Showing 72001 words to 75000 words out of 87750 words

Chapter 25 - GUDU DA WAIWAYE bilyn abdull

29 Jun 2024

13327

A takure tai wannan kari, har suka kammala ta tattare komai ta fita da wanke-wanke, shi kuma ya Wiba ruwan wanka ya sirka da wanda ta zuba cikin filas Win ya nufi bayi.
Tana bakin rijiya ya wuce, hakan yasa ta bisa da kallo, dan batasan zaiyi wankanba aida ta haWa ruwan takai masa.
A lokacinne Kausar ta fito daga Wakinta, sai da ta harari Rumana data juya mata baya kafin ta ?araso tana ?ar dariya,  Oh ni su amarya anyi bulum a Waki saboda yau oga ya dawo? .
Murmushi kawai Rumana tayi, ba tare data bata amsaba tace,  Ina kwana .
Nanma saida Kausar ta harareta ta wutsiyar ido sannan ta amsa, zuwa yanzu garin yayi Waf babu yayyafin, sai wani Wan hasken rana daya hasko mai Wumi.
Kausar tasan dama Rumana ba biye mata zatai suyi surutuba, amma sai ?o?arin janta take da hira, Maman Ama da taji motsinsu sai gata wuff ta fito daga Waki tamkar an jefota.
Itama Rumana gaidata tayi da tambayarta lafiyar yara, maman Ama ta amasa suna gulmar Rumana da ido itada Kausar, ahaka Ahmad yazo zai shigesu suka shiga gaishesa.
Amsawa yay kawai, ba tare da ko kallonsu yayiba ya shige Waki, sunata surutunsu ita dai Umm-Rumana na wanke-wankenta, tana kammalawa kuma ta mi?e tama bar musu wajen, da tabbacin Ahmad ya gama shiryawa ta shiga Wakin, sai kuma ta iske saSanin hakan, yadai gama shafa mai yasa singlet da boxer yana kwance a gadon ?afafunsa a ?asa.
Shigowarta ce ta sakashi buWe idanunsa ya zuba mata, yayinda ita kuma dukta dabarbarce tana neman juyawa ta koma saboda yanda ta gansa.
Katseta yay da faWin,  Zonan .
Tamkar zata fasa ihu haka taji, ta matso shikuma yana tashi zaune sosai, saurin ri?o hannunta yay ganin tana neman dur?usawa,  K wai nazama surukin kine? .
Yay maiganar yana Worata saman cinyarsa.
Kanta ta girgiza masa.
Yace,  Magana da baki nakeso .
Da?yar tace,  A'a .
 Eh mana, ba gashi bakison kallona ba, idan ina Wakinnan duk sai kibi ki takura kanki .
 To kayi ha?uri, bazan sakeba .
 Inma banyi ha?urinba ya zanyi Ruman, kinga tashi na gwadaki naje shago naWan sama miki kayan da zakije wajen bikin gobe, yau dai ki kwanta ki huta .
Idanunta suka cika da ?walla, danta saka ran zai barta taje tun yau, da ?ar shagwaSa tace,  Amma Yaya miyasa bazan fara zuwa tun yauba? .
Kallonta kawai ya tsayayi, kamar zai shareta sai kuma yace,  Gobenma na gadama bazaki jeba .
Bakinta taja ta tsuke, bata sake koda tariba.
Ya mi?ar da ita daga cinyar tasa shima ya mi?e, tef ya Wauka yazo gabanta ya tsaya, karon farko dazai gwadata dan zai musu Winki, hakan bai taSa faruwa ba, dan baya gwadasu sai dai yace su kawo kayansu yay amfani dashi.
Salon da ake gwada Winkin ya saka tsigar jikin Rumana keta tashi, badai ta yarda ta motsaba saboda yanda ya haWe fuska, tasan dai haushin maganar bikice da tayi, itama saida ta furta ne taga wautarta.
Yanayi yana rubutawa, harya kammala ya Wauki kayansa ya saka, sabuwar shaddace mai ?yau kalar ruwan sararin samaniya, duk da bamai tsada bace tai bala'in masa ?yau, ga Winkin ya zauna Wam cikin ?ya?y?yawar surarsa, ainahinsa na Barumen bakatsine ya fito masha ALLAH, ballema yayi aski da gyaran fuska, ?ar ?asumbar daya ajiye ta sake fiddo taswurar nutsatstsiyar fuskarsa, hannunta daya kamone ya maidota hayyacinta, ya saka mata turare a hannun.
Kallonsa ta Wanyi sai ya nuna mata jikinsa alamar ta saka masa.
A Wan kunyace ta fara fosa masan, sai da ta tabbatar ko ina yaji sannan ta dakata, hannunta ya kama ya jata gaban gadon, shi ya zauna ita kuma tana tsaye a tsakanin ?afafunsa idanunta a ?asa ta??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na kallon hannayensu.
Yace,  Kina jina .
Kanta ta Waga masa, sai kuma tai saurin cewa,  Eh saboda tuno gargaWinsa.
Ya murza hannun nata yana cigaba da faWin,  Ki kwanta ki huta, bance kije cikin matannan ki zauna ba, zan aiko Abubakar ya kawo miki abinda zakici, sannan abinda ya faru tsakanina dake sirrinmu ne, koda wasa naji bakinki na bama wani labari koda su Fa'iza ne bazakiji da daWiba, ki kama bakinki .
Cikin rawar murya Rumana tace,  To yaya, insha ALLAH zan kiyaye .
 Good ya faWa yana mi?ewa, matsota yay jikinsa ya rungume yana sumbatar kanta da shafa bayanta, a hankali ya furta,  ALLAH yay miki albarka .
Rumana dake lafe jikinsa tana sha?ar ?amshinsa ta amsa da amin a cikin zuciyarta tana ?o?arin maida ?wallar da suka cika mata ido..
?ago kanta yay ya kama fuskarta ya saka cikin tafin hannunsa yana kallo, ganin ta?i kallonsa sai ya Wora goshinsa kan nata,  A kalleni mana madam .
Kunya ta sake kama Rumana, taWan saki murmushi da a ma?oshi kawai taji sautin kayanta, shima ya sumbaci laSanta ya Wago ya sumbaci goshinta sannan ya saketa.
?a?ar ledar daya ajiye gefe ta viva ya Wauka yana faWin,  saina dawo mizan zo miki dashi? .
 Ba komai Yaya ta faWa tana Wan satar kallonsa.
KaWa kansa yay yana nufar ?ofa bayan ya zira takalmansa ba?e?e a ?afa,  Shikenan saina dawo .
 Ka gaidasu, ALLAH ya tsare .
 Amin ya faWa yana Waga labulen ya fice.

