Showing 33001 words to 36000 words out of 87750 words

Chapter 12 - GUDU DA WAIWAYE bilyn abdull

29 Jun 2024

13328

har yanzu kanta ke a ?asa,  Zubamin kaWan, sai ki haWamin shayin nan, anjima nasha kunun .
Da to ta amsa tana mi?ewa, ?aton banbun ruwanta da aka zuba kwanikan amfani ciki ta buWe ta Wauki filet da cokali da kofi, dukda a wanke suke fes sai da ta sake Waurayewa sannan ta dawo inda take, sai faman gyara gyalenta dake zamewa take harta kammala haWa masa shayin, ta zuba fankasu uku yace,
 ya isa haka, zuba miyar a kai kawai .
Da  to ta amsa.
Bayan ta gama taWan kallesa, a Warare tace,  Ko a saka Sallaya a ?asa .
Kai ya Waga mata yana cigaba da danne-dannensa a waya.

Ganin zai fara cin abincin sai ta mi?e zata fita.
 Kefa?
Yay maganar ba tare da ya kalleta ba.
 In....in..ba banajin yunwa tai maganar cikin in ina tana sosa gefen kunne.
Manyan idanunsa ya Wago ya kalle, hakan yasata saurin maida nata ta risinar.
 Dawo ki zauna ki karya ko ranki ya Saci .
Dawowa tai tabi Umarninsa, zata zuba wani fankasun yay mata nuni da wanda ta zuba masa.
Duk jikinta tsuma yake, itace yau zataci abinci kwano Waya da Yah Ahmad?.
Yanda ta takure kanta duk yana kula, amma sai yay kamar baisan tanayiba, yaci gaba dacin abincinsa duk da baya masa daWi sosai a harshe saboda zazzaSin da yayi, ga damuwar Samina tana nan daram a ransa babu abinda ya ragu a ciki.
Bai sake tanka mata ba har suka cinye ukun data zuba masa, wanda shine ya cinye kaso mafi yawa a ciki, buWe kwanikan yay ya ?ara wasu ukun ya saka miya, Rumana dai na kallonsa batako motsaba, gabanta ya tura filet Win ba tare da yace uffanba.
Ta kallesa da sauri suka haWa ido, yanda ya sake tsuke fuska ya sata maida kanta ?asa da sauri ?irjinta na lugude, tadai fahinci itace zata cinye wannan kenan?.
Yanda bai sake bi takansa ba itama ta kasa kallonsa, ya ajiye kofin tea Win da Wan saura a ciki alamar dai ya ?oshi, miya tuna kuma oho masa, sai taga ya jawo ledar da madara ke ciki ya fasa Wayan sacet Win ya zuba a kofin da sukari sai nescafe, ya zuba sauran ruwan zafin kofin ya motsa, gabanta ya ajiye ya mi?e nanma bai tanka Winba dai.
Da kallo ta bisa har ya Wakko ledojin jiya ya ajiye inda ya tashi, ya buWe banbun da kwanika ke ciki ya Wauki kofi, sannan ya buWe ?aramin banbun danya Weba ruwa amma wayam babu komai.
Mi?ewa Rumana tayi tana faWin,  Babu ruwa ai, naje zan Wiba a rijiya wai gugan ta faWa jiya, bara nasamo maka wajen maman Amatullah .
Baice komai ba ya mi?a mata kofin.
Bata jimaba ta dawo Wauke da ruwan leda a filet.
Koda ta ajiye a gabantsa sai ya tsirama ruwan ido kawai ba tare da ya Waukaba.
Hakan ya saka Rumana tsayawa tana kallonsa itama.
 Babu ruwane a gidan sai wannan? . Ya faWa yana nuna filet Win.
 Na tambayeta ne shine ta bani wannan wai na rijiyar baida daWi sosai suma wannan suke sha.
Filet Win ya tura gabanta, da alamun Sacin rai a fuskarsa kaWan yace,  Bani wancan haka nan .
Tamkar Umm-Rumana zata fasa kuka haka taji, yanzu mata tai musu abin alkairi kuma sai yace ta maida? To mi zata ce mata ita kuwa?.
 Zaki Wauka ne? ko sai kin gama tunanin? .
Kafin ya rufe baki ta sungumi filet Win ta fice cikin sassarfa..............
'





*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*=?-?=?O?
07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*=?O?
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*(12)*



