Showing 63001 words to 66000 words out of 87750 words

Chapter 22 - GUDU DA WAIWAYE bilyn abdull

29 Jun 2024

13343

 Wlhy A'a yaya, dan ALLAH kayi ha?uri bazamu sakeba .
Mudan dake shigowa ta bayansu ya tallare ?eyar Sadiya dake farko shima yana masifa,  Yah Ahmad karka wahal da kanka ai tun acan saida na basu maruka bibbiyu marasa mutuncin .
 Oh kace kainema kaje ka taho dasu? cewar Ayyah.
 Wlhy kuwa Ayyah, tun kusan takwas nake zuba idon ganin sun dawo amma shiru, har tara shiyyasa nai azamar ?arasa Winkin danake nabisu har can, sun mi?e ?afafu sam basuma da alamar tahowa .
?wafa Ahmad da takaici ya isa yayi, ya nunasu su duka yana faWin,  Wlhy daga yau wanima cikinku ya sake zuwa fatin saina kusa halakashi a gidannan, ?an iska kuwuce kuba mutane waje kawuna kamar she?ar angulu .
Da gudu suka shige Wakin Gwaggo dake saurarensu daga ciki, babama duk yana jiyosu, ya kumaji daWin yanda Ahmad da Mudanseer sukai musu, baida haufi akan tarbiyyar ?a?ansa, koda baya numfashi su Ahmad garkuwar ?annen sune.

Ganin iskar hadari ta fara tasowa Ayyah tace,  ?an albarka maza gida kafin wannan ruwan ya sakko kaji, ka gaida Wiyar tamu .
Sallama yay musu ya tafi, bayan ya le?a yayma su Iya ma sallama, wadda ta bashi wani abu a robar swan tana faWin,  Ungo wannan ka kaima Rumana, tashashi yanzu kafin ta kwanta .
 To Uwargida ran gida za'a bata ta gode, amma minene haka kamar zuma? .
 To shugaban matambaya ba zuma bace, maganin shawarace da naji su Salima nata ?orafin bata gajiya da kwanciya, shiyyasa na haWa matashi kartazo wajen taron nan taita langaSe-langaSe, tasha kamar kashi Waya bisa huWu .
Dariya Ahmad yayi yana cewa,  Oh kajimin iya, kina nufin matata raguwace dai kawai a fakaice?, karki damu nan gaba kaWan ?ofar gidannan saita mata kasaWan .
 Dako nayi farin cikin hakan Wan ?wal uba kawai, kaima ai gakanan ka Wakko sanwar fara kiban kamar iliyasu .
Fita Ahmad yay yana dariya Malam dake kwance yana tayashi.

A waje yay sallama da abokansa dake shirin shigewa gidajensu, ya tari Napep zuwa gida saboda harma an fara yayyafi.
A lokacinne kuma motocin su Samina ke isowa, da alama dai lokacin aka tashi daga kamun nasu da yasha banban dana saura.
Dan kowa dai yasan da yamma ake kamu tare da dangin amarya, dangin mijima ?alilan suke zuwa, to ita nata dangin mijin sunfi yawa, danginta WaiWaikune iya ma ?an uwan mama gaje ne, sai tarin ?awayenta.............
'


_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* =؋?d'?NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* =؋?d'?NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* =؋?d'?SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* =؋?d'?NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* d'?=؋?NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN=?G?=?G?_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin=?G?=?G?
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*=?G?=?G?

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuWi gida masoyan asali=? ?=?;?>?p?>?p?=?
?=?
?=??=??=?L?

Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN=??=?I?



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=?-?=?O? [7/27, 6:06 PM] Sis Hajiyyaye: *ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

*Ko kuma*

09032345899


*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*=?O?
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo


*_GDW_*



*(19)*



..............Tun su baba na saka ran dawowar Ahmad a kusa har abin ya fara basu tsoro, dan kuwa gashi ya shiga wata na huWu da tafiya.

