Showing 60001 words to 63000 words out of 87750 words

Chapter 21 - GUDU DA WAIWAYE bilyn abdull

29 Jun 2024

13347

hana Zainab wucewa, dan kallon da Ahmad ke mata duk ya sakata ruWewa, kamar zatai kuka tace,  Ki zauna su Fa'iza su zo mana, ?ilama Yah Madan yazo anjima saiki bisa .
Zainab taWan ?walalo ido waje tana fadin  Kai, Yaya Rumana ALLAH Ayyah dukana zatai, gara dai na tafi, gobe zan dawo .
Ahmad dai duk yana jinsu amma uffan bai ceba, yama ajiye kofin ruwan ya koma latsa wayarsa daya sake, dukda ba sabuwa bace tayi ?yau dan batasha wahalaba sosai.
Hamsin Rumana ta bama Zainab,  Tunda kin?in Zee shikenan, gashi saiki hau napep .
 Kima barshi Ayya naira sittin ta bani kuWin zuwa da komawa, kin gani zainab ta ?are maganar da nunama Rumana sauran talatin Win tana ?o?arin fita.
Ba yadda Rumana ta iya dole a gaban idonta zainab ta wuce.

Kanta a ?asa tanata faman gyara gyalen danya rufe mata ?irji ta maida hankalinta ga Ahmad da har yanzu bai daina latsa wayarba.
 Yaya a saka ruwan wankane ko zaka fara cin abincin? .
Ba tare da ya bar abinda yakeba yace,  Sakamin ruwan, dan zafi nakeji .
Da  To ta amsa, ta sanshi dason wanka da ruwan zafi dan haka ta Wakko na filas data saba ajiyewa ta juye a botiki ta fita danta sirka masa.

Da sauri Maman Ama da Kausar da suka haWa kai suna gulma a ?ofar kicin suka hau washe baki kamar gaske.
 A, Amarya barka fa ?an tafiya an sauka lafiya .
Umm-Ruman ta amsa da  Yawa, ngd .
Tasan dai gulmarta sukeyi, tunda kullumne babu fashi, har ma?wafta surutu suke zuwayi akan wai Yah Ahmad ya watsar da ita tsahon wata shida ya?i dawowa, ?ilama ya gudune, idan iyayenta sukaji zasuzo su kwasheta itada kayan tunda mai gidan haya dai ba lamuni zaiyiba idan shekara ta ?are.
Yanzukam gulmarta suke akan wai ashe tasan mijinta zai dawo shiyyasa taketa Sare-Saren gyara jikin tarbarsa, amma da suka tambayeta sai tace kwalliyar bikice.
Kausar harda cewa,  Yo kwalliyar iyakar fatar ido dai zata tsaya tunda ba wata uwa zai iya mataba .
Sosai maman Ama taita dariya da faWin,  Wa yaga lagwani shinema Rumana ta fito ta ritsasu.

Sai da taWan sake Wauraye masa bayin sannan ta ajiye ruwan ta fito.
A ?ofar Waki ta iskesa zai fito, hannunsa ri?e da abin wanka da brush da ya sakama makilin, ta matsa ya wuce bayan ya ajiye takalman daya fiddo na silifas.
Aiko harya shige banWaki su maman Ama na binsa da kallon ?urilla, so suke suga abin kushewa a samu nayi, sai basu ganiba, dan saima wata ?iba data ?ara masa cikar zati da kwarjini ya ?aro.
Sai suka koma faWin, ba dole ya narko ?ibaba yanacan yanacin daWinnsa ya bar Rumana anan cikin wahala daga fara da mai sai wainar filawa.
Karaf sai zance a kunnen Umm-Ruman data fito Wauraye filet Win da zaici abinci.
Kanta kawai ta girgiza tana mamakinsu ta koma Waki abinta dan gulma ta rufe musu ido basuko farga da itaba.
Koda Umm-Ruman ta koma Waki sai ta Wauki turaren tsinke ta sake kunnawa, duk da dai da safema ta kunna, kuma Alhmdllh ?amshin ya kama Wakin saboda nacin saka turaren da takeyi ga firishina ta haWawa da yaya maryam ta kawo mata mai Wan yawa, tanata Soyen abunta sai kaWan- kaWan take sakawa har turaren wutarma, na tsinkenne dai kullum saita kunna saboda da yawa aka kawo mata su..
Tana ?o?arin kunna fitila saboda duhun magriba da garin yayi Ahmad ya shigo Wakin da sallama, Amsawa tai ba tare data juyi ta kallesa ba saboda kunya, duk da tasan akwai jallabiya a jikinsa kuwa.
Batai auneba taji hucin mutum a bayan, cikin Wan hanzari ta juyo, Ahmad dake tsaye a bayanta ya mi?a hannu zai Wauki robar mai dake saman madubin, gefe Rumana ta matsa, duk da hakan kuma jikinsa na taSa nata saboda lungun wajen baida girma sosai.
Baice da ita komaiba, duk da ya lura da yanda taketa zare idanu, ya Wau mansa ya zauna abakin gadon danya shafa, ganin ta?i wucewa ya Wago fararen idanunsa ya Wan kalleta.
Saurin raSashi tai ta fice, ya bita da kallo kawai yana girgiza kansa.
Tana alwala a bakin rijiya yazo ya wuce zai fita massalaci, ta sha?i ?amshin turaren daya saka tana binsa da kallo, sosai taga canji daga garesa, sai taga kamar an wani canja matashi, dan yanda jikinsa kawai ya murje zai baka amsar tafiya tayi riba.
Da wanna tunanin ta shiga Waki itama ta kabbara salla.

