Showing 27001 words to 30000 words out of 87750 words

Chapter 10 - GUDU DA WAIWAYE bilyn abdull

29 Jun 2024

13332

abinda zai kawoma kowa kwanciyar hankali, ba tare da abinda muke gani dai-dai ya koma kuskureba. Son gaskiya nake miki Samina, wanda babu ta yanda idan na musalta za'a fahimceni, a tawa fahimtar ka bama abinda kakeso kowacce irin damar da yake bu?ata kuma zata kawo masa kwanciyar hankali da farinciki shine soyayya ta gaskiya, na fahimci a yanzu sam hankalinki baya gareni, to bazan tursasakiba, ni Ahmad Hamza Rabi'u ku shaida daga yau, na saki matata Samina saki daya, domin sadaukar da soyayyata ta gaskiya, taje ta auri wanda takeso, ALLAH ya basu zaman lafiya da zuri'a Wayyaba ._*
Ahmad ya ?are maganar yana share hawaye masu zafi dake gangaroma kumatunsa.
Tsit Wakin yayi, hatta da Samina sai da taji wani iri a ranta, amma tai saurin ture tausayinsa tana sauke numfashi irin na na rabu da ?aya Winnan.
Malam Rabi'u ya saki murmushi irin nasu na manya, cikin muryarsa ta tsufa yace,  Amadu ALLAH yay maka albarka, ALLAH ya tsare gabanka da bayanka, ya share hawayenka, ya sanya farinciki a rayuwarka har gaban abadan, lallai kacika namijin gaske mai soyayya dan ALLAH, inaji kuma a raina koda ba'a nan duniyaba zaka samu ?ya?y?yawan sakamako .
A tare baba Iliyasu da baba Yusha'u sukace,  Insha ALLAHU daga nan suma suka Wora da sanya masa albarka, baba Yusha'u yace,  Ahmad a karo na biyu inhar ka amince na baka auren Umm-Rumana, badan komai nake ?waWayin wannan haWinba sai ?yawawan halayenka, duk uba daya mallakeka matsayin Wa ya gama hayewa a rayuwarsa, hakama duk surukin da ya sameka matsayin suruki yaci riba, yanda naso wannan haWin zumincin bana fatar bijirewar wadda bata Waukeni da muhimmanciba zaisa gwiwa ta sarewa .
Murmushi nanma malam yayi, idonsa kafe akan Ahmad da ya kasa koda motsi, shida yake ?udirawa a ransa safiyar gobe zai bar garin gaba Waya yay nesa dasu shine za'a masa wannan dabaibayin kuma?.......
Cikin katsema Ahmad tunani malam yace,  Amadu inhar wannan haWin bai maka ba karka cutar da kanka, dan kuwa ba tilas bane a gareka, amma ni kaina nayi maka sha'awar hakan, dan Umm-Rumana yarinyar kirkice da kowane miji zaiyi fatan samu .
Innalillahi...... Ahmad yaketa ambata a ransa, wannan magana ta masa girma, shidai a yanzu bai dace ya bijirema iyayensa ba kodan abinda Samina ta aikata, sannan koba komai itama zai maida mata murtani, kamar kuma yanda yay al?awarin ha?ura da ita auren Umm-Rumana ne kawai zai tabbatar masa da hakan tunda ubansu Waya...
Ayyah ce ta dafashi, hakan yasa yay saurin kallonta, da ido taimasa alamar ya amshi auren, dan haka ya maida kansa ?asa ya du?ar yana faWin,  Na amsa baba, ALLAH yasa haka shine mafi alkairi .
Dandanan fuskar kowa ta washe da murmushi, banda Samina da mama gaje, dan mama gaje ma baki ta taSe ta mi?e ri?e da hannun Samina da tai gajeren tsa?i suka fice.
Babu wanda yabi takansu, balle a nuna an damu dasuma.


