Showing 3001 words to 6000 words out of 87750 words

Chapter 2 - GUDU DA WAIWAYE bilyn abdull

29 Jun 2024

13337

tana jinjira, haihuwarta biyu acan zaman ya?i daWi ta kashe auren ta dawo kano da Samina, dan wancan mijin ya kwace ?a?ansa.
Tunda kowa ya fahimci hakan a gidan sai ya fara jan Samina jikinsa, yayinda Ahmad yaytama Kawunsa Yusha'u naci akan ya dawo da mama gaje mahaifiyar Samina gidan dan ALLAH.
Da taimakon Ahmad daya kama kafa dasu Iya Ladi Mama Gaje ta sake dawowa gidansu, inda Samina da Ahmad suka kasance ?ar?ashin inuwa Waya.
A wannan karon Mama gaje da shirinta ta dawo gidansu Ahmad, dan kuwa sai da ta gama mallake zuciyar kowa musamman Malam Rabi'u da Iya Ladi.
Dawowarta kuma gidan ya sake Waukar sabon salon zama, sai dai kowa na dannewa da kawaici saboda yanzu akwai ?a?a a tsakani.
Da taimakon Ahmad dukan yaran gidansu suka samu shiga makaranta a yanzu, musamman ganin ita Samina tanayi tunda ba'a gidan ta tashiba.

A haka har Samina itama ta shigo sakandire Win dayake maza da matane a haWe, hakan ya saka sha?uwarsu ta sake ?arfi mai ban mamaki, tana aji Waya yana aji biyar, amma ko yaushe suna tare, hakan yasaka abokansa suka fara kiransa da suna Sharukhan baban soyayya=??............
'



_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* =؋?d'?NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* =؋?d'?NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* =؋?d'?SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* =؋?d'?NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* d'?=؋?NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN=?G?=?G?_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin=?G?=?G?
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*=?G?=?G?

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuWi gida masoyan asali=? ?=?;?>?p?>?p?=?
?=?
?=??=??=?L?

Mucigaba da shakatawa da wannan kafin a fara kafta WASAN=??=?I?



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=?-?=?O?



*_ B&?GUDU DA WAIWAYE.....!!_*
_(Shi ya kawo mugun zato)_


*_Bilyn Abdull ce>??


*(2)*


.............Yakanyi dariya kawai, dan a sannan ba soyayyar bace a tsakaninsu, duk da dai ta musu kamu basu saniba.
Tun ana yaya da kawa har abin ya fara rikiWa yana zama soyayya, soyayyarma mai ?arfi da sha?uwa, kowa ya san da hakan a cikin iyayensu kuma duk da iyayen Ahmad mata basuso hakaba saboda mugun halin Mama Gaje.
To Amma ya zasuyi da hukuncin UBANGIJI? Dole suka Wauke idanunsu suka koma musu addu'a da fatan ALLAH yasa kar Samina tayo gadon halin Uwarta.
Bayan Ahmad ya kammala sakandire saiya fara bin mahaifinsa kasuwa wajen sana'arsa ta saida yadikan maza da huluna, amma sai baban yace da hakan ai gara ya koya koda sana'ar Winkice ko wani abun.
Ahmad ya aminta da hakan Wari bisa Wari, dan haka yashiga wani shagon koyan Winki anan bayan layinsu kusa da makarantar su samina.
kusancin da suka samune ya kara sake ?ullesu sosai, dan kullum daga gida Ahmad da Samina tare suke tahowa, saiya rakata makaranta zai dawo shago wajen aikinsa.
Sannan da an tasosu daga makaranta komi yake a shago sai ya ajiye ya rakata har gida, wataranma sake biyoshi shagon ta keyi, data shiga gida babu daWewa zata fito wajensa su koma tare..
?an shagon kan musu dariya, musamman da suke ganin sunyi ?anana, badai za'ace za'ai musu aure a wannan shekarunba.
Lokacin da Baba ya fahimci wannan shashancin nasu sai yaytai ma Ahmad Win faWa, yakuma ce karya sake ganin Samina ta bishi shago bayan ta dawo makaranta.
Yaji faWan baba ya dakatar da Samina, amma dukda hakan wataran saita Wan zagaya a Soye taje, musamman ranar weekend da babu karatu.
Shekararsa Waya a shagon aka yayesa, zuwa lokacin kuma ya kware a aikinsa sosai dan ya nuna ?wazo matu?a.
Ayyah ta fasa Wan asusunta da takeyi da ribar kayan sana'arta ta siya masa keken Winki, yayi murna sosai, hakama yan uwansa sunyi farin ciki, wani Wakin dake cikin gidan aka fasama kofa ta baya aka saka masa keken Winkin, sai yazama shike Winkama baba yadika ana kaiwa kasuwa a siyar Winkakku, sai kuma masu kawowa da yakemawa, harma na mata yana dan jagulawa dukda bai wani ?wareba saboda dinkin maza ya koya.
A hankali hannunsa ya fara faWawa akan dinkin matan ma, kafin kace mi komai ya zama Alhmdllh, harma yana taimakawa gidansu da abinda ALLAH ya hore masa, gefe kuma yanama Samina hidima sosai dasu ta karatu da bu?atun yau da kullum.
Ganin yasamu madogara kuma yana samu Alhmdllh sai yay aniyar komawa karatu.
Kowa ya bashi goyon baya, dan haka ya shiga kokarin neman gurbi a jami'ar b.u.k.
Ya samu shiga jami'ar B.U.K, dayake takardunsa sunyi ?yau sosai, kuma a lokacin tsadar rayuwa batakai hakaba sosai.
Komawarsa makaranta yasakashi sake zama busy, ko Winkima sai yayi da gaske yake samu yaWanyi, ga kuma aikin yana samu, ganin zai iya korar customers ta wannan hanyar sai ya fara koyama ?aninsa Mudanseer shima, aiko Alhmdllh Mudanseer ma sai ya maida hankalinsa sosai, sai ya zam yana taimakawa Ahmad Win da wasu ayyukan.