Kausar da maman Ama da har yanzu suna inda Rumana ta barsu suna gulmarta duk suka zuba masa ido a kaikaice, harya fice kowacce da abinda take sa?ama ranta.
Shiko baima san sunaiba, dan basu ishesa kalloba.

Yana fita Rumana ko bakin gadon ta zauna tana sauke numfashi a hankali daWan murmushi, yanzu kam ta yarda Yaya Ahmad natane bana yaya Samina ba kamar yanda kowa ke faWa a baya, abinda bata taSa kawowa ba koda a mafarkinta, ALLAH kenan, mai tsara yanda yaso, ga kuma wanda yaso.
Mi?ewa tai ta Wora ruwan zafi a risho danta samu tai wanka, bata fitoba saida ta juyo a botiki, matan gidan nata ?o?arin Wora sanwar rana, batace da kowa komaiba ta shige bayi.
Sai da ta fitone maman Ama ke tambayarta wai ko zataje gidan bikine?.
Murmushi Rumana tayi dan tasan tambayar da biyu ce, sosuke suji ko Yah Ahmad zai iya barinta taje?.
Sai kawai tace,  Mizai hanani zuwa, zan dai jira su Fa'iza suzo mu wuce .
 A'a, toshi angon bacan ya nufaba da bakibishi kun tafi tare ba? .
Karon farko Rumana taji zata iya maida murtani, dan haka tace,  Maman Ama mi kikeci na baka na zubane? .
Shiru kuwa bakin maman Ama ya rufe ruf, suka kalli juna itada Kausar cike da mamakin Rumana, itako batabi takansu ba tai shigewarta Wakinta tana jan tsaki a zuciyarta.
Har tai shirinta bata sake jiyo tarin kowa a cikinsu ba, sai ga sallamar Abu, taji daWin ganinsa, ya ajiye mata ledar dake hannunsa yana tsokanarta da faWin,  Wannan ai kece amaryarma ba waccan fanWararriyarba .
Dariya Rumana tai masa,  Kai Yaya Abu wace fanWararriya kuma? .
 Amaryar gidanmu mana mai kan goba ya faWa yana mi?a mata ledan hannunsa,  Gashi inji Yah Ahmad .
Amsa tai tana godiya, ga ?amshi dukya cika Wakin, dagaji kasan kazace.
Abu da ko zama baiba yace,  Bara na fece amaryar Yaya .
 Yah Abu ina zaka fece,  dan ALLAH kazo muci .
Dawowa yay da baya yana rage murya kamar zaiyi gulma,  Hajiya takice ke kaWai, tamu nacan a shago ina faWa miki a ?yafe, gara naje kafin Yah Mudan ya handame rabi ya banni da ?wala idanu .
Dariya sosai Rumana takeyi, Abu ya fice shima yana tasa.

