Showing 21001 words to 24000 words out of 87750 words

Chapter 8 - GUDU DA WAIWAYE bilyn abdull

29 Jun 2024

13333

data siyoma Mama gaje tana faWin,  Babu komai mama, Yah Ahmad ne baida lafiya .
Shiru Mama gaje tayi bata tankaba.
Kishiyar mama gaje mahaifiyar Umm-Rumana da suke kira da Amma na daga bakin murhu tana haWa wuta, tana jin uwar da ?ar, sai dai batayi ko tariba, saboda tun a daren jiya ta jiyo kalaman Mama gaje akan Ahmad tasan akwai matsala, dan agaban idonta Samina ta shigo da ledoji ni?i-ni?i a hannu, daga baya ta jiyo murnar da Mama gajen takeyi daga cikin Waki, har tana kushe ?okarin Ahmad duk da wahalar dayay da Samina a baya, koma yake kanyi har yanzun.

Saminar ma batace komaiba ta juya ta zata fita, da sauri mama gaje tace,  Ina kuma zakije? Bayan nace ki wanke min zanin gadoncan dana ji?a tun jiya .
 Mama ina zuwa Samina ta faWa ba tare da ta saurari mamar tataba ta fice da hanzari.

Kanta tsaye sashen su Ahmad ta nufa, ta iske Gwaggo a tsakar gidan tanata aikinta na abinci, sai Sadiya dake taimaka mata da wasu ayyukan.
Gaisheta tayi, Gwaggo ta amsa da fara'a tana tambayarta yaushe ta dawo?.
FaWa mata tayi jiya cikin jin nauyinta, Sadiya dake dariya ganin yanda Gwaggo da Samina kejin nauyin juna itama ta gaisheta.
KafarWarta Samina taWan buga tana faWin,  Baki da kunya yarinyarnan, ina Yah Ahmad yake? Koya koma Wakinsu? .
 A'a yana Wakin Ayyah, sun tsareshi ita da Iya yana shan magani, kinsan maigidan naki da magani tamkar jariri yake .
Dariya kawai Samina tayi, saboda Gwaggo dake a wajen bata iya bama Sadiya amsaba..

Samina ta le?a Wakinsu Sadiya, dan taga takalman Fa'iza, ciki ta shiga da sallama, Umm-Rumana da Fa'iza dake Assignment na islamiyya duk suka kalleta.
Da yake ta girmesu, kuma suna kallonta matsayin wadda yayansu zai aura sai suke bata girma sosai, gaisheta sukai, ta amsa tana Sata fuska saboda ganin Rumana a wajen, dan mahaifiyarsu ta riga ta cusa musu ?in kannenn nasu da suke uba Waya sosai.
Umm-Rumana ma saita maida hankalinta ga Assignment Win bata saka musu baki cikin hirarsu, dan tasan ?aramin aikin Samina ne ta ci mata mutunci yanzun nan.
A gabanta Samina taja Fa'iza suka fita, danta rakata Wakin Ayyah ta duba Ahmad.
Batai yunkurin binsuba, dukda tanason taje tai masa sannu itama.

Sun shiga Wakin da sallama, Ayyah na tsaye akan Ahmad ita da Iya kakarsu suna lallaSashi yasha magani, sai kumbura fuska yake tamkar zaiyi kuka.
Iya ta dungure masa kai tana faWin,  Ragon kawai, ni nama taSa ganin namiji na tsoron magani inba kai ba Amadu .
Sake tsuke fuska yayi yana langabe kai gefe idonsa akan Ayyah dan taji tausayinsa.......
Ayyah zatai magana cikin son yin dariya su Samina sukai sallama, koda suka shigo bai kallesu ba, sai Iya ce tace,  To ai yanzu kasha tunda ga matarka nan ko .
Bai tanka ba, sai ruwan dake hannun iya ya amsa tare da watsa sauran maganin hannunsa cikin baki ya matse ido yana tuttula ruwa a baki ya haWiye da ?yar.
Yana gama shanyewa kwanciyarsa yayi a gadon Ayyah na karfe yayma kowa banza.
A hakane su Samina sukai masa sannu da jiki, takuma ?ara fahimtar fushi yakeyi da itane da gaske.
Duk kuma sai taji babu daWi, jikinta yay sanyi sosai, gwiwarta a sanyaye ta fito ta koma Sangarensu.