Ana idar da sallar magriba sai gashi ya dawo, a bakin gado ya zauna dai-dai tabarmar data Wora kayan abincin, waya yakeyi, dan haka ta matso ta fara zuba masa abincin a filet, harta kammala zubawa yana wayarsa, sai dai idonsa na kanta kamar ya samu talabijin, dukda tanajin yanda idonsa ke yawo a jikinta tunWazun ita bata yarda ta kallesanba.
Kauda kwanikan tayi gefe yanda zaiji daWin sakewa a wajen sosai, ta yun?ura da niyyar ta mi?e kawai babu zato taji ya ru?o mata hannu, kafin ta gama tantance gaskiyar lamarin ta tsinci kanta Ware-Ware bisa cinyarsa.
Kasa magana tayi dan matu?ar al'ajabinsa, ga jikinta sai wani yamm yakeyi, Ahmad ya ajiye wayar gefe tare da kallonta sosai, yanda yake kallon fuskarta babu wani alamun jin ba daidaiba ne ya sakata kasa jurewa ita, gashi fuskarsa sam babu walwala, kamar dai yanda ta saba ganintane acan baya.
Hannu ya saka ya Wago da haSarta yana ?o?arin zare hijjab Win, bata hanashi ba, dan batagama fuskar yin hakan daga garesaba, sai sake matse hannayenta take waje Waya illahirin jinin jikinta na gudu cikin kowacce jijiya da sauri.
Ya ajiye hijjab Win saman gadon ba tare daya tankaba, goshinsa ya Wora saman nata, mutuniyarku saita sake ruWewa, cikin in ina tace,  Ya..ya a...b in ....cin za..i zai huce fa .
Ahankali ya furta  idanma ya huce bakece kika ja ba? .
Babu shiri ta Wago idanunta sai suka afka cikin nasa, dan har yanzu goshinsa nakan nata, hancinsu gab da juna suna musayar numfashi, hakama bakinsu babu wata tazara duk da ita Rumana taWan du?ar da kantane ba kamar yanda nasa yake daret ba.
?asa ta sake maida idanun dan bazata jura kallon cikin nasaba, cikin muryar da ita kanta batasan tana da itaba tace,  Yaya ni kuma? .
Ahmad da muryar Rumana ta saukar masa da kasala yace,  Uhum mana, ke haka aka koya miki tarbar miji ne? Wata shidda bama tare amma sam banga wani murnar ganina ko kewata a tare da keba .
Karon farko da kanta ya kasa Waukar kalamansa, domin batai tsammanin wannan furucin daga garesa ba. Saita kasa bashi amsa, wasa dai taketayi da hannayenta dake bisa cinyarta, itako tana saman tasa zaune ko nauyinta bayaji.
Hannunsa dake zagaye da ?ugunta ya janye ya kamo hannayenta da taketa cuWawa waje Waya.
Sosai jan lallen da akai mata wanda ya gaurayu da zanen ba?i yayma choco fatarta dake kama da tasa ?yau, ya janye kansa daga goshinta yana sauke sassanyan numfashi tare da murza yatsun hannun nata duka cikin hannayensa.
 Tunda bakiyi murna da dawowar tawa ba, Wagani na koma inda na fito .
Da sauri ta girgiza kanta idonta na cikowa da ?walla  ALLAH yaya ba haka baneba fa, nayi murnar dawowarka mana .
Tsura mata ido yay, yanda idanunta suka kawo ruwa suna fidda wani ?yalli saboda hasken fitilar sun ?ayatar dashi, Wan yatsa ya Wora kaWan ya dangwalosu yayinda suka gangaro kaWan saman furkarta,  Har yanzu kina nan a shashasharki dai? .
Baki Rumana ta kumbura kaWan wai ita dole taji haushi ya cemata shashasha.
 Haushi kikaji?
Yay maganar cikin kunnenta yana sunsunar dokin wuyanta dake kamshin khumrar data shafa.
Da sauri ta sinne kai ?asa, jikinta na Waukar ?yarma saboda sabon al'amarin da yakeyi mata.
Baki yaWan taSe yana saka hannu ya Wago haSarta suka kalli juna,  Oh jan ajine komi? .
Kasa jure kallon tayi tana janye idanunta,  A'a kawai dai banyi zaton dawowar taka bane ba yanzu . Tai maganar cikin sar?ewar halshe.
Karon farko yayi murmushi har ha?oransa na bayyana, ya yun?ura tare da mi?ar da ita shima ya mi?e, harkan tabarmar suka isa hannunsa ri?e da nata, ita dai ji take tamkar ta tsilla da gudu, sai da suka zauna sannan ya saki hannun nata, yakai hannu ya jawo filet Win abincin gabansa ya faraci ba tare da ya sake cewa komaiba.
Rumana dai na zaune duk a takure, addu'a take ALLAH ya kawo mai belinta yanzun nan, sai dai addu'ar tata bataci ba, dan kuwa har ya kammala cin abinci babu wanda ya shigo, sai motsin matan gidan da suke jiyowa daga tsakar gida.
Shikam Ahmad yanacin abincine idonsa akanta, musamman ma ?ushinta data gama tsole masa idanu tun shigowarsa gidan, amma da yake jarumin dakewane bazaka taSa fahimtar hakan akan fuskarsa ba.
Ya kammala cin abincinsa tsaf sannan yasha ruwa yana yin hamdala, dai-dai nan aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i.
Wayarsa ya Wauka yay kiran wani da taji yana ambata da Nura, kusan mintuna biyu suna wayar sannan ya kashe, mi?ewa yay tsaye yana zira wayar cikin aljihun jallabiyarsa,  Bara naje salla, daga can zanje gidan dan bamu gaisa dasu baba ba .
Kan Rumana a ?asa tace,  Saika dawo a gaishesu .
 Uhum ya faWa yana ficewa daga Wakin.