Zama Rumana ta gyara taci kazarta tai nak tana lumshe idanu, ta Wora da maltinar da aka sakko mai sanyi kunnuwanta a mimmi?ewa sama, rabonta dacin nama harta manta lokacin, sai taji wani ?aunar yaya Ahmad na girmama a ranta, sauran ta ajiye gefe tai kwanciyarta a tabarma kamar yanda ya bu?ata.



________________________________

A gidan su Ahmad kam bikin dai daga danginsu ?an shema babu wani armashi, dan inna marwa ce kawai da iyalanta sai sukazo, sai maza da zasuzo Waurin aure gobe, dangin mama gaje ne kawai suketa zuwa, waWanda da yawansu kasan da biyune, dan sai habaici suke kala-kala, amma babu wanda ya kulasu hatta da Ammin su Rumana.
Koda Ahmad yazo gidan saida ya shiga har sashen ya gaida Ammin su Rumanan, aiko dangin mama gaje da ?awayen Samina da ita kanta saminar tamkar zasu cinyesa da kallo, kowa ya gansa yansan hankalinsa a kwance yake, gashi yau shar yake da ?yallin angwanci na gaske, fuskarsa ta sake yin wasai abin son kallon kowa ba tare da kaso ya gusa daga gareka ba.
Shikam koma kallon basu ishesa ba ya fito zuwa sashensu, dan sashen su iya ya fara shiga dama suka gaisa.
Bayan ya gaisa dasu Gwaggo da Ayyah su Fa'iza sukazo duk suka gaishesa, sai satar kallonsa sukeyi saboda ?yawun da yay musu, su baba dai duk sun fice wajen nema.

?akin Ayyah ya shiga suka buWe kayan da yazo dasu aka fiddama kowa tsarabarsa a gidan gwargwadon bajintar da ya nuna ta ?arfin aljihunsa.
Amma abin birgewa kowa aka bamawa sai murna yake da nuna jin daWinsa, sunata jera masa godiya.
Koda ya shiga Wakin gwaggo ya ajiye mata kuWi sai cewa tai  Ita Yaya ka batane .
Kasa ha?uri yay saida ya kalleta, yasan Ayyah ta wuce gaban raini a garesa, kuma duk abinda ya siya musu tare ya sai musu, kuWinma ya bata itama, amma saiya Wan ?arama Gwaggo wani abu matsayinta na mahaifiya, duk da yasan halinta dakamar wahala ta amsa, dan itama Ayyah idan su yaya maryam sukai mata alkairi inhar babu na Gwaggo bata amsa, sai dai idan ta raba musu dai-dai........
 Magana nake maka ka zauna kana kallona .
Murmushi yayi yana du?ar da kansa, yace,  Eh Gwaggo na bata .
 To ALLAH ya saka da alkairi, ya ?ara buWi na alkairi .
 Amin ya rabbi ya faWa cikin jin daWi sosai.

Daga haka sake dawowa yay wajen abokansa ya basu tasu tsarabar, yaWan zauna suka taSa hira bayan sun dawo sallar zuhur, ya jima sosai a wajen suna shan shafta irin tasu ta abokan da suka sha?u tun ?uruciya kafin ya tashi shi da Sufyan su nufi shago dan yanason yanka Winkin Rumana ya samu kafin dare ya haWa mata.
Yana aikinsa suna hira da bama juna labarin yaushe gamo...........
'



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=?-?=?O? [7/28, 1:22 PM] Haleemat M Musa: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*=?O?
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