Wata ranar alhamis Ahmad Win ya shiga wani shago na masu sai da yari, saboda kiran da mai shagon yay masa zai wanke masa takalmi, dan yanzu ya gama sanin gari ba tare suke yawo da Nura ba, kowa yana fita neman nasane, da yamma su haWu a inda suke zama, zuwa dare su wuce wajen gadinsu.
Tunda Ahmad ya zauna wanke takalmi mai shago ke binsa da kallon ?urilla, tun Ahmad bai fahimta ba harya fahimci kallon da mai shagon ke binsa dashi.
?an Sata fyska yay, hakan yasa mai shagon yin murmushi, yace,  Na dameka da kallo ko? kayi ha?uri, mamaki nike kamarka fine Boy da wannan sana'ar .
Ahmad dai baice komai sai murmushin yake da yay, harya kammala ya tattare kayansa zai wuce mai shago ya mika masa Wari biyu yana faWin,  Inda zaka yarda dana koya maka wannan sana'ar tamu ta yari? .
Shiru Ahmad yay yana kallonsa cikin nazari,
Mai shago ya sake cewa,  Karka zurfafa tunani ?anina, haka kawai haWuwar jini ta sakani maka wannan maganar duk da kuwa yauce rana ta farko dana fara ganinka, amma dai kamin kamanni da bakatsinen barume hakanne ya sakamin ?aunarka ta musamman, idan har ka aminta zakayi na baka dama ka samo jarinka kazo insha ALLAHU zan taimakeka .
Kai kawai Ahmad ya jinjina ya fita bayan ya amshi kuWinsa.
Koda ya koma ya sanarma Nura sai yay murna, yakuma bashi ?warin gwiwar karSar tayin Alhajin, dan acewarsa wata damace dasu basu samuba tazo masa dukda bai jima da zuwa garinba kuwa. Amma maganar jari ya jira wanda sukema gadi ya biyasu sai yayi amfani da kuWin.
Ahmad yaji daWin shawarar Nura, dan haka ya aminta sosai, washe gari yaje ya sanarma Alhajinnan komai, Alhaji ya amsa da babu komai shidai yana jiransa.
Kwanaki goma dayin haka suka jira a basu albashi shiru, har ha?urinsu ya ?are sukaima mai wajen magana, amma ?iri da muzu ya hanasu yama yi musu korar kare.
Wannan abu ya saka su Ahmad a takaici, harya hanasu talla a wannan ranar sukai yinin ba?in ciki.
Da abokansu suka dawo daga tasu sabgarsu suma sai suka sanar musu, suma ransu ya Saci, nanne wani ke basu shawarr idan zasu iya aikin sauke kaya suzo suje, shi mutumin kullun yake biya adadin kuWin aikin da kayi.
Da farko Ahmad ya musa, amma da Nura ya lallashesa saiya yarda washe gari sukaje.
Wajene kamar kamfani, ana kawo kaya sukuma za suke jigilar saukewa daga motar zuwa store. A sati ana sauke kayan sau biyar ne.
Duk da wahalar dake cikin aikin haka Ahmad ya dage, bayan sun kammala na ranar kuwa aka biyasu ha?insu, sunsha ciwon jiki saboda rashin sabo, dan da?yar sukai barci ranar, amma daWin kudin da aka biyasu ya saka washe gari suka sake komawa.
A hankali sai gasu sun zama ?an gida, dan kuwa harma sun saba komai anayi dasu na harkar dako a ma'aikatar.
Duk kuWin da suka samu Ahmad kan kai nashine wajen Alhajin nan yana tara masa, a randa suka cika sati na huWune kuma sai kawai ogan wajen ya basu sanarwar duk wanda yazo gobe yaga sunansa an kafe to karya sake zuwa aiki, an koresa kenan
Hantar cikin su Ahmad ta Wuri ruwa, dan kuwa suna samun alkairi a wajen babu laifi.
Washe gari duk a cikin damuwa sukazo, sai yazam gaba Waya waWanda aka cire hausawan ne, kukane kawai Ahmad baiyiba, suna shirin tafiyane kuma matar mai gidan ta dakatar da Ahmad, acewarta wanan ?ya?y?yawan babu inda zaije, dole ogan ya maida sunan Ahmad kuwa.
Duk da yaji dadi ya nuna damuwarsa na rashin Nura, haka ya cigaba da aikin har tsawon sati huWu sannan ya bari saboda yaga dai Alhmdllh yaWan tara wani abu da zai ishesa jari.
Lokacin da zai wucene sai matar ogan ta nuna rashin jin daWinta, hakan yasa tai masa tayin gadi a gidansu, zasu kuma bashi Wakin mai gadi ya zauna.
Nanma bai bata amsaba sai da yazo ya shawarci Nura, Nura kuwa ya bashi kwarin gwiwa akan hakan.
Ahmad bai amsa zaiyiba sai da ya koma wajen Alhaji aka fasa asusun kudinsa na dako da ya tara Alhaji ya haWa masa kwabar ?an kunne ta hannu, aka zuba kaya dai-dai kuWinsa sannan, ya bashi tare da sanar masa dabaru akan sana'ar.
Daganan kuma ya koma ga ogansa ya sanarma matar zaiyi gadin, amma zaike zuwa sana'arsa da rana.
Babu musu suka amince, a cewarsu aiba zaman gidanma sukeba da ranar.
Tundaga wannan ranar rayuwa ta sake sauyama Ahmad, dan kuwa a cikin watannan gaba Waya saiya cinyesa a yawon tallar ?an kunne da gadi, koda ?arshen wata yay yaga yaWan farfado sai ya fara tunanin zuwa gida, lokacin yanada wata shida cif a garin porthercout.
Babama har yayi fushi da rashin zuwansa ya ha?ura yabar masa magaba.
Tun daga randa yay aniyar zuwa gida yaWan fara sayen tsaraba yana ajiyewa wadda zai fuskanci gida da ita, haka kawai kuma sai yakejin Wokin ganin Umm-Rumanan sa.


