Showing 36001 words to 39000 words out of 87750 words

Chapter 13 - GUDU DA WAIWAYE bilyn abdull

29 Jun 2024

13344

 Yi ha?uri to zan tsaya ALLAH kuwa Zainab ta bama Gwaggo amsa.
Ahmad dake kallonsu baice komaiba ya lumshe idanu yana cewa  Ina kwana? .
Amsawa Gwaggo tayi kamar yanda ta saba masa, sai dai ta tambayi yaya jikinsa da Rumana?.
Yaji daWi sosai, ya amsa mata murya a raunane.
Ita dai sharesa tayi, duk da kuwa Wunbin tausayinsa da ga shi har Rumanar nacin ranta.
Shiru babu wanda ya sake tankama wani, har Gwaggo ta gama cirema Zainab ha?orin makka data sa ya ma?ale ya?i fita, tashi yay ya fito da ga Wakin yaje Wakin Ayyah suka gaisa itama.
Sai jero masa tambayoyi take akan jikinsa, yay murmushi saboda ganin yanda damuwa ke kwance a fuskarta, kwanciya yay a gadonta dan wani sabon zazzaSi yakeji.
Ayyah dake kallonsa ta Wora hannunta saman goshinsa tana faWin,  ?an albarka wani zazzaSinne fa? Anya kasha magungunanka? .
A hankali yace,  Nasha Ayyah, bani bargo sanyi nakeji .
Babu musu ta Wakko Bargo ta rufa masa, ahaka barci yay awon gaba dashi.

Sai da aka kira sallar zuhur Ayyah ta tashesa dan yayi salla, yay alwala ya fito shi da Mudanseer, a soron gidan sukaci karo da Samina taci kwalliya zata fita, kallo Waya yaymata ya Wauke idonsa, hakan yasa taja siririn tsaki.
Kasa jurewa Mudan yayi yay saurin kallonta yana cewa,  K da ubanwa kike? .
Baki ta taSe tana tauna cingam yay ?ara ?as-?as tai fari da idanu,  Da wanda ya tsargu man....
Bata kai ?arsheba ya sauke mata mari, zai ?ara na biyu Ahmad daya juyo ya kallesu ya dakatar dashi da faWin,  Kai wuce muje mana .
Samina kuwa sai ta fashe da kuka dafe da kunci, da gudu ta juya cikin gida tana kwalama mama gaje kira.

Ahmad sun dawo salla suka iske marin da Mudan yayma Samina ya zama Hayaniya a gidan, dan kuwa mama gaje hannun Samina ta kamo har sashen su Ahmad akan bazata yarda ba, wai Ahmad yasa Mudan ya daki Samina.
Gwaggo uffan bata ceba, sai Inna Asma'u ce ta tanka, sai ko Ayyah data idar da salla itama ta fito ta taya inna Asma'u, nanko abu ya zama hayaniya Mama gaje nata daddatsa magana wa jama'ar gidan, har Malam da Iya bata bariba, Ammin Rumana kam ai tafi kowa shan Zagi da su Ayyah.
Ahmad ya raSa ta gefensu ya shige Wakin Ayyah ya sake kwanciyarsa, ko kallon Waya a cikinsu baiyiba.
Hakan da yayi ba ?aramin ciwo yayma mama Gaje da Samina ba, dan sunso ya tanka su hau kansa.
Mudanseer kam cayay inhar Samina bata bar sashenba wlhy dukan mutuwa zai lakaWa mata, abinda ya ?ara rura hayaniyar kenan, Gashi su baba basa nan, sai da Iya ta shigo tai magana su Ayyah sukai shiru, Mama Gage kam ai kamar tunzurata akayi, taita zuba tsiya har sai da ta gaji tai shiru dan kanta............
'





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=?-?=?O?
07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*=?O?
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*(13)*