Tunda Ahmad ya shiga rayuwar Samina ya fara canjata sai baba Yusha'u kejin daWi sosai, dan abubuwa da yawa sai Samina tabar biyema mahaifiyarta, dan a hannunta ta tashi, lokacin da mama Gaje ta dawo gidansu Ahmad sai tarbiyyar Samina ya banbanta dana sauran yaran gidan.
DaWin hakan da Baba Yusha'u ya jine ya sashi zaunar da ?an uwansa duka a gaban iyayensu su iya ladi, aka kuma kira masa Ahmad da Samina, a gaban kowa ya kuma sake dam?a ma Ahmad amanar kula da Samina, tare da al?awarin aura masa ita a duk lokacin da suka kai munzalin girma, ya kumace ko bayan babu ransa bai yarda wannan al?awarin ya tashiba.
Murmushi kawai Ahmad yayi kansa a ?asa saboda kunya.
Yayinda sauran ?an uwa da tsoffi su malam Rabi'u wannan abu yay musu daWi, dankuwa koba komai zumincin ?a?ansu zai ?ara dan?o da ?arfi.
Albarka kowa ya sakama abin, tare da addu'ar kaiwa lokacin da rai.

Tun daga wannan lokacinne kuma Samina bata kula kowanne namiji, kowa yasan an mata miji Ahmad, hatta da danginsu na Shema kowa yasan hakan.
Mama Gaje dai batace hakan bai mataba, bakuma taji a ranta zuwa nan gaba idan Samina ta sami wanda yafi Ahmad zata hanata barin Ahmad Winba, idan kuma Ahmad yayi arzi?i dama ta dawo hannunta, dan kuwa sai yanda tayi dasu Ayyah akansa.

Tunda Ahmad ya gama secondary ya koya Winki yana kama ?an kuWaWe sai nauyin Samina ya kusan koma kansa, shine duk wani bukatunta na makaranta, shine dinkinta da bukatun yau da kullum na Wiya mace, hatta dasu kayan ciki na mata bai gazaba wajen bata kudin saye.
Wannan hidima da yake da ita sai ta ?ara saka mata girmansa da ?aunarsa a zuciyarta, bata da hira sai ta Ahmad, duk wani namiji a idonta mace ne, Ahmad Wintane kawai take kallo da gashin arzi?i, shine kuma kawai nagartaccen namiji a idonta.
Bayan samina ta gama secondary lokacin Ahmad na shekararsa ta ?arshe a jami'a sai yake bata shawarar komawa karatu.