............Jiki a sanyaye ta koma ?ofar Wakin maman Amatullah.
Maman Amatullah dake zaune tana Wura zoSo a gorori na saidawa ta amsawa Rumana sallama tana faWin  shigo mana Amarya .
Kunya duk ta lulluSe Umm-Rumana, ta ajiye filet Win ruwan tana magana cikin in ina  Dan ALLAH kiyi ha?uri, wai ya fi son na rijiyan .
Murmushi maman Ama tayi, tace,  Amarya karki damu, haka maza suke, abinda suke bu?ata kawai suke so, bara na Wiba miki wannan yafi Wan sanyi to .
Rumana dai batace komaiba, ta amsa ruwan tana mata godiya ta fice.
Inda ta barsa nan ta iske sa yana danna waya, ta ajiye kofin ruwan a gabansa  Ga shi .
Bai ce komaiba ya ajiye wayar.

Tana cin abincin da aka sakata dole tana satar kallonsa yanda yake shan magani kamar zaiyi kuka, sai yayi kamar zai sha sai ya fasa yana matse ido, idan kuma ya jefa a baki da ?yar yake haWiyewa kamar zaiyi amai.
Ba sabon abu bane a wajenta tunda tasan baya son magani, ya Sata lokaci sosai kafin ya gama shan maganin da bai wuce kwayoyi shida ba.
Ficewa yay, mintuna kaWan sai gashi ya shigo, botiki ya Wauka ya fita tare da ?aramin banbunsu.
Hakan yasa Rumana mi?ewa itama ta shiga tattare kwankan da suka gama, ta Wakko wani filet Win ta juye kazar jiya ta Wora a tiren da zainab ta kawo abinci ta ajiyesu gefe.
Mamaki ya bata ganin yana Wibar ruwa, da alama dai gugar ya fiddo dan ga ?ugiya nan a gefe ya ajiye.
Kwanikan ta ajiye gefe ta koma Wakin, tana ?o?arin shiga ta tsinkayo muryarsa yana faWin,  Ki kwashe kwanikan nan shima ki fiddosa .
 To kawai ta iya cemasa.
Yanzu ita ina zata saka waWannan kwankan haka? Duk da basu da yawa Wakin babu wani fili mai yawa daya rage, kuma dai bata ce zata jerasu a ?asa ba ai.
Haka dai ta gama fiddasu ta Wauki banbun takai masa, sai da ta Wauraye shi sannan ta ajiye.
Ya Wauki wanda ya cika da ruwan ya kai Wakin, itako sai kallonsa take, dan banbun yanacin kusan boket huWu.
Ruwan ta Wiba a ?aramar roba ta koma gefe tana wanke kwanikan, shi kuma ya Wauki banbun data ajiye ya maidashi ?ofar Wakinsu ya ajiye, idan ya cika botiki sai yaje ya juye.
Hakan da Rumana ta ganine ya sata mi?ewa tabar wanke-wanken, idan ya cika botikin sai taje ta juye, a haka har suka cika banbun da botikan uku, biyu na roba Waya na ?arfe.
?arasa wanke-wanke tazo tanai, shikuma ya Wauki ruwan botikin ?arfen ya nufi bayi.
A lokacin kuma Maman Ama... Ta fito ri?e da Amatullah tana kuka.
Rumana tai murmushi tana kallonsu da faWin,  A'a Amatullah yaya dai? .
 Rigima kawai mara dalili, Wan zoSon dana rage na ?asan botiki ta zubarmin a Waki, shine kuma bazan gogeba sai na bar mata tai wanka a ciki .
Rumana tace,  Lallai hajiyar Sarna kenan, ina Yayana shi? Ban ganshiba tunda na tashi? .
 Wannan ai tun jiya bama ya gidan, da ?anwata tazo jiya da yamma ya ma?ale mata sai da ta tafi dashi .
 ALLAH sarki, to ALLAH ya dawo dashi lafiya .
Rumana ta faWa tana kama Amatullah data rarrafo wajenta.
?aukarta tayi, ta zauna a bakin rijiyar tana mata wasa, ahaka Ahmad yazo ya wucesu.
?in shiga Wakin Amatullah tayi, har sai da ya le?o, kamar ance ta Wago sai suka haWa ido,  Zonan ya faWa kawai yana sakin labulen.