..............Koda Ayyah ta shigo Waki nasiha tai tayima Ahmad akan wannan sabon lamari da ya shigo musu cikin gida.
Ahmad dake jin zazzaSi yace,  Karki damu Ayyah, ni wlhy abunsu bai damuna, dan ALLAH kuma kubar biye musu, shima Mudan Win zan masa magana yabar shiga harkarta, tunda bata da kunya, duk yanda yake tunanin da da yanzu akwai banbanci .
 Humm su dai suka banbanta da son zuciyarsu Wan albarka, indai duniya ce kuma gasu gata nan, wanda ma bai zoba jiransa takeyi, wanda kuma duk yasai rariya yasan zata zubda ruwa, ni lalacewar wannan aurenma tsakaninka da yarinyarnan alkairine, dan kuwa na lura duk halin uwarsu ta kwashe, kuzo ku haihu kanaji kana gani ?a?anku su tashi ba tarbiyya, yanzu kuwa ALLAH yay maka sauyin alkairi, gidannan kaf babu mai cewa ga halin Umm-Rumana na banza, hakama uwarta, duk fitinar Gaje tayi ta barta, tunda ita dai ba tanka mata zataiba saboda ha?uri da kawaicin da ALLAH yay mata, dan haka ka kwantar da hankalinka akan yarinyarnan, insha ALLAHU wataran sai kace gwamma da akai hakan .
Idon Ahmad a lumshe duk yana jiyo nasihar Ayyahn sa, wannan itace shawarar da kowa ke bashi, tare da faWin gamma da akai, shidai jinsu kawai yakeyi, dan bazasu gane yanda Samina ta mallake dukkan zuciyarsa bane, yasan kozai shekara kwatanta musu irin mugun sonta da yayma zuciyarsa dabai bayi ba fahimta zasuyiba, gaskiya so bai masa adalciba, da yasan a haka wannan soyayyar tasu zata ?are da ya ro?i ALLAH mutuwa kafin wannan lokacin, kawai dauriya ya keyi, dan mutane karsu kallesa mara zuciya ne kawai, amma ko yanzu Samina ta yarda zata zauna dashi zai saki Umm-Rumana ya sake auren Saminar.


Humm, tur?ashi Ahmad, lallai zuciya batai maka adalciba kam.


_________________________


Anayin Sallar la'asar Ayyah tacema Ahmad ya tafi gida ya kwanta, dan su Fa'iza ma sun dawo anbar Rumana ita kaWai.
Badan ya soba ya fita Sufyan ya kaisa gida yauma a mashin Win.
Rumana na sharar Wakin Ahmad ya shigo.
Yanda ya shigo kawai yasata gane babu lafiya.
Matsawa tai gefe ya shigo, tai masa sannu.
Hannu kawai ya iya Waga mata ya haye saman gado hannunsa dafe da kansa ya kwanta.
Cikin damuwa ta kwashe sharar data tattara a ?ofar Waki, taje ta zubar ta dawo.
Ya lulluSe har kansa da bargo, hakan yasa ta zauna ta zuba tagumi kawai tana kallonsa, tausayinsa na sake kamata...
A wannan halin tajiyo sallamar Sufyan, le?owa tai suka gaisa, yace mata yazone da likitan da zai duba Ahmad.
Izinin shigowa ta basu, koda suka shiga saita fito ?ofar Wakin ta basu waje.
Zuwa wasu mintuna Sufyan ya le?o ya kirata, shiga tai Wakin, saita iske za'a Waurama Ahmad Win ?arin ruwane ashe, ?usa suke nema da zasu rataya ledar ruwan.
 Aiko Yah Sufyan babu ?usa a Wakinnan, amma bara na tambayi maman Ama... Ko za'a samu .
Har zata fito Sufyan yace,  Kinga bartama, bara mugwada ko tsahon zaikai jikin mirror Winan .
Gwadawa sukai sai sukaga yama kai, hakan yasa suka ratayeshi acan, sai da ya fara shiga jikinsa komai yay dai-dai sannan suka fice bayan likitan ya nunama Rumanan yanda zata saka Wayan idan wannan ya ?are, dan leda biyu za'a saka masa.
Suna fita sai kawai rumana ta zauna ta hau rusar kuka.
Ahmad na jiyota sama-sama, sai dai baice mata komaiba har barci ya kwashesa mai ?arfi.