Lokacin suna zaune a ?ofar gidansune a shagon Winkinsa suna hira, dama mafi yawan lokuta anan suke hirar tasu.
Kallonsa tayi da Wan murmushi ta dukar da kanta ?asa saboda kunyarsa, cikin muryarta mai cike da yanga tace,  Haba Hubby, kamar ka manta yanda al'amuran suke a gidannan namu, idan nace zan cigaba da karatu yanzu a ina baba zai samu kuWin Waukar nauyina?, kullum ana haWa na masara da ?yar a ina za'a samo na karatu kuma?, sannan a ziri'ar mu kaf babu macen data taSa gama secondary sai nifa, shima da taimakonka, saiko ?annenmu uku mata da ayanzu suma zasu kammala, iyayenmu ma bazasu amince naje jami'a ba nima nasani .
Murmushi Ahmad dake kallonta da tausayawa yayi, ya sauke ajiyar zuciya har lokacin idonsa a kanta, a hankali yace,  Samie na ai komai na ALLAH ne, indai kina da ra'ayin karatun baki da matsala, dan ba baba zamu dorama wannan nauyinba, nine zan Wauki nauyin matata da kaina, kinga insha ALLAHU idan ubangiji ya shige mana gaba sanda zaki kammala ?ila koda karamin aikine na samu, sai maganar aurenmu ko, kodama baki gamaba inhar aka samu Wan abin rufin asiri sai mu rufama kanmu asiri a wankemu a mi?amu daga ciki kowama ya huta .
Maganarsa ta ?arshe ce ta sakata jan hijjab Winta ta rufe fuskarta saboda kunya tana ?ar dariya.
Shima dariyar yayi mai sauti yana shafa kansa, yace,  Sorry bazan sake bama matata kunyaba, ammafa randa aka kaimin ita zan cire kunyarnan dukanta insha ALLAHU .
Babu shiri Samina ta tashi ta gudu zuwa gida, duk kiran da Ahmad yake mata akan ta dawo su karasa magana kasawa tayi, dole ya ha?ura ya ?yaleta.
Daya shiga gidan suka haWuma da sauri ta kauda fuska ta?i kallonsa, lokacin suna a tsakar gida itada su Rumana suna shafa kurkur a fuska.
Murmushi kawai yay yana Wauke kansa, dan baya wasa da yaran gidan, idan ka cire Samina babu mai yawan ganin ha?oransa a cikinsu.
Duk sannu sukai masa, ya amsa kamar yanda ya saba, sai da yazo gab da shiga sashensu ne suka haWa ido da Samina data saci kallonsa.
Ido Waya ya kashe mata yana murmushi, tai saurin Wauke kai tana murguWa masa baki.
Shigewa yay yana maijin nishaWi da ?arin kaunarta a ransa.

Da daddare Samina take sanarma mahaifiyarta yanda sukayi da Ahmad.
Mama Gaje da daWi ya lulluSe ta washe baki tana rungume Samina.
 Yo Samina wannan kuwa abin amincewane da guduma, damacefa tazo mana, ai wannan yaro bamusan abinda zamuce masaba a rayuwa, ALLAH dai ya saka masa da alkairi, yakuma kaimu lokacin aurenku, dan kuwa Suwaiba ta haifama Ru?ayya, niko Ru?ayya ta rainar mini .
Duk da Samina bata fahimci zaurencen mahaifiyarta na ?arshen maganarba Babu kunya ta amsa da amin, dan tana tsananin son Ahmad da har takai batajin kunyar yin duk wani abun daya shafesa a gaban kowa, iyayensu maza kawai take iya Wagama ?afa akan Ahmad.
Hatta kakanninsu Iya ladi da baba Rabi'u bata jin kunyarsu akan Ahmad.

Sai washe gari Ahmad ya samu sa?o a rubuce daga wajen Samina akan amsar cigaba da karatunta.
Yaji daWin hakan sosai, a ranar kuma ya samu su baba da batun su duka harma da kakanninsu.
Da farko dai tsoho mai ran ?arfe malam Rabi'u har yace a'a, danshi kam baiga dabara ba a wajen nan sam.
Amma sai Ahmad yayta lallashinsa da nuna masa ra'ayinsa akan matarsa tai karatu mai zurfi, tunda yanzu suna da dama saita fara kafin shi yaWan samu madogarar da za'ai hidimar aurensu, in yaso ita saita ?arasa karatun a gidansa.
Fatan alkairi yay musu, tunda ya fahimci Ahmad nason lamarin, bai kamata a katse masa hanzariba matsayinsa na babba namiji a gidan.

Kwana biyu dayin zancen Ahmad ya amshi takardunta ya tafi dasu makaranta.
Tun daga ranar Ahmad yashiga faWi tashi wajen ganin ya samawa Samina gurbin karatu, kasancewarsa mai ?okari a makarantar yasashi kusanci da mafi yawan malaman cikinta, ta hanyarsu ya samawa Samina gurbin karatu.
Lokacin da labarin hakan yazo mata tayi farin ciki harma ta rasa ina zata saka kanta dan daWi.
Hakama iyayensu kowa yaji daWi, babu kuma wanda ya nuna rashin dacewar hakan, dan a ganinsu Ahmad Win yanada ra'ayin matarsa tasamu karatu mai zurfi shiyyasa ya maida Saminar makaranta.
Sauran ?an uwantama ?ammatan gidan sun tayata murna da wannan cigaba, koba komai suma zasu saka ran cigaban tunda aka fara daga kanta.