*_GDW_*



*(21)*



...........Napep Win daya Wakko Ahmad na tsayawa a ?ofar gidan ruwan na ?ara ?arfi, Wari biyu ya mi?a masa, baiko tsaya amsar canji ba yace yatafi kawai.
Kusan tare da mijin Kausar da shima ya iso yanzu suka shiga, sama-sama suka gaisa yanama Ahmad barka da dawowa kowa ya shige Waki saboda saukar ruwan mai ?arfi.
Rumana da tun Wazun tai shirin barcinta, harta gaji da jiransa ta Wauki wani novel tana karantawa, zaune take saman gado ta jingina da fuskar gadon fitilar da batir yay sanyi na a kusa da ita gab yanda zataga rubutun.
Ajiye buk Win tai tana masa sannu.
Kallonta yay yana amsawa ya janye idanunsa, ?o?arin cire doguwar rigar jikinsa yayi yana faWin,  Kina ganin ruwa amma bazaki rufe ?ofaba? .
Kanta a ?asa saboda ganin zai cire riga tace,  kayi ha?uri Yaya, dan karna rufene kuma barci ya Waukeni kazo kaita bugawa banjiba .
Baice komaiba sai ?o?arin rufe ?ofar da yakeyi, hasken fitilar Wakin bai wani wadata ba, dan haka ya Wauka wayarsa ya kunna fitilarta, sosai Umm-Ruman ta kuma takura, amma ta lura shi ko a jikinsa.
Ganin yanda ta takura kantane ya sakashi buWe jakkar kayansa ya Wauki farar t-shart ya saka, duk da yasan idan zai kwanta saiya cire saboda hakan ya zamar masa sabo.
Sai a lokacin Rumana taWan samu sukuni, dukda ba iya kallonsa taiba daret tadai samu zarrar mi?ewa ta kawo masa ruwan sha.
Amsa yay yasha, dan Wan gudun shigowa gida da yay ma?ogwaronsa harya bushe, kallo ?asa-?asa ya bita dashi, ta canja kayanta ta saka doguwar riga mara nauyi ta barci har ?asa, sai ?amshi ne mai daWi ke fita daga jikinta.
Dan duk yanda Yaya Raheenatu da Sakina suka koya mata bata mantaba, sun tabbatar mata koda wasa karta bar jikinta babu ?amshi musamman da daddare idan Ahmad na gari, hakan ne data tuna ya sakata bayan fitarsa taje tai wanka duk da tana kallon su Kausar na gulmarta bata kulasuba, tazo ta shafa mai sama-sama saboda zafin hadari daya Waure garin, tabi lungu da sa?o na jikinta da khumra sannan ta zira doguwar riga tai zaman jiransa tana karatu......
 Yaya zaka ?ara cin abincine? .
Tai maganar tana dur?ushe a gefensa.
Bai bata amsaba, sai hannunsa daya mi?a ya kamo nata ya mi?ar da ita, batai masa musuba, saboda tun fil azal babu wannan wasar tsakaninsu, kusa da shi ya zaunar da ita har jikinsu na gogar juna, hakan ya saka Rumana Wan takure jikinta.
Abinda Iya ta bashi ya mi?a mata,  Gashi inji iya kisha .
Sai da ta kallesa, ganin shima ita yake kallo tai ?asa da nata idon tana amsar robar dake cikin ba?ar leda, ta cire ledar tana jujuya goran a hannu, Ahmad ya katse tunaninta da faWin tace,  Kisha Waya bisa huWu . Daga haka ya mi?e tsaye.
Rumana nason tambayar minene amma tanajin tsoro, sai kawai ta buWe goran ta mi?e ta Wakko kofi ta zuba, yanda abun ke zuba a kofin da kauri sai taga kamar zuma, sai dai wannan ?amshin kayan yaji yake tunma kanta kai bakinta, ganin yayi dai-dai da yanda iyan tacene yasata rufewa takai kofin bakinta, sosai za?i taji, dan haka mamaki ya isheta, amma da yake dama can ita sha zumamuce wajen ?waWayin abu mai za?i saita shanye kayanta harda suWe kofi=??.
Shi dai Ahmad tuni ya haye gadon yana kwance yana danna wayarsa, sai dai rabin hankalinsa naga kallon Rumana.
Tashi tai ta Wauraye hannunta da kofin cikin roba sannan tasha ruwa, ta gyara labulen da iska ke Wagawa ta dawo cikin Wakin sosai tana Waukar tabarma danta shinfiWa a ?asa, tunda taga Ahmad ya hau gadon, itama kuma a ranta tanaji ya cancanta ta barmasa ya kwanta kodan daWewar da yay bai hauba, dukda itama ba hawan takeba, dan tunda ya tafi a ?asa suke kwana dasu Salima, sun fara kwana a gadon tare, amma randa yaya Maryam tazo taita musu faWa akan hakan da sukai ai tsageranci ne, gadon da yayansu ke kwana zasu hau su jeru suna malelekuwa akai? Karta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login