&&&&

A wannan daren kam inhar Ahmad yayi barci to sai dai Sarawo kuwa, dan komai ya juye masa, har mamakin abun yake da tunanin koma dai mafarki yakeyine?.
Ya ayyana hakan a ransa yafi sau dubu, harma Mudanseer dake kwance gefensa ya kasa jurewa ya tashi ya fara masa nasiha da shawarwari duk da kasancewarsa yayansa, tare da ha?uri akan canjin da ALLAH yay masa akan Umm-Rumana, inhar yay ha?uri ya ri?e watarana zaiyi dariya insha ALLAHU, ya cire zancen Samina a ransa, ya fuskanci sabuwar rayuwar gida wata soyayyar, kamar yanda itama ta nuna ta manta da shi da komansa.
Yaji daWin shawarar ?anin nasa sosai, dan haka ya samu ?warin gwiwar tashi yayo alwala yazo ya fara nafilfili yana mi?ama ubangiji kuka sa.
Ranar haka ya kwana kan sallaya, sai da suka dawo sallar asubahine ya samu ya kwanta ramuwar barci.


**********

?angaren Samina jinta take sakayau, duk da wani gefe na zuciyarta yana suka akan maganar haWa Umm-Rumana aure da Ahmad, sai dai kuma tana ?okarin kauda abin a ranta baki Waya, musamman yanda jikinta har yanzu babu ?arfi, ga Mama Gaje kuma nata zuga ?o?arinta akan abinda tayi har Ahmad ya saduda ya saketa.
Ranar dai da tsantsar farin ciki tai barci, kusan raba dare sukai tana hira ita da Ma'aruff a waya, kowa na ?ara jadadama Wan uwansa irin ?aunarsa da yakeyi cikin zuciya da ruhi.

Umm-Rumana kam batasan bikin da akeba a kanta, dan babu wanda ya sanar mata da komai, ko mahaifiyarta batace mata komai akan maganarba.
Amma batayi ba?in ciki akan aurar da Wiyarta ga Ahmad ba, dan kowa yasan mutumin kirkine, bashi da wani mugun halin da za'ace abin gudu a rayuwarsa, to mizaisa tayi ba?in ciki da hakan, tunda har mahaifin Umm-Rumana da kansa yaga nagartar Ahmad yakuma ji a ransa zai masa halacci da Wiyarta, fatan alkairine kawai nata da musu ?ya?y?yawar addu'ar zaman lafiya.


___________________________

Babu wanda yay tsamanin a ranar za'a sake Waura auren, sai gashi kusan ?arfe goma sha Waya na safe motocin ?an shema har huWu sun dira maza da mata, dandanan gidan ya kacame da hayaniyar ?an bikin da sam babu shiri, hakama dangin Ammi mahaifiyar Umm-Rumana sun cika gidan, dangin gwaggo ma haka na kusa sai Sullowa sukeyi ta ko ina, to abinka da maganar waya.
Duk wannan abu dake faruwa Ahmad bai saniba, sai da Mudanseer ya tadashi akan ya tashi lokacin salla yayi, mamaki ya kamashi lokacin daya shigo yaga gidan a cike.
Babu kuma wani Soye-Soye Ayyah ta sanar masa aurensa za'a sake Waurawa bayan sakkowa masallacin juma'a da Umm-Rumana.
 Ayyah da wuri haka? Nazata ai za a bari sai nan gaba ta kammala makarantarta .
 Haba Wan albarka, minene wani abin jinkiri anan, Rumana dai ai ta isa aure, kuma ba ba?uwarka bace balle kace kanason sanin halayenta, kaima ba ba?onta baneba, idan batun soyayya ne kuje can a gidanku zaku ?ullata, tamafi ta shirmen wajen nan daWi da nagarta, makaranta kuma duka wata nawa ya rage, idan taje gidan naka saita karasa ai, muma munfison ayin kawai hankalinmu ya ?wanta, dan nafison ka riga yarinyarnan yin auren, muyi addu'a kawai ALLAH yasa haka shi yafi alkairi, maza je kayi wankan ga waWannan kayan saika saka .
Jiki a sanyaye ya amshi farar shaddar dake a cikin leda viva yay mata godiya..........
'






