Showing 30001 words to 33000 words out of 87750 words

Chapter 11 - GUDU DA WAIWAYE bilyn abdull

29 Jun 2024

13329

ga ma'abota soyayya ..
Itadai kanta a kasa tana hawaye bata iya bashi amsaba, ya juya ya fita yana faWin ta rufe ?ofar shi ya wuce.


&&&&&

Sama-sama Ahmad ke jin Sufyan harya fice, daga bayama barci mai ?arfi yay awon gaba dashi.
Har lokacin Rumana na tsaye tana hawaye, sai da taji tsayuwar ta gundireta ne ta ajiye ledojin hannunta ta nufi ?ofar ta rufe addu'a Wauke da bakinta kamar yanda mahaifiyarta ta koyar da ita.
Zama tayi kawai ta zuba masa ido tsawon lokaci, tausayinsa na sake ratsa zuciyarta.
Itama kantane ke mata azabar ciwo, dan haka ta lallaSa taja bargon dake saman gadon ta lullubama Ahmad data lura yana rawar Wari, tana sakawa kuwa taga yajashi har saman kansa ya sake kudundunewa da ?yau, ajiyar zuciya ta sauke tausayinsa na sake kamata.
Tsawon lokaci tana wajen har ta farajin saukar numfashinsa ya canja alamar barcinsa yay nisa sosai.
Tasan dolene a tausayama Yah Ahmad, dan halin da yake ciki abin dubawane, akwai tashin hankali abinda ka girma dashi a zuciyarka yazama shine sanadin rusa dukkan farin cikinka a dare guda.
Sabuwar tabarmar dake a Wakin ta dauka ta shinfiWa ?asan ledar da aka saka a Wakin ta kwanta ba tareda ta saka koda zaniba, sai filo data Wauka kawai a gado saboda bata iya kwanciya babu shi.
Gyalen jikinta ta rufa dashi dukda bashi da wani kauri sosai.
A haka taci gaba da kukanta har itama barcin yay nasarar saceta, ga kanta yana sara mata sosai da ciwo.


_______________________________


A wannan darenma Samina da Ma'aruff sunsha hirarsu ta masoya, inda mafi yawan firar duk ta karkata wajen tsara yanda shagalin bikinsu zai kasance.
DaWi tamkar zai narkar da ita, sai wani lumshe ido take tana dafe ?irji da washe ha?ora, har yanda take bu?atar lefenta ya kasance da kalar akwatunan da takeso da kayan gidan dazai zuba mata duk sai da ya tambayeta, sai events na garari na nunawa a gidajen tv da social media shima duksun tsara abinsu.
Cikin shagwaSa take shaida masa yafayi ta turo manyansa, dan ita yanzu dukta tsani komai na gidansu, sotake ta kara gaba tabarsa kodan ?an bani na iya.
Daga can Ma'aruff yay murmushi yana faWin,  Karki damu gimbiyar mata, ni kaina na kagara na jiki a jikina lafe, ina baki gangariyar soyayya da babu sirkin ruwa a cikinta, burina kawai mallakarki tunda kinki bani damar hakan tun a yanzu, kince sai munyi aure, niko nayi biyayya na ha?ura har a Waura a kawomin ke babie .
 Oh ni kana bani kunya, gara dai kayi ha?uri harnazo, dan saboda na faranta makane ma nai duk abinda ya dace kar wancan shashashan ya sameni, dan kaWan daga aikinsa ya kwata cikin ?arfi, niko kai kaWai nake burin cikama al?awarin kawo maka budurcina har gida .
 Nagode ta wajena, shiyyasa nake ?ara jin sonki na ?aruwa a raina a kowacce da?i?a, dolene nazo na samu su baba ayi komai da wuri, insha ALLAHU nanda karshen wata kina nan kwance a ?irjina .
Yanda yay maganar da wani irin salone yasaka tsigar jikin Samina tashi, ta sauke nannauyan numfashi daya sake haukatar da Ma'aruff daga can, hakan yasashi kuma manne karuwarsa dake barci a jikinsa, dan saida ya gama holewarsa ne ma ya kira Samina Win.
 Sai da Safe
Samina ta faWa a sanyaye saboda kasalar da ya sakar mata da kalamansa.
Shima da  Uhmm kawai ya iya amsa mata ya yanke wayar yana sake maida karuwarsa a network.