Sai da Rumana ta jiyo fitarsa daga gidan gaba Waya sannan ta sauke numfashi tana murmushi, ta kalli hanunta sosai da yasha murza a nasa ta lumshe ido, wai yau itace bisa cinyar Yah Ahmad zaune Wane-Wane, yana mata magana cikin taushin murya da sanyi.
Duk da tasan ba sonta yakeba hakan ba ?aramin daWi yay mataba, salla ta mi?e ta gabatar sannan ta zauna ta cinye sauran abincin da ya rage a filet Win tana mai jin wani tsagwaron nishaWi...


&&&&&&

Koda aka idar da sallar isha'i Ahmad gidansu ya nufa, inda ya samu damar gaisawa da kakanninsa da iyayensa maza, waWanda yayi mamakin baiji sun rufeshi da faWan rashin dawowarsaba, dukda yayi tsammanin hakan kuwa, ko baba baice dashi komaiba akan hakan.
Yanzun kam har Waki ya shiga ya samu gwaggo ya sake gaisheta, duk da bata sake masaba sai da ta jero masa tambayar ya hanya da sauransu.
Yaji daWin kulawarta, dan haka ya amsa yana faWaWa fuskarsa da fara'a.
Ba tare data kallesa ba tace,  Kai yanzu nan kana ganin abinda kayi mai ?yaune? Ka tafi kabar ?ar mutane har tsahon wata shidda? Kana ganin inda badan gida bane iyayenta zasuyi shiru su zuba mana idanu? .
 Nasan ni mai laifine Gwaggo, amma dan ALLAH ku gafarceni, wlhy inda ALLAH yay zaman nawa mai nisane, sannan harna kwashe kusan watanni uku bana fuskantar komai a sana'ar tawa, saboda bada jari najeba, lokacin ko kuWin motar dawowa aikine a gareni, amma insha ALLAHU bazan sake kwatanta hakanba, kuma ALLAH ya huci zukatanku, itama zan bata ha?uri na kuma nema gafararta .
Shiru gwaggo tayi kamar bazata amsashi, sai kuma zuwa can tace,  Shikenan, ALLAH ya yafe mana baki Waya, abu na gaba shine karnaji wani abu daban agareka cikin hidimar bikinnan, babu ruwanka da sabgar yarinyarnan komi zasuyi, ka kama kanka ka kama girmanka, suma su Mudanseer ka sake gargaWinsu akan karnaji karna gani .
 Insha ALLAHU gwaggo an wuce wannan wajen yanzu, babu wani abu saSanin mai daWi da zakiji, ni yanzu babu wani abu daya shafeta da yake a gabana sam .
 Hakan ya fi .
Gwaggo ta faWa a ta?aice, daga nan shiru Wakin ya Wauka babu wanda ya sake cewa uffan a cikinsu, shi dai Ahmad badan hirar ta ishesa bane, haka ita gwaggon, tadaiyi shirune saboda dama tun fil azal babu irin wannan sabon na doguwar hira a tsakaninsu.
Kusan mintuna biyar saima ta mi?e ta fice tabar masa Wakin gaba Waya.
Sassanyan murmushi yayi yanajin ?aunar mahaifiyar tasu cikin ransa, maimakon tace ya tashi yaje, shi yaga ta koresa shine ita ta bar masa Wakin dan kar ace ta saka Wan fari a Waka suna hira.