*_ALLAH ya gafartama iyayenmu=?-?=?O?
07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*=?O?
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuoeSgXuo


*(10)*

............?arfe biyu da rabi na rana Wunbin jama'a suka sake shaida Waurin Ahmad akaro na biyu tare da Umm-Rumana, akan sadaki naira dubu ashirin.
Kansa kawai ya du?ar ?asa yana haWiyar zuciya, wai shine aka Waurama aure a karo na biyu cikin kwana uku kacal, sannan kuma bada Saminar sa ba, wadda ya Wauki dukkan buri ya Woramawa, dukkan rayuwar aurensa da kullum yake tsarawa a zuciyarsa da itane, amma yau gashi ta nuna masa data zauna dashi gara ta kashe kanta ko shi ta kasheshi.
Kenan yanzu da Rumana zaiyi rayuwar aure? Yarinyar da bai taSa mata cikakken kallon minti biyarba duk da a gida Waya suka tashi, shi zaima iya rantsuwa bai taSa maganar data kai kalma Wari da itaba cikin lokaci Waya, tsakaninsa da ita a kullum gaisuwa ce, saiko aike, shima sai idan wani dalili yasa ta gitta ta gabansa ne........
Da ?yar ya iya haWiye abinda ta toshe makoshinsa, ya Wago kansa saboda dafansa da akayi a kafaWa.
Baba Iliyasu dake kansa tsaye yay masa nuni akan ya mi?e, babu musu ya tashi tsaye, kama hannunsa kawun nasa yayi har zuwa gaban jama'ar shema, nanfa Ahmad ya shiga gaishesu cike da girmamawa, saboda yasan dayawan cikinsu dukda bawani sosai ma yake zuwa Shema Winba.
Atare suka rankaya zuwa cikin gida, inda aka baje musu tabarmi a zaure suka zauna cin abinci, shi dai Ahmad baici komaiba, yana gefe abin duniya duk ya gallabesa, sai sauke ajiyar zuciya yake a jere a jere.
Bayan sun kammalane sukasa aka kawo musu Amarya Rumana, wadda tun a safiyar yau mahaifiyarta ta zaunar da ita cikin hikima da nasiha ta sanar mata abinda ake ciki.
Tasha kuka, amma tasan ko giyar wake tasha bazata bijirema iyayenta ba, dan ba wannan tarbiyyar mahaifiyarta tai mataba, fargabarta Waya tayaya Yah Ahmad zai sota? Mutumin da baya kallon kowacce mace da arzi?i inba Samina ba, ita kaWai ke ganin fara'arsa, ita kaWai ke iya jin doguwar maganarsa, ita kaWai tasan sau?insa.
Sukam da ko wasa bayayi dasu, iyakarsu dashi su gaisheshi ya amsa, saiko idan hanya ta haWaku ya aikeka idan da bukatar hakan, ko Winki zai musu baya tsayawa jin style Win da suke bukata ko wani ra'ayinsu.
Nasihar da mahaifiyarta da ?an uwanta sukai mata ce ta sata sake Wammarar sakama ranta ha?uri, koba komai zata zama sanadin dai-daita barakar dake neman shigo musu a family, sannan zasu hana fitar ha?oran ma?iya da sunan musu dariya, bakin ?an bani na iya zai rufe ruf wajen maida yanda akayi.
Kanta a ?asa ta rufe fuska sosai da gyalenta ruwan hanta da akaima kwalliyar ruwan madarar les a baki suka fito, tana sanyene da atanfa ruwan madara mai ?yau, kayantane na salla da Ahmad yay musu Winkin ita da su Samina, kasancewar babansu ne yay musu kayan, dayake sawa biyu kawai tai musu sai kayan suke fes tamkar sabbi, sai ?amshi take mai sanyi.
Inna marwa dake ri?e da ita tai mata izinin ta zauna, dan sun iso soro inda ?an shema suke.
Tun shigowarsu kuma Ahmad yake binta da kallo ?asan ido, wani iri yakeji a zuciyarsa game da wannan auren.....
Nasihar da ?an uwan nasu ke musu ta sashi katse tunaninsa ya maida hankalinsa garesu.
An musu nasiha mai ratsa jiki, wadda duk ta kuma sanyaya jikin Ahmad, harma da ita Rumana Win, dan koba komai ta fahimci wannan auren nasu farin cikin mutane masu yawane, sannan kwaranyewar hawayen mutanene masu Wunbin yawa da Samina taso sakawa kuka.
Bayan an gama musu nasiha kakanni da abokan wasa suka koma tsokanarsu, yayinda wasu acikin ?an uwan ke karesu, dansu duka babu mai bakin ramawa, bare dama daga Ahmad Win har Rumana dama basu da yawan magana.