Nauyin karatun Samina daya dawo kan Ahmad sai ya sa abubuwa suka sake masa yawa, dan kuWin shigarsa basu kai nauyin Wukar hidimar da yakeyiba, gashi dai-dai da kuWin mota wannan sai Samina tazo wajensa take amsa. Ga nauyin karatun Mudanseer ma shine yake bada mafi yawan ?arfinsa, dukda mahaifansu na taimakawa tanan San garen.
Kuma a gefen hidimar gidama baya zuba ido baneba, yanayin ?o?arinsa wajen taimakon mahaifinsu.
Wannan abubuwan da sukaimasa yawane ya sakashi fara tunanin faWaWa neman kuWin nasa, akuyarsa da ya saya Ayyah na kula da ita yace zai saida ya zuba kayan Winki na saidawa, saboda akuyar ta haifi yara biyu sai Ayyah ta amince masa aka saida, da kuWin akuyar yaWan sayo kayan su zare da wasu ?ananun abubuwa irinsu allura, almakashi, zips da sauransu ya zuba a shagon, teloli dake cikin gida da masuma shagunan dake kusa sai sukanzo sukan saya anan, kamar wasa sai ALLAH ya sakama abin albarka ake ciniki, idan duk suna makaranta sukan Wan Webo kayan sayarwar a ajiye cikin gida, duk wanda yazo saya sai yayi sallama a bashi.
Ahmad bai tsaya ananba kawai, har komawa yay idan ya taso makaranta ya sari lemuka ya Wora a kansa yana zuwa bakin titi saboda motoci masu wucewa, wani lokacin kuma biredi, ko kayan fruits haka.

Da waWannan sana'oi da wahalhalu Ahmad ya cigaba da kula da karatunsu shi da Mudanseer da samina, sauran ?annensa ma yakan basu gudunmawa, hakama yayunsa dake gidan aure sukan taimaka masu da abinda ALLAH ya hore musu.
Ahmad ya kammala degree Winsa ya samu yay bautar ?asa, daga nan kumane ya dawo zaman gida sosai, dan babu dai maganar aiki.
Yaci gaba da sana'oinsa na Winki da saida kayan Winki, zuwa yanzu kuma hannunsa ya faWa sosai ya ?ware, Winkuna yake na zamani masu birgewa, duk wasu samari ?an kwalisa da ?ammata zaka samu Winkinsu ya fitone daga shagon Ahmad, wanda aka fi sani da Ahmad sharukhan, idan Winki yaWan kwanta saiya koma sana'arsa ta sai da lemo da ruwa, kokuma kayan fruits.
Yanzu dai haka takai Ahmad yana hayar keke napep ne, yay Winkinsa da yamma ko dare, da safe zuwa la'asar yana neman taro da kwabo da adaidaitarsa a gari.

Matsala ta farko data fara shigowa tsakanin Samina da Ahmad shine, bayan barinsa makaranta Samina tayi sabbin ?awaye, sanda yana nan koda yaushe suna tare, sai dai lokacin karatune zaka samesu ba tareba, duk wanda ma yake mu'amula dasu yasan suWin masoyan junane.
Samina tun tana secondary takanyi karatun novels Win hausa, rayuwar jin daWi da dukiya da akeyi a novels na ?ayatar da ita, har wani lokacinma takanyi addu'ar ALLAH ya buWama Ahmad Winta shima yay arzi?i ya gina musu ?aton gida, ya narka musu kayan alatu da jin daWi, su ringa hawa motoci na alfarma ita dashi.
A wancan lokacin burin nata bai taSa kaita ta nemi canjin Ahmad da masu irin suffar jaruman littafiba, shiWin dai takema addu'ar ya samu su mora.
Takai koda Samina ta karanta littafi sam bata wani damuwa da Waukar darussan rayuwa ko ilimin da littafin yazo dashi, ita kawai soyayya da kayan ?awane ke Waukar hankalinta da ?ara faWaWa burinta, tama kai inhar buk bana masu ?azamin arzi?i bane ?an gayu batason karantawa, data fara karatun taji ana faWin jarumin littafi nashan wahalar neman nakansa sai buk ya fitar mata akai ta ajiyeshi, tafi son taji ana suffanta ?yawun jaruman littafi tare da dukiyar da tunani bazai iya musaltawa ba, to takanji kamar tai tsalle ta ganta a buk Win saboda shau?i.
HaWuwarta dasu Nafy ne ya fara nuna mata hanyar samun cikar wannan burin nata, tun tanajin haushin kushe mata Ahmad da sukeyi akan talaucinsa har zuciyarta ta fara rawa da aminta da maganarsu.
Dan kuwa dai sunyi nasarar fara tsundumata shafe-shafen mayukan bilicin, dukda kuwa tanada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login