Mi?ewa tai Wauke da Amatullah ta nufi Wakin.
Tsaye ta iskeshi yana taje sumarsa a gaban mirror, tace,  Gani Yaya .
Bai tankaba sai da ya gama, ya ajiye kum Win yana faWin,  Bara naje can gida baba na kirana, naga babu abin girki ko? .
Tai jimm saboda bata gane kan tambayarba.
Katse mata tunani yay da cewar,  Risho nake nufi ko abin gawayi .
 Eh babu, amma inaga zasu kawo yau sukace .
 Okey kawai ya faWa yana ?o?arin Waura agogo a hannunsa, mikuma ya tuna sai taji ya ja siririn tsaki tare da kuncesa ya buWe jakar daya Wauki kaya ya jefashi ciki, ya zaro wani ya saka, kumatun Amatullah dake mi?a masa hannu tanason ya Wauketa yaWan shafa ya wucesu batare da yace komaiba.
Rumana tai ajiyar zuya bayan ya fice tana Wan girgiza kai, aranta tana tunanin ko yaya wannan zama nasu zai kasance kenan oho?.
Fitowa tai tsakar gida tanama Amatullah wasa, inda maman Ahmad ke Wan mata hira daga kicin Winsu tana girkin rana.
Ita dai Rumana murmushin ta yafi hirar yawa, dan dama can ita bamai yawan magana bace, ta kuma kula Mama Amatullah akwai surutu.
A haka su Fa'iza sukazo suka iskesu, sosai Rumana taji daWin ganinsu.
Suka shiga Waki sai sha?iyanci suke mata, harda tambayarta wai yaya jiyan? Dan sunga Yah Ahmad a gida yanata ?yallin angwanci.
Duka takai musu, suka kauce suna dariya, haka sukaita tsokanarta, kazar kuwa da suka gani sai da ta Wiba musu, suka kuwa ci suna faWin,  Tunda ke tsoro ya hanaki kici muko ci mukayi, Rumana wai dan ALLAH da wuya kamar yanda ake faWa? .
Rumana ta kalli Salima mai maganar tana faWin,  Minene? .
Gado Salima ta nuna mata da yin magana ?asa-?asa kamar mai munafunci.
Tashi Rumana tayi tsaye,  Oh ni ALLAH ya shiryeku, ni dai babu ruwana wlhy, kuje ku tambayo Yah Ahmad Win mana .
 Kutumelecy amma baki da man kai Rumana yasin cewar Fa'iza.
Salima tace,  A'a so take ya maidamu ni?a??iyar gyada ta ?uli-?uli alkur'an, kinga kuwa yanzu da muka haWu dashi a gida sai wani cin magani yakeyi, niko a raina har gulmarsa nayi, nace waishi Yah Ahmad yamayi auren bazai canjaba ne? .
Dariya Fa'iza da Rumana suka sanya, Salima ma mai maganar ta tayasu tana sake cewa  Wlhy na zata yau zan ganshi fuska a washe, Rumana ko dai baki bada kai bane? .
 Wai Salima yaushe kika koma hakane? To ALLAH ya gyara lamarinki da wuri, kema dai na kula auren kikeso .
Fa'iza tai saurin faWin,  Mi takeci na baka na zuba, Wlhy Malam yace muma mu kawo mazan aure, wai muna gama jarabawa aure za'ai mana, abinda Yaya Samina tayi ya tada hankalin kowa, bazasu sake yarda ?a?ansu suyi zurfi a karatuba sai dai idan mijinka naso ya kaika da kanshi .
Cikin marairaice murya Rumana tace,  Kuma godema ALLAH kuda gashi zaku ?arasa, ni kam nasan ai nayi kenan .
 Karkice haka wlhy, tunda Yah Ahmad nason karatu zai barki ki ?arasa, ALLAH dai yasa kar bebin mu yay shigar sauri kawai .
Hararta Umm-Rumana tayi.
Suka sanya mata dariya.
Daga nan suka koma hirar Samina, tare da iskance-iskancen data tsuro dasu a gidan a safiyar yau.
Rumana tace,  ALLAH ya ?yauta to, ALLAH ya shiryeta .
Amin dai, su Fa'iza suka faWa a tare.