Bayan sallar la'asar ?an shema suka juya zuwa gida, tunda bikine bana shiriba suma basuzo da shirin kwana ba, mutum huWu kawai aka bari suma tsoffine.

Tafiyar ?an shema tasa hayaniyar gidan raguwa, hakan yasa Ahmad shigewa Wakinsu ya cire kaya ya ?wanta saboda zazzaSin da yakeji sosai, har ya fara rawar sanyi ma.

Daga cikin gida kuwa babu wanda yasan halin da ake ciki, dan sunata shirin kai amarya Wakinta, kayan Samina da aka kaine za'a barma Rumana Win, tunda dama babu ko cokalin Mama gaje acan, duk dangin su Ahmad Winne suka tara suka kai.
?an kayan da Ammin Rumana ta fara tarawa na auren Rumana Win aka fiddo ake Wan wankewa, dukda bana kirki bane zasu taimaketa ko yaya dai.
Duk bikinnan da akeyi fa Samina na gidan, saboda ta nuna abinma bai dametaba komanta yinsa take kai tsaye a gadarance a gidan, hakama Mama gaje, har dariya takema Ammi akan haWin auren Rumana da Ahmad, wai saji sa gani, nan za'a ringa ?ullar tuwo a kwano ana wucewa dashi gidan Rumana, dan sunsan dai Ahmad bashi da abinda zai ri?e Rumana.
Babu wanda ya kulata akan zancen, dan kowa kwllon wawuya yake matama yanzu, daga ita har ?ar tata.
Gefe kuma ga munafukan Soye irinsu Umma (Sailuba uwargidan baba Iliyasu, aminiyar Mama gaje a gidan idan baku mantaba) dan tana Waya daga cikin mai tunzura mama gaje da Samina akan auren Ahmad, bayan itama akwai sangamemiyar budurwa a gabanta Salima, dan sa'arsu Rumana Wince, tarema suka tashi su uku tamkar tagwaye, Umm-Rumana, Fa'iza ?anwar Ahmad, sai Salima Win.