Haka Samina tai barci da Wunbin begen abokin hakittarta, dolene ma tai yadda zatai ai aurensu da Ma'aruff a nan kusa, koba komai ta samu nauyin shekaru dake gallabarta ya fita. A shekarun da suka shuWe Ahmad kawai take iya suffantawa da wannan yanayin, amma zuwa yanzu sam ba haka bane.
Wani gefe na zuciyarta yace yanama can yana hutawa da kanwarki amaryarsa kuma Rumana.
Baki ta taSe tana jan tsaki, sai kuma Wayan gefen zuciyarta ke shaida mata sam Ahmad bazaiyi hakanba, dan tafi kowa sanin halinsa idan ka Webe iyayensa, dan ko ?an uwansa tafisu sanin wanene Ahmad akan abinda yake so, tasan kafin Rumana ta samu gane kan Ahmad za'a yara, dan soyayyarta ta riga ta masa ?ullin yaWon wake a gona, kafin zuciyarsa ta fara kallon Rumana matsayin mace sai anyi babban dagama...............
'







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O?
07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*=?O?
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*(11)*



............Kiran sallar farko Ahmad ya farka, zazzaSin ya sauka masa, sai dai akwai ciwon kai kaWan-kaWan, sai nauyin jiki da yakeji.
?amshin sabon fenti dana katako ne ya tuna masa da inda yake, ya janye bargon da yake a ciki a hankali yana yun?urawa ya tashi zaune, babu haske a Wakin, dan Rumana ta saba idan zasu kwanta sai Ammi tace su kashe fitila, shiyyasa jiya da zata kwanta bayan ta gama shan kukanta sai ta kashe ta ajiye kusa da ita, a tunaninta ai zata riga Ahmad tashi da asuba.
Ahmad ya Wan laluba ko zaiji wayarsa a jikinsa, sai dai babu, ya tura hannunsa ?asan filon da ya tashi nanma babu.
Iska ya huro ?aWan a bakinsa yana janye bargon baki Waya, da lalube ?afarsa takai ga bakin gadon, ya zurasu gaba Waya yana ambaton ALLAH a kan laSSansa.
Da sauri yay ?o?arin janyewa saboda jin ya Wora akan mutum, sai dai nan Winma sake Worasu yay akan jikin nata.
Zafin da Rumana taji a ?irjinta ne ya sakata farkawa tana faWin  wayyo ALLAH Kadija zaki kasheni, bakicewa na haska miki fitila, ji yanda kike takani a ?irji..
Yanda tai maganar cikin yanayin barci da sanyin murya irin ta wanda yaji zafi sai da tsigar jikin Ahmad ta tashi, bai kawo a ransa tana wajen kwance ba, duk da ma dai zai iya cewa ya manta da ita a Wikin.
Yana ?o?arin janye ?afafun nasa Rumana ta kunna fitila Wakin ya gauraye da haske.
Ba ?aramin faWuwa gabanta yayi ba ganin Ahmad zaune, sam ta manta inda takema ita, tai saurin jan gyalenta ta rufe jikinta saboda da daddare takura mata rigarta tayi shine ta zuge zif Win ya koma ?asa sosai.
Kallo Waya yay mata ya Wauke idonsa, ya sake ziro ?afafunsa ?asan batare da yace mata komaiba.
Itama dai ko motsi bata sakeba harya Wauki buta Waya cikin guda biyu da aka zubama ruwa aka ajiye farkon ?ofar Wakin.
Hannu yasa ya zare sakatar Wakin da ta saka ya fice, yanda iskar asuba ke kaWawa a hankali ce ta sakashi buWe hanci ya zu?a sosai sannan ya fesota ta baki yana lumshe idanu.

Rumana dai kasa motsawa tai, sai kalmomin data faWane ke mata kaikawo a rai, takai hannu saman ?irjinta daya taka kunya na sake kamata, dukda ba nauyi ya sakiba taji zafi, kuma tana Wanji har yanzu kaWan, maida zif Winta tayi ta mi?e jiki duk babu ?wari, ta Wauke filon data kwanta tare da naWe tabarmar.
Yanda fitilar tasu taWan hasko waje tana hangenshi yana alwala a ?ofar Wakin, da yake gidan bawani girmane da shiba, babu wani isashshen tsakar gida sam....
Ya katse mata tunani yayinda yake Waga labulen ya ajiye butar, kamar zai tafi sai kuma ya dawo da baya ya shigo Wakin.
Ta gabanta yabi zuwa gaban gadon, ya Waga filo yana sake duba wayarsa, ganindai babu ita saiya maida kallonsa ga Rumana dake tsaye jikin Wadrobe kanta a sunkuye tana kallonsa gefen ido.
 Sufyan bai bada wata bane? .
Da farko bata fahimci tambayar tasa ba, dan haka taWan Wago ido ta kalleshi, ganin ya tsareta da idanu tai saurin janye nata, cikin in ina tace,  A'a, ?ila ya manta ne .
Baice komaiba yazo ya sake raSata ya fice.
Tana jiyoshi ya buWe gida ya fita, hakan ya sata sauke ajiyar zuciya itama ta Wauki fitila ta fita duk da tana Wanjin tsoro.
Tana cikin alwala mijin Wayar matar gidan ya fito, ganinsa da ga shi sai gajeren wando yasa Rumana saurin du?awa tana wanke ?afa, bata ce masa komaiba shima baice mata ba ya shige bayi, itama tai saurin faWawa Waki.