_________________________________

Zuwa wannan lokacin maganar Ma'aruff ta shiga gidansu Samina, yayinda alakarsu ta sake ?azanta sosai, dan tunda aka tsaida bikinsu wata biyu kacal sai yazam babu abinda Ma'aruff ke burin samu daga gareta sai jikinta.
Har takai dai yau yaci galabar rabata da budurcinta a gidan gonarsa, tasha kuka iyakar iyawa, shiko ya katsatstsareta da lallashi da daWin baki akan ai babu komai tunda shine zai aureta, kuma bikin nasu duka saura wata Waya ne kacal ai.
Tun tana kuka da ?arfin zuciya har ta aminta da daWin bakinsa, ya tainaka mata ta gyara jikinta, tare da saka abokinsa ya kawo mata magunguna da allurar rage raWaWi, ya kuma kaita Shop rite yay mata shopping na hauka da bai taSa mata irinsaba, ya maidota hargida tare da bata ma?udan kuWi.
Mudanseer dake shago Shi da Abu yana kallon yanda Ma'aruff keta saukema Samina kaya niki-ni?i, baki kawai ya taSe ya Wauke kansa danshi yanzu babu abinda ya damesa da ita.
Maimakon lokacin da aka shiga da kayan Mama gaje ta fahimci halin da Samina take ciki sai idonta yafi karkata ga manyan ledojin.
Duk uwa mai hankali aka taSa mata yarinya, kuma yarinyar ta dawo gareta a randa abin ya faru dolene ta fahimci akwai matsala, dan duk macen da aka raba da budurci komai tsahon shekarun da take dashi babu aure wlhy sai taji daban, idan ko babu aurene fargabar fara yinta bata hanyar daya daceba koda itace takai kanta saikin sameta tattare da ita, iyaye kalubale ne agareku, dan yanzu har sai ?aton banza ya gama lalata miki ?a a waje ta Wau ciki ta zubar bama ki saniba saboda sakaci da sakarci kosan duniya irin namu.
Da wannan damar rashin kulawar tamu samari keta lalata yara ta yanar gizo da zahiri ba tareda kun fargaba, damuwarki kawai ki gyarama mijinki kanki dacin kwalliyar tafiya biki domin ki birge mata ?an uwanki, idan kishiyace dake hankalinki na kanta, saikiga ?anin uban yarinya ko ?aninki ko wani na kusa daku ya gama warware tufkar tarbiyyar da kukayi kina nan shatata da baki, sai rashin mutunci ya saka saurayi sakin videon baWalar da yay da ?arki a yanar gizo ki haukace har takaiki da faWawa wani hali ki kamu da ciwon hawan jini kona zuciya, bayan kuma kinbar gini tun ran tubani.
A tunanina duk uwa datasan ?arta budurwa nada wayar yakamata tazam mai saka mata idanu akan wayar, kodama bata da ita ki saka mata ido tunda akwai ta ?awaye.
Tanan suke shiga yanar gizo su haWu da ?an iskan facebook, ko istagram, ko litatafan batsa dake yawo a kowacce irin kafa ta yanar gizo, ko ?awa ta sakata a group da sunan group Win matan aure wanda idonsu ya rufe basajin tsoron ALLAH duk abinda yake haramun shine abun kallonsu, wanda yake haramun shine abin furtawarsu da jinsu a zuwan wai koyan rayuwar aure, ke wane kidahumancin ya baki tunanin sai an Wakko shaiWancin tsiraicin wani kin ganine zakisan yanda zaki rayu da mijinki?, wlhy matan aure kaiconku da wannan wawancin mai toshe ?ofofin hasken zuciya da kashe gani.
?ammata da yawa daga shiga irin waWannan groups suna canja suna komai ke fara tabarSare musu, idan k uwa ba?ya bibiyar lamarinta daga haka sai kiga komai da kika gina ya tarwatse.
Wlhy kuzama masu kulawa kafin ku riski ranar kuka da nadama akan ?a?anku, domin sai ALLAH yay miki tambaya dalla-dalla akan tarbiyyarta.
Wannan sakacin ne ya hana Mama gaje fahimtar komai akan Samina har Ammin su Umm-Rumana ita ta lura, ba ?aramin ruWani ta shigaba, sai dai tana tsoron tace wani abu aga za?ewarta.
Samina kuwa kwanciya tai wahala ta sakata barcin dole, bata tashi farkawaba sai bayan sallar magriba, agaban mama gaje ta dafa ruwan zafi taje tai wanka dashi ta sake gasa jikinta kamar yanda taga ana cewa a novels, koda ta fito sama-sama taci abinci ta sake kwanciya, kobi takan kayan da mama gaje ta baza a Wakin bataiba saboda ita tasan wahalar da taci kafin ta samo kayan.

