasu sake alwala irinsu Ahmad.
Bayan sun idar da salla zama sukai islamiyyar da suka tsarama kansu kamar yadda suka saba a kowanne dare, malam Sulaiman ne malaminsu, wato limamin massalacin, bayan ?arin karatu yay musu nasiha kamar yanda ya saba.
?arfe tara da rabi dai-dai suka fito, kowa daga nan gida ya shiga domin cin abinci.

Tsakanin gidansu Ahmad da majalissarsu gida biyar ne, hakan yasakashi takawa a hankali suna tafiya shida Salisu da shima gidansu ke ma?waftaka da nasu Ahmad, suna isowa kowa ya shige.

Gidansu Ahmad gidane na talakawa irin masu ?aramin ?arfinnan sosai kamar yanda kukaji tun a farkon labarin, ginine irin na zamanin daya shuWe, duk da dai yana mulmule da suminti har jikin bango, amma kallo Waya zakaima gidan ka fahimci ingantaccen ginin daya samune yasaka sumintin daWewa bai zabtareba, saika shiga soro biyu kafin ka iso ainahin tsakar gidansu, amma a shiga farkon gidan zakaci karo da turken awakine da mahaifansu mata ke kiwo, sai kejin kaji daga gefe wanda baida nisa sosai da ?ofar banWakinsu.
A shiga farkon gidan Wakunan kakanninsu da aka zagaye da katanga zaka fara iskewa, sai sashen Baba Iliyasu daga bangon gabas, sai sashen Baba Yusha'u mahaifin Samina daga can Bangon arewa, suna kallon sashin kakanninsu, sai sashen iyayen Ahmad a bangon yamma suna kallon sashensu baba Iliyasu.
Tsakar gida zaka fara tararwa, sannan kabi siririyar hanyar da zata sadaka da ainahin sashen da matan Baba Hamza mahaifin su Ahmad suke.
Ya shafa kan tunkiyar daketa Sara kuka saboda rashin ganin Wanta kusa da ita,  K dan ALLAH ki rage ihunan, tunkiyarnan sam baki da hankali akan ?a?a, inama ya shiga shima uban Sarnar Ahmad ya ?are maganar yana le?a ?asan kejin kajinsu kozai gano Wan jaririn ragon tunkiyar.
Can kuwa ya hangoshi kwance, dan haka yasa hannu ya za?ulosa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login