&&&&&

Ana idar da salla Ahmad ya shigo, kasancewar massalacin a ?ofar gidan yake, Rumana na zaune saman abin salla tana azkar.
Yanda yay sallama ciki-ciki haka ita ta amsa masa a hankaki, baice mata komaiba yazo ya sake hayewa gadon ya kwanta.
Rumana ta ?arasa azkar Winta sannan tace,  Ina kwana .
Kamar bazai amsa mataba sai kuma taji ya amsa da  Lafiya .
Daurewa tai ta sake cewa  Ya jikin? .
Nanma dai shirun yayi, harma sai da ta fidda tsammanin zai amsa sai kuma yace,  Alhmdullh .
Daga haka kowa yay shiru, shi dai barcine ya sake kwasheshi, saboda maganin bai gama sakinshi ba.
Itako duniyar tunani ta faWa, a ranta sai ?ara girmama hukuncin ALLAH takeyi, yanzu nan Yah Ahmad matsayin miji yake a gareta? Wata zuciya tace,  To gashi ma kun kwana a Waki Waya .
Nannauyan numfashi ta sauke, wanda har Ahmad ya jiyota sama-sama a Wan barcin da ya figesa.

Umm-Rumana na zaune a wajen har gari ya fara haske, Wakin kawai take bi da kallo daki-daki, Ahmad dai nata barcinsa, wanda daga inda take tana iya jiyo saukar numfashinsa a hankali.
Sama-sama ta fara jiyo motsin matar gidan da yarinyarta dake kuka, sai kuma zuwa can tajiyo maganar mijin shima suna fira.
Idanu ta lumshe tana tuno gidansu, yanzu tasan gidan nacan da hayaniyar yara daga kowanne sashe, musamman ma sashensu da ke da ?ananun yara da sashen baba ilyasu.
Barcine ya sake saceta a kan abin sallar itama.

Sallamar Zainab ce ta farkar da Ahmad, ya buWe idanunsa kafin ya tashi zaune yana amsawa, yakai idonsa kan Rumana da ko motsi bataiba, janyewa yay ya bama Zainab Win izinin shigowa.
Sai da ta sake yin sallama sannan ta shigo, ta sauke tiren kanta da aka Wora kofin silba babba da kwanon silba guda biyu akai.
 Yaya ina kwana ta faWa lokacin da take kaiwa ?asa dur?ushe.
Amsa mata yay yana ?o?arin sakko da ?afafunsa ?asa.
Tace,  Gashi inji Ayyah, tace yaya jikinka? Idan kaci abinci dan ALLAH kasha magani, idan kasha zataji a zuciyarta kasha, idan kuma bakashaba ma zataji bakashaba .
Guntun murmushi yayi badan ya shiryaba, a ransa yana kuma jin ?aunar Ayyah sosai.
A hankali ya furta,  Kice mata zansha insha ALLAHU .
 To yaya zan faWa Zainab ta amsa tana taSa ?afar Umm-Rumana yanda Ahmad bazai luraba.
Shi baima san tanaiba, ?o?arin sakkowa yake daga gadon.
Dai-dai nan Rumana ta buWe idanunta.
Zainab ta matsa kusa da ita tana ?ar dariya, Ahmad kam buta ya Wauka ya fita ya barsu suna gaisawa.