_______________________________

Wasa-wasa dai sai da ciwo yaja Ahmad kusan kwana uku, dan daga ciwon kai abu sai ya koma zazzaSi, har saida yasha ledar ruwa biyu, kullum sai Samina tazo gaishesa, amma baya kulata sam.
A yaran gidan duk wanda sukazo gaisheshi yana amsa musu koda a gabantane, amma ita sai baya kulata.
Duk da abin na mata ciwo sai ta daure ta faWama Sufyan halin da ake ciki, Sufyan bai tsaya mata rufa-rufa ba ya sanar mata ganin da sukai mata a ?ofar gidan su Inna mari, harma ya nuna mata video din daya Wauka dan yaga tana neman musa cewar itace.
La?was jikinta yayi, nanfa ta shiga haWo ?arya ta shirya masa akan ita bata da ala?a da Ma'aruff, saurayin ?awartane Nafy, tayi kuskure amma ya bama Ahmad hakuri akan shiga motar ma'aruff Win da tayi.
Dole dai akan wannan magana sai da Sufyan yasaka su zama su uku ya sasantasu, Samina harda kukanta tana bama Ahmad hakuri.
Daga baya bayan masifar da taci a wajensa yace ya hakura.

Tun daga ranar komai ya sake koma musu kamar da, suka cigaba da tattali da soyayyar junansu, yayinda a Soye Samina take tare da Ma'aruff, idan yaso su haWu gidansu Inna mari take zuwa su haWu a can.


&&&&&&

?angaren yaya Maryam kam babu wanda yasan miya faru, sai ga mijinta har gida yazo yana bama su Baba hakuri akan abinda yake mata, sannan itama ya bata ha?uri da neman afuwarta.

Babu irin tambayar da Ayyah bataima Ahmad ba akan ya sukayi da mijin Maryam Win, amma ya?i faWa, yace shi babu komai.
?yalesa Ayyah tayi kawai badan ta yarda ba, amma ta fahimci koma minene shine ya aikatashi, kuma ko Maryam Winma bata san asalin miya kawo gyara a cikin lamarin auren nata daya nema hargitsewa ba a shekarunnan..

Matsaloli sun sake kunno kai tsakanin Samina da Ahmad, dan ta sake birkice masa ya rasa kanta.
Gashi yanzu abubuwa yake gani a wajenta wanda bashine ya siya mata ba, yasan kuma iyayensu basu da ?arfin saya matan, dan har waya ta canja, tun tana Soye masa har komai ya fito ya ganta da wayar.
Duk iya tuhumar da yay mata kuma ta?i sanar masa gaskiya.
Abinda ke ?ara tada masa hankali kuma da ita sam yanzu batajin shakkarsa balle akai ga tsoro, ?iri da muzu take masa rashin kunya idan yay mata faWa akan kuskure.
Dan akan wayar nan daya gani a hannunta sosai rikici ya Sarke a tsakaninsu har takaisu ga zuwa gaban kakanni, saboda maganar taje wajen iyayensu mata, sukuma suka gumtsawa mazan, daga nan ne kuma su iya sukaji suma, malam Rabi'u kuma ya kira Ahmad Win da Samina domin yaji gaskiyar maganar.
Da farko Samina ta musa, amma da taga babanta na neman dukanta a wajen saita faWi gaskiya.
Ran kowa ya Saci ranar a gidan, dan haka take a wajen malam Rabi'u tsoho mai ran ?arfe ya tsaida watan bikin Ahmad da Samina, a cewarsa ko haya gwara a kama musu su fara zama kafin ALLAH ya hore asan abinyi.
Kowa yaji daWin yanke hukuncin da Malam yayi, dan kuwa kusa aka saka bikin, wata biyu kacal, lokacin Samina ta gama exam Winta, a cewar malam taje gidan mijinta ta ?arasa karatun, tunda dama shine ya nace akan sai tayi
Wannan abu ya mugun tada hankalin mama gaje da Samina, dan zuwa yanzu dai gaba Waya tunaninsu ya karkatane ga Ma'aruff dake kashema Samina kuWi tamkar baisan ciwonsu ba.
Ahmad kuwa ji yake kamar an masa rahama, dan sakayau ya jisa, shi kansa dama a bu?ace yake da auren ainun, saboda muguwar sha'awar da ya fahimci yana da ita akan abokiyar halittarsa............
'

_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* =؋?d'?NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* =؋?d'?NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* =؋?d'?SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* =؋?d'?NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* d'?=؋?NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN=?G?=?G?_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin=?G?=?G?
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*=?G?=?G?

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuWi gida masoyan asali=? ?=?;?>?p?>?p?=?
?=?
?=??=??=?L?

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN=??=?I?