Ayyah da bataga giccin Ahmad ba tunda aka dawo Waurin aurene abin ya dameta, dan haka ta aika a duba matashi ko yana ?ofar gida wajen abokansa.
Koda Abu yaje ya tambayi su Rabilu sai sukace aisu tunda aka dawo daga Waurin aurenma basu sake ganinsaba, sun zata yana cikin gida yana wani abun.
Babu shiri Ayyah ta fito zuwa Wakinsu Ahmad, saita iskeshi yanata rawar Wari a bargo, hankalinta ya tashi sosai, tasaka Abu ya kira mata Baba Hamza.
Tunda baba yaga halin da Ahmad yake ciki sai tausayinsa ya kamasa, sunata jera masa sannu shi da Ayyah, a Soye ba tare da kowa ya saniba Mudanseer ya kira wani mai aikin asibiti anan kusa dasu ya duba Ahmad Win.
Bai Soye musuba ya sanar musu damuwace tai masa yawa, shine harta haddasa masa zazzaSi, dan baya samun isashshen barci ma, ga malleria kuma a gefe itama.
Magunguna ya basa, yace yaci abinci sannan yasha ya kwanta danya samu isashshen barci.
Har Ayyah ta kawo masa fura yasha da ?yar, zata bashi maganin baba ya dakatar da ita akan ta barshi ba yanzuba, tunda likitan yace akwai na barci suWan Waga ?afa zuwa anjima, dan Malam yace yau za'a kai Rumana, to kenan bayasha magani yay barci a nanba kuma, bayan an kaita sai yasha yatafi can ya kwanta.
Dole Ayyah tabi wannan umarni na mijinta, suka bar Ahmad, sai dai ruwan Wumi da aka kawo masa yay alwala yay sallar magriba da isha duk a Waki, lokacinne kuma Ayyah ta sawo Gwaggo gaba a Soye tazo ta duba Ahmad Win.
Sannu tai masa sau Waya ta Wauke kanta sai kace bata damuba, nanko ranta sai suya yake da halin da yaronta ke ciki, amma kawaici ya hana agani koda a fuskartane.

Kusan ?arfe tara aka mika Rumana da tasha kuka tamkar hawayenta zasu ?are Wakinta, tasha nasiha a wajen iyayenta da dangin mahaifiyarta, malam ya bata ?yautar da ko ita batasan minene a cikiba, hakama Iya ta bata.
Duk wanda yaga yanda take kuka saita bashi tausayi.
Haka suka mikata, basu wani jimaba suka barota tana cigaba da sharSar kukanta.

Tunda Ayyah taga ?an kai amarya sun wuce tazo ta tada Ahmad, da ?yar ya iya tashi ya watsa ruwan zafi da Ayyah ta Wumama masa, Abu yakai masa bayi, bai wani jimaba ya fito, jallabiya kawai ya bukaci a basa ya saka, dan haka Mudan ya fesheta da turare sannan ya bashi.
Baice komaiba ya saka, Ayyah tai zaman lallaSashi yasha magani, da ?yar yasha kuwa yana tsuke fuska da yamutseta, harda yun?urin amai saboda tsanar da yayma magani.
Suka dai samu ya haWiye duka da kyar.
Nasiha Ayyah ta sake masa da baba, kafin Mudanseer ya rakoshi inda Sufyan ke jiransa da mashin.
Shine ya Waukesa ya kaisa gida, kafin suje sai rawar sanyi yake, yanata sake ?udundune hannunsa a ?irji, ga jiri na Wibarsa sabida rashin ?warin jiki.
Dole Sufyan ya taimaka masa har cikin gida, yay sallama a ?ofar Wakin Umm-Rumana da har lokacin take zaune tana kuka ta amsa.
Izinin shiga Sufyan ya nema, ta bashi sannan ya shiga ri?e da Ahmad cikin Wakin.
Babu shiri ta mike tana kallonsu a firgice, dan sam batasan Yah Ahmad baida lafiya ba, da taimakon Sufyan Ahmad ya kwanta saman gadon, Sufyan ya mikama Rumana ledar maganin Ahmad da kazar da suka saya musu da lemon Sawo sai kankana.
 Amarya kiyi hakuri, angonki ya shigo miki ba yanda kowanne ango ke shigoma amryaba, bashi da lafiyane, muna fatan zaki kula mana dashi nanda kwanaki kaWan ya dawo mana Ahmad Winsa jarumi mai yawan juriya da kowa ya sani, ALLAH ya baku zaman lafiya da zuri'a Wayyaba, ya kara muku hakuri da fahimtar juna, ya dasa muku soyayyar juna a zukatanku mai karfi daban mamaki da kwatance

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login