Har magriba ruwan bai ?areba, saboda a hankali suka sakashi, alwala tayo tazo tai salla, bayan ta idarne ta tashi ta saka masa Wayan ruwan kamar yanda suka nuna mata, duk da dai a tsorace tayi komai, lokacinne kuma Maman Ama.. Ta sake shigowa danta dubashi.
Maman Ama na fita Abu ya shigo gidan da sallama, maman Ama dake ?o?arin fita ta amsa masa tana bashi hanya ya shigo,
 To, abun ya kai harda ?arin ruwa kenan? . Abu ya faWa yana ajiye kwanikan hannunsa
Rumana ta share hawaye tana faWin wlhy kuwa Yah Abu, ni tsoroma nakeji kar wani abune ke damunsa ba'a saniba, garama akaisa asibiti tunda dai wannan ba likita bane babba .
 Karki damu Umm-Ruman, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu akaga jikin ya?i daWi ai gara aje asibitin, ga tuwo nan inji Ayyah, bara naje na sanar musu dan basusan an saka masa ?arin ruwa ba .
Kai kawai Rumana ta iya Waga masa.
Ya fice da hanzarinsa, ita kuma ta koma ta zauna ta zuba tagumi.
Koda aka kira sallar isha'i da ?yar ta iya tashi tayi, tana ?o?arin ninke abin sallar tajiyo sallamar matan gidansu, da sauri ta amsa tana Waga labule, ganin da gaske sune sai daWi ya kamata, sai da suka gaisa da maman Ama sannan suka shigo Wakin.
Ayyah ce da matan baba Iliyasu, Gwaggo da mama gaje da Ammin ta ne basu zoba.
Tabarma ta saka musu suka zauna, ta dur?usa ta gaishesu, suka tambayeta mai jiki tace da sau?i.
Ta mi?e ta zubo ruwa a kofi ta kawo musu, Ayyah tace,  Rumana waye ya saka masa ruwan? .
 Ayyah tare da yaya Sufyan daya kawosa sukazo, leda biyune, da Wayan ya ?are shine na saka Wayan kamar yanda suka nunamin .
 ALLAH ya ?ara afuwa suka faWa kusan a tare.
Sun daWe a gidan sunata jajanta abun, har Mudanseer ya shigo da ba?ar leda a hannu, shima har cikin Wakin ya shigo suka gaisa da Rumana, ya tambayeta jikin Ahmad Win yana ajiye ledar hannunsa.
 Ga wannan kananzir ne tun Wazun yace na kawo shaf na manta wlhy, saboda Winki ya Wauke hankalina, kawo risho Win a haWa .
Mi?ewa Rumana tayi ta Wakko kwalin ?aramin risho da su Fa'iza suka kawo ta ajiye gabansa, buWewa yay ya fiddoshi daga ciki, ?aramine amma yanada Wan ?yawunsa, suna nan zaune harya gama zira lagwanin ya haWa komai yasa kananzir Win, sai da yaga tankin ya cika ya mi?a mata sauran yana faWin,  Sai ki adana wannan ko .
Amsa tayi cikin girmamawa kamar yanda aka koyar dasu ga dukkan yayyensu.
Su Ayyah suka mi?e suna faWin bara su wuce kar dare yayi, idan ya tashi tai masa sannu.
Tamkar Rumana zatai kuka haka taji, ta rakasu har soro tana share guntun hawayen da suka cika mata ido.
Umma tace,  Haba Rumana miye abin kuka anan, kowa da haka ya fara kinji, ALLAH ya baku zaman lafiya dai da ha?uri da juna .
 Amin Ayyah ta amsa, Umma babba kam baki taWan taSe tana wani mosan mugunta, kusan dai ?awar mama gaje ce.
Ayyah na kallonta amma tai kamar bata ganiba suka fice, Rumana ta koma cikin gida tana share sauran hawayenta.
Zama tai suna Wan hira da Mudanseer, dan dama can shi yana sake musu ba kamar Ahmad ba, sannan mutum ne mai yawan barkwanci ga kowa. Shine ya sakata dole taci tuwon da Abu ya kawo, sannan yace ta bashi tukunya da ruwa ya dafa musu ruwan zafi, idan Ahmad ya tashi sai kawai ta juye masa yay wanka tunda ALLAH yasa akwai filas.
Tashi tai ta ciro tukunya daga kayanta, ta Wauraye ta zubo ruwa ciki ta kawo masa ?ofar Waki inda ya maida risho Win yana ?o?arin kunnawa, ta Wauko filas Win shima ta wanke dan su Fa'iza duk suka kawoshi tare da risho.
 Bara naje na dawo kafin ruwan yayi Mudan ya faWa yana ?o?arin fita.
To ta amsa masa, shikuma ya fice.
Bai jimaba sosai ya dawo da leda a hannu, ya mi?a mata tare da buWe tukunyar, ruwan nata ?o?arin tafasa ne, dan haka ya buWe murafan filas Win ya matso dashi kusa. Yana tafasowa kuwa ya kwashe sa, sai da ya cika sannan ya mi?a mata bayan ya rufe, ya kashe risho Win ya Wako da kansa ya maido mata Waki.
 To Umm-Rumana bara naje gida dare ya farayi, idan ya tashi ki tabbatar dai yasha magani, amma ki haWa masa tea yasha zaiji daWin jikinsa, ALLAH ya ?ara afuwa, da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo naga yaya ya tashi, idan munga babu wani canji sai aje asibiti ALLAH ya rufa asiri .
Kanta ta Waga masa, ji take kamar tace ya tsaya karya wuce shima, amma bata da ikon hakan, tana kallo ya fice ya barta ita kaWai sai Ahmad daketa barcinsa dan Mudanseer ya cire masa ?arin ruwan tun Wazun saboda ya ?are.