Haka Samina taita jiyyar jikinta har kwana biyu, ko Waga wayar Ma'aruff batayi idan ya kirata saboda haushinsa da takeji, amma taji daWin yanda ya nuna damuwarsa a kanta, sai turo mata massegea yake kamar hauka, wannan yasa a cikon kwana na huWu ta kulasa.
Yako kalailayeta da daWaWan zantuka ranar, haryaci galaba a kanta tafito makaranta taje Office Winsa ta samesa, acan yakuma lallaSata ya ?ara na biyu, ranarma taci kuka dan tasha wahala, amma daya lallaSata da mayaudaran kalamanasa saita goge hawayenta saboda ta yarda dashi.
Tun daga wannan ranar ya maidata kamar wata matarsa, a gefe kuma yanata sakar mata kudi itada ?awayenta suna shirin biki. Sati na biyu da kauda mata martabarta aka kawo lefenta daga gidansu ma'aruff akwati ashirin da huWu cif, tare da katuwan jakkuna uku manya-manya, Waya na babanta, Waya na Mama gaje, Waya na danginta.
Ranar dai kam su Ayyah sunsha kallo, sun kumasha gori wajen mama gaje da danginta, ?an anguwa kam ai kamar sa fasa gida kallon kaya, harda ?an gayyar soWi, dan ko su Maman Ama sai gasu sunzo ganin ?waf daga jin su Salima na sanarma Umm-Ruman cewar gobe za'a kawo lefen Yaya Samina.
Shine mutanenku sukai shiri Rumana bata saniba sukazo wai yimata kara tunda ita har yanzu bata fara zuwa gidaba baba Yusha'u ya hana, yace tai zamanta har Ahmad ya dawo ya bata izinin hakan, makaranta kawai take fita, shima kuma jarabawama suke zanawa ta ssce.
Ranar su Nafy ?awayen Samina haka sukaita yawo da wannan lefe a social media, yayinda ya tadama ?ammata da yawa hankali da fatan suma sai an musu irinsa koma wanda ya fisa.
Harda masu takaicin inama sune, irinsu Kausar.
Koda sukaje suna bama Rumana labari tasha mamaki, dan ita bama ta kawo can sukajeba, amma sai batace dasu komaiba akan hakan dukda taji haushi.


_________________________________


Baba ne ya gindayama Ahmad sharaWin ya tabbatar yazo gida anyi bikin Samina dashi, tunda shine namiji babba a gidan bai ?yaitu ace baya nanba.
Dukda baiso hakaba dole yabi umarnin baba, tunda yanzu dai Alhmdllh, duk da bawasu ma?udan kuWi ya samuba babu laifi tafiya tai riba, dama kuma ya gama shirinsa tsaf.


&&&&&&

Umm-Rumana duk da bata da tabbacin zuwa gidan bikin haka ta wanke kanta Salima ta yarfa mata kananun kitso, suka kawo ?awarsu har gida tai mata ?unshi mai ?yau, haka kawai ta tsiri juya fasalin Wakinta.
Tako tsare su Fa'iza suka tayata, komai suka canja masa muhalli ya koma kamar wani sabon Waki, aranar kuma su Samina ke shirya fatin ?unshi a wa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ni haWaWWen hotel tsadajje.
Su Fa'iza duk sun gudu sunbarta ita kaWai a gidan, dan haka bayan tai wankanta tai kwanciyarta tana kwasar barcin gajiyar aikin da sukayi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login