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=?-?=?O?
07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*=?O?
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


*(8)*

............Sosai hankalin mama gaje da Samina yake a tashe, tunda suka baro sashen su Baba Rabi'u sai suka kasa zaune suka kasa tsaye.
Samina da ke share hawaye tace,  Wlhy mama bana sonshi yanzu, kinajifa wai Wakin haya Waya za'a kama a ajiyeni kafin komai ya warware? Har sai yaushene komai Win zai warware a garesu baki Waya, tunda muka dawo rayuwar gidannan a talakawansu muka iskesu, shekara kusan goma sha takwas basuyi arzi?iba sai yanzu da za'a cuceni za'ace zaizo, wlhy nama kula danginmu ?ashin tsiyane dasu, shiyyasa duk wanda sukaga ALLAH zai Waukaka sai su nema dakushesa, kaf yaran gidannan da sukai aure tunda kan su yaya Maryam har zuwa su yaya Binta waccece ba'a cikin wahalar rayuwaba?, kowacce matsalolin fatara da babu sun gama isar rayuwarta, duk sun lalace sun zama wasu tsofaffi sa'anninku, babu wata mai gidan nunama sa'a a cikinsu. Mama kinga kuwa gidan Ma'aruff inda zai ajiyeni, wlhy ko za'a haWa kaf dukiyar ahalinmu bazata sayi wannan gidanba, na rantse da ALLAH ko sama da ?asa zata haWe bazan zauna da Ahmad ba, inba hakaba kuwa ALLAH guduwa zanyi daga gidannan......
 Ki gudu ina? Babu inda zakije yarinyata, dolene ko sunaso ko basaso su baki wanda kikeso, dan koni ban amince ki rayu da Ahmad ba, yaron da ko rigar sakawa ta kirki baida ita, ki kwantar da hankalinki duk nasan maganinsu, ni warkice dai-dai da ?ugun kowanne shege wlhy, iyakaci dai suce ya miki wahala ko? To su faWi duk abinda yay miki za'a biyashi, dan sune matsiyata .
Samina dake shashshekar kuka tace,  Yo mama dukkan wahalarma da yaymin Win ta nawace? Wlhy nasan ko Ma'aruff yaji saiya ninka masa ma abinda ya kashemin Win .
Tsaki mai ?arfi Mama Gaje ta ja tana yin ?wafa, ji take a ranta koda aurenta zai sake mutuwa bazata yarda Samina ta auri Ahmad ba, dan tasan ko barin gidannan tayi akan auren Samina da Ma'aruff gaba zataci ba bayaba, tunda da dai zasu ji?e da naira ne.

Duk surutan da Mama Gaje keyi ita da Samina a kunnen Baba Yusha'u ne dake alwala a tsakar gida, amma sai ya nuna tamkarma bai jiba, ya ajiye butar hannunsa ya fita.
Ammi ma duk a kunnenta komai ya faru, amma saitayi kamar batasan anaiba, da dai ita ba kishiyar uwa bace data basu shawara akan suyi ha?uri kar son zuciya ya kwashesu suyi GUDU DA WAIWAYE.......

A tsaitsaye Baba Yusha'u ya shiga sashen iyayensa shi da baba Iliyasu, sun Wanyi magana suka fito a tare ri?e da malam Rabi'u zuwa massalaci, inda acan suka iske baba Hamza ma, yayi mamakin ganin Malam a massalaci yau, dan sam baya iyawa, yakai kusan wata huWu ma ko waje bai le?oba, dan ya tsufa sosai.
Salla aka tayar, bayan an idar mutane na niyyar fita Malam Rabi'u ya saka baba liman ro?on alfarmar su dakata.
Babu musu akaita dawowa, ciki kuwa harda Ahmad da abokansa, shima yayi mamakin ganin kakan nasu a masallaci, jira yake kawai su fito ya tambaya.
Mamaki ya sake kamashi jin liman ya ambaci cewar Malam ne yace jama'a suyi masa alfarmar tsayawa.
Abu tamkar daga sama yaji ana Waura aurensa da Saminar sa, mutuwar zaune yayi a wajen, duk taSashin da abokansa sukeyi na alamar tambaya da taya murna bai iya kula kowaba, bayan an kammala Waurin auren jama'a suka shiga zuwa bashi hannu suna tayashi murna, hannun kawai yake iya mi?a musu yana amsawa da amin a saman laSSa, amma a zahirin gaskiya baya tare da duniyarsu sam.