Bayan tafiyar Zainab da Rumana taita ro?on ta zauna ta?i, acewarta ance karta daWe.
Rumana tahau gyaran Wakin dan Ahmad bai dawo ba, sai da ta gama shara ne ta fito danta share waje sai taga butar a jiye, kenan nan ya ajiye ya juya ya fita.
Share tsakar gidan tayi gaba Waya, tana ?o?arin wanke banWaki matar gidan ta fito Wauke da kwanikan da suka karya.
 A'a amaryace dayin shara da safen nan? Harda su wankin bayi? .
Murmushi Rumana tayi, cikin girmamawa tace,  Ina kwana .
 Lafiya lau amarsu, ya amarci da angon naki? .
Kasa amsawa Rumana tayi, saboda jin kunya, matarma tayi dariya kawai tana ajiye kwankan bakin rijiyar dake gidan.
Rumana ma ta fito daga bayin ri?e da botiki, gaban rijiyar ta ajiye tana faWin,  Rijiyar akwai ruwa kenan .
 Eh akwai ruwa Amarya, sai dai babu guga wlhy, jiya da safe Ahmad ya jefashi cikin rijiyar saboda tsabar rashin jinsa .
Kallon rashin fahimta Rumana tai mata, jin ta ambaci sunan Ahmad.
Matar data farga da kallon sai tayi dariya,  Au yi ha?uri, na manta sunan mai gidanki kenan Ahmad, bas??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????hi nake nufiba, yaron wajena shima sunansa kenan, sai ?aramar FaWima muna kiranta Amatullahi .
Rumana tai murmushin jin kunya tana cewa,  ALLAH ya raya mana su akan sunna .
 Amin ya rabbi Amarya, amma ke yaya sunanki? Ni sunana Husna, amma yanzu dai anan anguwar anfi sanin maman Ahmad .
 ALLAH sarki, ni Umm-Rumana, sai dai ni zanke ce miki Maman Amatullah to .
 To babu damuwa Umm-Rumana amaryarmu, ai dole a Soye sunan mai gida, kije ga ruwa can a banbuna ki Wiba kafin Abban Ahmad yazo ya Wakko gugan .
 Nagode sosai
Umm-Rumana ta faWa tana nufar Banbun ruwan kalar ganye dake ?ofar Wakin Maman Ahmad.

Wanka tayo da ruwan data Wiba, tayi alwalar walha kamar yanda ta saba ma kanta tun tana gida.
Kayanta da aka jera cikin Wadrobe ta buWe ta Wauki zani da riga na leshi ta saka, sama-sama ta shafa mai saboda zafi da aka fara, batai wani kwalliya ba sai fauda data shafa da kwalli a idonta.
Ta fara jin yunwa, dan haka ta matsa gaban tire Win da zainab ta kawo ta buWe, Fankasu ne da yay luhu-luhu a kwanon silban farko, sai miya a Wayan kwanon tana ta ?amshin manshanu, kofin kuwa kunune na tsamiya shima sai ?amshin kayan yaji yake, tana rufewa Ahmad na shigowa da sallama, kanta a ?asa tai masa sannu.
Ya ajiye ledar hannunsa da kofin roba mai murfi madai daici yana amsawa.
Zama yay a bakin gadon idonsa akan kwanikan data gama buWewa yace,  Miye wannan a ciki? .
 Fankansu ne da kunu .
Baikai ga amsawa ba wayarsa tai ring, fiddota yay daga aljihun jallabiyarsa ya duba.
 Manyan ?asane haka suka tuna damu? yay maganar wayarsa a kunne.
Daga can Zaheedah tai dariya tana maida masa amsa da  Ai kune manyan ?asa Shema, yanzu gudun namu da akeyi har takai ai bikinka babu gayyata? .
Murmushi yayi mai sauti, wanda har ya saka Umm-Rumana satar kallonsa da mamaki, ta daWe bataga Murmushi a fuskarsa ba, duk da dama can itadai bayi mata yakeba sai da taga yanayi a majalissar abokansa ko idan yana tare da Samina, maganarsa ta sata sake maida hankalinta garesa batare da tasan dalilin hakanba.
 Bani da bakin kare kaina kam, amma dai ina ro?on amin uziri, nasan dai Sufyan ne ya sanar miki, kuma inada tabbacin bazai gaza miki bayani ba .
 hhh hakane kam ango, ai banyi fushiba, yanzu ma dai taya murna na kira nayi, ALLAH ya sanya alkairi, yasa nanda wata tara muzo suna tunda ba ai biki da muba .
Sai da ya saci kallon Rumana dake wasa da yatsun hannunta kanta du?e ya lumshe ido, sannan yace,  Humm, kina lafiya? Ya mutan gida? .
 Lafiya lau kowa da komai yake Zaheedah ta amsa duk da taso ya bata amsar maganarta ta farko.
Sun Wan taSa hira kaWan, a cikin hirar take faWa masa sai tazo ganin amarya.

Bayan ya ajiye wayar ya kalli Rumana da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login