Su Fa'iza na gidan har Sadiya da Na'ima ?anwar Rumana suka kawo abincin rana da ?an tarkacen kwanika da aka ?ara saima Umm-Rumana, harda ?aramin risho da abin gawayi, sai Abu dake biye dasu da ?atuwar jakkar Ahmad ta kaya da tarkacensa.
Sannu Rumana tai musu, suma suka zauna aka Salle hira, Abu nata zuba musu shirme suna kwasar dariya, yaran anguwa kuma nata shigowa jefi-jefi ganin Wakin amarya, harma da mata ma?wafta ?an gutsiri tsoma, dan yanda auren ya kasance duk ya shiga kunnensu.


_________________________


Ahmad kuwa koda ya fita dauriya kawai yakeyi, dan bayajin ?arfin jikinsa sam, ga zuciyarsa har yanzu a cunkushe take, kansa kuma bai daina masa ciwo ba.
A majalisar abokansa ya fara yada zango, ya zauna suka gaisa yana sake musu godiya, sukuma suna tambayarsa jikinsa da amarya.
Yaja kusan minti talatin a wajensu kafin ya mi?e ya ?arasa gidansu, sashen su Malam ya fara shiga suka gaisa, Malam nata saka masa albarka, hakama tsoffin da aka bari ?an shema su huWu da Iya, yaWan daWe anan ma, ya fito yana murmushin ?arfin hali na tsokanarsa da sukeyi irin dai wasan jika da kaka.
Sashen Baba Ilyasu ya shiga, ya gaida matansa sannan ya fito zuwa Sashen su Rumana.
A tsakar gida ya iske Ammi da Mama gaje, kowa na hidimarsa, ya risina ya gaidasu tamkar yanda ya saba, Ammi ce kawai ta amsa masa cikin jin nauyinsa da batayi da, Mama gaje kuwa Waki ta shige bata amsashiba.
Bai damuba ya mi?e ya fito abinsa.
Ya shiga sashensu, ?an biki duk sun kama gabansu, sai ?anwar gwaggo kawai data rage bata wuceba inna Asma'u.
Da Ayyah ya fara cin karo a tsakar gida suna ?o?arin kwance zare a ?afar Waya daga agwaginsa ita da Mudan.
Ya ?arasa gabansu yana faWin,  Ayyah miya sameta ne? .
 Wlhy Wan albarka zarene ya sar?e ?afarta, gashi nama lura kamar ?afar tata ciwo take tun jiya wajen taron nan, to ALLAH baisa nasamu kamata ba suka fice sai yanzu abun ya faWomin arai, shine nashiga nemanta sai kuma na ganta jikin kejin kajincan a takure kamar wadda aka Waure, ashe zarene ya dabai baye ?afar .
 To, bai dai ji mata ciwo ba ko? .
 Eh bai jiba, amma Yaya ina ganin gara a saidasu kawai, kwanan nan naji ana maganar agwagi suna fama da murgwi, na gidan malam kalla sai mutuwa suke suma . Madan dake maganar ya faWa idonsa akan Ahmad.
Ahmad yace,  To Mudan saika cigita mai sayen muga idan zasu Wanyi daraja, amma abar guda biyu, dan nagama wata fara mai yarfin ba?i kamar ?wai takeyi .
Ayyah tace,  Ai naga kamarma fa ta fara ?yan?yasa da safenan indai ?ar budurwar nance...
Kafin Ahmad ya bada amsa Inna Asma'u ta fito daga Wakin Gwaggo ri?e da kayan wankin Gwaggon.
 A'a, ango Wan gidan Ayyah ne a gidan? Jiki yayi sau?i kenan? .
Maida hankali gareta Ahmad yayi, ya taka zuwa inda take yana risinawa ya gaisheta, ta amsa cike da kulawa tana tambayarsa jikinsa.
Ya amsa da cewar da sau?i.
 To Alhmdllh, ai haka muke son ji, Ina Wiyar tamu amaryar ?amshi? .
Kansa ya kuma sunkuyarwa ya amsa da cewar,  Tana lafiya itama .
Daga haka ya mi?e ya shiga Wakin Gwaggo.
Tana zaune Zainab dur?ushe gabanta tana cire mata abu a ha?ori, sai yarfa hannu take tana kukan shagwaSa na autanci.
Zama yay yana kallonsu, Gwaggo da sallamarsa kawai ta amsa ta bige hannun Zainab dake ri?e nata,  Idan bazaki tsaya ba tashi kiban waje, ji iskanci saikace ina cire miki rai .
 ALLAH Gwaggo da Zafi fa Zainab tai magana tana share hawaye.
 To jeki kicire da kanki mana .

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login