Falalu ?anin Samina da suke uba Waya, wato Wan Wakin su Umm-Rumana ne ya shiga gidansu da zancen Waurin auren.
Babu shiri Samina dake ban Waki tana wanka tajawo zani ba tare data Wauraye kumfar jikinta ba ta fito kamar wata taSaSSiya tana faWin,  Kai Falalu ubanmi naji kake cewa? .
Yaron yaWansha jinin jikinsa, hakanne ya sakashi haWiye murnar da yakeyi yana komawa bayan Amminsu ya Suya, Samina ta daka masa tsawa tana sake tambayarsa abinda ya faWa.
A dai-dai lokaccinne Mama gaje tayo waje itama daga Waki, dan da salla takeyi, saboda sauri har tuntuSe tayi, kaWan ya ragema ta faWi ta dai samu ta ri?e ?arfen barandarsu.
Falalu dake a laSe bayan Ammi da tai tsayuwar sojan badakkare yace,  Ai dai malam ne ya Waura miki aure da Yah Ahmad yanzu a massalac.......
Wani ihu Samina ta kurma tana buga tsalle ta dire ?asa, sai gata wanwar a sume zani a gefe.
Jikin Umm-Rumana na rawa taja Zanin gadon Ammi dake a kan igiyar shanya ta yafama Samina saboda tsirara take.
A lokacinne kuma iyayensu maza duk suka shigo, harma dasu Ayyah da matan Baba Iliyasu, dan casuke wani abunne ya faru da Saminar.
Ahmad ma da Mudanseer sai gasu sun shigo, nanfa kowa ya rufu akan Samina, yayinda Mama Gaje keta kuka akan bazata yardaba idan ?arta ta mutu, tunda tace batason auren miyyasa zasuyi?.
Kalaman mama gaje sun fahimtar da kowa daga ina matsalar take, hakan yasa Gwaggo zare jikinta tabar sashen ganin an zubama Samina ruwa ta kawo numfashi.
Samina dake hawaye ta fara sakin sambatu,  Wlhy kozaku haWa wuta ku sakani bazan zauna da Ahmad ba, nace bana sonshi, na rantse da ALLAH sai ya sakeni, inba hakaba kasheshi zanyi, wlhy saina yankashi da wu?a idan kuka matsa saina zauna dashi, randa aka kaini a ranar zan kashesa, garama na ?are rayuwata a prison da na zauna zaman aure dashi .
Da sauri Baba Yusha'u ya buge bakin Samina, ya kuma kai hannu zai doketa Baba Hamza ya ri?e hannun yana girgiza masa kai.
Daga ?arshema sai yaja hannunsa suka fice, baba Iliyasu na biye dasu.
Mudanseer da zuciya tazo masa kusa ya nuna Samina yana zagi,  Banza kawai mara tunani, to dan uwarki saiki tashi ki kashesa ga shinan, butulu kawai mai manta alkairi, kwaWayayya mara tarbiyya, idan kika kuma zagin Yah Ahmad a wajennan wlhy kafin ki kasheshin ni saina kasheki dan uwark.......
Jan Hannun Mudanseer Ayyah tayi tana share hawaye,  Kaga ya isa haka Mudanseer, idan ita bata da hankali kaima baka da shine? Kunga ku wuce muje tai maganar tana jan Hannun Ahmad dake tsaye kawai yana kallon kowa kamar ya samu TV.

Koda suka koma sashensu ma zama kawai yay ya dukar da kansa ?asa yana kallon sumintin ?ofar Wakin iyayen nasa, yayinda Mudanseer da Abu keta zage-zage Fa'iza da Zainab na tayasu, Sadiya ko tanada sanyin hali tamkar su Ahmad, sai tayi shiru kawai tana share hawaye.
Gwaggo kuwa ai saikama rantse batasan mi ake yi a gidanba, sai aikinta take kamar komai bai dameta ba, nanko jin zuciyarta kawai take tana tsitstsinkewa kamar zata faWo ?asa dan damuwa.

Cikin lokaci ?an?ani gidan ya harzi?e, dan bakin Samina bai mutuba sai da baba Iliyasu ya lakaWa mata dukan kawo wu?a, tai tiSis Win da ko yatsa bata iya Wagawa.
Mama gaje kuwa ta fasa kuka da kururuwar za'a kashe mata ?a.
Kafin kace kwabo labari ya fara fitowa a anguwa, dan duk ma?wafta najin abinda ke faruwa.



________________________________

Yanda Samina ke ambaton ?iyyar Ahmad a bakinta abun na bama kowa mamaki, duk da dai an fahimci harda ruWin ?yale-?yalen duniya ke kwasarta, amma tabbas akwai zuga dake aiki akanta, bakuma kowa bane ke zugata sai mahaifiyarta Mama gaje, saiko Inna mari kakarta da itama tai Ware-Ware a zancen, gefe kuma gasu Nafy sunayi ta waya da zahiri idan sunzo gidan da ?aryar dubata.
Dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login