Kai shikam bazai yarda Rumana taima ?arsa ko Wansa na fari wannan abunba gaskiya, dan kuwa akwai cutuwa, yanzu shi badan gwaggon ta samu Ayyah mai ?ya?y?yawar zuciya ba da yaya kenan?.
Mi?ewa yay yaje ya haye gadonta ya kwanta kamar yanda yakeyi a Wakin Ayyah.
Gwaggo dake tsakar gida tana ?an kaye-kaye saboda ganin hadari sai zuba ido take taga ya fito amma shiru, gashi Ayyah na sashen baba saboda yau itace da girki, yaran kuwa duk sun fice wajen kamu sai Zainab kaWai a gidan itama tana sashen su Samina.
?akin ta dawo dan taga mi yakeyi a ciji da bazai fito ya tafi gidaba gashi har goma tayi, dan taskar labaraima akeyi a redio.
Sosai mamakin ganinsa saman gadonta ya kamata, dan sam koda yana yaro ba Wabi'arsa bace hawar mata gado, sai da Wakin Ayyah.
 Kai lafiyarka kuwa? Wace irin Wabi'ace wannan? .
Dariyace taso kufcema Ahmad dako motsi baiyiba, amma sai ya daure ya haWiye da ?yar yana faWin  Oh gwaggo bakiso na hau sai ?a?anki kawai su Mudan? To nima ai suna hawa gadon Wakinmu idan sun shiga shiyyasa na rama, kuma wlhy ki tambayi Ayyah kiji .
Ayyah dake tsaye bakin ?ofa ta kwashe da dariyar sha?iyancin Ahmad,  ALLAH ya shiryeka Wan albarka, ammafa kamin dai-dai, maza ka rama mana kuwa muma hawar mana gado da ?a?anta keyi ehe .
 Yauwa Ayyah ta, shiyyasa kike burgeni akan faWar gaskiya .
Harara Gwaggo ta bankama Ahmad tana cije baki,  Tashi ka fitarmin a Waki fitsararren banza kawai .
Kasa daurewa Ahmad yay ya sakko yana dariyar yanda Gwaggo ta haWe gabas da yamma kamar zata makesa, yayinda Ayyah ke tayashi daga waje tana faWin,  Kaga fito kama tafi gida karta makemin kai daga dawowa .
 Aifa ganinan Ayyahna .
Gwaggo dai bata tanka musu ba, duk da tana jiyosu suna mata dariya a tsakar gida har su Fa'iza suka shigo.
HaWe fuska Ahmad yay yana kallonsu, dukansu sunsha jinin jikinsu duk sai sukai tsaye suka kasa ?arasowa.
 Daga ina kuke a wannan lokacin!? .
Tuni jikin Sadiya ya fara Sari, hakama Salima uwar tsoro, sai Fa'izace cikin ?arfin hali tace,  Yah Ahmad wajen kamu .
 Kamu?, har zuwa wannan lokacin da yake baku da hankali? .
Guri Waya duk suka cure saboda tsawar da yay musu.
Ayyah tace,  Wlhy nima tun Wazun abin ya dameni, babanku ma sai faWa yakeyi, namazo ne nai maka maganar kozaka tura Abu yaje ya kirasune .
Sosai ran Ahmad ya Saci, yace,  Okey sabon iskancin da yazo muku a kai kenan saboda bana gidan? .

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login