Tun tana kallonsa harta fara gyan gyaWi, ahaka Ahmad ya farka kusan Wayan dare ya ganta, Wakinsu buWe ga hasken fitila ?au saboda sabon batiri dake a ciki, idanunsa yaWan lumshe ya buWe a kanta, sai ta bashi tausayi, an haWata da aikin da sam bai dace da itaba.
Bargon ya janye ya sakko daga gadon, yaWanji ?arfin jikinsa saboda ?arin ruwan da aka saka masa.
Motsin saukarsa ya saka Rumana buWe idanunta, cikin Wan rikicewa take masa sannu, ya amsa murya a dushe.
Buta ya Wauka ya fita, itama saita mi?e ta fara zuba ruwan sanyi a botiki kafin ya fito taji idan zaiyi wankan, a haka ya fito ya sameta, kanta a ?asa tace,  Yaya Ko zakayi wanka? .
Kamar bazai amsa ba sai kuma yace,  Inason yi amma akwai sanyi .
 Ruwan Wumine ai
Kallonta yayi sosai, ganin haka yasata saurin cewa,  Eh ai Yah Mudan ya kawo kananzir Win, shine ya dafa maka .
Janye idonsa yay akanta yana jin ?aunar ?anin nasa, da hannu yay mata nuni data haWa masa, ya mi?e ya hau cire kaya.
Da sauri ta fita da ruwan takai masa bayi, a tsakar gida suka haWu yana sanye da jallabiya, ta wuto shikuma ya shiga bayin,
Tea Win ta haWa masa kamar yanda Mudan yace tayi, ta shimfiWa abin salla ta ajiye shayin a gefe da biredi, sai ?wai da Mudan yasa aka soya masa shima ta juye a filet ta rufe.
Ahaka ya shigo ya sameta, ya Wauki buta ya sake fita, babu jimawa ya dawo, sai da ya kulle Wakin sannan ya ?araso, Rumana na gefe zaune kanta a ?asa ya tada salla.
Kafin ya ?arasa ramuwan sallar magriba da isha'in har Barci ya fara kwasar Rumana a wajen, ta riga da ta saba da barcin wuri.
 Ki tashi kije ki kwanta nutsatstsiyar muryarsa ta daki kunnenta.
BuWe ido tayi da sauri tana gyara mayafinta, ta Waga masa kai tana Wan matsowa gabansa, buWe shayin tai da ?wan ta matsar gabansa sosai,
 Su Ayyah sunzo dubaka da Umma ?arama da Umma babba, hakama yah Sufyan yazo sake dubaka baka tashiba .
 Na gode ya faWa a hankali.
Shayin ya Wauka ya fara sha saboda yunwa yakeji dama, Rumana ta mi?e ta Wakko ledar magungunansa ta ajiye gabansa, tabarmar data kwanta jiya ta Wauka zata shimfiWa a Wayan lungun gadon tunda Ahmad na zaune inda ta kwana jiya sai ya dakatar da ita.
 Ki hau gadon ki kwanta .
Yanda yay maganar a dake tasan babu zancen musu, sai dai jikinta har rawa yake kaWan, taya zata iya kwana dashi bisa gado Waya?.
Kamar mai tsoron a saceta haka ta Wofana a bakin gadon ta cure jikinta waje Waya.
Ahmad na kallonta baice mata komaiba, ya gama shan shayinsa yasha magani da ?yar, Rumana dayake ta juya masa baya batasan hidimar da yakeba.
Ya daWe zaune a wajen har barci Sarawo ya sace Rumana dake kwance a Wofane.
Jin barci na neman sake Waukarsa saiya mi?e ya Wakko filo daga gadon da bargo, jallabiyarsa ya cire ya kwanta akan abin sallar yana rufa da bargon duk da kuwa garin akwai sirkin shigowar zafi.

&&&&&


Yau dai kam duk yanda yaso fita a gidan bayan sun gama karyawa hakan ya gagara, dan sosai ciwo ya kaishi ?asa, daga ?arshe dai sai da Rumana ta amsa wayarsa ta kira Mudanseer.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login